ita ba ce ta zo Mimisco ta kira."
"Na shiga uku Kin san faɗan Momi kuwa?
Gimbiya ta fada tana ɗora hannu a kanta.
"Ai gwara ta yi miki faɗa"
Kafin ta samu zarafin magana muka ji ana taɓa kofa ni na fara fita falo sai muka haɗe da Mimisco sama sams muka gaisa na yi mata jagora zuwa ciki yadda ta ga an yi baza baza da kaya ba sai ma ta tambaya ba.
"Me ke faruwa ne Nene ta kirani cikin damuwa da cewa na zo na gani Sadiya ta kira ta ce kun sami saɓani da Tafida har yana mganar saki?
Ta faɗa tana kallon Gimbiya ko zama ba ta yi ba.
Sai Gimbiya ta kasa mgana ta fara matsan ƙwalla.
"Ba kuka na ce ki yi mini ba malama"
Bakinta na rawa ta fara faɗa mata tana zuwa wajen fashe gilasan mota Mimisco ta ce" Amma dai ba ki da hsnkali ko Saudatu?
Sai ta fashe da kuka tana faɗin"Momi.."
Hannu ta ɗaga mata kafin ta ce" in kina hauka ne Tafida ya fi ki hauka. Saboda kishi ki jawo masa asara? Ina ruwanta ita ta siya motar! Ba kuɗin mijin ki ba ne?
Ke da Allah ya rufa ma asiri amma kina ma yar da kan ki baya? Kin taɓa jin an ce ga Sadiya can da Tafida suna rigima sabo da ku! Ko ita ba mace ba ce?
Ta ƙarishe faɗa cikin faɗa har tana yi mata tsawa.
"A yi hakuri Mimisco."
"Sadiya Saudatu ba ta jin mgana gwara Tafidan ya sake ta ko za ta yi hankali."
"Ba za a yi haka ba in sha Allahu.'
Sai a lokacin ta zauna a gefen gado tana faɗin'" Ina shi Tafidan?
Na ce mata yana bangaren Rabi'atu.
"Tun bai iya fada ba kin ko ya ma Tafida iya tsiya kala kala. Ina daɗin shi don Allah?
Ita dai Gimbiya tana ta kuka wayarta ta ɗauko jaka ta kira shi, har sau biyu bai ɗaga ba.
"Nima ya ƙi daga kirana."
"Ki je ki same shi ne."
"Mu je to ki rakani."..
Ta mike tana faɗin haka.
"Ke kuma ki gyara ɗakin nan ki ma yar da wannan akwatin ƙaryan na ki."
Ta ce ma Gimbiya da ke kuka
"Kukan me kike yi! Ai ba ki yi kuka in dai kr ba za ki ji magana ba! Me ye ban faɗa miki ba? Na ce ki yi haƙuri ki kauda kai, ki yi ko yi da Sadiya amma ba ki ji ba? Wallahi in yaƙi saurarena ba zsn matsa masa sai ki tattara ki tafi can Rano wajen Hajiya burin ki ya cika kina ta kawo mana matsaloli a dangi."
"A yi hakuri Mimisco "
Na faɗa sai ta yi gaba tana faɗin" Sadiya lamarin Saudatu kamar ka yi ta dukan ta ne "
Muna tafe tana ta faɗa ni kuma ina bata haƙuri muna kofar shashen Rabi'atu take kara tambayata abin da ya faru na warware mata komai.
"Kin ki ko? Ina tarbiya mijin na faɗa kana faɗa? Ai bai burgeni ba da dukan tsiya ya yi mata ba kumbura baki ba."
Sai da na yi dariya sai a lokacin na tuna ashe bakin Gimbiya da ya ta sa Yallabai ne ya make mata baki a ɗazu da suna mgana.
kiran shi ta sake yi aka samu sa a ya ɗaga sai ta ce ga ta nan a ƙofar shashen Rabi'atu tana jiran shi, ganin ta samu ya ɗauka sai na ce mata zan je na duba yara.
"Je ki Sadiya. Ni ba ri na yazo na ga ko zai saurare ni."
"ZAi saurareki In sha Allahi."
Na faɗa ina dariya.
"To tunda ke ma yau aka ƙi sauraran ki nima da sauƙi."
Ni dai ina ta dariya na shige bangarena na iske Baby ta gama soya dankali da kwai suna karyawa ita da su Khalipa nima sai na bi bayan su bayan mun gama na ce Baby ta je ta yi musu wanka ni zan gyara wajen,.
Sama da awa biyu ina bangarena ba wanda ya kirani har Baby ta yi ma su Khalipa wanda da yake akwai kayansu a bangarena ba su da matsala suna can falon su, suna ta wasannin su
Ni ko sai dai waya a hannua Jidda ta kirani muka gaisa ta ce tana ta kira Abban na su ba ya ɗauka na ce wata ƙila yana da bsƙi ne na yi mata ƙarya. Ta ba ni har Ummu Salma mun gaisa sannan muka yi sallama sai can Mimisco ta kirani ta ce na fito za ta fito. Na fito na gan ta tare da gogan yana ts wani cin mgani ko mgana bai yi mini ba a gabana ya sake rantsewa sai Gimbiya ta biya asaran da ta yi masa ita kuma ta ce ba damuwa za ta saka a zo a ɗau motar a kai wajen gyara.
"Shike nan?
Ta faɗa tana kallon shi, kamar ba ya son mgana ya ce" Shike nan amma dom ke ce. Da na sha alwashin sai ta bar ta je Rano ta yi wata tukunna za ta dawo."
Mimisco ta yi dariya kafin ta ce" Na gode daka ji mganata. Ka yi hakuri ai ta baka hakuri kuma na ce ta sake baka."
"Ya rage nata."
Ya faɗa yana zakuɗa kafaɗa hannayen shi cikin aljihun wandon dake jikinsa.
Ni Mimisco ta kalleni tana faɗi " Sadiya ki sake ba ma wannan rigimammen mijin naki haƙuri. Na samu ya hakura na hada su na yi ma Saudati faɗa ta kuma ji ta ce ta yi nadama na sakata ta duka ta bashi haƙuri ya ce ya wuce. Don Allah ki sake kwaɓar ta kin ji ko?
"In sha Allahu '
Na amsa mata ina mirmishi ganin Yallaɓai na ta hararata sai ka ce ni ce na yi masa laifi.
Direba ne ya kawo ta tace na gai da yara tana sauri ne yau baban su Naja zai bar kasar yana gida yans jiranta. Ta shiga mota direba ys ja suka fice daga gidan Yallaɓai ya juya zai wuce bai yi mini mgans ba.
"Yallaɓai."
"Ba ruwanki da ni to."
Ya faɗa yana haɗe rai sai na yi mirmishi kafin na ce"Allah ya baka haƙuri."
"Ni da gidana duk hukuncin da zan yamke sai kin ce ba haka ba? Ki fita daga idona Sadiya Tam"
"In na fita idon wa zan shiga Yallaɓain?
Na faɗa ina masa wani kallo.
"Uhm za ki yi bayani ne."
"Sorry Oga."
Na faɗa ina dariya ganin yana mirmishi sai da ns saka shi ko dariya ƙarshenta ma bangarena muka koma tare ya je wajem yara ya daɗe a tare da su sannan ya zo ya na challagin ɗina wai me ya sa yaran shi ba su je makaranta ba?
Ina hararan shi na ce" Tun asuna ka fara mana yaƙi a gida ne za ka zo kana tuhumata."
Sai ya fara dariya wanka ya yi bangarena ya shirya. Ya ce zai sauke Rabi'atu a makaramta zai wuce office tun ɗazu Musbsbu ke kiran shi akwai waɗanda ke jiran shi na yi masa fatan dawowa lafiya.
Bayan fitan su na rana na leƙa Gimbiya ta sha dai kuka amma dai an warware kaya. Ni dai na sake jadadda mata ta yi haƙuri in tana so ta zauna lafiya. Ranar girki ma duk Baby ta yi mana itama nan shashena ta ci abinci muna tare da ita har dare sannan ta kwashi yaran ta suka koma bangarenta.
A ranar Yallaɓai ys ƙarishe kwanan shi a ɗakin Rabi'atu washegari ya dawo ɗakina ya yi kwana biyu sannan ya koma na Gimbiya. Ni ban san halin da suke ciki ba na ɗauka komai ya daidaita ashe ba haka ba ne, Yallaɓai dai na kwana a bangaren Gimbiya in ranar girkinta ya zagayo shima a falo kuma baya jin abincinta baya mgana da ita daga gaisuwa sai gaisuwa. Ni ban sani ba sai da ta zo tana kuka tana faɗa mini na ce ta sake bashi haƙuri amma duk da haka bayan kwana biyu ta dawo ta ce mini ba abin da ya sauya.
Jin haka da zuciya daya na ce zan yi masa mgana amma in ɗauko magamar yadda ya fara yi mini ihu a saman kaina ne na san cewa Gimbiya ta gama ɓata ma Yallaɓai rai ya gama jin haushinta shi ya sa kallonta kawai yake yi.
"To tun da ta baka hakuri ka haƙura mana? Shi kenan ita ba za ta yi kuskure ka ba ta da mar gyarawa ba?
Kawai sai Yallaɓai ya ce tun da ni ce Nene na yi masa faɗa saboda na ce abin da yake yi bai kyauta ba Allah zai kama shi.
"Ki bari Ubangijin nawa ya kamani amma ba ke ba."
Zan sake magana ya ɗaga mini hannu.
"In kika sake tare ni da mganar da ta shafi Gimbiya wallahi zan kai ƙaran ki wajen Allah. Haba kin dame ni? Kin fi sanin abin da ya kamata ne? Ko sai na ce Allah ya isa ne sannan za ki ƙyaleni da wannan mganar ne?
"Allah ya ba ka haƙuri. In sha Allahu ba zan ƙara mgana bam"
"Better for you."
Tun da ya yi mini haka na koma gefe itama Gimbiyar na faɗa mata tun da ta bashi hakuri ya ƙi haƙura ta fita batun shi in ya gaji zai seuko da kansa na faɗa mata nima irin tijaran da ya yi mini daga faɗan gaskiya. Gaskiya ne yanzu Yallaɓai ya zama masifaffe abu kaɗan sai ya fara faɗa yana yi ma mutane ihu. Maganar gaskiya Gimbiya ta ba ni tausayi duk ta rame ta saka ma kanta damuwa kuma Mimisco washegarin ranar da ta zo ta saka aka zo aka tafi da mota aka aka gyaro ta dawo kamar sabuwa. Kamar ma wani abu bai same ta ba Yallaɓai da kan shi yake sake koya ma Rabi'atu mota duk da iya amma hannunta bai faɗa ba, sannan abin da na ɗan fahimta Rabi'atu ta fara raina Gimbiya ba ta jin kunyar kallonta cikin ido kuma ba ta jin kunyarta kamar farko domin akwai rana tana shashena Gimbiyar ta shigo wallahi ba ta gaisheta ba sai da na yi mata mgana. Da man abin da na kr gudu kenan yarinyar nan ta zo ta fara raina ta, ba ta da yadda ta iya.
Ban san ta in da mganar abin da ya faru ya zaga dangin su Yallaɓai ba. Amma na fi tunanin Gimbiyar ce ba ta dandara ba ta fidda mganar. Sai ga Munnira ta kirani tana ba ni labarin jiya ta je Gwamnaja Anty Bahijja tana ta masifan wai Gimbiya mahaukaciya ce za ta jama Tafida asara ita sun lura kishinta na hauka ne da man shima ina ta jiye ma Gimbiya kar ta kai wannan lokacin sai ga shi da kanta ta zo har falona tana kuka tana faɗa mini Anty Bahijja ta je ta same ta a shago sai abin ta manta ba ta faɗa mata. Wai har tana cewa in haukan ta ya tashi ya tsaya a kanta kar ta sake gigin taɓa kayan Tafida tun da ita ba ta da hankali.
"Allah ya kyauta amma ni na san irin wannan ranar za ta zo"
Haƙuri na yi ta bata tun da ni kam ba ni da yadda zan yi da su Anty Bahijja nima ai haƙuri na ke yi da su. Na ji daɗi dai Gimbiya ta fahimci duk da tana na su akwai wani wajen da za su iya nuna mata Tafida ne ya fi kusa da su kuma tun ba a je ko'ina ba ta fara ganin haka har kuma lokacin Yallaɓai bai sauko ba ni na ba ta shawara ta kira Baba Tafida ta faɗa masa komai shi ya tako har gidanmu ya hada su ya yi musu sulhi mu ma ya tara mu ya yi mana faɗa. Dalilin zuwam Baba Tafida ys sa Yallaɓai ya sauko ya dawo yana sauraran Gimbiya amma ta ɓarar da alfarmanta mai yawa a wajen Yallaɓai
motar da ta gama faɗa a kanta tana ji tana gani Rabi'atu ke hawa motarta tana zuwa makaranta, tana kuma shiga gari da abin ta amma ita miji ke jin haushi har Rabi'atu tana ɗaukan Gimbiya a mai yi mata hassada tun da na san za ta faɗa ma dangin ta kuma kowa da maganar da zai kawo mata
Balle na ga tana da ƙawaye suna biyo ta gidan ni dai ba ruwana nawa ido ne tun da mijinta bai hanata tarkacen ƙawaye ni a wa? Iyaka dai in sun zo za ta kawo su har bangarena su gaisheni abinci ma ni nake ba su wani lokacin tun da in dai tana makaranta ni ke dafa abinci da ita ba kuma wanda ya sakani ni na saka kaina ganin wata rana sai yamma take dawowa ta gaji ba za iya wani girki ba shi ys sa nake yi dafa abincin da ita.
Mota kuma Yallaɓai ya ce bai siya ba in Gimbiya ta isa faɗan ya sa ya siya. Na ce ta yi shuru ta ƙyale shi, sai yanzu ne Gimbiya ke son dawowa jikina ta makara amma duk da haks ban gwasale ta ba. Ina ba ta shawara kamar yadda zan ba ma kaina kums ni daga ita har Rabi'atu daya na ɗauke su.
*****
Mun yi azumin watan Ramadana mun yi salla. Jidda ta dawo gida salla amma ana fice sallata koma saboda za su fara jarabawa. A bayan salla muka muka yi auran Anti yar wajen Ya Murja Kaduna muka kai ta muna gama nata muka faɗa ma Firdausin Ya Balki. Ita kuma Funtua muka kaita auran gida babanta ya yi mata. Duk fa mun zama iyaye girms ya kams mu tun da mun aurar mun kai ga jikoki ma.
An saka ma zainab ƙanwar Ma'u rana itama dangin mahaifinta a can kura ne za su aurar da ita ga ɗan katsina.
Lokacin da muka yi sha'anin Rabi'atu ba ta nan ta tafi Maiduguri ganin gida, Gimbiya ce kawai ta zo mini biki da ƙannenta har da Maryama da muka taba samun matsala. Yanzu sai gaisuwar mutumci ina anfanin to rigima? Har su Munnira duk na ce su saki tun da itama ta saki a cewar Munnira wai da ta ga uwar bari ba, domin abin mamako har su Anty Bahijja yanzu Rabi'atu na zuwa gidajensu lafiya lau kamar ba su ne masu taya Gimbiya a dawa ba.
Da ta dawo daga maiduguri tazo da tsaraba ba wamda ba ta ba shi ba, ni kaina turaren wuta har ina kyautar shi.Yarinyar an yi mata huɗuban kyauta yadda za ta siye kowa to haka take yi ko Gwammaja za mu je ba za ta zuwa hannu rabbana sai ta riƙe ma su Nene wani abun. Cikin lokaci kaɗan Rabi'atu ta yi farimjini a dangin Yallaɓai wai har Anty Bahijja wata rana a ɗakin Nene mun je gaisheta ni da Gimbiya da yara ta zauna tana yabon Rabi'atu tana faɗin yarinyar akwai hankali sai daga baya ta yi ma Tafida uziri shi ya ga abin da ya gani. Har Nene yabon ta take yi in ta zo gida nan ta yi wannan ta yi wannan har kunshin su na yan maiduguri take zuwa na musamman ta ƙun sa ma Nene a kafa da hannuwana duk wani abinci da ta san Nene na so in za mu je za ts yi ta je mata da shi, wani abun ma ni ke faɗa mata. Mimisco da man ba ruwanta ko ita tafaɗa ta ce Yarinyar nan tana da wayau ta san dubarun zaman duniya.
Kuma ita ba ta ware kowa ba, kowa na ta ne, har su Suwaiba haka take girmama su shi ys sa cikin lokaci kalilan kowa ya san Rabi'atu har mazan fa in suka zo gidan haka za ta yi ta musu rawan jiki. Yallaɓai ko sai jin daɗi yake yi yana fahari Gimbiya ko sai kuka da nadama ba ta da yadda za ta yi ƙaramar yarinya ta zo ta sha gabanta.
Muna gidan Halima za ta zo ba ta shiga shashen Gimbiya ba ta yini a bangaren Rabi'atu ba abin da ba ta bata in dai ta gani ta ce tana so za ta ce ta ɗauka. Ni dai ta so ta sake shigowa jikina na ce nahi. Ai kin ci taliyar ƙarshe amma dai muna gaisawa sannan in ta zo gidan tana shigowa mu gaisa ni ce ba na sakar mata. Da baffan Rabi'atu ya je makka shi da Antyn ta, Har Nene da su Maman farko sun samu tsaraba Yallaɓai Jallabiya da Darduma da casbaha da dabino da ruwan zam+zam. Ni kaina an siyo mini abaya yara ma kowa da na shi har Jidda dake makaranta Gimbiya ma ta samu abaya. Ni kaina wayon yarinya na ba ni mamaki sumu sumu da ita ashe ta san abin da take yi.
Su Anty Bahijja ko duk an bi su da dabino da ruwan zam-zam suna ta taɗin suna jin daɗi. Ni dai ban damu ba da duk abin da take yi ba lokacin ta ne ta yi wata rana ba za ta yi ba mu kan mu ai duk mun yi wannan bin a farko muka gaji muka haƙura Gimbiya ce ke damuna kuma na faɗa mata ta yi haƙuri amma fa ba ta da yadda ta iya da Rabi'atu. Wacce ko zazzaɓi Nene ta yi kaf yan gidan su sun zo duba ta. Na cen maiduguri su kira waya me ya sa Yallaɓai ba zo so ta ba?
Nan da ya samu hatsari Allah dai ya tsare buguwa ya yi a hannu sai gocewa a ƙafa haka suke tururuwan zuwa duba shi danginta na nan Kano na can ko suna ta kiran waya. Kamar ta goya Yallaɓai haka take ki da shi, biyayya take yi masa ko abi za ta ba shi sai ta rusuna ni fa ina gefe ne amma ni kaina na san yarinyar nan bariki kawai take gwada mana. Ni kaina zuciyata na motsawa ballanta Gimbiya? Ga shi kaumar yaran mu take yi kamar ita ta haife su an ce mai ɗa wawa. Har ta su Khalipa yanzu in dai tana gida suna bangarenta ita kenan ba su abubuwa suna ciye-ciye an ce mai ɗa wawa Yallabai gani ya ke yi a kan Rabi'atu xai iya faɗa da kowa. In Jidda za ta koma makaranta ba ta zaune ba ta tsaye sai ta ga ta koma ita ce kawo mata wancan ta ya ta wancan kuma duk ya gani kuma wallahi hakan yana tasiri. Baby ko daman ta zam yar ɗakin ta ko gidansu muka je wani abu