Turken Gida Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   52 / 55

153K to 156K   out of 163.1K words

sun yi mini barka da dawowa.

Su Baby na tafiya na rufe kaina a ɗakin barcina na kuma kashe wayata na kwanta ina ta barci ban san meke faruwa ba sai da na ji ana ta buga mini ƙofar bedroom lokaci ɗaya ana kiran sunana.

"Umma"

Can a cikin barci na ji buga ƙofar bayan na ɗan motsa sai kuma na ji kiran sunan nawa, da hanzari na miƙe zaune ina mutsike idanuwana.

"Maman Jidda"

Na ji an sake kira sai na diro daga saman gado ina laluban hular da zan rufe gashin kaina, ina kuma tunanin waye? Kamar ban ɗau muryan ba.

"Waye?

Na faɗa ina isa kusa da kofar, hannuna guda ɗaya ina ƙara tusa gashin kaina da ya hargitse cikin hulan da na sanya yanzu yanzu.

"Ni ce"

"Salima?

Sai da ta ce ita ce na ganeta.
Na buɗe kofar lokaci ɗaya ina kiran sunanta.
Salima ce ƙanwar Rabiatu.

"Lafiya kuwa Salima?

Na fada cikin mamakin ganin ta har ƙofar ɗakin barcina abin da ba ta taba yi ba iyakarta falo ko ɗakin Baby.

"Anty Rabi'atu ne da Maman Khalifa suke faɗa."

Ta faɗa tana haƙi, ai sai na yi sansarai domin kamar an mantar da ni ma ko su waye sai daga baya na fahimci mganarta.

"Faɗa? Innalillahi a ina?

Na faɗa ina yin gaba sai da ta biyo bayana lokaci ɗaya tana faɗin" A can bangaren Maman Khalifa."

Ban tsaya ko saka takalmi ba, daga ni sai rigar barci Allah ya taimaka ma doguwa ce, kuma tana da kauri haka na fito haraba na kwashi gudu zuwa bangaren Gimbiya Salima na bin bayana hankalina a tashe.

Ban ɗauka lamarin ya lalace haka ba ni da ta ce suna faɗa na ɗauka cacan bakin da suka saba ne, ashe ashe abin ya yi muni ko da na shiga bangaren Gimbiya a tsakiyar falon ta na iske Gimbiya kan ruwan cikin Rabi'atu tana kilarta, Rabi'atu na kuka tana neman ɗauki Gimbiya ko maruka take kai mata lokaci ɗaya tana faɗin.

"Don ubanki na yi miki kama da sa'arki ce? Ni za ki ja da kokuwa? Yau sai na nuna miki bambamcin aya da tsakuwa."

Da gudu na yi kan Gimbiya ina salati ina ƙokarin ɗagata amma tana fizgewa.

"Subhanallah. Gimbiya me ye haka? Don Allah ɗagata haba mana."

Amma ba ta jini ba kai mata duka kawai take yi itama bakin Rabi'atu bai mutu ba.

"Allah ya isa muguwa, an ja ki da faɗan ke din banza."

Sai da na ce Salima ta matso tare da ita muka samu muka ɗaga Gimbiya daga kan Rabi'atu.

"Haba Gimbiya me ya kai ki yin dambe da Rabi'atu?  Ba girman ki ba ne wallahi sannan kar ki manta ba ke kaɗai ba ce fa."

Na faɗa ina rike ta, tana haki ta fizge hannunta tana gyara wuyan riganta.

"Bar ni Maman Jidda, yadda yarinyar nan ta raina ni gwara da nuna mata ƙyaleta na ke yi amma ba ta fi ƙarfina ba."

Lokaci ɗaya tana hararan Rabi da Salima ta taimaka mata ta ɗagata.

"Me ya faru ne? Ke Rabi'atu me ya sa wai ba ki jin mgana ne?

Kawai sai ta fashe da kuka tana faɗin" Ai ita ce ba ta da gaskiya daga na zo ina mata mgana shi ne ta shiga zagina."

Gimbiya ta tare ta da faɗin" Maƙaryaciya. Yarinyar nan yar bariki ne,"

"Wai me ya haɗa ku ne?

Na fada ina katse su saboda na gaji da hayaniyarsu.

"Kan turaka dai Maman Jidda, shekaranjiya da zan karbi girki haka na iske shashen kaca kaca ta fita ba ta gyara ba, ban yi mgana ba na gyara nima ko yau de zan fita na ce ba zan gyara ba na bar mata shi ne da ta je shashen ta gan shi haka ita ishasshiya ta zo har shashena tana faɗa mini mganar banza. Na je na gyara yau Mijinta zai dawo ban isa na kwana da miji ta yi mini bauta ba, ni kuma sai na ce ai bauta ta gama tun da sai da na jagwalgwala na ba ta take suɗewa daga faɗin haka sai yarinyar nan ta ce wai in ban tashi na je na gyara ba zan ga abin da zai faru ni kuma na ce in ta fasa, saboda tsabar ta raina ni kawai ta jawo ni ina kan kujeran nan sai da na faɗo ƙasa ni ko da raina ya ɓaci ina miƙewa na kifa mata mari shi ne ita ishasshiya ta jani da dambe shi ne na nuna mata ba ta isa ba."

Gimbiya ta gama bani labari tana faman haƙi

Kallonsu kawai na ke yi ina mamaki har yauahe ne za su daina fada kan wancan turakan da Yallaɓai ya samar da ita a cikin gidan nan ne? Shi kamar ma jin daɗi yake yi suna ta kara kaina akansa.

Kai na girgiza kafin na ce" Haba don Allah wai mene ne da Turakan nan? Ko da yaushe a kanta ne kuke faɗa?

Na faɗa ina kallon su gabaɗaya

"Ita ta ja, da ta san ba ta gaskiya me ya sa ba ta tashi ta je ta gyara ba? Kuma ai Abba ya ce duk wacce za ta fita ta gyara abin da ta ɓata."

"Ba zan gyara ba, ke da kika fita a gyaren kika bar mini? Sai ke ce mai bakin mgana? To na ƙi na gyara ki ɗau matakin da za ki ɗauka."

Gimbiya ta faɗa har tana sake rike kugu, ga cikinta har ya fito amma ba ta ko jin nauyin jikinta.

"Za ko ki gani wallahi."

Rabi'atu ta faɗa tana cije baki, har ya tasa ga jini a lebenta ta daku, ganin ga Salima a wajen yasa na kalleta ina faɗin" Salima koma bangaren Rabi'atu ki zauna da su Ayush."

Sai ta amsani da to ta sake ta Rabi'atu sai ta ce tare za su tafi ni kuma na ce ta tsaya ina da mgana da su ita da Gimbiya sai da Salima ta fice sannan na kalleta ina faɗin"

"A wannan rigimar gaskiya ke ce ba ki da gaskiya Rabi'a."

"Ni kuma"?

Ta fada tana wani tura baki, na ko haɗe rai ina faɗin." ƙwarai  ke fa, ai ke ce ƙarama, yau ko da Gimbiya ce mara gaskiya ya dace ki biyo ta bangarenta kina yi mata rashin kunya? Ban da Yallaɓai da auro ki ya goga kafaɗarki da ta mu ke kin isa ma ki haɗu damu a hanya ki yi mana mgana ballanta har sa'in sa ya haɗa mu? Na fahimci kwana biyu nan kina ji da rashin kunya to ki kama kanki ko ba aure Gimbiya ba sa'ar yin ki ba ce ballatana tana gaba da ke a gidan nan, abin da kika yi ba dai dai ba ne, tun da kin yi itama ta rama ba shike nan ba? Amma saboda fitina sai ki biyo mata har bangarenta ki ja ta da Dambe? Ai gashi nan kin sha wuya gaba ma sai ki ƙara."

Kawai sai yarinyar nan ta saka kuka tana faɗin" sai ki yi son kai ki goyi bayan ta ? Sai kawai  ki yi ta mini faɗa akan gaskiyata ai Abba ne ya ce kowa ya ɓata ya gyara."

"E an yi miki faɗan, kin yi ba dai dai ba ba za a gaya miki ba? Abba ya ce wacce ta gyara ta bata kema kin ɓata ta gyara itama ta ɓata ba sai ki gyara ba? Da gaske ne ba ki da kunya ki kuma daina wannan halin ba zai ɓulle da ke ba, ni dai gaskiya na faɗa miki."

Kawai sai ta juya har tana yi mini tsaki.
"Mtswww. Bari Abba ya dawo wallahi sai na faɗa masa."

"To in kin fasa faɗa masa kin raina kan ki. Shashaaha kawai."

Raina ya baci daga faɗan gaskiya bayan fitan kan ta Gimbiya na koma ina ta mata fadan me ya kai ta dambe da wannan yarinya a ga shi nan ta raina ta nan gaba ko a ina ne ba za ta ji shakkar jan ki da faɗa ba

"Da ko da ta daku wallahi kambu"

Ƙaramin tsaki na ja kafin na ce" Ba ki kyauta ba me ye sa  kika biye mata ba."
"Har fa ɗakina ta biyo ni? Sai na raga mata?

Ni haushi ma ya hana ni mgana na bar mata bangarenta na koma nawa, ina barcina sun hanani sukuni, dole na yi wanka na  iske Baby ta soya doya da ƙwai sai na hada tea na ci da shi, ina yi ina tsaki saboda takaici da man kwana biyun can rashin kunya na fahimci Rabi'atu na fama da shi, ba kuma kowa ya ja ba sai Yallaɓai shi ya ja mana wannan wulaƙancin, ya sa ƙaramar yarinya tana ganin ɗaya take damu, ni wallahi daga Yallaban har matan na shi da gidan sun fita daga raina, ina can cikin yan uwana na ma manta da wannan hatsaniyar.

Yini na yi a bangarena ban fita ba, har yamma daga Gimbiyar har Rabi'atun ban san isalinsu ba, su Baby sun dawo ba daɗewa sai ga Yallaɓai ni da na ga ma Yamma ta yi ban ɗauka a ranar zai dawo ba sai ga shi, kuma a turakarsa ya sauka, ni kuma ban yi rawan jiki zuwa na gaishe shi ba, ina idar da sallar mangariba na zauna ina duba wayata, Baby da sauran yaran suna shashen Gimbiya.

Kawai sai ga kiran Yallaɓai ban kawo ma kaina har Rabi'atu ta kai mganar nan ba sai da na ɗaga kiran na ji shi a fusace har yana yi mini ihu a waya.

"Ki zo bangarena yanzu Sadiya."

Kuma yana gama faɗin haka ya katse wayar, wayar na koma ina bi da kallo cikin mamaki kafin na furta a fili" Ikon Allah!.

Na yi niyyar zuwa a lokacin amma ina miƙewa sai cikina ya karta, shi ya sa na tsaya sai da na shiga tiolet na rage ciki ina fitowa da man na yo alwala jin ana kiran sallar isha'i na tsaya na yi sallata ina yi ko sai kiran wayata ake yi tun kafin na sallame na san shi ne, ban ɗauka ba saboda na san ihu zai yi mini shi ya sa da hijabin jikina na fita zuwa bangaren Yallaɓai.

Ina shiga na gan su tsaye a falo cirko-cirko shi da matansa, Gimbiya na tsaye kiƙam rike da kugu shima haka hannayensa a bayan shi yana ta kai gauro da mari a falon Rabi'atu kuma na zaune tana sunne kai, falon na sake bi da kallo kaca kaca, alamun dai Rabi'atu ba ta gyara ba kamar yadda ta rantse.

Tun kafin na kariso ciki Yallabai ya tare ni da hargagin shi da ya koya yanzu.

"Sadiya ni za ki wulakanta? Ni za ki yi ma wulaƙanci?

"Me na yi kuma?

Na faɗa cikin mamaki, domin ganin su Gimbiya kawai na tabbatar mini da Rabi'atu ta kai masa labarin abin da ya faru ɗazu.
Ni ko ina ruwana da zai sako ni a ciki don Allah?

"Ban sani ba. Na ce ban sani ba kar ki raina mini wayau kin ji ko?

Kallon shi na yi ganin shi a fusace kamar yana jirana ina kokarin danne abin da ke taso mini na ce" Gani ina fatan lafiya?

"Ko lafiya lau ya dace na kira ki sama da minti talatin ki shanya? Kin kyauta kenan?

Ina yamutsa fuska na ce" Ka kirani ina shirin zuwa cikina ya motsa na shiga makewayi, bayan na fito na ji ana kiran salla shi ne na tsaya na yi salla, ban ɗauka ai kana jirana ba ne"

Na faɗa ina mai zaman kan kujera mai zaman mutum ɗaya domin na gaji da tsayuwa.

Kasa mgana ya yi yana kallona ni ko na haɗe rai domin na yi alƙawarin yau ba zan yarda na ɗaukin renin wayau Yallaɓai da matan shi ba wallahi, gwara na tsage musu gaskiya in ba haka ba zai san ina yi mishi kawaici da kara ba ne.

Ya gama cika yana batsewa sannan ya kalleni kafin ya ce" Me ke faruwa ne a cikin gidana wanda ban sani ba?

Na yi kamar ban ji ba, saboda sai na ga tambayar ba ta shafe ni ba, tun da ya ce gidan shi a matsayin shi na megida ya saka ido mana ni ina ruwana.

"Da ke fa na ke mgana Sadiya kin yi mini banza"

"Ni?

Na faɗa ina nuna kaina.

"Aa ni "

Ya faɗa a fusace, ban bari ya sake ɗauko wata mgana ba na tare shi.

"To ai na ga tambayar kamar ba tawa ba ce shi ya sa na yi shuru. Gidan nan fa naka ne in ma wani abu na faruwa kai ne shugaba kai ya kamata ka fara sani ba ni ba"

Wani kallo ya yi mini kafin ya ce" To na ji ni ina yini a gidan ne? Ke ce walikiyata duk abin da ya faru ki tsaya ki wakilceni in na dawo kuma ki zo ki sanar da ni."

"Ko?

Na faɗa ina kallon shi, sai ya kasa mgana su kuma sun yi shuru suna jin mu.

"E shi ya sa yau kika ɓata mini rai, ya za a yi har a yi dambe a gidana ba ki kira ni kin faɗa mini ba? Sannan kuma kika yi hukunci har kina zagin Rabi'atu kina cewa ita ce ba ta da kunya? Ita Gimbiyar kin binciketa kin san abin da ta yi mata har ta kai su ga Dambe?

Ya faɗa yana kallona ni baki na saki ina kallon shi, na jinjina kai na juya ina kallon Gimbiya itama sai ta kalleni baki a buɗe.

"Koma me ta yi mata ya dace ta yi dambe da ita! Sa'arta ne? Ban da siyar ma da kai mutumci, ji yadda ta kumbura ma matata baki? Koma me ya faru ba za a iya jirana na dawo ba ne?

Ya faɗa yana tsare ni da ido, mamakin shi na ke yadda idanuwanshi suka rufe akan Rabi'a..

"To ni yanzu me ye nawa a cikin wannan mganar?

Na tambaye shi ganin kamar ni ya fi jin haushi.

"Naki shi ne ba ki yi hukuncin kan gaskiya ba, kin goyi bayan Gimbiya tun da kuna tare, sannan ni ba ki kirani kin gaya mini ba? Kin kyauta kenan? Girman kenan?

Na buɗe baki haa ina kallon Yallaɓai Gimbiya ta saki sheewa ta tafa hannu ni ko na ma kasa mgana tsabar mamaki.

"Ni fa Abba abu ɗaya ya yi mini zafi, wai Maman Jidda ta ce ina yi musu rashin kunya! Kuma ni wallahi ba wacce cikinsu na ke yi ma rashin kunya Maman Khalifa ce yau daga zuwa na yi mata mgana ta fara zagina"

Ta karishe faɗa har tana shessheƙan kuka, kawai sai Yallaɓai ya juya wajenta yana faɗin" Ki yi shurun ki ai na san halin kowa a cikin ku, tun tuni ba ki yi rashin kunya ba ne sai yanzu? Da man ita Saudatu fitinnaniya ce, na san za ta aikata ita kuma Sadiya ban san ta da bangarenci ba sai yau, amma duk zan yi mganin abin yanzu nan."

Ya faɗa yana nuna mu da yatsa, a kausashe, Gimbiya ta sake sakin shewa kafin ta ce" Za ka sake mu ne? Shi ne karshen mganin mu da ka ce za ka yi ko?

Ta faɗa tana tsare shi da ido, shi kuma sai ya taso mata tana faɗa yana faɗa, har yana ce mata hakuri kawai yake yi da ita darajan iyayansu. na gaji da hayaniyar sai na saka baki.

"Don Allah ku yi hakuri wannan fa ba girman ku ba ne."

Daga ba da hakuri kawai nima Yallaɓai ya dawo kaina yana yi mini masifa.

"Ai duk laifinki ne, haɗa kai kuka yi za ki kashe mini mata ko? Don kun gan ta yarinya ko?

Ban san na mike ba sai da na ganni tsaye kan kafafuwana.

"Dakata."!

Na faɗa da karfi ina ɗaga ma Yallabai hannu idanuwana har rufewa suke yi saboda bacin rai da bakin ciki wallahi tun da bai san ina yi masa kara ba yau sai na yi ma yallaɓai wankin babban bargo.

"Ka dakata Yusuf.."

Na sake faɗi cikin ɗaga murya, saboda raina ya baci zuciyata ma tafasa take yi a lokacin.
Ba shi ba, har matan na shi tsayawa suka yi suna kallona saboda mamakin tsawar da na daka masa.

"Ni kike yi ma ihu Sadiya??

"An yi maka Ihu, an yi maka ihun Yusuf ka yi abin da za ka yi don Allah Haba."

Na faɗa ina yarfa hannu, bayan na nuna shi da hannu, sai na ga kawai ya tsaya yana kallona cikin mamaki.

"Maman Jidda yau ba Yallaɓan?

Gimbiya ta faɗa cikin mamaki.

"Na bi yallabai da gudu, haba ka isheni a cikin gidan nan da fitinarka, na yi maka shuru na yi maka shuru amma na fahimci ba ka san kara ba, kuma ba ka san ina yi maka kawaici ba, to wallahi na gaji, na gaji da jidalinka da na matanka na gaji Yusuf"
Na ƙarishe faɗa ina ƙara daga murya saboda a lokacin ji na yi zuciyata ta yi duhu ko gani ma bana yi saboda bacin rai.

Sai falon ya yi shuru ganin na harzuƙa.

"To yi hakuri zauna mu yi mgana."

Yallaɓai ya faɗa cikin sigan lallashi ganin yadda na taso masa ya san halina in na fusata ba ni da kyau.

"Ba zan zauna ba, lokacin da na ke zaune ba ka so a yi mganar cikin laluma ba, yanzu sai dai kai ka koma ka zauna ka saurareni domin ni ce zan yi mgana."

Ban jira cewarsa ba na cigaba da faɗin" Yusuf auren soyayya ne a tsakanina da kai, a shekarun mu har zuwa matakin yau ba ka taɓa fahimtar cewa ina yi maka kara ba ne? Ba ka taɓa jin cewa a ranka kana yi mini wasu abubuwan da suka yi kama da cin fuska ina kyaleka ba! Mene ne ba ka yi mini ba, mene ne ba ka faɗa mini akan auran ka da Gimbiya ba? Wani baƙincikin matanka ne ban ƙunsa ba? Wani takaicin yan'uwanka ne ban ƙunsa a cikin zuciyata ba? Mun yi aure tun ba ka da komai muka yi gwagwamaryan arziki tare, daga baya da me ka saka mini? Ka yi mini gorin haihuwa na yi haƙuri, ka yi mini na gida na yi hakuri, ka yi ta mini alƙawaruka amma ba ka cika ba, na yi maka mgana? Ka nuna mini bambamci a kan matanka na taɓa yi maka mgana? Ka goyi bayan yan uwanka a kaina na yi maka mgana? Gimbiya ta yi mini abubuwa ta ci kasuwa a kaina kala kala amma duk ban ɗaga kaina ba, saboda kai Yusuf. Saboda karan da na ke yi maka, shi ya sa duk kake yi mini wasu abubuwa ba na ɗaga kaina, ba wai

52 / 55