ya faru ita da danginta kamar si goya mu. Itama in ta shiga damu dangin haka za ta daraja su. Maganar gaskiya sai dai ƙin gaskiya amma Rabi'atu tana da hallaya mai kyau. Ta bakin Gimbiya ta kan ce an yi ma Yallaɓai surkullrn yan maiduguri ya ruɗe kan yarinya na kan yi dariya na ce ba surkulle sannu ciwon kai ne kawai.
Mun yi babbar salla Rabi'atu ba lafiya ashe ciki ne. Yallaɓai kamar bai taɓa haihuwa ba Gimbiya baƙuwa a harkan mu ai mun zama yan gari. Haka yake kiran waya yana faɗa ma mutane Rabi'atu na da ciki. Tarewa gabada ya yi a bamgarenta yana kula da ita tun da laulayi take yi mai zafi, Ni ko duk abin da yake so a yi masa ni zai kira itama in tana son wani Umma kaza Umma kaza, na roƙi Allah ya cire mini kishin nan na hauka shi ya sa da ni ake renon cikin Gimbiya ko sai dai kuka a ɓoye in ta yi magana cibi ya zama ƙari lokacin da ya tare a bangaren ta yi magana da cewa ai muna gida ɗaya ba sai ya tare a wajemta ne zai kula da ita ba buɗe bakin Yallaɓai sei cewa ya yi ya tare ɗin sai ta hana shi ganin ya harzuƙa ya sa na shiga tsakani na lallaɓa shi ita kuma Gimbiya na ce mata ta yi bamza da shi duk abin shi dai ba zai dauwama a wajen ta ba.
Gimbiya faɗa mini take yi ba za ta iya jarumta na ba. Ba za ta iya juran ganin Yallaɓai na rawan jiki akan wata na da ciki ba. Na ce gwara ma ta saba domin yanzu aka fara. Wataƙila bayan Rabi'atu ma ya ƙaro wata itama ta zo tana gasar haihuwar to ya za ka yi in ba ka yi haƙuri ba?
*Janafty*
*TKG320B*
*Littafin TURKEN GIDA 1K ne on Telegram. 09069067488.*
Kina buƙatar kayan kitchens domin ƙawata Kitchen ɗin ki? Ya ke Uwargida kina buƙatar chanza ma megidan sabbin kwanukan cin abinci? Ko kina buƙatar sauya masa kofin shan ruwa? Ko kina so ki burgeshi da farantai masu kyau da yarari? Ko Amarya ce yar ƙwalisa da ke son ƙawata gidanta da kayan alfarma? To ku matso kusaa domin JANAFTY EXLUSIVE AVAILABLE Muna kawo muku ko wani nau'in kayan Kitchen da na kwalliya gida domin farincikin ku, kuma akan farashi mai rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina daga in da muke, ku tuntuɓemu ta wannan lambar domin ƙarin bayani.
09069067488
+234 706 234 9732
Rawan jiki da ɓare-ɓare kam Yallaɓai na yin shi a kan cikin Rabi'atu ga shi cikin na ta ya zo da laulayi ga shi ba ta son cin abinci in ku ka ga yadda Yallaɓai ke lalacewa a gaban yarinyar sai kun yi mamaki. Ni kuma duk abin da ta ce tana so haka zai marairace yana roƙo na domin na samar mata, ni kuma tausayi take ba ni ko bakomai nima uwa ce, wani lokacin kuma Baby yake sawa dafe-dafe nan Gimbiya dai ya san ko giwan wake ya sha ba zai tunkareta ba domin ba ma yi za ta yi ba iyakarta da Rabi'atu sannu Allah ya ƙara lafiya.
Kwanciyarta asibiti biyu sannan ta ɗan samu kanta sai da ta koma gida ta yi satuttuka. Antynta ta ɗauke ta ganin wahalan da take sha, Yallaɓai ya so ya hana na dakatar da shi da cewa ya barta a gidansu a kula da ita. Ya bari ɗin amma fa can yake tarewa in ya dawo daga aiki sannan ya dawo gida ya zaunar da ni yana bani labarin in na ga Rabi'atu sai na yi mata kuka ta rame kaza kaza, ni har gajiya na ke yi kamar a kanta aka fara samun ciki su 'ƴaƴan gidan ba a gaban sa aka samu cikinsu ba daga sama ya gan su, duk dauriyata sai da ya riƙa motsa mini zuciya. Tana gidansu sau biyu yana sakani muna zuwa duba ta ni da yara Gimbiya dai an tashi zuwa sai ta ce ba ta da lafiya duk da ya san ƙaryanta ne ba ya matsa mata sai ni. Ni dai na yi sakacin da gabaɗaya Yallaɓai ya gama raina ni in dai akan lamarin matansa ne ko abu ne ba zai tunkari Gimbiya ba sai ni. Saboda ina yi masa kara shi kuma hakan sai ya bashi damar ya rika cin ko wata kasuwa a saman kaina , yanzu kuma lokaci ya kure mini na yi sakacin da ba zan gyara komai ba tun farko da ban bashi fuska zan iya ɗauka ba da wataƙila nima zai shakkar tunkarata da sha'anin matarsa kamar yadda ya ke jin shakkar tunkaran Gimbiya.
Ba ni kaɗai ba dangin shi ma sun ta sintirin zuwa duba ta zuwan mu na ƙarshe can na ga Halima ta yi baje-baje kamar a falon Nene ban yi mamaki tun fa yanzu ai Rabi'atu uwar ɗakin ta ce. Gimbiya ta ɗauka bayan ita ba wata macen da Yallaɓai da dangin sa za su yi ma rawan jiki saboda samun ciki sai ta ga ma suna abin da ya fi wanda suka yi mata a baya. Sai ta sha mamaki domin tun cikin na ƙaramin sa Yallaɓai ya gama tsara in mace ne ga sunan da zai saka Aisha in namiji ne kuma Alhajinmu zai yi ma takwara zai yi zai yi kaza har na haddace su a kaina.
Gimbiya ta yi ta ƙunci in an yi wani abu da ya bata haushi ta same ni da mganar na gani ko? Na ce na gani mana amma ban nuna na ji ko na gani ba itama in ta yi haka sai ta zauna lafiya. Amma ba ta ji shawarata ba kafin Rabi'atu ta dawo gida sai da suka yi tsiya akan ranar girkinta yana kai wa dare a can. Ta ga fa nima har ranar da yake ɗakina abin da yake yi kenan amma ta na gani ban ma na nuna na gane abin da yake yi ba, amma ita da shegen kishi ta yi masa mgana har tana saka ni a ciki wai na faɗa masa gaskiya ba ya adalci tunda yana jin mgana ta.
"Tana gidan nan ma rashin adalci yake yi mana Maman Jidda. Ba ta gidan ma ba zai daina ba."
Ina zaman zamana a bangarena ta kira ni a waya sha ɗaya saura na dare. Na ji dawowarsa ba daɗewa ni na ma ɗauka wani abu ne ya same shi amma sai na iske shi zaune fuskar nan kamar hadari ya ɗora kafa ɗaya kan ɗaya a saman kujera yana karkaɗawa alamun yau fa akwai masifa in Gimbiya ta cigaba da zungurin sa.
Kallonta na yi, Baiwar Allah ta yi masa kwalliya da fa zafi ka zauna jiran miji har sai ka siƙe sannan zai dawo. Amma yanzu in na ce bai kyauta ba daga ni har ita zai iya cewa mu bar masa a gidansa a yadda dai yake zaman taƙama nan yana kaɗa kafa ji yake yi yana daidai da koma wacece.
"Fisabillahi yana kyautawa? Sai ya je ya shantake? Tun ƙarfe nawa na gama shirina ina jiran shi? Ni ban hana shi zuwa ba amma sai ya yi abin na shi da tunani a ciki.'
"Ok wato kina so ki ce ba ni da tunani ko Saudatu?
Ya faɗa yana daga zaune, a ɗan kuma fusace domin ni fa na daɗe ban ji yana kiran ta da Daughter da ya saba ba itama tuni Daddy ya kama kan shi Babansu Jidda ne ko Abban Khalipa.
"Ni ban ce ba amma dai na ce ba ka yin tunani in za ka yi wani abu."
Kawai sai ya yi wani mirmishi na san in ya tashi magana ba zai faɗi mai daɗi ba ita kuma ta harzuƙa za a iya yin abu mara kyau.
"To ke kiyi haƙuri don Allah. Zuwa gobe in hankula sun kwanta cikin tsanaki sai ki nuna masa in da bai yi daidai ba sai ya gyara."
"Ba zan gyara ba."
Ya katseni a fusace na yi jage ina kallon shi sai kawai ya miƙe kamar zaki ya fara nuna Gimbiya da yatsa kafin ya ce" Ke wai me ya sa kin raina ni ne! Komai abin kishi ne a wajen ki? Rabi'atu ba ta da lafiya na je gidansu na dubata na shigo kin yi tunanin ki ce mini ya mai jiki.? Matata ce fa ke kuma y'ar uwan ki ce fa?
"Aa ni wallahi ba yar uwata ba ce. Ta tsaya iya dai matsayin matarka dai."
Ta faɗa har tana ɗaga masa hannu sai ya yi wani slow kafin ya cigaba da faɗin"Ok yanzu na ma gano ki. Duk wannan ihun da kike yi cikin ne baki so ta samu ba ko?
Ta buɗe baki za ta yi mgana ya hanata ya ɗaga mata hannu yana cigaba da faɗin" Ba sai kin yi magana ba na gano ki baƙinciki ne da hassada dankare a zuciyarki. To bari ki ji na faɗa miki haihuwa yanzu Rabi'atu ta fara sai dai ki mutu wallahi"
"Haba Yallaɓai."
Na faɗa saboda na ga kalaman na shi sun yi tsauri amma sai ya juyo ya balla mini harara kafin ya ce" Ki yi mini shuru kema ai zan iso kan ki."
"Topha"
Na faɗa a zuciyata me kuma na yi?
Gimbiya ta ba ni tausayi ta jawo ma kanta cin mutumci Yallaɓai haka yake ta jifanta da manganganu wai ita kaɗai ce matarsa! Ni me ya sa ban taɓa masa ƙorafi ba sai ita daga dawowarsa ta san abubuwan da suka faru da shi yau? Ta san wani hali ya yini a ciki ba tarba ba kalamai ma su daɗi kawai ta zaunar da shi tana challanging ɗin sa a kan mganar banza! To wallahi in ya ga dama sai ya kwana a duk in da ya ga dama kuma ba wacce ta isa ta hana shi.
"Allah ya ba ka sa'a ka koma gidan su Rabi'atu a ba ku ɗaki sai ka riƙa kwana "
Gimbiya ta faɗa tana tsane hawayen baƙin ciki. Ba ita ba ni kaina wallahi na ji zafin mganganunsa haba wai kamar Yallaɓai ya fara haukacewa.
Ni ina ta tsoro ma kar su Khalipa su ta so.
"Ina ruwan ki? In ma a hotel zan ɗauke ta mu je mu kwana wannan duk ba damuwarki ba ce. Matata ce."
Da na so ba zan ƙara mgana ba amma ganin lamarin ya fara lalacewa shi ya sa na sake mgana.
"Don Allah Yallaɓai ka yi haƙiru ke ma Gimbiya ki yi hakuri ku bar mganar nan. Dare ne kar ku ta shi su Khalipa."
Ita dai Gimbiyar ta yi shuru tana ta jan majinar kuka shi ko uban gayyar komawa ya yi ya zauna yana huci shi kaɗai da man ina tsaye ne ban zauna ba sai na ce" Sai da safe"
"Dawo nan kema"
Ya kira ni a ɗan zafafe, ni fa ban san me na yi masa ba amma na fahimci ba mganar Gimbiya ba da man yau a fusace ya shigo ita kuma kishi ya rufe mata ido ba ta gane ba ta je ta taɓo shi.
"Na'am kana kirana ne?
Wajen zama ya nuna mini a kujeran da ke gefen shi ta zaman mutum ɗaya sai na zauna ina jiran na ji ni kuma me za a sauke mini?
Gimbiya ya kallah kafin ya ce" Da kika kira Sadiya ita ɗin uwa ce ita! ?
Daga ni har Gimbiya sai da muka kalli juna sannan muka dawo muna kallon shi saboda mamaki.
"Zugwai-zigwai kin ɗaga waya kin kirata na ce ita din Nene ce?
Dukkan mu mun kasa mgana daga ni har ita saboda ba mu da abin cewa.
"Sadiya ke aurena ko ni nake auran ta? Ni ne shugaba a gidan nan a cikin ku ba wacce ta isa na faɗa muku."
"Ikon Allah"
Na iya faɗa a saman leɓena kamar an turo fa Yallaɓai.
"Kar ki ƙara mini wannan sakarci muna mgana ki je ki kira mini wata wallahi in kika ƙara ranki sai ya ɓaci na ma faɗa miki."
Ya faɗa yana nuna Gimbiya da yatsa, ni ta kalla sai na gyaɗa mata kai alamun ta ba shi haƙuri.
"Ka yi haƙuri."
Ko sauraranta bai yi ba ya juyo kaina ai ni na yi suman zaune tun da yau Yallaɓai ya ke kirana da wata ai na san kuma sai abin da ya manta.
"Ke kuma ki daina ganin ina jin mganarki ki ɗauka ko wani abu na rayuwata sai kin shiga. Ba ruwan ki da tsakani da kowacce a cikin matana. Ki tsaya in da na saka ki, ni ne mijinki ba ke ce mijina da za a ce komai ya faru ki tasani kina yi mini faɗa kamar wani ɗan ki ba. Ba na so na faɗa miki bana so"
"Ka yi haƙuri "
Na faɗa cikin sanyin murya.
"Ban yi ba."
Shima ya ma yar mini a fusace.
"Allah ya huci zuciyarka."
"Amin."
Ya faɗa a ƙufule kafin ya tashi ya shige bedroom har yana bango mana ƙofa.
Gimbiya ta kalleni kafin ta riƙe baki tana faɗin" Kin gani ko Maman Jidda? Wallahi ba ƙalau yake ba"
Miƙewa na yi tsaye kafin na ce" Lafiyar sa ƙalau. Da a ce kin ji shawara da duk ba ki jawo ma kan ki tozarci ba, nima da ba ki jawo mini wannan jan kunnen da ya yi mini ba. Don Allah Gimbiya ki daina sakani cikin rigimarki. Ba zan iya da Yallaɓai ba nima kina dai ji ya ce ni ba Nene ba ce ina yi masa shisshigi, in dai kin san ba za ki dinga haƙuri da wasu abubuwan ba nima to ki yi ma Allah ki daina saka ni a ciki."
"Ki yi hakuri."
.
Ta faɗa a sanyaye to itama ai ta gani yadda ya zauna yana ta yaɓa mana mganganu.
"Na ce miki ki riƙa kauda kan ki. Ba fa komai ne sai ka yi mgana ba. Ki bar shi ya yi ta kai wa daran mana in kin ga za ki iya jiran shi ki jira shi in ba za ki iya ba ki yi kwanciyarki. Ke in ya ga dama duk ranar girkinta ya je can ya kwana me ye na ki? Gidan shi abin da ya dama shi za mu sha, kuma Allah ai yana sama yana kallon shi cikin mu duk wacce ya danne ma haƙƙi sai Allah ya tambaye shi.
Duk tsiyar shi ba zai kwana can ba zai dawo kuma yau da gobe ba ta bar komai ba in kika yi haƙuri itama ai wata rana za ta zama ɗaya da mu. Ai mace ce haihuwa za ta fara. Kamar yadda ya ganta ya auro wata rana haka zai ga wata ya auro itama a fara gwagwarmaya da ita ba, ai Namiji ne shi a rayuwar namiji mai ya yi ne da kuma ɗauka da ajiyewa ke dai ki zura ido kawai ki daina ma tanka shi, ki nuna ma kamar ba ki san abin da yake yi ba shi da kan shi zai shiga taitayinsa."
"In sha Allahu ba zan ƙara mgana ba."
Ta faɗa tana miƙewa itama.
"Ya dai kamata gaskiya."
Ba mu ji ko ƙaran buɗe kofa ba sai ganin shi muka yi kawai a kan mu a falon, ban san ko ya ji manganganun mu ba ko kallon mu bai yi ba ashe ya manta wayarsa a saman kujeran da ya tashi ita ya ɗauka a fusace ya koma ciki ina ganin haka na kama hanyar fita ina yi ma Gimbiya sai da safe, mganganun sa ba su wani dame ni ba Gimbiya ce washegari ta ce ba ta iya barci ba a raina na ce ba za ki yi ba kam nima haka na kwana kuka a ranar da Yallaɓai ya ce ina baƙin ciki da su Khalipa. A cikin zuciyata na ce Gimbiya Welcome to the Game.
Wannan tsiyar da Gimbiya ta jawo ta aka yi ita ta ja mana Yallaɓai sati ya yi daga ni har ita yana yi mana cin mgani
ko abincin mu ba ya ci da gani har ita, sai ma bangaren shi da ya turo ma'aikata suka fara ida sa gyarawa ko gaya mana bai yi ba, ni in ranar kwana na ba yan gaisawa ba ma mgana sai dai ya yi ta aikinsa a kan system ko kuma ya yi wasannin shi da ƴa'ƴan shi, nima ko ganin haka na kama kaina ban ga abin da na yi masa na bashi haƙuri tun a falon Gimbiya ban san kuma me ya ke so ba ko so ya ke yi na kwanta masa saboda yana fushi da ni, ni ko na ce a cigaba da tafiya gabar nan ce ya san ni na fi shi kwarewa. Da na fahimci ba ya cin abincina sai na daina ma yi masa ta yi, Gimbiya ta ce itama haka ba ya mata mgana in ta yi masa mgana da kyar yake amsawa. Ita duk ta damu kamta ni fa na faɗa mata an riga an zo matakin da ɗan zaki ya riga ya girma ni Yallaɓai ai ya daina hana ni sukuni da takaicinsa tuni na ke tattara shi na watsar na kama sabgogin gabana. Balle da na dawo da sana'ar hijabai na gadan-gadan ina na gama ta lokacin shi, da man hatsiyar tariyar da bukukuwa ne suka saka na yi sanyi ganin ina so ma na taba jarin kuma ga mutane na so shi ya sa kawai na saka aka ɗinko mini da yawa aka aiko mini da shi.
Gimbiya ko ga shagonta ga aiki amma duk da haka ta zauna Yallaɓai na neman kasheta da haushi. Wai tana faɗin ya fara gyaran bangaren shi bai sanar damu ba na ce ina ruwan ki? Shi da gidan shi da kudin shi? Ni ko a gefen gyalena to da Rabi'atu za ta dawo bai sanar da mu ba ranar ni ba na nan na je gidan Ma'u na duba ta tun da ta haihu ɗin ba ta ƙara lafiya ba lafai lafai ce, Gimbiya kuma tana shago yara suna makaranta danginta suka zo suka yi mata gyaran bangarenta sannan da daddare suka dawo da ita. Ni ina muka sani ba sai dai muka gan su ba kawai ni dai na shiga bangaren Rabi'atun na yi musu sannu da zuwa itama na yi mata sannu duk ta yi wani fari ta rame.
"Ai mun zo ɗazu gyaran bangaren Rabia megadi ya ce duk ba ku gidan"
Kai