baya nima na yi baya. Ya kuma kalleni ni ma na kalle shi amma kowannen mu sai ya kauda kan shi, ya shiga ɗakin barcin mu ni kuma na shiga tiolet.
Tun safe na shirya takwas da wani na safe aka kirani an samu mota ana jirana. Kuma ga Yallaɓai bai fita ba. Ba domin yana falon shi ba da ba abin da bai hana ni tafiyata ban yi masa sallama ba. Amma ganin shi a falo ya sa da na fito na yi masa sallama na ce na tafi amma mutumin nan ya na ta duba abu a system ɗin shi bai ko ɗago ba ya ce min Allah ya kiyaye hanya. Kamar zan ce masa zan yi kwana ɗaya amma yadda ya nuna mini halin ko in kula, ya sa na yi tafiya ta ba tare da na yi masa wata mgana ba amma har na kai ɗorayi raina na ƙuna.
Na fara shiga gida na gai da Gwaggo na iske ƴaƴan Ya Abubakar wai zaituna ta tafi Funtua biki, na ce sai su ɗebe miki kewan Alhaji Gwaggo. Ƙarfe tara da rabi muka kama hanya a golf da aka yo mana tasha. Balaraba 5k na ba ta sannan na nuna mata abin da na siya ma Saude ta yi ta mini godiya. Ni ko na ce haba ai Saude ƙanwata ce ballantana ta yi min alheri ƙwarai kuma sakamakon alheri to ya zama alheri ne. Mun isa da azahar lafiya mun iske ana ta suna dangin miji da makota sun cika gida Saude ta ji daɗin ganina sosai ta nuna murnan ta mun sha suna Rahila ta kirani ta ce ta zo gida Gwaggo ta ce ina Jigawa na je suna. Na ce mata wallahi ga shi sai ma gobe zan dawo mun daɗe muna waya da ita kafin mu yi sallama.
Da daddare mu muka gyara gidan da aka ɓata sannan muka shirya ma Saude kayan ta na tafiya. Ta samu kayan suna ba laifi, sai godiya shima mijin na ta ya iya bakin ƙoƙarin shi, bayan duk mun gama ayyukan ina kwance a kan kafitar da aka shimfiɗa mana ni da kanwar maman su Saude Yallabai ya kira waya ta sai na fita falo ina duba agogon bangon da ke ɗaki goma har ta gota amma abin mamaki me ya sa ya ke kirana?
"Assalamu alaikum"
"Kina ina ne?
Ko amsa sallama ta bai yi ba ya tare ni da mganar ko ina ina ne ?
"Ina gidan Saude a jigawa."
"Can za ki kwana ne?
Sai na haɗiye wani abu a maƙoshina saboda na ji kamar a zafafa ya ke mgana.
"E sai gobe za mu dawo tare da ita."
"Da izinin wa za ki kwana? Kin faɗa min kwana za ki yi Sadiya?
Sai na kasa magana tun da dai ba ni da gaskiya.
"Sadiya don kina gaba da ni ba shi zai hana tasirin ni mijin ki ba ne ya yi aiki a kan ki ba. Ki na yin abubuwa gaban kan ki ina ta kauda kai amma wallahi kin fara ƙure ni kar ki bari na faɗo kan ki"
Ban yi mamaki ba. To daman ni da ya ke ji ra bai samu dama ba sai yanzu.
"Kin aiko min Jidda da cewa za ki je suna na ce sai kin dawo na aika miki da kuɗi kin dawo min da su Sadiya me kike nufi
da ni? A she ba zan ci albarkacin Jidda ki karɓi kuɗin nan ba? Dole sai kin nuna mata ni da ke babu jituwa ko! To kin kyauta kuma ya yi miki kyau."
Ashe dai ya ji haushin dawo masa da kuɗin da na yi. Na ko ji daɗi a cikin zuciyata da ya ji shima haushin da na daɗe ina ji.
"Allah ya kai mu goben ki dawo. Za mu zauna sai ki faɗa min duk abin da na yi miki da zafi da ya sa kika maidani ni da banza duk ɗaya Sadiya."
"Ka yi haƙuri."
Na faɗa saboda ina so ya ƙyale ni barci nake ji na gaji.
" Bakomai kawai ban ji daɗin da ba ki faɗa mini zaki kwana ba ne."
Baki na buɗe na sake rufewa ya wani sassauta murya jin na bashi haƙuri sai ma abin na shi ya ba ni dariya sai da na murmusa shima ina jin sa ya ɗan yi dariya kafin ya ce.
"Na yi kewar mirmishin ki Sadiya ta. "
"Uhm!"
Na faɗa a ƙasan maƙoshi.
"Sai kin dawo goben a matsayina na Babba zan ba ki haƙuri a duka laifukan da kike tunanin na yi miki su Sadiya."
Ban yi magana ba amma na yi shuru ina jin sa. Ban yi mamaki ba daman na san ya na neman hanyar da za mu shirya ne.
"Na gaji. Na gaji da wannan horon da muka yi ma juna. Ki dawo mu zauna mu warware komai a tsakanin mu kin ji ko?
Ya faɗa cikin sanyin murya sai na gyaɗa kai kamar ya na ganina kafin na ce.
" Sai da safe.'"
"Sai da safe Madam."
Daga haka na katse wayata. Na daɗe zaune ina tunani daman ai yanzu duk zai ce na yi haƙuri shi ba da gayya ya faɗin duk mganar da ya faɗa ba. In ma na haƙura amma ba shi zai saka na manta da abin da ya yi mini ba.
*Janafty*.*TKGB30C3*
*Littafin TURKEN GIDA 1K ne on Telegram. 09069067488.*
Kina buƙatar kayan kitchens domin ƙawata Kitchen ɗin ki? Ya ke Uwargida kina buƙatar chanza ma megidan sabbin kwanukan cin abinci? Ko kina buƙatar sauya masa kofin shan ruwa? Ko kina so ki burgeshi da farantai masu kyau da yarari? Ko Amarya ce yar ƙwalisa da ke son ƙawata gidanta da kayan alfarma? To ku matso kusaa domin JANAFTY EXLUSIVE AVAILABLE Muna kawo muku ko wani nau'in kayan Kitchen da na kwalliya gida domin farincikin ku, kuma akan farashi mai rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina daga in da muke, ku tuntuɓemu ta wannan lambar domin ƙarin bayani.
09069067488
+234 706 234 9732
Washe gari tun safe muka tashi da aikin nama muka soye shi a ka raba a ka ɗibar ma dangin mijin Saude kafin mu haɗa kayan tafiya. Tashar mota ya samo mana tun daga ƙofar gidan Saude a garin Jigawa har zuwa ƙofar gidan su a anguwan Ɗorayi da ke Kano, zuwa la'asar duk muna Kano ni daman muna isowa na shige gidan Gwaggo na yi salla na iske har lokacin Alhajinmu bai dawo ba.
"Gaskiya Alhajinmu ya ga wuri. Yashe ta yi masa daɗi wannan karon."
Na faɗa ina dariya Gwaggo ta ce ai ko wannan karon dai ya daɗe, ni kaina ban samu kiran shi ba sai a lokacin har ya ba ni Baba Aminu muka gaisa da shi yana ta saka mana albarka.
Ina shirin tafiya sai ga saƙon naman suna da yawa daga gidan su Saude har da omo da sabulu na Gwaggo. Da zan tafi tare da Gwaggo muka shiga gidan ta yi ma Saude barka a nan na bar ta na wuce gida na shiga gida ba daɗewa domin ruwan zafi kawai na ɗora ban ma san me zan dafa ba su Jidda suka dawo daga makaranta kawai sai na sulala mana indomie na haɗa da ƙwai na dafa mana muka ci, tun da yamma ta yi sannan yau Yallaɓai na gidan Gimbiya ba ni da wata matsala.
Saboda yana neman shiri bayan mangariba sai ga kiran shi, tambayarsa ita ce na dawo? Na ce masa na dawo tun ɗazu sai ya ce mini zai shigo gidan in ya dawo. Ban ma san ashe tafiya ya yi ba sai da ya zo gidan wajajen taran dare, ina ɗakina saboda yana son shirin da gaske har ciki ya biyo ni, muka gaisa shi ne fa ya ke faɗa mini Dutse ya je akwai wani gidan radio da za a gina kuma shi a ka ba ma kwangilar wajen shi ya sa ba ya samun zama ni dai nawa fatan alheri kawai.
Tare da shi muka fito falo ina ba ma su Jidda naman sunan da a ka bani na gidan su Saude. Tsoka bibbiyu na ba su ni kuma sai na saka sauran tsoka ɗayan a bakina akwai kuma saura biyu a hannuna da ƙashi.
" Umma Sadiya. Ni ina nawa naman sunan?
Ba zato kawai na ji maganarsa ban tsaya nuna masa mamakina ba na miƙa masa sauran na hannuna. Sai dai na shanye mamakin nawa da na ga ya saka hannu ya karɓa har kuma ya ɗauki tsokan da ta rage ya saka a baki ya na taunawa.
"Lah Abba kai ma kana cin naman suna?
Baby ta faɗa tana yi masa dariya duƙawa ya yi daga in da muke tsaye a bayan kujerun falon ya lakace mata hanci yana faɗin" E mana. Ai har na ki naman sunan na ci."
"Na Ya Jidda fa?
Ta faɗa ta na dariya.
"Har na ta ma na ci."
"To na Umma fa?
Sai na kalle shi, nima ni ya kallah kafin ya yi dariya ni kuma sai na kauda kaina na zagaya na zauna saman kujeran da Jidda ke zaune ta na ta duba wani littafin Chemistry ba ta shiga maganar Baby da Abban na ta ba.
Na ga dai ya yi mata raɗa a kunne tana kallona tana dariya amma ban san me ya faɗa mata ba. Bai zauna ba ya yi mana sallama ya tafi. Saboda gulma har yana zuwa yana sumbatar goshina. Yaushe rabon duniya da ayyarahe? Amma dai ban kushe sa ba, na yi masa yaƙe Baby ce ta raka shi har haraban gida amma daga ni har Jidda muna daga in da muke ko motsawa ba mu yi ba.
Washegari da safe bai zo ba amma ya kira ni a waya yana tambayan yadda na tashi ni da yara. Na ce masa muna lafiya sai ya ce zai ta fi Dutse sai zuwa anjuma in ya dawo na ce a dawo lafiya. Ranar a gida na yini ina warware gajiya mun yi waya da Anty Laila maƙotan ta na son hijabai sun gani a wajenta da yake ta siya kuma shima Ya Auwal ya siya mata wasu. Nan da nan na ji ciniki na ce ta tura mini colours da simple ɗin irin wanda suke so sai na tura a ɗin ka musu daga can za a tura musu Abujan ba sai an ma an kawo mini shi nan ba. Datti ma mun yi waya amma ni na kira shi ina masa tsiyan tun da ya fara zaman kansa ya daina neman mutane.
"Kai Ya Sadiya ko kwanaki ba na kira ki ban same ki ba "
"Uhm kai Datti fita idanuwana na rufe. "
Sai ya fara dariya yana faɗin" To na ji na amsa laifina a yi min afuwa"
Sannan na yarda muka gaisa yana tambayan ya yara na ce suna lafiya.
"Ko jiya sai da Jidda ta yi zencen ka da cewa Uncle Datti shuru kwana biyu"
"Allah sarki Jiddodi ta na lafiya ko? Ya mganar jarabawarta?
"Yallaɓai ya ce a wannan shekaran za ta yi har Jamb ma."
"Za ta iya ai ta na da ƙwanya mu ta yi gado"
Dariya na yi shima yana ta ya ni, mun sha hira da shi ya ce ma ƙarshen wata zai shigo garin ba sa samun hutu ne mai tsawo ni ko na ce daman aikin kamfani ai sai mai haƙuri. Ina jin zumunci har Ya Aina na kira da Ya Balki muka gaisa Ya Murja ce da na kira ba ta gida yara suka ɗau wayar Rahila kuma Ya Muntari ya ɗauka ya ce min wayar na hannunsa tun jiya wutar layin su ta lalace wayar ta kwana ba chaji sai ya fita da ita yau ɗin domin ya sa mata chaji bai ma daɗe da kunna wayar ba sai ga kirana. Na dai ce ya gaisheta in ya koma gida ya ce in sha Allahu zai faɗa mata. Amina ce kaɗai da ban kira ba saboda ita ko kafin tafiya ta Jigawa ai mun yi waya. Ma'u kuma daman na yanke alaqa da ita, ba ta kirana ba na kiranta sai dai in mun haɗu a gidajen ƴan'uwa amma dai ban goge lambarta ba kamar yadda nima na ke da yaƙinin ba ta share tawa ba.
Daga nan na yi ta shige shige na a I. G. Ni kaɗai ban taɓa jin ina jin haushin halina ba sai kwanakin nan ba ni da wata ƙawa Aminiya shaƙiƙiyan da yau in na shiga matsala zan je mata da mgana ta saurareni kuma ta ba ni shawara kamar yadda na ga wasu suna dashi, ni ko ni ɗaya tal ban taɓa ƙawa ba bare ba sai su Munnira su kuma aure ne ya haɗa ni da su duk da mun shaƙu amma akwai wani matsalan nawa da ba na iya faɗa musu saboda shi aure ai sirri ne, kuma cikin kowani aure da zamantakewa akwai matsaloli kowa kuma da irin na shi matsalan. Ba komai ba ne za ka zo kana faɗa akwai wani abun da ya ke buƙatar sakaya. Yau da a ce bani da shigen halin rashin sakin jiki da mutane da yanzu ina da ƙawaye na tuna tun muna makaranta ƙawayen da suka yi ta shige mini ina ba sar da su. Har na zo matakin jami'a yan set ɗin mu sun yi ta shige mini amma na ƙi ba ma kowa fuska har Maijidda ma ta layin mu ta so ni har muka haɗu a jami'a da ta ga dai ba na yi da ita sai ta kama kanta.
Ta yi aure a cikin garin Kano nan amma ban taɓa zuwa gidan ta ba na dai je bikin da Rahila ta matsa mii kuma har gida Maijiddan ta kawo min IV da mintin gayyata. Kaf waɗanda muka yi karatun jami'a da su ba na zumunci da kowa. Wasu ina ɗan kiran su a waya jaje ko murna shima na zo na daina daga baya nima tun suna bina har kowa ya rabu da ni ina dai cikin group ɗin kuma ina ganin ana ta abubuwa in sha'ani ya tashi na ɗayan mu a haɗa kudi kuma a je, ni dai na kan ba da wani lokaci amma zuwa ban taɓa yi ba. Sai dai in ga ana turo hotuna suna zumunci su amma ni na ware kaina kamar saniyar ware. Ban taɓa jin abin ya dame ni ba sai yanzu amma a ƙasan zuciya na ƙudiri a raina nima yanzu zan nemi jama'a domin na fahimci jama'a rahama ne.
Ranar ma sai dare Yallaɓai ya zo gidan kuma again a ɗakin barcin mu ya sameni ina ta rubutu.
"Madam wai labarai kika fara rubutawa ne?
"Me ka gani?
Na ɗago ina kallon shi bayan na dakata da rubutun da nake yi. Gyara zama na yi a gefen gadon lokaci ɗaya ina gyara zaman doguwar rigar material ɗin dake jikina.
"To gani na yi kwanan nan kina ta faman rubuce rubuce."
Kallonsa na yi ina tuna yaushe ne ya ganni ina rubutu? Ni dai ina tunanin wannan ne na biyu amma zai ce wai kwanan nan ya na ganina ina rubuce rubuce.
"Kawai abin kasuwanci ne. Ina rubuta waɗanda suka karɓi hijabai ne."
"Da kyau Hajiyar Business"
"Ya Hanya?
Sai na kau da maganar ganin duk ya gaji daga yanayin ma yadda ya ke mgana.
"Lafiya lau. Amma na gaji sosai"
"To ka zauna mana."
Na faɗa ina nuna masa gefen gado saboda na ga yana tsaye kuma ga shi ya ce ya gaji."
"Bari kawai na ƙarisa gida na yi wanka na huta gabaɗaya."
"Kuma fa haka ne."
Na faɗa ina kau da tunanin ya ƙi amsar ta yi na ne. Ni fa taimakon sa na yi ganin ya ce ya gaji kuma yana tsaye kamar wani dakaren soja.
"Maganar mu fa Sadiya?
"Wacce magana?
Na tambaya ina kallon shi.
Sai ya gyara tsayuwa yana mai harɗe hannayensa a ƙirji kafin ya ce.
"Mganar da na ce in kika dawo za mu yi. Domin mu warware rashin jituwan dake tsakanin mu."
Sai na yi mirmishin takaici kafin na ce" Muna gabar ne har yanzu? Ai ina jin kamar mun warware komai."
"A'a.
"To me ya yi saura?
"Komai ma."
Ya katseni ya na mai tsareni da idanuwansa.
"Kin daina gaba da ni amma kuma kin ƙi komawa kamar yadda kike a baya Sadiya."
"Mun daina gaba da juna za ka ce ko?
Ya na kallona na cigaba da faɗin" Tun da kaima ba ka yi mini magana Yallaɓai."
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Duk na ji na amsa laifina shi ya sa na ce mu zauna mu yi magana domin mu fahimci juna."
"Na ji za mu yi in sha Alkahu."
Na faɗa ina ƙokarin komawa in cigaba da rubutuna.
"To yaushe?
Sai da na ɗago na kalle shi ido na cikin ido sannan na ce.
"Sai ranar da na karɓi girki."
Murmishi ya yi kafin ya ƙariso gaba na ban yi aune ba kawai ya ɗan rankwafa ya sumbaci laɓɓana kafin ya miƙe ya fice yana faɗin.
"Sai da safe Sadiya ta."
"Sai da safe."
Na amsa masa a saman laɓɓana bayan fitan shi har ina shafa wajen. Yaushe rabon da a yi haka! Tun kafin faɗan mu da shi a kan Khalipa. Yaron na raina ina son tambayan shi amma na fasa tun da ya nuna min iyakata ya je amma ƙaunar da nake yi ma jininsa ba zan fasa saboda shi ba, ko faɗan mu ne ya sa kwana biyu tun da na dawo bai tarkatomun Khalipan ba, amma na ƙudiri niyyar in na ga ba a kawo shi ba zan kira Gumbiyar na ce ta kawo shi ya yi mini kwana biyu na saba da shi duk da ɓarnar shi, shi kuma na san ya yi sabo da gidana sosai kawai dai kwana ɗaki ɗayan da Yallaɓai ya tsiro da shi na ga ana cutata shi ya sa na yi magana amma ba da niyyar Khalipa ya daina zuwa ba tun a baya ban hana shi zuwa ba sai yanzu?.
******
Tun da yau Yallaɓai zai dawo gida na na kira Maman Nana na ce in ta samu lokaci ta zo ta yi mini kitso. Da safen ko ta zo ta yi min 2step ƙananu. Kuma kitson ya yi kyau tun da na duba a cameran waya ta na gani. Sai azahar ta tafi bayan na yi mana girki duk dai macaroni na dafa mana muka ci da ranar. Bayan tafiyan ta na gyara gidan na yi shara na saka turare ɗan kwanciya na yi na ɗan huta zuwa la'asar na tashi bayan na yi sallar la'asar
Sannan