Turken Gida Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   46 / 55

135K to 138K   out of 163.1K words

yi magana ba, daga nan Gwamaja muka koma, Sadi na kira ya zo ya kai mu gida Yallaɓai na can tare da su Kawu, Gimbiya sai daga baya ta dawo kamar Direban Naja ne ya mai do ta.
Na yi ta ba ma Rabi'atu haƙuri da ta ce ba za ta ci alalen ba.

"Karɓi abin ki ki ci, haka suke kin san kowani dangi suna da na su matsalan. Sai kin kauda kai akan maganganun Anty Bahijja ko Anty Maimuna. Gimbiya kuma tana gaba dake so karki ɗauka da wani abu. A hankali za ki saba."

Sannan ne ta karɓa, kuma na ga hankalinta tun da har kwana biyu da faruwan abun ban ji Yallaɓai ya yi magana sai na tabbatar ba ta faɗa masa ba. Jidda ranar laraba ta koma makaranta laraban ma da ta kai ni ce na saka baki da litini tun safe Yallaɓai ya ce ta koma na ce ya barta ta ɗan yi wanki da sauran shiri, sannan ya amince. Tun bayan bikin Adnan kuma sai na natsa a gida ba in da nake zuwa. Gimbiya tana fita shago ko wajen aiki Rabi'atu kuma makaranta ita da yara ni kaɗai ce ake bari ina gadin wannan wargajejen gidan.
Su Inna Mariya da iyalan Gandun albasa sun zo mini ganin gida gabaɗayansu sun saka albarka kuma wallahi na ji daɗi. Suma dai nasihan su na yi haƙuri na zauna lafiya da abokan zamana domin samar ma da mijin mu kwanciyar hankali na ce In sha Allahu.

Gimbiya ce ta fito da tsarin kwana ɗaya amma daga baya sai ta ce wai ba ta ganewa mu ma yar da shi kwana bibbiyu.
Har falona ta zo ta sameni wata ranar asabar da safe. Baby da su Khalipa sun tafi Tahfez Yumna ce kawai ita kuma tana shashen Rabi'atu wajen Yallaɓai da safe da ya shigo mu gaisa ta dafe shi.

Kallonta na yi cikin mamaki ni da man na san tun da na gan ta a falona na san banza ba ta kai zomo kasuwa.

"Kwana ɗaya nan gaskiya bana gane mishi. Mu koma biyun kawai Maman Jidda."

Ta sake faɗa sai na yi dariya kafin na ce" Ba matsala da man ni biyun na ce ke ce a baya kika ce mu ma yar da shi ɗaya."
"Gaskiya mu dawo biyu nan ɗayan nan bana gane mishi."
Sai da na sake murmusawa sannan na ce mata shike nan.

"Za ki faɗa ma Baban su Khalipa ne? Yau ba Daddy su Yallaɓai an koma Baban su Khalipa na fahimci tunda ya yi auren nan ta daina kiran shi da Daddy sai da Baban su Khalipa."

"Ina ruwan shi? In dai duka mun amince shi ba shi da matsala kin sani "

Sai ta gyaɗa kafin ta miƙe tana faɗin" To sai ki faɗa ma ita Rabin"
Sai na amsa mata da cewa zan faɗa mata har ta bar falona ina mamakinta. Ranar Yallaɓai sai Yamma ya fita, Rabi'atun da ta shigo na faɗa mata mun sauya tsari ta ce to, Yallaɓai kuma na manta ban faɗa masa da ya bar ɗakin Rabi'atu ɗaki na ya dawo ya yi kwana ɗaya ya koma ɗakin Gimbiya ya yi kwana ɗaya, ashe ita a tunanin na sanar da shi ni kuma na sha'afa saboda a ranar da yake wajena aka yi ma Ma'u C.S An ciro mata jariri ba rai ta zubar da jini sosai hankulan mu duk sun tashi mun ɗauka ma ba za ta yi rai ba. Ba gidan nake yini shi ya sa ban ma yar da kaina na sanar da shi ba.

Ina gidan Ma'u tun da an dawo da ita gida. Baaba ke kwana da ita can muka kai dare tare da su Ya Aina Yallaɓai ya kira wayata ni na ɗauka zai yi mini faɗan na kai dare alhalin ya hana ni yin dare in dai na fita da mota. Sai na ji muryansa a kausashe sannan ina jin tashin mgana amma ban san ko ta wace ce ba.

"Kin taho ne?

Lokacin takwas ne da wani abu na dare kenan yau ya dawo gidan da wuri.

"A"a zan dai ta so. Ban san ma lokaci ya tafi ba ka yi haƙuri "

"Ki taho yanzu ina jiran ki"

"Me ya faru?

"In kin zo za ki ji "

Ya faɗa sannan ya kwashe wayar ina jin haka na san ba lafiya, ina jin haka ban tsaya ba na yi musu sallama tare muka fita da su Ya Aina na ajiye su a juction na wuto gida.
Abin da ya ba ni mamaki Yallaɓai na haraba yana jirana shi da Gimbiya kamar yaƙi.

Ina gama parking ɗin motana  na fito Gimbiya ta taroni da cewa" Maman Jidda baki faɗa ma Baban su Khalipa mun sauya tsarin kwanaki kwana ba ne?
"Ban faɗa masa ba me ya faru?
Na faɗa ina kallonta saboda mamakin abin da ke faruwa.

Yallabai na kalla kawai sai na ga ya juya zai shiga shashen Rabiatu Gimbiya ta bishi tana faɗin"Ai ka ji sai ka dawo bangarena sai gobe ne za ka koma mata."

"Ba zan koma ba. Wannan tsarin ku ne ba nawa ba, nawa wanda na sani jiya na shiga ɗakin ki, yau da daddare na fita zan kwana a bangaren Rabi'atu."

"Wallahi ba ka isa ba"

Gimbiya ta faɗa cikin ɗaga murya ta juya zai shiga ta sha gaban shi har tana riƙe masa riga.
Ni dai sai na yi tsaye kawai ina ganin ikon Allah.

"Ba ni hanya in wuce."

"Ba fa za ka koma shashenta ba sai gobe wallahi "

"To ni kuma yau a nan zan kwana in kin isa ki hana ni "

"Ni kuma wallahi in har ka kwana a ɗakin yarinyar nan Da haƙƙin kwana na Allah ya isa ban yafe ba"

Gimbiya ta faɗa har tana shan wallahi. Shi kuma Yallaɓai ya fizge rigar shi ya tureta gefe ya shiga yana faɗin" Da sauki tun da ba tsine mini za ki yi ba "
Ta kwashi kururuwa za ta bi shi ciki, shi ko yana shiga ya rufo ƙofar ta ciki sai ta fara bugu tana kiran sunan shi.

"Yusuf ni za ka wulaƙanta? Wallahi in har dai ka kwana a ɗakin nan ban yafe maka ba tun da dai haƙkina ne yau "

Kawai sai ta fashe da kuka ni wallabi ban saba ganin haka ba yasa sai jikina ya yi sanyin da na kasa motsi. Ganin maigadi na gefe yana kallon komai ita kuma tana ta kuka tana buga ƙofa tana Allah ya isa ba ta yafe ba. Yau ba Baban Khalipa Yusuf ne kai tsaye.
Ƙarisawa na yi ina mai saɓe da yumna da ta fara barci a mota na ƙarisa wajen Gimbiya ina kiran sunanta amma ba ta ji na.

"Haba don Allah wannan ba girman ki ba ne. Ki zo mu tafi bangaren ki."

Amna bata saurareni ba, ganin kamar ba ta cikin hayyacinta yasa na saka hannu ɗaya na rike ta ina fadin" Megadi na ji fa kar ki jawo mana mutane don Allah."

"Gwara ya ji. kowa ya ji cewa ba ya adalci. Maman Jidda yau fa yana dawowa shashen yarinyar nan ya tare na shiga na yi masa mgana a bangarena yake ya fara masifa shi bai san da haka ba. Ita kanta ta ce masa kin faɗa mata amma bai yarda ba ya kira ɗin ma ya tabbatar daga bakin ki amma ki duba fa a gabanki ya shige ciki saboda zalunci har yana rufe mini ƙofa saboda tozarci?

Ta faɗa tana kuka, abin da Yallaɓai ya yi bai kyauta ba amma ita ta ja ma kanta, da ƙyar na lallasheta na ja ta bangarenta. In da Allah ya taimaka yara suna bangarena tare da Baby. Haka na zauna ina ba ma Gimbiya haƙuri amma tana ta kara shan wallahi in dai ya kwana a bangaren Rabi'atu ba ta yafe masa ba

"Ki yi hakuri mana. Ki yi masa uziri tun da bai sani ba."

"Da bai sani ba amma ai yanzu ya sani."

Ta faɗa tana jan majina.

"Ki yi haƙuri zuwa da safe sai mu yi magana gabaɗaya "

"In yana so na saurare shi to ya fiti daga ɗakin yarinyar nan in kuma ya kwana wallahi ba zan saurari kowa ba "

Jin haka yasa na ɗaga waya na kira Yallaɓai sai da ta katse na sake kira ya ɗaga ko mgana bai yi ba daga gani ranshi na ɓace ne.

"Yallaɓai don Allah ka fito mu yi magana."

"Ba zan fito ba. Ke ma ina mai ba ki shawara karki dame ni in ba haka ranki ya ɓaci."

Ya faɗa a fusace.

"Ka yi haƙuri ka fito don Allah."

"Ta ce Allah ya isa to zan kwana Allah ya bi mata haƙƙin ta kamar yadda ta ce."

"Ba za a yi haka ba. Ka dai yi haƙuri "

Da ƙyar na samu ya anince zai fito mu yi magana da ya fiton ma cewa ya yi ba zai shiga bangaren Gimbiya ba jan shi na yi zuwa bangarena mu ka yi magana, ina ba ma Yallaɓai haƙuri yana yi mini tsawa.

"Ina ruwan ki? Ki ƙyaleni kar ki dane ni "

"Kar ka yi haka. Ka je ka kwana ba gobe ba ne shike nan!

"Ba zan kwana ba "

Ya katse ni, sannan ya cigaba da faɗin" Kina faɗa mini wai ta fada za a dawo kwana biyu ni kun faɗa mini ne? Kuma ma haka za ta zo tana mgana da ni gaban Rabi'atu tana yi mini rashin kunya?

"Ka yi haƙuri ai ta fada mini laifina ne da ban faɗa maka ba"

"To kema ki fita idanuwana. Ke ce ke aurana da za ki riƙa yanke hukunci a gidana ba tare da sanina ba?

Ai ina jin haka sai na yi shuru, ya riƙa masifa har da rantsuwan  zai gyara bangaren shi da yanzu sai dai bishi can in ya ga dama ya kori kowa ya kwanta shi kaɗai.

"Ka yi haƙuri '

Nawa kenan ban haƙuri, dakyar na samu ya amince zai kwana a ɗakin Gimbiya.

"Ka yafe mata Allah ya isa da ta yi sheɗan ne "

"Ke ina ruwanki da abin da zan yi mata? Sadiya kina mini abin ba na so wai nan gidan gidan ki ne ko gidana?

Ina dariya na ce"Gidanmu dai Ranka ya daɗe "
Sai da na saka shi dariya. Na samu dai ya shige ban san yadda suka ƙare ba, yara ma a bangarena suka kwana da safiyar Allah Gimbiya ta bugo mini waya tana sharban majina wai da na sani na ƙyale Yallaɓai ya yi kwanciyarsa a in da yake so.

"Tun da ya shigo ya ke faɗa sai abin da ya manta bai faɗa mini ba. A falo ya kwana a kan kujera da asuba da na gaishe shi wai in na ma sake gaishe shi zai yi mini Allah ya isa."

Ni gabaɗaya ma sun sakani a tsakiya. Yallabai tun bakwai na safe ya fita na kira shi a waya
Yace kar na dame shi kamar ya san maganar Gimbiya ne ya taka mini burki.

"Sadiya in dai ba ke kika auro mini Saudatu ba to ki fita a mganata da ita. Tsakanimmu ne ba ruwanki."

"To ta zo tana mini ƙorafin kai ma kace in ta sake gaisheka Allah ya isa."

Kawai sai ya yi tsaki kafin ya ce" in ta sake zuwa ki kore ta. Ki faɗa mata ni na ce ba ruwanki"

Zan yi magana ya tare ni da cewa"Wallahi kema zan yi miki Allah ya isa in baki ƙyaleni ba haba."
Ai ina jin haka na kama kaina daga ƙarshe ya ce in na sake yi masa magana wallahi zai yi mana yaji kuma in ya tafi ba zai dawo ba sai ya ga dama."

"Abin har ya kai haka? To Allah ya huci zuciyarka "

Ya ce Amin a fusace ya kashe wayarsa tun da na ji haka na cire kaina a ciki. Da Gimbiya ta dawo tana faɗa mini wai ita Baban su Khalifa zai wulakanta saboda wata zaunar da ita na yi na faɗa mata gaskiya da cewa ta yi haƙuri ta kauda kanta a kan Yallabai da Rabi'atu in ba haka ba wata rana komai zai iya faruwa. Ta koma gefe ta zama yar kallo amma ba ta ji ba.
A cikin kwanakin ma sun sake wata rigima wai in ya shiga ɗakin Rabi'atu da daddaee zai yi mata sallama yana ɓata lokaci, rigima suka yi sosai Gimbiya ta sake masa Allah ya isa a kan haƙkinta shi kuma ya ce ya gaji ya ɗaga waya ya kira Nene ya faɗa mata. Sai da Nenen ta zo gidan sulhu ne na ji labari gabaɗaya ta taramu ta yi mana faɗa shi dai ta jadadda masa ya yi adalci ne.

"Nene ina iya bakin ƙoƙarina. Saudatu ta cika ƙorafi sannan ba ta da hakuri tun da na yi auren nan ba ta bar mu mun zauna lafiya bq"

Ita kuma tace me ya sa yake mata rashin adalci in yana da gaskiya ai ba za ta riƙa mgana ba.
Rabi'atu dai shuru bata mgana, Yallaɓai ya rantse ya ƙara rantsewa  in  Gimbiya ta sake masa Allah ya isa zai dauƙi mummunan mataki a kanta Nene ta yi mata faɗa ta kuma sakata ta bashi haƙuri nima ta yi mini faɗa da nariƙa nuna ma Gimbiya wani kuskureta in ta yi wani abun

"Ko ta nuna mata wannan zata ji ta ne? Wallahi Nene Sadiya ba ta taba ɗaga mini hankali da zan auero Saudatu  ba a wannan auren ma bata ɗaga mini ba. Amma kin ga wannan y'ar taki? Haƙuri na ne ya ƙare amma ta yi mini diɓar albarka ba adadi ina shanyewa."

Nene dai ba ta bar gidan ba sai da ta yi musu sulhu. Kwana biyu kamar an samu canji. Rabi'atun ma na nuna mata ta riƙa bin Gimbiyae har ɗaki tana gaisheta. To na ga tana shiga, amma fa kishi Gimbiya take yi da ita kamar hauka kishin da take yi da ni ne ya koma kan Rabi'atu tun da ta ga Yallabai a gaban mu ma yana nuna mata rawan jiki.
Rigima ta lafa sama da wata ɗaya kawai a wani dare muna kwance da Yallaɓai yake faɗa mini ya siya ma Rabi'atu mota saboda zirga-zirgan makaranta cikin satin nan za a kawo motar. Kamar zan yi masa mgana na ce ya manta da Gimbiya! Domin ko kwanaki ta yi masa mganar ya sauya mata mota ko ciko ne ya yi mata ta saida tata ta siya wata ya ce sai zuwa gaba.
Kar yace ina baƙin ciki ya sa ban ce komai ba. Mun yi maagana da kwana biyu mota ta iso, Musbahu ya tuƙo ta ya kawo ta gidan Corolla ce Gimbiya ta ɗauka motarta ce har ta fara murna sai gogan ya ce na Rabi'atu ne.
Gimbiya ta cika ta yi fam Rabi'atu ta yi ta santin mota tana murna nima dai na fito na gani na taya murna lafiya lau muka kwanta da mota amma ko da garin Allah ya waye gabaɗaya an yi ma gilashen motar nan rugu rugu.


*TKGB3020A*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX


Assalamu Alaikum Fanmily, mun fara saro muku kayan Kitchen ko wani nau'i, duk abin da kuke bukata na gyaran Kitchen ɗin Amarya da uwargida duk za ku same su a JANAFTY KITCHEN ITEMS, kayan mu masu kyau ne da inganci sannan za ku same su akan rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina a falin Nigerian nan. Domin karin bayani ku tuntuɓe mu ta waɗannan lambobin kamar haka.
09069067488.
+234 706 234 9732

Muna maraba da masu siya ɗaya ko sari🥰

Ni dai har ga Allah bayan fitan Yallaɓai masallaci na ji kamar ƙaran fashewar abu amma sai ban mayar da kai ba tunani kunnuwa ba su jiyo mini sautin daidai ba. Ashe ko acikin gidan ne tun da Yallaɓai ya ce har ya fita sallar asuba motar na nan lafiya ba abin da ya same ta. Kenan bayan fitan shi ne koma me ya faru ya faru ɗin.

"Innalillahi ko jifa aka yi ne daga waje Yallabai?

Na faɗa ina riƙe baki saboda duk mun fito haraba har da su Baby gabaɗaya ana ta jimami amma Gimbiya ba ta ko buɗe ƙofar shashenta ba.

"Wani jifa? Wannan aikin da gangan ne, da kuma niyya aka yi shi an fasa gilashin gaba an fasa gilashin window just imaging fa Sadiya"

Ya faɗa yana zagaye motar yana dubawa, Rabi'atu ta yi tsaye da hijabi ta kasa magana wannan shi ne ta ga samu ta kuma ga rashi.

"To waye ya yi wannan aikin?

"Ko waye ma za mu sani yanzu."
. Yallaɓai ya nufi wajen Megadi Yumna ce ke zillo daga hannuna ya ce kar na sauke ta saboda gilasan da ke watse a wajen.

Mu dai muna tsaye da ni da Rabi'atu da Baby ina riƙe da Yumna muna jajantawa Baby faɗi take yi" Za a iya gyara motar Anty Rabi'atu kar ki damu."
Nima ganin ta damu ina ta ce mata kar ta damu za a ce a saka wasu gilasan ba damuwa ba ce ni fa har tunani na yi ko tsawa ce sai na tuba ba damuna muke ba, amma ban taba kawo ma kaina Gimbiya ce ta aikata wannan ɗanyen hukuncin ba.

Muna nan tsaye sai gani kawai muka yi Yallaɓai ya dawo daga wajen megadi a fusace kamar zaki ya zo ya wuce mu ina ts kiran shi amma bai saurareni ba. Kofar shashen Gimbiya ya fara bugawa kamar mahaukaci yana kiran sunanta da tsawa abin da ban taɓa ji ba, ina jin ko ita Rabi'atu ba ta taɓa jin muryan sa cikin fushi haka ba.

"Saudatu!. Saudatu! Saudatu!"

Haka yake kiranta lokaci ɗaya yana buga ƙofa kamar zai balla na ruɗe na biyo shi ina faɗin" Subhanallah lafiya Yallaɓai?
Ko kallo na bai yi ba sai ma ya matsa baya kaɗan ya fara tokarin ƙofar da ƙafarsa.
"Haba Yallaɓai wai miye haka ne?

Na faɗa ina ƙoƙarin rike shi ya fizge jikinshi yana ce mini na matsa baya.

"Ɓalla ƙofar kuma za ka yi?

"E ina ruwan ki? In ma na ɓalla ma ba gidana ba ne?

Hake ya ce mini a tsawa ce sai na yi shuru kawai na kasa mgana ina kallon shi.

"Ki koma baya in ba za ki yi zama yar kallo ki koma bangaren ki "

Na sake yunƙurin mgana ya kira sunana a tsawace kafin ya ce" Kar ki sake yi mini mgana."
Tsawa ya yi mini sai da na yi baya Yunma ta tsorata ta fashe da kuka ai sai na yi gefe ina maimaita innalilllahi a ƙasan raina ina tunanin meke faruwa ne?  Ganin ni

46 / 55