Turken Gida Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   3 / 55

6K to 9K   out of 163.1K words

yi da kaina.

"Ina za ki je daga nan Ya Sadiya?

Amina ta ƙara tambaya na ni kuma sai na yi mata shuru har muka gama ninke kayan gabaɗaya na ja akwatin na rufe daman sauran kayan na ciki na ja ta can gefen wardrope in da take a jingine sannan na koma in da na tashi na sake zama.

"Na ƙi ba zan faɗa miki ba."

"Don Allah fa na ce."

Ta sake marairaicewa kamar wata ƙaramar yarinya.

"To Yashe zan wuce."

Sai ta ƙwalalo ido ta na kallona kafin ta ce"Yashe fa Ya Sadiya?

Sai na gyaɗa mata kai kafin na ce" To ina zan je in ba can ba?

Sai Amina ta gyara zama har da matsowa kusa da ni ta na faɗin" in ba ki shawara Ya Sadiya?
Ina kallonta sai na gyaɗa mata kai kafin na ce" Me zai hana? Ina sauraran ki."

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce" Gaskiya in dai za ki ji shawarata kar ki je ko'ina. In dai ba za ki zauna  anan ba sannan ba za ki je Abuja gidan Ya Auwal ba, ko gidan Ya Hamza ba to shawarata ita ce da dai ki je wani wajen gwara ki koma gida kawai Ya Sadiya."

Ta gama faɗa har tana ɗaga mini hannu ni kuma daman kallonta nake yi kafin na daƙuna fuska ina faɗin.
"Wani gidan kenan?
"Gidan auran ki mana Ya Sadiya."

Wata uwar harara na jefa mata kafin na yi ƙaramin tsaki ina faɗin" Ai ni da ke  na faɗa miki megidan har gorin gidan ya yi mini ko?

"To ai bai kore ki ba Ya Sadiya ɓacin rai ne."

"Oh kina nufin na koma duk cin kashin da ya yi mini ya tafi a banza kenan ko?

Da sauri ta ce" Ni ban ce ki ƙyale shi ya tafi a banza ba."

"To me kike nufi Amina?

Na faɗa a ƙufule.

"Ba ki ba ni dama na gama maganata ba ne shi ya sa."

"In jin ki."

Na faɗa a tsume har ina kauda kaina domin ita kanta Aminar sai na ji ta fara ba ni haushi so ta ke yi ni ta kwaye min baya ta goyo bayan Yallaɓai?

"Nufina yanzu duk in da za ki je Ya Sadiya wani ƙarin tonon asiri ne. Abin da ba ki taɓa yi ba kar ma ki fara. Har gwara ma ki koma gida wajen Gwaggo da ki je Yashe can fa ƙauye ne in wani ya yi shuru wallahi wani ba zai yi shuru ba. Gwara ki koma gidan ki amma shi ma Yallaɓai ki gasa mai aya a hannu yadda zai fahimci shayi ruwa ne madara ake saka masa ya yi kauri."

Ta gama faɗa ta na kallona ganin na ƙi mgana kuma na ƙi sakin fuska sai ta marairaice ta na sake faɗin" Ko ba haka ba? Ki duba magana ta da idon basira Ya Sadiya."

Yadda ta ce idon basira ne ya sa sai da na yi dariya, itama sai ta hau dariyan Kafin na jinjina kai ina fadin" Haka ne kin yi gaskiya."

"Yauwa Ya Sadiya ki koma ko saboda su Jidda."

Sai na jinjina kai a karo na biyu kafin na ce" To shi ke nan zan koma Amina."
Sai ta murmusa kafin ta rumgumoni tana faɗin" Ko ke fa My Ya Sadiya."
Mirmishi kawai na yi ba tare da na yi mgana ba. Duk in da ɗan uwa ya ke daɗi gare shi ni kaina sai na ji kamar kar na tafi, sai dai kuma gaskiya ta faɗa minj duk in da zan je yanzu kamar na soka wuƙa a cinyata ne na yi kururuwa na yi kirari gwara na koma amma ni da Yallabai zaman yan marina za mu yi tsakanin ni da shi.

Falo na kuma wajen yara Amina na kitchen ta na girkin Yamma. Yasir ne da Sumayya a gidan Afra ta tafi islamiya daga baya barin su na yi a falon na shiga kitchen wajen Amina ina ta ya ta aiki jefi jefi muna hira har muka gangaro kan mganar Ma'u.

"Wai Ma'u shuru kamar ba ta nan"

"Ta na nan, ai tun da aka yi wannan turken ni da ita sai ta shafa mini lafiya."

Amina ta ƙyalƙyace da dariya ta na faɗin" Ni kaina sai mu daɗe ba mu yi waya ba, ko a group na gida ta daina mgana kamar baya."

"Ni kaina na ga ta yi sanyi kamar ba ita ba."

Na faɗa ina yanka albasa.

"Rabon da mu yi waya tun lokacin da ta kirani ta na faɗa  mini auren shema'u na ce mata ba zan samu zuwa ba."

"Ni dai bayan nan mun ɗan hadu a ɗorayi "

Na ba ma Amina amsa, an yi bikin Shema'u ko wata biyar ba a yi ba ta yi aure a gombe. Wani tsohon chairman ta aura matansa huɗu ɗaya ce ta rasu ya cike da ita dukkan mu mun je bikin amma ba mu je can Gombe ba Ma'un ce ta je su Shema an gama yawon duniya an gaji dai an yi aure can kwanaki da na je gida Gwaggo ke faɗa mini ta zo ganin gida har ta shigo gaishe su har ta ba ma Alhaji dubu biyar a raina na ce su shema an samu duniya kenan.

Mun cigaba da hiran Ma'u ni da Amina har muka gangaro kan Anty Bahijja nan na ke ba ta labarin irin sunayen da suke kiran Gimbiya da cewa ita ce mai ƙashin arziƙi.

"Allah na tuba Amina ai ni da arziƙina Yusuf ya aure ni. In ma tsiyar ne sai dai in shi ne ya goga mini"

Me Amina za ta yi in ba dariya ba har ta na rike ciki na kusa buga mata ƙasan wuƙan hannuna ina faɗin" Ban son iskanci fa Amina"

"To ke ce Ya Sadiya da wata magana."

"Allah kuwa. To har ni za a yi ma gorin ƙashin arziƙi."

Ni da ita muna ta dariya cikin annushuwa da hira muka gama girkin nan ana ta kiran sallar mangariba ni da ita muka je muka yi salla, Afra ta dawo ta isko ni daki tana mini hira akwai surutu kamar Baby ce daman kuma tsaran juna ne.

Bayan sallar isha'i muna falo muna cin abinci Yallaɓai na ta kiran wayata bai haƙura ba.

"Ya Sadiya ki ɗauka ki faɗa masa gobe za ki dawo"

"Wallahi ba zan ɗauka ba."

Na faɗa ina hararanta sai ta sunne kai tana yar dariya. Kira uku ya yi mini bayan na ɗazu da na shiga sallar asuba na ga huɗu, ni kuma na ce wallahi ba zan taɓa daga kiran shi ba sai yau? Sai yau ne ya tuna da ni matarsa ce? Sai yau? Ai ya makara wataƙila da ya kira kafin yau ɗin da wata ƙila na saurare shi.

Mun gama cin abinci mun dawo falo Amina ta kunna mana kallo ni ba na ma kallon hankalina na wajen Afra ina koya mata aikin makarantan da a ka ba su a english Yasir da sumyyah na ta wasannin su a tsakiyar falon

Na ji ana kiran wayar Amina amma ban dai bi ta kai ba sai da na ji tana faɗin" Ya Hamza ke kirana."

Ban kawo komai a raina ba na ce" To ki ɗaga mana."

Na ji ta ɗauka da sallama suna gaisawa daga nan sai na ji tana faɗin" Ya Sadiya wai? E ga ta nan ina ga wayar tana ɗaki ne shi ya sa ba ta ga kiran ba."

Sai na dawo da hankalina kanta har ina miƙewa. A ina Ya Hamza ya san ina gidan Amina.?

"Ga Ya Sadiyar"

Na ji Amina ta faɗa lokaci ɗaya ta na ta isowa in da nake ta miƙa mini wayar na karɓa ina mata inkiya da ido a ina ya san inan nan?  Sai ta rika min nuni na yi mgana Ya Hamza na jin mu.

"Salamu Alaikum Ya Hamza."

"Sadiya kina lafiya?

Ya faɗa daga bangarensa.

"Lafiya lau. Ya su Anty Khaleesat da yara?

"Duk suna nan lafiya."

Shuru na wani lokaci na kasa mgana amma gaba na ya faɗi ina tunanin a ina ya san ba na gida ina kaduna ko dai Yallaɓai ne ya kai masa ƙarana?
Dam! Na ji ƙirjina ya amsa ban samu sararin mgana ba na ji Ya Hamza na faɗin

"Ashe kina kaduna?

Ina shirin na amsa masa sai kawai ya cigaba da faɗin.

"Ke haka ake yi ehe da ga zuwa ziyara sai ki shantake a gidan ƙanwarki sama da kwana goma ba ki da ranar ƙomawa gidan mijin ki?

Mamaki ma ya hana ni mgana. Mamakin Yallaɓai da zai tashi wasa da ni.

"Dama daman gobe nake shirin komawa."

"To ya dai kamata. Shi ya kirani yanzu yana faɗa mini ba ki a gida sama da sati ya na ta kuma kiran wayarki ba ki ɗauka ba."

"Wayar ta na silent ne ban ji kiran na shi ba."

Na samu kaina da furtawa.

"To sai ki kira shi yanzu ku yi magana. Sannan gobe ki koma gidan ki Sadiya. Shi kan shi Dr sai ya ga rashin hankalin mu gandan gandan dake, ke ba suna kika zo ba sannan ba biki ba daga kun ɗan samu matsala da miji sai ki kama hanya ki tafi gidan ƙanwarki? In ma yajin za ki yi kuma tun da ba ki je ɗorayi ba me ya hana ba ki taho gidana ko gidan Auwal ba?

"Ka yi haƙuri Ya Hamza."

"Ba maganar haƙuri ba ne. Ba a haka kin ji ko? Amina ƙanwarki ce bai kamata ki je gidan ta in wani abu ya faru ba. Mu ya kamata ki fara nema."

"To Ya Hamza."

Na furta ina ƙokarin mai da ƙwalla da suka cika mini ƙwarmin idanuwana.

"Ki yi haƙuri ki koma giden ki ki rumgumi mijin ki da ƴaƴanki. Ya faɗa mini da kan shi ranshi ne ya ɓaci ya ɗan faɗa miki wasu mganganu ma su zafi sai kika ji haushi kika ce za ki taho kaduna. Ya ce ya bar ki taho ne saboda ke da shi ku samu zukatan ku su huta sai kuma ya ga kin shantake kin ƙi dawowa yana ta kiran wayarki kuma ba ki ɗauka ba."

Shuru na yi domin kalaman bakina sun gama ƙarewa. Yallaɓai ya shirya wasan ƙwaikwayon shi ya nemi yan wasa kuma har an yi wasa an tashi karshe dai shi ke da nasara akaina bayan tarin tozarcin da ya yi mini

"Ki yi haƙuri kin ji ko? Haba Sadiya da girman ki ai yaji bai kamace ki ba, ki yi hakuri ki koma gidan ki, ke yanzu uwa ce sai dai ma ki yi ma wasu faɗa."

"To Ya Hamza in sha Allahu gobe da safe zan koma."

"Yauwa. To mu kwana lafiya amma ki kira shi yanzu."

Da haka muka yi sallama da shi muna gama wayar Amina ta zauna gefena tana faɗin" Wai me Babansu Jidda ya kira Ya Hamza ya faɗa ma sa? Na ji ya na miki faɗa ne?

Sai na kalleta, lokaci ɗaya hawayen da na ke ta riƙewa suka kece mini amma sai na yi saurin saka hannu na goge hawayen ina faɗin.

"Ya kira shi ya faɗa mai mun ɗan samu sabani ranshi ya ɓaci ya ɗan faɗa mini mganganu ni kuma sai na ji haushi na ce zan taho Kaduna a cewarsa ya bar ni na taho saboda ni da shi mu samu zuciyarmu ta yi sanyi amma sai ya ga na daɗe ban dawo ba kuma yana ta kirana a waya ban ɗauka ba"

"Lalle ne ma. "

Amina ta faɗa ta na riƙe haba kafin ta cigaba da faɗin" Yallaɓan nan na ki ya Saduiya sai ke"
Ta faɗa tana dariya na kalleta amma ban yi mgana ba.

Na fahimci manufarsa ya yi saurin kiran Ya Hamza ne ya faɗa masa saboda ni ya rigani wanda ko daga baya na faɗi wata mgana ba za a goya mink baya. Yallabai ya san ni sarai kamar yadda na san shi ciki da bai. Ya san ba zan taɓa zuwa na kai ƙaran shi ba ya kuma san ba zan taɓa fasa mganar faɗan mu ba amma ya san ina da kafiya zan iya ƙin dawowa a lokacin da ya so ya kuma san in ba Ya Hamza ko Ya Auwal ba, ba wanda zai matsa mini na koma shi ya sa sai ya yi saurin kiran Ya Hamza. Ya san da gangam na ƙi ɗaga wayarsa ya kuma sha jinin jikinsa ko kunya ne zencen ban sanin masa ba. Sai yanzu ne ya tuna da ina da amfani a rayuwarsa? Wallahi tallahi sai ya raina kansa kuma bashin gorin da ya yi mini na gida da na haihuwa watan tara na zai biya su. Sannan ya yi sanadiyar na rasa gudan jinina bana jin ko da na yafe masa laifinsa to ba na jin zan iya yafe masa wannan kasadar da ya ja mini na rasa wani abu mai muhimmaci a rayuwata.

Zan koma ba domin Ya Hamza ya yi min mgana ba sai domin ina da niyyar komawar. Amma kuma kiɗa ya sauya dole rawa shima ya sauya. Na daɗe ban yi barci ba ina tunanin mafitan da zan nema ma kaina in na koma gida.
Na yi tunanin zan koma makaranta na yi masters ɗina sannan zan inganta sana'ata ta hijabai har ma da ƙarin wani sana'o'in na daina dogara da Yallaɓai na kuma daina dogara da duk abin da ya ke takaman ya mallaka. Daga ni sai ƴaƴana domin nan duniya su ne kaɗai na aminta da ɗari bisa ɗari ba za su taɓa juya min baya ba.

Da safiyar talata na yi shirin komawa Kano. Tare muka fita da Amina za ta je saloon ita da Yasir ne Afra da Sumaiyya na makaranta Amina sai sha'awata take ba ni ta iya driving ba in da ba ta zuwa a garin Kaduna da yar motar ta da Dr ya siya mata. Ni ma a raina na kudiri niyyar zan dukufa da sana'a har nima na mallaki mota ta kaina da gumina. Ita ta kai ni tasha na samu mota sannan muka yi sallama sai da motar ta tashi na bar ta a tasha. Kuma har kuɗin motar ita ta biya mini da cewa Dr ne ya ce ta ba ni na ƙara riƙewa a hannuna. Mun rabu ina ɗaga mata hanmu tana ɗaga mini nima.

Motar mu ta tashi goma saura ba mu isa Kano ba sai biyu na rana. Daga tasha na hau adaidaita zuwa gidana. Ba kowa a gidan sai da na saka makulli na buɗe gidan na shiga ko'ina ya yi ƙura. Na shiga cikin bedroom ɗina na ijiye akwatin hannuna da jaka sannan na zare mayafi na shiga tiolet na kama ruwa na yo alwala na taho na yi salla ina idarwa na tashi na shiga kitchen, shima dai duk ya yi ƙura amma dai ba a yi amfani da komai ba.

Gas na kunna na dafa ruwan zafi na sha tea, sai ƙwai da na soya guda uku bayan na gama na koma ɗaki na ɗauko wayata kamar in kira shi sai na fasa. Domin ban bi umarnin Ya Hamza, jiya ban neme shi ba shima bai sake nema ba ina da tabbacin wata ƙila ya sake kiran Ya Hamzan ne shi kuma ya faɗa masa na ce yau zan koma gida.

Ganin ba zan iya kiran shi ba sai kawai na tura masa saƙo.

"Na dawo gida."

Ina gama tura masa sai na kira wayar Salisu direba bayan mun gaisa na ce masa yau in ya dauko su Jidda ya kawo mini su gida na dawo. Yana ta min sannu da zuwa na gama waya dashi kenan Balaraba ta kira ni ta na faɗa mini  Saude ta sauka duk sai na ji ɓacin raina ya tafi ina mata barka ta samu megida tun da namiji ta haifa. A Lokacin na kira wayar sai mijinta ya ɗauka ya ce ta na wankan da yake ba a asibiti ta haihu ba a gida ne amma sun kira anguwan zoma. Mun rabu a kan cewa in ta fito zai faɗa mata za ta kirani. Sai ko gashi ta na fitowa ta kira ni muka yi magana abin hamdalar shi ne ta haihu lafiya ba wata matsala na yi mata mganar za ta dawo gida ne ko anan za ta zauna sai ta ce min ita ba ta sani ba, ni ko kai tsaye na ce mata gwara dai ta dawo gida a kula da ita ko bayan suna ne sai ta ce mini za ta yi magana da megidanta na ce ya kamata.

Na ɗan kwanta sai la'asar sannan na tashi na yi salla sannan na fara gyaran gidan na share ko'ina na goge na saka turaren wuta gidan ya fara ƙamshi duk da na gaji ban zauna ba na fara tunanin abin da zan dafa na duba friza na sai na ci karo da miyar da na yi ana gobe tafiyata tana nan ba ta yi komai ba kuma ina da sauran kayan miya da kayan lambu sai dai duk sun bushe sai na kwashe su kawai na zubar har da ma su kankana suma duk ƙanƙara ya sa sun yi wani nakwa nakwa saboda daɗewa sai kawai duk na kwashe na zubar a bola na goge firizan. Miyan na sake gyarawa na dafa mana farar shinkafa na gama shidda saura na yamma na goge kitchen ɗin sannan na je na yi wanka na fito kenan ina saka kaya na ji ana buga get a raina na ce to yan makaranta sun dawo.

Wani riga da wando na saka pakistan ne rigar ja ne da baƙi ba ta da hannu sai daga kasa an ɗan zoɓa ta, sai wando sakakke ne bai kama min jiki ba sai na saka hula baƙa mai kwalliya ta sama, kaina akwai kitso a can Kaduna Amina ta yi min shi duk da ba ta wani iya kitson ba amma na gaji da kan ya tsufa sai na tsife na ce ta yi min ko kalaba ne shi ne ta zarga min shi haka, kuma gashi ba ta kama shi da kyau ba duk ya fara sukurkucewa har kunya na ke ji na buɗe kan a gaban mutane.

Silafas ɗin cikin gida na saka sannan na saka mayafi na fita zuwa haraban gidan na buɗe ma yara ƙofa suna ganina har Jidda sai da suka faɗa jikina suna min oyoyo na tarbe su cikin farinciki. Da gaske na yi kewar su sosai musamman ma surutun Baby. Salisu bai tafi ba daman in ya kawo su sai ya tabbatar da an buɗe gida

3 / 55