Turken Gida Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   50 / 55

147K to 150K   out of 163.1K words

tsaye na ce ni na je dubiya ne Gimbiya kuma daga wajen aiki ta wuce shago. Kuma ba mu san yau za su dawo da ita ba.

"Ai ko dai tun jiya ma Megidan ya so ta dawo Allah bai yi ba sai yau."

Wato kenan yana sane mu ne dai bai ga damar sanar damu ba ya yi ma kansa ruwa na kawo musu ba su ma  sha ba.

"To ga Rabi'atu nan mun san ana ƙoƙari kula da ita Allah ya ba da lada."

Na amsa da Amin Gimbiya sai da suka fito haraba ta leƙo suka gaisa direban da ya kawo su ya kwashe su ya ma yar. Na koma na sake duba Rabi'atun muna ɗan yi hira kaɗan ta ji sauki sai dai ta rame. Ni dai na ga abin mamaki yarinyar nan tana jin diran shigowar mota ni ko ina zaune na ce ina jin Yallaɓai ne ai sai da na yi suman zaune saboda barikin da na gani ganin idanuwa. Yarinyar nan tana zaune amma sai ga ta kwance ta narke kamar ruwa, yana shigowa da man bangarenta ya nufo, yadda ya ganta kwance tana wani lumshe ido ko lura da ni bai yi ba ya nufeta duk ya  rufe ya tarairayota jikinsa yana tattaɓa goshin ta.

"Baby me ya faru jikin ne?
Kan ki ke ciwo? Ko zazzaɓin ne?

Ya ke faɗa yana taɓa kanta da cikinta ita ko ta narke masa tana shagwaɓa kamar wata jaririya.

"Abba uhm"

Ta ke faɗa har da gutun hawaye, shi kuma gabaɗaya ya ruɗe.

"Me Abba ya yi? Uhm faɗa mini."

"Ba kai ne ba'

Kawai sai ta fashe masa da kuka cikin rawan jiki ya ƙamƙameta yana faɗin"Abba ne ko? To Abba ba zai ƙara ba kin ji ko?

Ɗankari!

Haka na faɗa a zuciyata. Gimbiya ta daɗe tana ce mini yarinyar nan muguwar yar bariki ne ban sani ba, sai yau da ta nuna mini Umma na ke ita kuma Rabi'atu ina zaune tana abin da ta ga dama in shi bai ganni ba ita ai ta san da ni. Zuciyata ta motsa amma ban bari na zubar dakaina a gaban su ba sai na miƙe ina mirmishin ƙarfin hali.

"Mu kwana lafiya Rabi'atu."

Sai a lokacin shi ya farga da ni, ya ɗan yi shock tun da har ya ɗan sake ta, ta bar cinyarsa ta zauna da ɗuwawunta a saman kujera.

"Umma to sai da safe."

Ta faɗa cikin sanyin murya ji na yi kamar ma juya na kamata na yi bugu. Ban taɓa jin kishinta da haushinta irin na yau ba.

"Sadiya da man kina nan zaune?

"Sannu da dawowa."

Na faɗa ban jira amsar shi na bar musu falon, duhu duhu hazo hazo na ke gani kafin na kai bangarena. Na yi shuru zaune ina tunani,ko ma me ya faru yarinyar nan da gangan ta yi, tun da ai ni da ita ne zaune muna hira, raina ya ɓaci kenan ta shirya mini wulakanci ne? Daga abin arziƙi duk abin da ta ga ina yi mata darajan Yallaɓai ne da sauke haƙƙoƙin zaman tare amna ni ai ba ta isa na koma bayan ta ba. Amma tun da ta ce haka mu zuba mu gani, ni ko zan nuna mata na riga ta zuwa duniya ita yarinya ce har yanzu. Ranar raina a bace na kwana ko Jidda ta kira ni a waya ban wani saurareta ba na ce ina jin barci washegari da safe sai ga Yallaɓai ya shigo yana yi mini kame kame ya ɗauka zan nuna masa wani abu ne ya ga bayan gaisuwa kallon musulumci ni ban yi masa ba ma shima ai munafukin ne.

Ko kunya bai ji ba yana faɗa mini Rabi'atu na son tuwo, na ɗauka zai ce ne ni na yi mata wallahi da in na fara faɗa masa mgana sai abin da na manta sai ya taimaaki kan shi ya kira Baby ya saka ta. Asabar ne ba makaranta Tahfiz kuma suna ajin bita ne yau ba ta je ba. Tun da y'arsa ya saka ban yi magana ba na yi shuru kamar zan ce ta je can bangaren nata ta yi mata sai na fasa ganin gogan yana can ya tare. Ranar ko fita bai yi ba har su Adnan gida suka zo suka same shi Gimbiya ko tun safe ta wuce Rano an yi musu rasuwa sai gobe za ta dawo shima Yallaɓai in dacewa zai yi ai ya dace ya je tun da yaron ƙanin Hajiya ce ya rasu saurayi ne ma Gimbiyar take faɗa mini to yarinya ƙarama ta saka shi a gaba har lahadi bai fita ba Baby ya samu tana yi mata wahala ranar ma da na ce ta wuce ta je Tahfiz hanawa ya yi wai ta bari wani sati kawai.

Ban yi magana ba saboda na shirya mafita na. Ranar litini da safe ya fita ya ce mini za su je Rano gaisuwa. Na ce Allah ya tsare ni da man mun tsara da ni da su Munnira Gimbiya gobe za ta dawo ranar bakwai za mu koma tare da ita amma na kira ta a waaya ta haɗa ni da Hajiya na yi mata gaisuwa. Tun ranar nan da na kama shi yana wannan ɓare ɓare jikin ya daina sha mini ƙamshi, ni ko na yi kamar ban ma gane shi ba tare suka fita da Rabi'atun ya sauke ta a makaranta ai ko ta gane ba ta da wayau sai yamma ta dawo gida ban yi kuma abinci da ita ba. Sai ga ta shigo shashena ta zauna ta ɗauka irin baya ne in ce ta shiga kitchen ga abincin ta ga na yi mata kiri ƙiri.

"Umma ba ki yi sauran abinci ba?

Kai tsaye na ce mata yau ban yi girki ba indomie ce Baby ta dafa da suka dawo makaranta. Ba su nan kuma sun tafi islamiya na samu an saka su wata islamiya anan anguwar da muka dawo ba nisa. Su Khalipa da man wajena Gimbiya ta bar su da za ta fi.

"Ki je ko yar indomoe ki sulala ki ci.'

Ta ce mini to, ta tashi ta wuce na rakata da harara ba wai haushin abin da ta yi mini ba ne a'a haushin yadda ba ta raga mini ko don karan da na ke yi mata ba.
Na yi kyafci na ce za ki gane ba ki da wayau yarinya.
Tun daga ranar na daina ije mata abinci sau biyu tana zuwa tambaya na ce yara sun cinye daga nan ta fahimci dai ba zan ba ta ba ta kama kanta. Sai Yallaɓai ya ce ba ta da lafiya ba ita iya komai amma ranar girkinta su kule ba ka jin motsin su to da man ni ce na ɗaukar ma kaina kuma na yaye Gimbiya da man yar gaskiya ce ba za ta yi ba shi ya sa bai taɓa saka ta ba.

Da Gimbiya ta dawo kamar zan faɗa mata sai na fasa kawai na share saboda kowa ya ji sai ya yi mini Allah ya ƙara. Munnira ta zo ranar jumma'a mganar tafiyar mu Gobe muka shiga wajen Rabi'atu ta duba ta. Da ya ke muna ta knoking shuru ni kuma na ɗauka ko tana salla me tun da bayan mangariba ne sai muka tura kofar tun da a buɗe yake muka shiga abin mamaki ta gyara ɗakin nan tas  yana tashin ƙamshi sai na tuna ashe yau gogan yana ɗakin ta ne, sai muka zauna saman kujera muna jiran ta ba ta ji shigowarmu ba sai ga ta fito da wata shigewar riga marabanta da tsirara kaɗan ne. Ko ta yi tunanin shi ne ya dawo ko da man dai haka take yawon ta a ɗakin ta ban mu sani ba da ta gan mu ta ji kunya da gudu ta koma ɗaki ta ɗauko hijabi ta saka ta fito muka gaisa tana rufe fuska muna fita haraba Munnira ta kalleni kafin ta ce.

"Ke na taɓo ki da mgana. Wai yarinyar nan ne ta kile haka?

Ina dariya na ce" Ras. Ai Namiji ya kilar da ita."

Munnira ta riƙe baki kafin ta ce" Wallahi in ka ganta kamar ka saka mata yatsa a baki ba za ta iya cizawa ba.'
Uhm kawai na ce saboda Rabi'atu ta sauya idanuwanta sun buɗe ko na ce yanzu ta san daɗin namiji shi ya sa.

"Kin ga idanuwanta ƙif ƙif na marasa kunya yanzu."

Mirmishi kawai na yi ban yi mgana ba.

"Ba shakka Tafida ya ba ta zuma ta ɗanɗana. Sadiya sai ku shirya za ta haɗa kafaɗa da ku yanzu."

"Me ya rage? Ai tama fara haɗawa."

Na fada ina danne abin da ke ta so mini, yarinyar da Yallaɓai ya ce kwana take yi da zazzaɓi ne haka shi ya sa da man ya ce ita ba za ta je Rano ba ni da man na yi masa mgana ne kar daga baya ya ce an ware ta tun da yanzu ba ya so wani abu ya same ta. Washegari su kaɗai muka bar ma gida da yara kaf muka tafi ya ba mu mota Sadi ya kwashe mu, su kuma su Hauwa suna motar gidan Mimisco har da su Anty Bahijja aka yi tafiyar da Mubeenan Musbahu da tsohon ciki har ina ta faɗa na ce kamar dole ta zauna a gida mana tun da cikin ta ya tsufa.

Can muka yini sai dare, Amma mun je gidan Marwa an haɗu ana ta hiran duniya mun haɗu da Sameena ta ce mini gobe ma za ta koma tana dariya ta ce ya ta gan mu da mutuniyar nima ina dariya na ce ta ji wuya ne ta dawo muka haɗa kai don Allah, Sameena na ta dariya ina ta ya ta. Sai bayan isha'i muka koma gida muna mota Jidda ta kirani tana faɗa mini wai Abban su ya kirata ya ce in sun samu break ta zo gida ta duba Anty Rabi:atu ba ta da lafiya sosai.
Kamar Jidda ce Yallabai na rufe ta da faɗa ta in da na ke shiga ba ta nan na ke fita ba.

"Ko hutu kuka samu ki tafi gidan Ya Hamza ma ji kin kamo hanya kin dawo sai na ci uban ki Jidda. Saboda kawai duba Rabi'atu sai ya ce ki bar karatun ki  taho! Gaskiya Yallabai ya fara samun matsala."

Ita dai da ba ta san mafari ba hakuri ta ba ni ta ce wai ta faɗa masa suna ma test ne, bayan mun gama wayar na kalli Gimbiya ina faɗin" Kin ji mijin ki ko Gimbiya?
Ta yi uhm kafin ta ce" Wallahi ni dai ina tunanin ba haka nan ta bar sa. Ba ki ganin yadda ya ke fita hayyaci a kanta ne?
Wai Jidda ta zo dawo makaranta kawai saboda ta duba yar gold? Da wani abun ne ya taso tsaye zai yi ya ce ba za ta zo ba amma da ya ke yar gold ce ya ce a zo a duba ta mana."

Ni takaici ma ya hana ni mgana, ko da muka isa gidan yana bangarenta shi dai ya zo ya yi mana bangajiya ban da ita ni Gimbiya ta ma ce mini ko gaisuwa ba ta yi mata ba da a ce da ne zan yi mata mgana yanzu ko kiɗa ya sauya shi ya sa rawa ma ya sauya. Shi kuma gogan bai nuna mata abin da ya kamata ba. Yadda bai nuna mini ya kira Jidda ba nima ban nuna masa na ji aikin da ya yi ba. Sai da kan shi ya zo yana ce mini Jidda ta so ta zo gida amma tace suna test a raina na ce ta so ko ka so,  ya na neman ya riƙa kashe ma Baby karatu saboda matarsa kawai sai ya ce ta zauna ta yi ma Rabi'a girki ne ga an yi sau ɗaya sau biyu ana uku na ce ba zai yuyu ba.

"Ba zai yuyu ba kika ce Sadiya?

Ya faɗa da safiyar lahadi sun shirya Sadi na jiran su zai kai su Tahfiz wai Baby ta zauna ta je bangaren Rabi'atu ta yi mata shara sannan ta tambayeta abin da take so ta dafa mata yarinya ta ce hadda za ta je tana bita yau amma ya ce ta haƙura ai jiya ta je.

"E gaskiya ba ta yuyuwa ka kashe ma yarinya karatu kawai saboda bukatar matarka. Yallabai ta ɗauko wata daga can garin su ko ka samo mata wacce za ta kula da ita fakat kenan."

Sai ya kasa mgana ni ko na yi masa mai gabaɗaya sai na ce" Kuma ni ban ga aikin da zai gagareta ba ai ba ta ciwo tun da ta iya ji da hidimarka to za ta iya ji da hidimar kanta da gidan ta ma"
Tun da ya ji na faɗi haka ya kiyayi tsayar mini da karatun yarinya ban san ko maganar da na yi masa ba ne, ko da man sun tsara hakan sai ga wata yarinya an kawo kamar za ta ɗan girmi Baby ƙanwar Antyn ce ta yi candy aka kawo ta taimaka ma Rabi'atun ta bakin Gimbiya ta ce da man akwai wacce za ta taimaka man aka bar shi yana ta faman wahala. Tun da ga lokacin kowa ya samu lafiya ta warke tun da yanzu laulayin ya bi jiki amma tun da makira ce a ko da yaushe nuna masa take yi tana cikin ciwo saboda ya lalace a kanta.

Mubeena ta haihu amma aiki aka yi mata da nagudan ya taso mata ni Musbahu ya kira uku na dare na ce ya zo gida ya ɗaukeni tun da ba zan iya driving ba. Yallaɓai na ɗakin Gimbiya a waya na kira shi sai ga shi ya fito, da man ina haraba ina jiran Musbahu yana zuwa bayan sun gaisa kawai ya ɗauke ni muka tafi, muna asibitin har safe ba ta haihu ba kan yaro ya jirkice suka ce aiki za a yi mata Musbahu ya saka hannu. Bawan Allah duk ya ruɗe sai da Adnan ya zo yana bashi baki. Da safen Yallaɓai ya zo shi ya biya ma kudin aikin da aka yi mata an samu nasaran fito mata da yaron ta namiji ƙato mai kama da uban shi.  Ba ni na koma gida ba sai da na ga ta farfaɗo y'anuwanta sun zo suna ta mini godiya domin ni ce na tsaya a tare da ita har ta samu kanta na ce ba komai Musbahu da Mubeena sun ɗaukeni da daraja shi ya sa nima nake daraja duk abin da ya shafe su. tun da kuma aka yi haihuwar bana zaune kullum sai na je asibitin kwanan ta huɗu suka koma gida to can ma gidan haka nake sintiri , suna an ɗaga sai sati biyu kan lokacin maijego ta ji sauki. Y'anuwanta sun ce za su dauketa bayan suna da Musbabu ya nemi shawara ta na ce ya barta ta je gidan kamar gobe ne.

An yi suna yarinya ta ci sunan Hajiya iya Hafsat. Musbahu ya yi ƙoƙari ya yi abin da kowani uba zai yi raguna biyu aka yanka mata Ya Usman ya siya ragunan sunan. Mun sha suna har Nafisan katsina ta zo da Safiiya ni da man mune yan gaba gaba Gimbiya da wuri ta zo har yara da suka dawo makaranta na saka Sadi ya kawo su, Amaryan Yallaɓai sai yamma ta zo daga makaranta saboda kuma tuƙo kanta ta yi ba ta yi dare ba da dokar megidan ban da tukin dare. Wannan kan gaskiya ne daga ni har Gimbiya in muka fita da mota muka kai dare ba mu dawo ba haka zai yi ta kira yana mana faɗa. An yi suna lafiya an watse bayan suna da kwana huɗu yanuwanta suka ɗauketa zuwa gida sai dai ya riƙa zuwa yana ganin ta.
Ni dai na yi mata atamfa da kayan Baby iya karfina. Sai da ta gama wanka za ta dawo ne Musbahu ya zo da kanshi ya ke faɗa mini abin arzikin da Yallaɓai ya yi masa ni ban ma sani ba cewa ya yi ya tashi daga gidan shi ya yi ƙarami ya bashi gidan da na taso ya zauna a ciki ya bar masa na wajen na shi sai ya saka haya a ciki. Kai na yi masa murna kuma na san Yallaɓai ya yi haka saboda ni, domin ko kwanaki da ya ce zai saka haya magiya na fara yi masa ina son gidan nan bana so na ga an bama wani can bare gwara na gida.

Da na yi ma Yallaɓai  godiya hararata ya yi kafin ya ce" To ya zan yi? Gidan nan ji kike yi da shi kamar me. In na ce zan siyar ki ji haushina in na ce haya ma kice aa. Shi ya sa sai na yi tunanin gwara na ba ma Musbahu shi sai ya bar mini na shi, tun da na ga in shi ne zaki ji daɗi yaron ɗakin ki ne"

Ina ta dariya ban yi magana ba wai zan ji daɗi yaron ɗaki na ne kuma na ji daɗi sosai. An je an yi ma gidan fenti da gyare-gyare Mubeena ta dawo, ta kuma zo har gida ta yi mini yini ita da Anna(Hafsat) daga baya nima na je gidan na da wuri sai na ke ganin kamar zan waiwaiya na gan ni ina shiga ina fita a gidan wasu shuɗaɗdun al'amura ba za su taɓa shuɗewa ba, saboda a gidan nan abubuwa da dama sun faru sai dai godiya tun da yanzu mun samu cigaba ne.
Kowa ya ji labari sai ya yi ma Musbahu murna tun da ya samu cigaba gidan shi kuma Yallaɓai ya saka yan haya.

An gama gyara shashen Yallabai falo ɗaya ne da bedroom uku. Ni har mamaki yawan bedroom ɗin na yi da na tambaye shi cewa ya yi ba ruwana na jira mana na gani. Sai na kama bakina. Ya yi shirin shi har kayan funitures ya siya ya gyara bangaren shi tas kuma kowani ɗaki ya saka gado, wato dai wulaƙanci Yallaɓai ya ƙaro ashe wai kowacce ranar girkinta da ɗakinta in kin fita ki rufe ranar da kike da miji ki zo ki gyara ku kwana da miji in kin fita kina da key dinki ki rufe.
Ranar da ya ta ramu yana faɗa mana na kasa haƙuri sai

50 / 55