faɗa mini har Rabi'atu ta saka ta yi ma baban na su magiya amma bai amince ba ni ta so na saka baki ni kuma na ce ba ruwana ta zauna ta yi karatunta kamar yadda ya ce ba a gama ba, ga bikin Adnan nan tsakaninsu sati uku ne su har sun fidda anko ma, mu dai na Datti ba mu fitar ba lokaci ya kure kowa na shi zai saka.
Ban raba cinghan ɗin gayyata ba amma na sanar da baki. Kaf dangin Yallaɓai suna da labarin ƙanina zai yi aure. Balle ma na san Yallaɓai zai sanar a group ɗin su na gida nima kuma Munnira ta sanar a wanda muke ciki ta ce muna gayyatar kowa da kowa. Rabi'atu da Gimbiya ko kowacce har shashenta na kai mata kati na sanar da ita. Rabi'atu ce ke murna ita da Baby amma Gimbiya ce mini ta yi itama ranar tana da biki a Rano can ma za ta kwana. Ni kuma sai na ce in ta yi ma addu'a ya wadatar. Yallaɓai kuma ya ce mini zai je ɗaurin aure sannan Datti ya kirani ya ce na taya shi godiya 100k Yallaɓai ya tura mai da na yi masa godiya sai ya shafa kumatuna yana faɗin" Nima ai Datti ƙanina ne."
Sai na jinjina masa kai amma duk da hakan dai na yi masa godiya.
Ana gobe biki acan na kwana ni da Yumna kaya ma Baby ce da safe suka taho mini da shi ita da Rabi'atu. Na ga kara sosai su Munnira tun safe suka zo mini biki su Suwaiba duk sun leƙe min har Mimisco ta zo, ta ba ma Gwaggo 10k. Gimbiya dai da safe ta leƙo ko minti talatin ba ta yi ba ta ce mini za ta wuce Rano na yi mata godiya na rakata har waje. Da yake ɗaurin auren na safe ne zuwa la'asar tuni har yan ɗaurin aure tun kamo hanya da Amarya. Yallabai da Kawu sun je ɗaurin aure Tariq da dake can ya samu zuwa, mu kuma muna gida muna shirin tarban su, sun iso wajen biyar na yamma kai tsaye gida suka taho da ita muka tarbeta a ɗakin Mama aka sauke su ita da y'an uwanta da ƙawayenta abinci da komai ba su da matsala duk mun tanada.
Marwa tun jiya itama ta na nan, Mubeena ce kawai ba ta zo mini biki ba tana gidansu ba ta da lafiya laulayi. Ta samu ciki sau biyu yana zubewa sai yanzu ta sake samu. Ma'u ma sai fama da tsohon ciki, riki riki ita abokan zamanta sun zo mata biki, ni kam da man Rabi'atu tana gidan nan tun safe sai dare sannan Yallaɓai ya zo ya ɗauketa suka koma gida. Ni da yara duk nan gida muka sake kwana. Dangi an haɗu gabaɗaya kamar kar a rabu yan gandun albasa ma sai ranar lahadi suka koma, mu kam sai litini sai da aka ci aka suɗe a ranar duk su Ya Hamza suka koma da matan su, a bikin ne muka ji an saka ranar auren Anti ɗiyar Ya Murja, Ya Balki ma ta ce mai son Firdausi an turo, ina tunanin bikin nan zai yi mana rudgudu, yanzu dai sai dai in Ma'u ta haihu za mu sake haɗuwa. Muka baro gida da Amarya sai Gwaggo da Baaba amma dangin ta sun kawo kayan fulawa da kololi, da sauran kayan al'ada kuma duk an rarraba mana har dangin Mama suma an ɗibar musu na su kason
Ranar litini gidan ya watse. Ni kaina sai dare na koma gida ni da yara. Sadi ne ya je da mota ya ɗauko mu Rabi'atu har ranar lahadi ta dawo sai mangariba ta tafi, litini kuma da man tana da makaranta ko a hakan ma na gode. A bikin ma su Suwaiba na ji suna taɗin su Anty Bahijja sun ce wai na haɗa kai da ƙaramar yarinya saboda na ƙuntata ma Gimbiya maganganu dai gasu nan ni ban biye musu ba, saboda in da sabo na saba da ire-iren mganganun su a kaina. Ni ban haɗa kai da Rabi'atu ba amma dai na san daga ita har Rabi'atu ina da zaune da su tsakani ga Allah, ita ce kawai yarinyar take darajani ta kuma ɗauke ni da ƙima fiye da yadda ita Gimbiyar ta ɗauke ni,sai a ga laifina don ina kula mai kulawa da ni? In fa tana gida a shashena take rabin yini na in ba ni ce na ce ta koma bangarenta ba, barin ma in Yallaɓai na ɗakinta sai na ce su je Baby ta ta ya ta ayyuka shine fa za ta tafi, amma in dai yana bangarena ne, ko bangaren Gimbiya sai dare sannan zai rakata ta koma shashenta ita da Baby dake tayata kwana nan take cin abincin ta yi koman ta ta zauna da yara su yi ta hira, barin ma Yumna da har ta saba da ita, da ta ganta za ta dafe mata. Sannan ko y'anuwanta wallahi suna darajani in dai suka zo gidan nan sai ta fara kawo su bangarena mun gaisa sannan su ke wucewa shashenta. Kuma in za su tafi za su yi mini sallama Gimbiya ko sai mu kwana uku ba mu ga juna ba muna gida cikin gida ɗaya kofar bangarenta ma yana rufe ne, ba ta neme ni ba ni ko ai ba zan lalace a kanta ba. Ni dai ba na gaba da ita in muka haɗu ko ba ta gaisheni ba zan gaisheta. Yallaɓai ba ya yini yake yi a gida ba ni kuma ba ni da halin ƙorafi balle na sanar da shi wasu abubuwan. Shi dai tun da bai taɓa jin an samu wata matsala bq sai hankalin shi ya kwanta. Ba ruwana da sanin tsakanin matan shi kamar yadda nima ba sab tsakanin mu ba. Na kama kaina gefe sai kuma na samu zaman lafiya.
Kafin tafiyar su Datti Kaduna ya kawo mini Amarya har gida ta gaishe ni, ba ni ba kaf ɗin mu haka bi da ita gida gida ta gaishemu. Ranar sati na zagayowa suka wuce Kaduna. Ni kuma anan Gwammaja muka shiga hidimar bikin Adnan, abin da ya sa na shiga sha'anin Adnan nawa ne kamar Musbahu ne, mun yi anko gabaɗayanmu Yallaɓai ya siya mana har da su Jidda da ya amince za a ɗaukota ta yi biki ta koma. Adnan anan Kano zai ɗauko matarsa a can tarauni, shima ya haɗa lefensa na gani na faɗa da taimakon yanuwan shi, sai da bikin ya matso na ji labarin Adnan a gidan da Gimbiya ta tashi zai zauna Yallaɓai bai faɗa mini ba amma sai na yi masa uzuri ayyuka sun yi masa yawa wataƙila ya manta ne. Gida an ce an yi mass fenti tas ya dawo kamar sabo a bakin ni Hauwa na fara ji tace itama Mutaƙƙa ya faɗa mata sai da na koma gida a daran Yallaɓai na shashena na tambaye shi sai ya ce mini haka ne. Ganin ba shi da gida zai kama haya shi kuma tun da yana da gidajen sai kawai ya ce bari ya bashi guda ɗaya ya zauna. Na ce tabbas ya yi tunani Allah ya bar zumunci. A satin bikin aka kai lefe ni kaɗai na je Gimbiya ba ta je ba Rabi'atu tana makaranta su Anty Bahijja ne yan gaba gaba da yayarsa Ummu salma da su Nasara. Mu dai muna gefe ba mu yi baya ba kuma ba mu tusa kan mu ba.
Sai da muka haɗu a sha'anin bikin Adnan ne sannan Anty Maimuna ke yi mini Allah ya sanya alherin auran Datti na amsa amma sai da na yi musu tsiya da gayya kuma Anty Bahijja na wajen na yi musu jirwaye mai kamar wanka na ce na tare kowa ya zo ya ga waje ya saka albarka ita da Anty Bahijja ban gan su ba.
"Sai mun sake komawa? Ai ina ce in mutun ya yi zuwa ɗaya shike nan."
In ji Anty Maimuna.
"Shi na gani. Duk ba gida ɗaya ba ne. Mun je lokacin tariyan Gimbiya kuma da auren Tafida da yarinyar nan"
Haka Anty Bahijja ta faɗa Allah ya sa Rabi'atun ba ta nan da ta ji wani iri kamar ba ta san sunanta ba.
"Bisa adalci kun je ma Gimbiya. Kun je domin Rabi'atu ni kuma sai ku kasa zuwa saboda ni? An ya kun yi adalci kuwa?
Sai suka kasa mgana ganin na daure su da mgana. Anty Maimuna tace shike nan bayan bikin za su zo in sha Allah. Nene na wajen ta ce ba su kyauta ba ya kamata su je su saka albarka. Anty Bahijja ta yi muƙus ba ta yi magana ba ni ko na gama faɗin abin da ke raina na kama harkan gabana.
Har su Anty Zabba sun taho sha'anin bikin Adnan, ranar jumma'a Sadi ya je ya ɗauko Jidda sai murna take yi a bikin nan na sha surutu kau da kai kawai na yi, ganin har da Dangin Rabi'atu da suka zo ni suka fara nema na kuma yi musu jagora falon Nene na sanar da ita iyayen Rabi'atu ne sannan ganin ta tana tare da su Jidda, in wani abu take ɓukata za ta zo ta ce mini Umma kaza shike nan aka saka mini ido a gidan bikin nan da nan su Anty Bahijja suka fara yawo da ni da cewa na haɗa kai da yar cikina saboda neman suna. Gimbiya kam tana gefe da man ko a sha'ani ba ma zama bangare ɗaya amma na san ba haka ta so ba, ta so ne wata ƙila itama Rabi'ar ta fi ma rashin ganin darajata hauahi take ji ta bakin Munnira ganin yarinyar ta ɗauke ni da daraja. Anty Zabba ta ce mun ba ta sha'awa na riƙe Rabi'atu ta gam bisa Amana hausawa sun ce kai ma ka gaida mai gaishe ka.
Nan Gwammaja aka fara kawo Amarya bayan isha'i. Muka tarbeta gabaɗaya bayan an shisshiga da ita ko'ina. Dangin mahaifiyar Adnan ma suna gefe sai dai in an kira su amma dai an sauke ta a farko a shashen mahaifiyar Adnan ɗin ne. Misalin wajen tara na dare za su koma da ita sai aka ce mu yi mata rakiya gabaɗayanmu za mu je c a motocin gida tun da ga abokan Adnan nan duk da motocin su, har mun shiga mota sai na ga ban ga Rabi'atu ba, ban ga Jidda ba sai Baby ta ce mini ta bi motar Uncle Musbahu. Rabi'atun ne tana shashen Hajiya Iya tana salla in ji Jawaheer. Ni kuma jin haka sai na ce don Allah a ɗan jira ta.
Kawai sai Anty Bahijja ta fara faɗa wai ba ta son sanabe in ta idar da salla ga motoci nan su kawo ta mana. Da man Mimisco ce ta ce a tafi gabaɗaya kar ace za a raba tafiyar.
"Baƙuwa ce fa bai kamata mu tafi mu barta ba."
Na faɗa har a cikin zuciyata."
"Gaskiya ne kuma"
In ji Anty Zabba.
Gimbiya na cikin mota ita da Naja da Halima sai ga sun fito suna tambayan ba a si.
"Uwar iya ce ta ce ba za a tafi ba sai an jira Amaryan ku."
In ji Anty Maimuna.
Kawai sai Gimbiya ta yamutsa fuska kafin ta ce" To sabon salo tusa a lasifika."
"Ni fa ban ce ku tsaya jiran mu ba ku yi gaba za mu taho daga baya."
Na faɗa ganin suna neman su taso mini har su Hauwa na ce su yi gaba cikin gida na koma sai ma muka haɗu da su a tsakar gida ita da Nafisan Kabir sun ɗauko kololin abinci Mimisco na bin bayan su. Sai take ce mini an manta ba a tafin musy da abinci ba, sai na ce Rabi'atu ta kawo kulan amma taƙi ba ni. Ko da muka fito sun tafi sai da muka jira Musbahu ya dawo ya ɗauke mu zuwa can gidan mun iske gida cike da dangin amarya da mu kanmu da man ashe akwai wasu masu ganin gidan Amarya da ba su zo nan Gwammaja ba.
Har ga Allah ban san abin da aka dafa ma yan kawo Amarya ba ni dai na ga Mimisco ta saka su Naja sun yi abinci ashe shinkafa ce jalop da kaza sai alele sai pepe chicken, amma ita Rabi'atu ta gani muna zaune a falo tare da su Hauwa ta zo gefena ta yi mini raɗa wai za ta ci alale amma tana jin kunyar tambaya sai na miƙe ina fadin bari na je na samo mata. Anty Zabba na gefe tace mene da ba za a faɗa a fili kowa ya ji ba.
"Sirri ne"
Na faɗa ina dariya ita kuma sai ta sunkuyar da kanta akwai kunya ita, Munnira na yi mata tsiyan ko Yallabai ne ya yi kira sai ta saka kanta cikin mayafi tana dariya. Nan da nan suka bushe mata da dariya.
"Amaryan Tafidanmu akwai kunya."
In ji Jamila kuma ba ganin ido ba tana da kunya, ba ta iya haɗa ido da wanda ya girmeta.
Duk sai hankula ya dawo kan mu, Rabi'atu kanta na ƙasa sai mirmishi amma ba ta mgana. Hauwa na ce ma ga amana nan bar mata zan je na dawo sai ta ce ta karɓa ta dawo kusa da Rabi'atu tana faɗin" ƙyalesu ƙanwarmu."
Munnira ta daddage ta saki guɗa tana dariya, ni ma dariyan na ke yi, Gimbiya na gefe ita da Halima kamar su mutu saboda baƙin ciki. Amma ba halin mgana.
Ciki na shiga in da dangin Amarya suke na ga suna ma zuba abincin wata cikin su na yi ma mgana ina son alele, sai ta ce mini haba bakomai ta samu filet ta saka mini guda huɗu sai da na ce ta rage za ta sanya mini nama na ce wallahi ta bar shi, wannan ɗin ma sha'awa ce wata ƙanwata ke so.
"Allah sarki hala kwaɗayin ƙaramin ciki ne?
Sai na yi dariya kafin na ce" Muna dai saka ran haka"
Sai itama ta rakani da dariya sai da ta faɗa sai na yi jim a zuciyata ina tunanin ko dai an samu rabon ne? Amma kuma ban ga alamun ciki a wajen Rabi'atu ba da man na san ta akwai son alale ko ni in na yi har ajiyewa take yi. Itama tana yawan yin shi sai na cire tunanin haka a raina. Na fito falon dai dai ana cewa mu ta shi mu tafi, tun da mun rako amarya gida fa kamar ba shi da yake sun yi jeren su da wuri Gimbiya kafa ɗaya kan ɗaya kamar falonta ta manta ya tashi daga falonta yanzu ya koma na wata.
Kowa ya ganni da alele bai yi nagana ba sai Anty Maimuna tana tambaya ta ni kuma kai tsaye na ce" Rabi'atu ke so shi ya sa na samo mata.".
Matar nan ba sai ta fara faɗa ba.
"Miye haka? Ta son tana so tun a can ba ta yi magana ba sai da muka zo nan?
"Renin wayau ne "
In ji Halima.
Anty Bahijja na can gefe tana waya tana gamawa itana ta zo aka faɗa mata ba ta bi ba a si bq sai ta ara ta yafa wai wulaƙanci mu zo da abinci daga gida amma mu koma muna roƙo saboda zubar da kai.
Sai Rabi'atu ta ba ni tausayi sun ta so mata, cikin rawan murya ta ce" Ban san an yi alelen ba ne sai yanzu na gani raina ya biya. Ku yi haƙuri "
Ta faɗa kamar ta fashe da kuka har ta ma fara hawaye. Sai Anty Maimuna ta fara faɗin"To daga mgana sai kuka?
Ta faɗa cikin mele baki ni kasa ma mgana na yi, na ba ta alalan baiwar Allah ta ce na ma yar ba za ta ci ba.
"Karɓi abin ki me zai hana ki ci?
Sai ta yi shuru. Suwaiba ta ce na samu leda na saka mata in mun je gida ta ci amma yadda aka taso mata yanzu za ta ji ya fita ranta ne.
Sai na yi haka na koma na tambayo leda a ciki aka bani mai girma na juye mata alalan ina fitowa da karfi Anty Bahijja ta kira sunana gaban mutane har da waɗanda ba ahalin mu ba. Na amsa mata duk da na san kiran ba na arziƙi ba ne.
"Ke wai ba za ki kama girman ki ba ne, ji yadda kike rawan jiki a ƙan ƙaramar yarinya?
Sai na buɗe baki amma na ma kasa mgana.
"Ai ba da ita ya kamata ki haɗa kai ba. Gimbiya ce dai da ke sai ita data ke ƙarama ta bi bayan ku amma abin da takaici ji yadda kika ma y'ar da kan ki baya a kan yar cikin ki, domin ko za ta girme ma Jidda da kaɗan ne."
Na ji na muzanta amma ban bari ta fahimta ba sai na yi mirnishi kafin na ce" Ai kema kin ce sa'ar y'ata ce. Shi ya sa sai nake yi mata kallon ƙanwa. Kuma maganar na ma yar da kaina baya ba haka ba ne, ni ina daraja wanda ya san ina da daraja, da Rabi'atu da Gimbiya duk ɗaya suke a wajena. Tun da matan Yallaɓai ne, abin da za ki fahimta wanda ba ya yi da kai ba za ka takura shi sai ya yi da kai dole ba. Wanda kuma yake yi da kai kar ka kwabe masa ƙokarinsa ka ta ya sa nuna girman karramawan da ya yi maka."
Sai na dakata ina kallon Anty Bahijja kafin na sake yin mirmishi na ce" In dai wannan shi ne kike kira na zubar da kaina na yarda ki yi ta ɗauka a hakan."
Jamila ta kada baki ta ce" Ni ban ga abin ceceku ce a kan wannan maganar ba wallahi ina laifin yarinyar nan? Duk in da Sadiya ta yi tana biye da ita sai kawai ta wulakanta ta! Haba Anty Bahijja kuma ai ba komai za ku rika mgana ba "
Jin kowa ya taso yana mgana yasa sai ta yi shuru. Baiwar Allah har sun saka ta kuka. Yumna ce ta je wajen ta hau jikinta ta ɗauketa shi ne ma ta daina sharan ƙwalla duk sai na ji ban ji daɗi ba. Gimbiya sai taɓe taben baki da fuska take yi amma ba ta