Turken Gida Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   43 / 55

126K to 129K   out of 163.1K words

daga gani suna da hali da rufin asiri. Sannan kamar yadda suka ce ne Tuwon girma miyan shi nama shima Yallaɓai ya yi harkan girma in sun yi masa kara babu laifi a ciki. Ban bari su Muniira sun tafi ba na ce su tsaya mu raba kayan nan suka ce bai kamata ba na bari in Yallaɓai ya zo ya gani sannan sai da suka faɗa na yi wannan tunanin. Dare ya yi sosai shi ya sa ban kai su gida ba tun da Yallaɓai ya hana ni tukin dare tun da na faɗa rami wata rana na dawo daga ɗorayi ni da Baby da Yumna mota ta maƙale na kira Yallaɓai a waya. Ƙarshen ta dai nan motar ta kwana sai washegari aka ciro ta daga ramin.

Mun yi waya da Marwa sun wuce. Farida ce ta ce mini tana Gwammaja can za ta kwana sai a safe za su ɗau hanya. Ni da kaina na faɗa mata kayan da dangin Rabi'atu suka kawo mini sai itama take ce mini.
"Haka suka kai ma Gimbiya. Sannan nan ma bayan na su Nene har da na yayyen miji, har maza suna da kula. Waliyi kuma Baba Tafida na da shadda."
Na riƙe baki ina faɗin" Haka Musbahu ya ce. Ma sha Allah. Allah ya saka da alheri ya ba mu zaman lafiya."
Ta amsa da Amin ta cigaba da faɗin" Ai Gimbiyar da kyar ta fito fuskar nan ta kumbura saboda kuka na ce sakarya zauna ki kashe kanki saboda namiji. Shi kin ga bai fasa ba, ba kuma zai fasa ba ko da mutuwa za ki yi"

"Wallahi.."

Na faɗa ina jinjina kaina.

"Da zai fasa tun boren da ta yi a farko da ya fasa ɗin."

"Ai ba zai fasa ba wallahi. Ko don ya ga karshenta ma sai ya ce sai ya yi. Ai an ce da safe Mimisco ta je ta yi mata faɗa akan abin da ta yi jiya. Nene ma an ce ta kira ta a waya shi ne har yau ta ɗan saki jiki kaɗan."

"Allah ya kyauta "

Na faɗa ta amsa da Amin sannan muka katse wayar.
Su Jidda sai wajejen goman dare Adanan ya dawo da su ina ta ma kiran wayarta ba ta ɗauka ba suna shigowa na fara masifa sun barni ni kaɗai a gida ta je sun yi zaman su.

"Ki yi hakuri Umma. Ba mu samu me dawo da mu ba ne. Uncle Musbabu ne kuma Anty Mubeena ba lafiya ya tafi gida. Sai Uncle Adnan ne shima bai daɗe da dawowa ba."

"Ba sai ki fito ki jagoranci ƙannen ki ku samu adaidaitasahu ku dawo gida ba? Sannan ina kika saka wayarki ina ta kira ba ki ɗauka ba?

"Ban ji kiran ba Umma tana jaka "

Hararanta na yi ta wuce tana dariya. Adnan da man bai shigo ba yana ajiye su ya juya. Baby ce ta fara mini surutu wai Amaryan Abba an kawo ta Gwammaja, kaf labarin abin da ya faru sai da ta ba ni Yumna saboda Gajiya a can ta fara barci ko da suka shigo tana saɓe a kafaɗan Jidda. Sai na ce ta shigar mini da ita ciki.
Sai da duk ta gama surutunta sannan ta ce mini wai yunwa take ji.

"To ni ce zan ta shi na dafa miki abin da za ki ci kenan uwata Maimuna?

Na faɗa ina hararanta sai ta miƙe tana dariya ta wuce na rakata da tsaki. Kayan da man su Munnira suka kama mini na kai shi ɗayan bedroom ɗin da niyyar sai Yallabai ya gani sannan zan yi kasafin shi. Na ɗauka zai shigo yi mini sallama ne amma tun da na ga sha ɗaya ta yi na cire rai. Ni kaɗai a falo su Jidda sun gama duduman su sun shige ciki.
Nima dole na tashi na kashe komai na shiga ciki. Tiolet na shiga na kama ruwa ina fitowa na ga wayata na haske kafin na ƙarisa wayar ta katse.

Yallabai ne, ina shirin bin bayan kiran shi sai ga saƙon shi ya shigo.

"Ku kwanta sai da Safe Sadiya ta. Tariq ya rako ni yanzu haka ma muna ƙofar gidan."

Sai na ji jim ina sake bin saƙon sa da kallo, to mi ye na sai ya wani faɗa mini za a raka shi ɗakin Amarya. Duk da na so kar na ji zuciyata ta motsa sai da kishi ya taso mini. Shi ya hana ni mayar masa da amsa, ganin kamar zuciyata ta ɓaçi sai na juya na koma tiolet na ɗauro alwala na zo na yi shafa'i da wuturi na yi addu''o'ina da Allah ya cire mini damuwa a wannan daran ya sanyaya mini zuciya.
Na yi ta maimaita LA'ILAHAILLAH ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZ ZALIMIN.
Sau arba'in har sai da na ji zuciyata ta yi sanyi.
Ina idarwa na yi shirin barci Yumna da man tuni ta kai england. Gefenta na kwanta bayan na yi mana addu'an barci na shafe mu gabaɗaya wutar ɗakin na rage sannan na kunna suratul Maryam a wayana na ɗan rage ƙara na saka shi gefena na rumgume y'ata muka shige bargo.

Da farko sheɗan ya fara hasko mini abubuwan da ba su kamata ba na yi ta ta'awizi a cikin zuciyata cikin ikon Allah sai barci ya fara fizgata ban daɗe ba barci ya sace ni, ba ni na farka ba sai asuba na kuma ta shi wasai kamar ba ni ba. Na ɗauka zan ga Yallaɓai a ranar shima haka aka yi har dare ba shi ba wayarsa da Amina ta zo yi mini sallama ma nuna mata kayan sannan na diɓa mata kayan fulawan da kayan kwalliya na ce ta kai ma su Afra sai filet da kula guda ɗaya. Tun da gogan yana can yana cin amarci bai samu fitowa ba, aka sake kwana ba Yallaɓai ba wayarsa ni kuma ban neme sa ba na riƙe mutumcina amma in na ce zuciyata ba ta motsa ba wallahi na yi ƙarya daurewa kawai na ke yi. Amma ni kaina na san Yallaɓai ya samu chajiin Lambu ba zai yi wasa da ban ruwa ba.

  Da na ga ba shi da niyyar zuwa ranar laraba da yamma Rahila da Ma'u da ke da tsohon ciki suka sake leƙoni da man ina da niyar kiran Hauwa ko Munnira ne su taya ni na raba kayan sai ga su Rahila. Su suka taya ni muka zauna na kasa shi, har Gwaggo sai da na dibar ma turaren wuta da kayan fulawa haka su Ya Aina. Hauwa da Munnira ma daidai da nawa na ɗibar mana saboda a sha'anina ko ya'nuwana albarka yadda suke tsaya mini. Kayan kwalliyan kuma suka ce na bar ma yara tunda ƴaran mata gare ni, Alhajinmu ma zaɓa masa yar kula mai kyau na ce zan kai masa Atamfar kuma suka ce na ɗinka tunda ni suka ba mawa. Su suka tafi da y'an gidanmu har na Gwaggo da Alhajinmu tun da Dorayi suka ce za su fara sauka kafin su wuce gidajen su, jin haka yasa na diɓi kayan fulawan da turare na ce Ma'u ta kai ma Baaba, duk da ta daɗe a can Yashe sai a satin nan ta dawo Kano.

Sun fita ba daɗewa aka kira mangariba ina cikin yin salla na ji ana ta kiran wayata sai da na idar na duba na ga Yallaɓai ne sai bayan kwana biyu ya tuna damu. Jidda ma sai jiran shi take yi tana so ta komawa makaranta ranar lahadi. Ta ce mini ta kira shi bai ɗauka ba, na ce kar ta sake kiran shi ai ya san da komawar na ta.
Sau biyu yana kirana ina salla sai da na idar ya sake kira wayar na hannuna na ƙi ɗauka haka kurum na ji ina jin haushin shi. Har kwana biyu muna gari ɗaya amma Yallaɓai bai neme ni ba! Gwara Gimbiya suna gida ɗaya na tabbata ba zai kwana su tashi ba ta gan shi ba.

Sai da ya kara kira na huɗu sannan na ɗaga tana ma gabda katsewa.

"Umma Sadiya."

Ya faɗa yana ɗariya. Sai na ji zuciyata ta ƙuntata, wai Umma Sadiya sai yau na ji kamar da gayya ya faɗi sunan e mana na zama Umma shi ko yanzu ai sabuwa gare shi.

"Uhm Ango."

Na faɗa ina ƙoƙarin daidaita yanayina.

"Uwargidata."

Yallaɓai ya iya bariki da ban sani ba sai da ya auri Gimbiya na san ko lauya ya karanta sai haka in dai wajem lauya zence ne.

"Ina yini? Ya amarci?

Na faɗa ina ƙoƙarin sakin fuska kamar yana gabana.

"Lafiya lau. Ya yarana  ya gidan? Sai kuma kika manta da ni Abar ƙaunata?

Kamar na yi masa ashar sai kuma na fasa.
Cije baki na yi kafin na ce" Ah na bar ka ne ka ci amarcinka. Ina Amarya?
"Ga ta nan tana jin ki."
Ya faɗa yana yar dariya.
"Ayya ka gaisheta. Ina fatan ba ta yi baƙunta ba?
"Ta yi fa, ta na ma kan yi, ga ta nan ma kwance sai rakin tsiya."

Kasa magana na yi saboda na ma rasa me zan ce. Hakan bai sa Yallabai ya yi shuru ba ina jin sa yana dariya yana mata magana a ƙasa ƙasa wai ga ni ina son magana da ita ni yaushe muka yi haka da shi? Ina hamgame da baki ban rufe ba na ji muryanta tana yi mini Sallama.

"Umma ina yini"

Shike nan daga Anty na koma Umma, Yallaɓai ya gama da ni.
Sai na danne na saki fuska kamar tana ganina na amsa mata gaisuwar ina tambayanta baƙunta ta yi mirmishi.
"Ki saki jikin ki kin ji ko? Ai gidan ki ne"
"Yaushe su Jidda za su zo mini?
Ina riƙe baki na ce" Ba yanzu ba. Sau nan gaba Jidda ma ranar lahadi za ta koma makaranta in sha Allahu."
Sai ta ce Allah ya nuna mana, sai ya karɓi wayar yana ce mini gwara dai na yi mata faɗa taki sakin jiki.

"Ka yi haƙuri za ta saki na ɗan lokaci ne. Kuma ka san haka ke faruwa da kowacce amarya."

"Wallahi na tuna kema haka kika yi ta mini. Da na matso kusa dake ki fara mini kuka kina faɗin don Allah kar ka taɓa ni ba na so."

Ya ƙarishe faɗa yana kwaikwayin muryata wai, baƙinciki da takaici suka yi mini rufdugu kamar Yallaɓai ya ruɗe, ni na ma kasa mgana ina shirin ma na kashe wayata ne na ji yana faɗin" To itama haka take yi mini, in na kalleta ke kawai na ke tunawa a wancan zamanin Sadiya ta."

"Uhm"

To me zan ce? Ko na ce wani abu ba zai gane ba giyar amarci ne ke ɗiban sa.

"Maganar komawar Jidda makaranta ranar lahadi ne."

Na faɗa da ƙoƙarin na kaudar da maganarsa.

"E wallahi na sha'afa sai da na ga kiranta jiya. Zan tura mata kudi ta yi siyayya kafin na shigo gidan.'

Wato ba ma yanzu ba? Duniya sabuwa a wajen Yallaɓai.

Ban ce masa yaushe zai zo ba? Na ce Allah ya kaimu. Yumna ya tambaya na ce masa tana falo na ɗauka ya kirani ne mu gaisa amma sai na ji yana faɗa mini kwana daya daga gidan Mimisco aka kawo musu abinci jiya ko da yau ma duk takeway ya yi musu.

"Gaskiya. Ga Gimbiya a kusa ai ita ya kamata ta baku abinci har sai Rabi'atu ta yi bakwai."

Sai ya yi shuru maimakon ya amsa maganata sai kawai ya ce" Ina neman alfarman daga gobe ki dan riƙa dafawa damu, sabon direba zai riƙa zuwa yana ɗauka."
Na buɗe baki kamar yana ganina kafin na ce" Har sai an zo nan? Miye amfanin matarka dake gidan?

"Ai na san da ita na kira ki Sadiya."

"To me ya sa sai ni? Kana da tabbacin zan amsa alfarman taka ne?

Sai ya yi mirmishi kafin ya ce" Nima ban san me ya sa a komai nawa in ya taso ke nake son kira ba. In wata bujata ce wajen ki nake son fara zuwa. Ina da yaƙinin ko ba ki yi mini abin da na ke so ba in na faɗa miki kina bani mafita."

Kalamansa suka kashe mini jiki da na kasa mgana.

"Ita ta ce ba za ta yi ba Sadiya ba zan kuma taɓa matsa mata ba. Ke ce na ke da yaƙinin kina yi ma zaman auren mu kara na kuma san wannan karan ma ba za ki ƙi yi mini karan da kika saba ba."

"Uhm"

Na faɗa a ƙasan makoshi.

"Ba zan takura ba, in kina ganin ba zai yuyu ba sai mu bar shi na cigaba da oder. Amma kamar bai kyautu ina da matan aure har biyu na riƙa siyan abinci a waje ba, sannan ita kanta ya za ta fassara lamarin?

Sai na ga kuma gaskiya ya faɗa duk da wata zuciyar na ce mini na ce ya cigaba da siya amma na kasa. Sai da na tuna da kalaman Alhajinmu da ya ce  na yi ma abokan zamama alheri da ƙarfina da jikina da aljihuna. Ruwan su ne su ma yar da alheri da alheri ko su ma yar da alheri da sharri. Ni dai in dai na yi don Allah ladana na wajem Ubangiji kuma ya gani na sauke haƙƙi da nauyin zaman tare. Sai kawai na ce masa to shike nan da yaushe da yaushe za a riƙa zuwa karɓan abincin?

Cikin murna ya ce" Ko sai ɗaya a rana is ok."

"Shike nan Allah ya ba ni iko."

"Na gode Abar ƙaunata. Allah ya kare mini ke."
Na amsa da Amin a ƙasan maƙoshi, ban wani ja mgana ba muka yi sallama bayan ya ce mini za a kawo cefane a raina na ce tunda hidimar amarya ya tashi ba. A washegari aka kawo cefane har da su Nama da kaji, Sadi ne ya kawo sabon Direba Salisu Yallaɓai ya ɗauke shi ya koma direban kamfani. Sai Salisun ya kawo Sadin a matsayin madadin shi anan gida tun kafin ma bikin ga shi shima har an saba ya fara zama ɗan gida ya kai yara makaranta ya dawo da su sannan ya yi aike aike da kawo cefane.

Ban faɗa ma kowa ba, ni na ke yi abincin Sadi na kai ma Yallaɓai da Amarya. Kuma a satin na je gidajen su Hauwa na kai musu sakon su amma ban amince na yi musu ma zencen ba, dalilina shi ne ba komai ne na aure ya ke buƙatar fallasa ba na bar ma cikina. Kuɗi Yallaɓai ya tura ma Jidda ita da direba suka tafi kasuwa ta yi siyayya. Kayan abinci da man daga gida take ɗiba kayan kwalama ne su bickit sai mayuka da su pad da kayan tea ta je ta siyo. Anan gida ta yi miyanta ta yi cincin  da Donut za ta tafi da shi, tun ina sa ran zuwan Yallaɓai har na cire ma raina, ganin ma daga wajen Amarya sai ya fara dawowa wajena kafin ya koma wajen Gimbiya shi ya saa na kira Surayya Dee ta aiko mini da haɗin kazar sababi na uwargida. +234 803 277 3332
Sai kuma a gida ina ta cin ganye da kayan marmari, ba domin wai na gyara ma Yallaɓai ba aa sai domin nima macece ina bukatar na gyara kaina. Ko da na ba ma arba'in baya ban tsufa ba akwai  ruwa a jikina har yanzu kuma ko gobe ai ruwa na mganin dauɗa nima asabuwar Yallabai ya aure ni muka gurji juna har ta kawo mu ga yau, saboda haka in ma ya manta mafari zai dawo mafarin na shi dolen shi dai.

Ba Yallaɓai ya zo gidana ba sai ranar lahadi da safe ranar da ya cika sati ɗaya a ɗakin Amarya. Kun gan shi da wata bakar jallabiya ya yi kiɓa ya yi haske ga tumbi ya ƙara tasawa. Shima dalilin zuwan saboda tafiyar Jidda ne. Adnan ne zai ma yar da ita. Ita ta kira shi ta ce za ta tafi ba su yi sallama sai ga shi da jallabiya iriin ma fitowar na dole ne.
Baby da Jidda suna ta murna ganinsa suka dafe shi suna ihun ga Abba ni ko kallon su ban yi ba. Yallaɓai ya ba ni mamaki muna gari ɗaya? A wayar ma sai ya ga dama yake kira ko kuma in ta shi buƙatar ya taso shi zai kira yana rage murya yana daidaiciyar mgana.

Jidda na tafiya kunya ce ta hana shi shima ya wuce sai ya ɗan shigo ciki. Ni ko abun kari ban yi masa ta yi ba sai ya ce wai na ware shi kamar ba ɗan gida ba.

"Na ɗauka ka ci kai da Amarya."

"Ba mu tashi ba wayar Jidda ce ta tashe ni, na baro ta can tana barci.'

Ko kunya Yallaɓai ke faɗa mini haka na tusa buredi a bakina na yi masa wani kallon renin wayau bai ma gani ba yana can yana mgana da Baby, Yumna kuma ta ishe mu da kiran sunan shi Abba sai ya amsa sai ta yi shuru sai kuma ta sake kiran shi. Tare da mu ya zauna ya karya yana hira da ya'yan shi, ni ina gamawa na shig ciki sai da zai wuce ya biyo ni yana yi mini sallama nan ne na ke nuna masa sauran kayan da dangin Rabi'atu suka kawo mini sannan na faɗa masa na yi kyauta da wasu.

"Kar ki damu kayan ki ne fa. Ke suka kawo mawa kina da damar yin abin da kika ga dama da shi, yau ko da ma nawa ne tuni na yarje miki ki aiwatar da gabaci in dai ba na nan."

Ban bari daɗin bakin shi ya yi tasiri a kaina ba na yi masa sallama. Har yana cewa ko rakiya babu? Na shige tiolet ina faɗin fitsari ya matse ni ya fita yana dariya shi kam shi ya san na zille ne kawai sai da na ji tashin motarsa sannan na fito ina ƙunƙuni ni kaɗai.
A ranar na kira Alhajinmu na gaishe shi shi ne yake faɗa mini jiya Yallabai ya kawo masa Amarya ta gaishe shi Amarya ta kawo masa kyautar turare. Sai na saki baki ina jin Alhajinmu kawai ina mamakin Yallaɓai bayan daɗin baki yanzu har makirci duk ya iya.
Kafin mu yi sallama Alhajinmu Jadadda mini yake yi na zauna lafiya da abokan zamana don Allah , na ce to ni kam ai ban isa na ƙara komawa gida na ce Yallaɓai ya yi mini wani abu ba sai Alhajinmu ya ce sharri na yi masa.

Can da

43 / 55