Turken Gida Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   27 / 55

78K to 81K   out of 163.1K words

yi, wannan fa koya ma yarana nake yi faɗan kare kai domin wata rana."

Ni da Jidda muka kalli juna na tsintsire da dariya itama tana ta ya ni, ganin muna yi masa dariya ya sa ya ce" Au dariya ma kuke yi mini ko? Shi ke nan."

"Yallaɓai baka da aikin yi ne yau?

"Kin san dai ba zaman banza na ke yi ba ko?

"To na ga ne yau kana ji da karfi."

Yana ɗaga power ɗin hannun shi kafin ya ce" Sosai. Amma yau din rana ce ta musamman domin iyalaina da yarana."

Ina dariya na ce" Ka ce yau Happy Family day ce Yallaɓai"

Banza ya yi dani ya koma ya zauna yana sauke ajiyar zuciya. Jidda ya ce ta ɗauko masa ruwa mai sanyi a fridge su Baby na kalla har suna kusa ɓaro mini da Tv ƙasa cikin ɗaga murya na ce" Duk barnan da aka yi mini baby ke ce za ki ɗauki asara domin bugun tsiya zan yi miki. Kuma ki sani ku gama ke za ki gyara mini falo na ma faɗa miki."

"Ubanta dai kike so ki ce ya gyara ba ita ba."

Ina dariya na kalli Yallaɓai kafin na ce" Ni dai ban ce ba"
"In ma kika ce ai kin san ba zai gagare ni ba malama."
"Na sani."
Na amsa ina masa dariya Jidda ta kawo masa ruwan gora da kofi bai ma zuba a kofin ba ya buɗe ya kafa kai kaɗan ya rage ina kallon shi na ce.
"Lalle Yallaɓai ka gajiyar da kanka."
"Ni ai ba malalacin namiji ba ne. Lebura ne ni mai aikin ƙarfi."

"Allah ya taimaki Md Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana."

Na faɗa ina masa dariya har ina aika masa da jinjina. Miƙewa ya yi bayan Jidda ta koma kitchen mai da kofin da ruwan, Yunma ke zillo za ta wajen shi sai ya ƙarbeta yana faɗin" Ke kuma za ki shiga wasan ne?
Ina jin haka da sauri na ce" Yallaɓai don Allah kar ku wahalar mini da ƴa'"
Amma ki saurarena bai yi ba sai ma ya juya yana ce ma su Baby" Mun samu ƙarin patner.'

Suka fara ihi kafin in ce me ina zaune an dadumar mini yarinya na miƙe ina kiran sunan Yallaɓai amma ya yi biris da ni shilla sama yake yi yana caɓewa maimakon ta yi kuka sai dariya kwantar da ita ya yi a ƙasan cafet yaran suka rufu kanta suma mata wasa suna kai mata hannu itama jaira tana kamawa.

Ihu na yi musu ina faɗin" Wallahi Yallabai kada kai da yaranka kun halaka mini yarinya to."

Ko sauarara na ma ba su yi ba da na ga za su ma yar da ni mahaukaciya sai na bar musu falon amma ina cike da fargaba kar su naushe mini yarinya. Kitchen na shiga na ɗibo abinci na koma ɗakina na ci na koshi, har lokacin ba su bar wasan ba har daga ɗaki ina jin iface ifacen su Yunma ina jiyo dariyanta na ɗauka za ta ga ji ta fara kuka sai ta ba ni kunya ko kukanta ban ji ba. Sai da aka kira mangariba Yallaɓai ya hakura da wasan nan ya zo ya yi wanka ya tara su Khalipa zuwa masallaci Yunma kuma an kawo mini ita ina ba ta nono na cire mata pampers na sake yi mata wanka da ruwan zafi sai barci ina ta masifa ni kaɗai.

"Ai dole ki yi barci kin sha wuya."

Falo ma da na fita bayan na yi salla kaca kaca Baby ba ta gyara ba ai da muryan ɓacin rai na fara kiran sunanta sai ga shi ta fito da hijabi alamun salla ta idar.

"Ke ubanki kika bar ma falon ya gyara ko ni?

Sai ta fara sosa kai kafin ta ce" Umma na gaji ki bari da safe sai na gyara."

"Ko mutuwa za ki yi yau sai kin gyara mini falo na aike ki ki yi mugun wasa har ki gaji?

Sai ta girgiza mini kai shammatanta na yi na ƙarisa gabanta tana shirin guduwa na damki kunnenta ɗaya na matse ina faɗin" ba ki da hankali ashe ban sani ba Maimuna?
Sai ta fara kukan shagwaɓa tana faɗin" Umma zafi kunnena."

"Ke namiji ce da za ki je kina wasan maza?

"Umma Abba ne ya ce na shiga."

"Abban ne ya ce ki shiga ko? Ya ce ki shiga dole ne? Ba ga ƴar uwan ki nan ba kin ga ita ta shiga ne?

"A'a"

Ta faɗa cikin kuka har ta fara hawaye, ƙara jan kunnen na yi ina faɗin" Wallahi in na sake ganin kin shiga irin wannan wasan sai na yi fata fata da ke a cikin gidan nan"

"Kin ji ko ba ki ji ba?

Na faɗa cikin tsawa da sauri ta ce" Allah ba zan ƙara shiga ba Umma."
Dundu mai lafiya na yi mata a baya sannan na sake ta ina faɗin" Ki ma ƙara ki gani ɗin. Maza ki gyara mini falo wawiya kawai kin girma amma kina cin ƙasa."

Sai ta yi gefe tana sosa kunnenta lokaci ɗaya tana faman hawaye daidai shigowar su Yallaɓai ganin tana kuka ya sa ya kalleni yana faɗin" Me ta yi miki kika da ke ta?
Na yi masa banza na wuce, ina jin sa yana faɗin" Sadiya ki daina duka mini yarinya fa. Na faɗa miki ba na so amma kin ƙi jin magana ta."

Na yi shigewata Bedroom ina masifa ni kaɗai yarinya na mace amma tana yin abubuwa irin na maza shi kuma Yallaɓai ba zai fahimci illa abun ba sai nan gaba ni ko ina uwa ba zan zauna in yi shuru ba.
Daga yaran har Yallaɓan ban ƙara ganin su ba sai bayan sallar isha'i da ya zo ya shirya ya ce mini za su ta fi saboda su Khalipa na fito ina da jakar lilipop na ɗauko na ba su shi da Anwar na Yumna ne da Suwaiba ta kawo mata tun da ta shan zaƙi, abinci ma na fara ba ta mai ruwa ruwa kamar tea kwai da sauran su ruwa daman tun haihuwanta na ce zan yi exclusive Yallaɓai ya ce ya bi Exclusive da gudu ba takalmi in har na yi ma yarinyar sa mugunta na hana ta ruwa bai yafe mini ba, shi ya sa ba mu yi ba sannan ga shi ta sha madaran yara sosai shi ya sa kullum ƙara ƙiba kawai Yumna ke yi tana ba ma masu ɗaukanta wahala ni kaina sai ina nishi in zan ɗaga ta.

Saboda Baby ba ta da hankali ta yi ɗamara za ta bi su, kallo ɗata kawai na yi mata ta shiga taitayin ta Yallaɓai na cewa ta ɗauko kayan makarantar ta, ta je can ta kwana cikin masifa na ce" Ba za ta je ba.
"Saboda mene?
"To me za ta je ta yi? Su Khalipa ne kuma ba ga su nan sati uku tare damu yau ne za su koma ba?

"To ina ruwanki tana son ta je. Ba ta gaji da ganin su ba."

"Sai dai ko ta mutu amma ba yau ba. Ba za ta je ba."

Yallaɓai zai yi magana na tare shi da faɗin" Wallahi ba za ta je ba, ka ji ma na rantse."
Yallabai ya kasa mgana ya kira sunana na yi kamar ban ji ba, na shafa kan Anwar ina faɗin su gaida mamannsu.
"Bye Umma."
"Bye Khalipa."

Na faɗa ina ɗaga musu hannu, na yi shigewata ɗaki ina jin idanuwan Yallaɓai a kaina na ki yarda ma mu haɗa ido. Ai suna fita na sake fita falo suna ɗakin su Jidda na ninke ƙananun kayanta da ta wanke Baby na kan gado tana kuka saboda na hana ta zuwa. Ban yi wata ba ta ɗaka mata duka a baya sai ta banƙare tana ganina ta yi tsalle ta yi ƙarshen gado tana matse kukanta.

"Kuka kike yi mini saboda wannan mganar?

Sai ta fara girgiza kai cikin kuka kafin ta yi magana na tare ta da cewa" To kukan me kika hau gado kina yi mana a cikin gida?

"Ba komai."

Ta faɗa  tana hadiye kukan ta.
Kallonta na yi kafin na wata dariya ina nuna ta da yatsa kafin na ce" Kin ga Jidda na yin haka? Ke ce mara jin magana ko? ke Yarinya ce?

Nan ma ta girgiza mini kai zare mata ido na yi kafin na ce' Wallahi ya zama na ƙarshe in sake yi magana a gaban babanki ki ce za ki yi mini gaddama kika ga yadda zan yi ƙulin kubura dake a cikin gidan nan."

"Ki yi hakuri Umma"

Ta faɗa cikin kuka sai ta ba ni tausayi amma ban nuna mata ba.

"Ki yi haƙuri Umma ba za ta ƙara ba."

Jidda ta faɗa cikin sanyin ta sai na yi ƙyafci na fita daga ɗakin fuu har ina bango musu ƙofar na koma ɗaki ina masifa ni kaɗai daga baya sai na koma ina dariyan kaina. Na rasa haushin wa na ke ji? Yallaɓai ko yayan shi? Tun daga cikin Yumna na samu wannan ɗabi'ar abu kaɗan yake harzuƙa ni in ta faɗa kan abin da bai kai ya kawo ba.

******
Jidda ta gama jarabawarta gabaɗaya sannan Walimar saukar su kuma za a yi a farkon watan August ne, sai kawai na ce za mu haɗe shi da waliman gradution ɗinta da birthday ɗin ta na cika shekara  sha tara a duniya duk da ta ɗan gota amma zan haɗa mata kayattaciyar Walima. Yallaɓai ne wani lokacin ko na ce za mu yi sai ya ce a'a na dai yi musu tun suna yara amma suna kawo girma sai ya riƙa hanawa iya fa mu kaɗai a gida amma sai Yallaɓai ya ce wai birthday haramun ne.

Wannan karon dai na ci karfin sa ya amince. Tun da har da Waliman saukar su sannan Amarya ta saka baki Gimbiya ba. Shi ya sa ya bari sannan ya saki kuɗi aka yi ta shirye-Shirye kuma dai daman Jidda is his fav Daugther. Ba wani gayya muka yi ba iya yan makarantan su na boko sai ƙawayenta na Tahfez su goma ne mata za su yi sauka sai maza huɗu. Sun yi ankon Hijabai masu ruwan ƙasa da dogayen baƙaƙen riguna sannan sun haɗa kudi kowa 20k amma Yallaɓai 50k ya ba ma makarantar suna ta godiya.

Ni dai daga gida na yi mata memo da yar jaka ƙarama, ita kuma Gimbiya ta yi mata kayan su Snacks, Mimisco ta yi mata sabbin kaya kala huɗu har da jallabiyoyi da takalma sannan ta yi mata jaka na takarda babba a ka saka hoton ta. Ai na ci dariya domin ni da na ce zan yi na hoto Yallaɓai ya tuma ya ce bai amince ba sai ga shi Mimisco ta yi da ya gani sai ya kasa magana. Anty Maimuna ta siya maltina katan goma da ruwan gora. Anty Bahijja ta yo abinci mai rai da lafiya, Suwaiba ta kawo mata sabon alqur'ani da casbaha. Naja ta kawo mata darduma na Makka da hijabi, sauka ne Jidda za ta yi da walimar Graduation amma ta samu kyatttuka sai da na yi mamaki kaf dangin Babanta sun nuna mata bajinta. Hatta Babanta Usman ya aiko mata da 50k. Ya Auwal Laptop sabuwa ya aiko mata da shi Ya Hamza kuma ya gwangwaje da kayan su chaculte kala kala sama da guda biyar. Musbahu kuma ya gwangwaje ta da sabuwar waya. Jidda sai da ta yi kuka da ta ga irin kayan da a ka haɗa mata Baby na ta tura bakin ba a kawo mata ba ta ce sai ta yi ƙoƙari itama ta sauke Qur'ani sai a yi mata abin da ma ya fi haka.

Kaf yan gidanmu suma sun yi bajinta matan da Mazan. Alhajimmu ya saka aka yanka mata tinkiya cikin dabobbinsa na ƙauye Baba Aminu ya taho da ita tare da kaji da zabbi shi ya sa Yallaɓai bai siya komai ba yana gefe iyayenta sun gama mata komai. Ranar saukar lahadi ce tun tara muna haraban tahfezz ɗin su Jidda. Kaf ɗin su Ya Aina sun taho Rahila ce kaɗai ba ta zo ba laulayi, Kawu Abba shi da Marwa da tsohon ciki Gimbiya tare da su Khalipa da Naja, su Maman farko da Hajiya Iya. Su Munnira da Hauwa hatta Mimisco ta zo ita da Anty Bahijja da Anty Maimuna. Kaf din su Musbahu da Adnan Muttaƙa da su Suwaiba suna wajen taro sosai Jidda ta gani sai hamdala. Yallabai na da ganawa da wasu mutanen sai daga baya yazo lokacin ma Jidda aka kira tana karatu.

Sai da na yi ƙwalla da Jidda ke karatu, y'an uwanta na ta ɗaukan ta Video cikin burgewa. Bayan sun gama karatu aka kaddamar da su sha huɗu masu sauka aka ba su allon sauka. Mun yi hotuna tun da Adnan ya kira mai hoto, ta samu kyattuka, wajen malamai Kawu a envilop ya saka mata sabbin yan 1k A wajen a matsayin shi na Uba ta rumgume shi tana masa godiya. Duk mun zo da abinci da lemuka da ruwa da abun rabo. Tantin da muka zauna ba fariya ba sai muka zama abun kallo Jidda haka ta yi ta rabon jaka da Memo da abinci ruwa da maltina haka suke rabo. Baby kaf yan ajinsu ta gayyato suka ci suka sha, daga makaranta muka dawo gida muka ya da zango muka cigaba da walimar a gida. Mazan daman daga makarantan muka rabu da su.

Mimisco har gida ta biyo ni ta ci abinci sannan ta tafi. Su Anty Bahijja sai la'asar suka tafi har Gimbiya ranar sai dare. Na aika da abincin walimar da naman da kayan Snacks da abin rabo na aika da shi Gwammaja da Ɗorayi suma su shaida. Sauran kuma duk wanda zai fita jakan sa cike da kayan walima. Rahila ma na ba da saƙo akai mata Halima ce ba ta zo ba a cewar Gimbiya ba ta da lafiya ne, amma ni ban damu ba ta kanta na ke yi ba. Ranar gidana cike da jama'a har dare ranar ba gidana Yallaɓai yake yi ba sai washegari ya dawo gidan, sannan ya ga kayattukan da Jidda ta samu sai da ya shafa kanta kafin ya ce.

"Good girl. Am so proud of you Daughter."

Ga waya ga laptop, shi Yallaɓai Tab ya siya mata sabuwa, tsohuwar ya ce ta bar ma Baby, da take ta tura baki ita ba a siya mata komai ba ya ce ta ƙara ƙoƙari itama za a siya mata. Hotuna sun yi kyau na yi ta carbi a status mutane nata saka albarka bayan kwana biyu na saka ta , ta shirya ta je Gwammaja ta kai ma Nene allon saukar ta, daga can ta wuce Ɗorayi ta kai ma su Alhajinmu suka gani suka saka albarka.

Kuɗin da Jidda ta samu na tattara su na siya mata ɗan kunnen gold na ba ta ta maƙala a kunnen ta. Sai da na yi shawara da Yallaɓai shi kuma ya ce kudi na Jidda ne in ta amince sai na siya mata. Da na tambayeta  tace mini tana so shi ne muka je tare kasuwa na siya mata. Amma na cire 30k a ciki na ƙara jarin hijabai da na ce ma na ara sai ta ce ba aro ba na baki Umma, na yi ta saka mata albarka. Adanan ya kai ta ta yi register ɗin layi tun da ta yi waya. Ta sha dokoki wajen Yallaɓai ban da shige shige WhatsApp kawai ta buɗe lambobi daga na mu sai na kawunta sai na yan ajinsu sai na y'anuwanta su kenan a cikin wayar. Ganin za ta fara zaman gidan kafin cuku cukun makaranta sai ta ce mini tana son ta koyi kayan su Snack haka sannan tana son koyon kwalliya na aminta da shawaranta sai na yi ma Yallaɓai magana shima sai ya yi na'am da mganar ya ce ta nemi in da ake yi sai ya ba ta kudi ta shiga..

Gimbiya na yi ma mgana saboda na ga ita duk ta iya su, ni kuma ba su dame ni ba, ita ta yi ma wata da ta sani mai yin snack sosai ta buɗe online class aka saka Jidda sannan ta na yin na gida sau biyu a sati alhamis da jummaa wata uku 20k Yallaɓai ya biya mata ta fara zuwa. Sannan na kwalliya ni kuma da na ke yi followimg ɗin su a I.G na yi ma wata Zahrajj magana da bayanin kuma ita a sharaɗa take amma tana da shago a nan zoo road wajen kamfanin Yallaɓai. Da na yi ma Jidda rigister ita sau uku ne a sati jumma da asabar da lahadi da safe. Shi kuma na Snack daman da yamma ne.

Jidda tana da naciya da dakiya in dai ta sa kanta za ta yi abu. Ko sati biyu ba ta yi da fara zuwa ba ta fara iyawa. In ta dawo gida sai ta gwada Yallaɓai kuma ya ɗaure mata kugu ya sa aka kawo mata fulawa da siga sauran kayan kuma ya ba ta kuɗi ta siya kwalliya kuma Tariq ya aiko mata da babban kit na ƙwalliya, Baby ta yi jin haushi ta ce an fi son Jidda a kanta in ta yi mata dariya. Maganar gaskiya Jidda na da farinjinin jama'a sosai saboda yanayinta na sanyi da rashin hayaniya.

A tsukin Marwa ta haihu an samu mace ta ci sunan Innayi ana kiran ta Afiya muka tafi Rano suna har Gimbiya ta je, itama cikinta har ya turo gaba. Kwana uku muka yi a gidan Marwa ni da Munnira da Hauwa da su Ma'u da Rahila sai Ya Balki. Su Anty Bahijja sun zo suna amma ba su ko kwana ba, dangin Baban Marwa ma sun zo amma washe-gari suka koma mu kaɗai aka bari muka yi soye muka natsa. Ana gobe za mu koma gida ne muka yawata garin mun je gidan su Kawu gidan su Nene kenan daga nan muka je gidan su Hauwa. Na karshe shi ne gidan su Gimbiya. Hajiyar Tafida na nan da ƙannen Gimbiya da suka zo gida.

Ƙiri-ƙiri suka yi mana wulaƙanci ita dai Hajiyar ta karbe mu faram faram amma ƙannen Gimbiya saboda ni a wulakance suka amsa gaisuwar mu. Shashen Mamansu Sameena me kawai aka karrama mu. Bayan mun fito daga gidan Munnira na ta kumduma zagi ni da Hauwa muna yi mata dariya. Na ɗan

27 / 55