Turken Gida Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   44 / 55

129K to 132K   out of 163.1K words

yamma sai ga kiran Yallaɓai da cewa anjuma zai kawo su Gimbiya gidana zai yi zama da mu.
"Har sai ka tarkato su gidana ? Ka yi musu duk maganar da za ka yi acan ni in ka zo sai ka faɗa mini ba ni da matsala."
Na faɗa masa haka har a cikin zuciyata
Kawai sai ya fara mini faɗa wai ni zan faɗa masa ga yadda zai yi?

"A'a yi hakuri daga shawara."

"Riƙe shawaranki sai na ce ina ɓukata. Malama za mu zo anjuma nan sai ki hana ɗin."

Daga haka ya katse wayarsa sai na bi wayar da kallo ina riƙe da baki da man tun lokacin da ya kira wayar na ji muryansa a sama ina kyautata zaton shi da Gimbiyarsa ne aka tafka wata tsyar shi ne zai sauka akaina ƙaramin tsaki na ja ina tura baki kamar yana ganina

Ni da Baby mu ka share gida muka goge. Tare kuma muka yi girki cous-cous da kayan lambu mai hanta sai na yi mana kunin Aya da zoɓo muna gamawa na bar mata gyaran kitchen na ce kuma ta jera komaI a saman dining ni kuma na shiga wanka. Gayuna na ci da man ni duk wanda ya sanni ya sani da ban yarda da zama haka ban gyara kaina da jikina ba. Wata doguwar rigar amfata na saka sabuwa ban ma taɓa sata ba, ɗinkin A shafe ne ta yi min ɗas a jiki na kashe ɗaurina na maryam babangida. Da man na yi kitso Maman Nana ranar asabar ta zo ta yi mana ni da yara har da Jidda tun da ana gobe za ta koma ne.

Na idar da sallar isha'i Saude ta kirani a waya na tsaya muna gaisawa. Har suka iso ma ban sani ba sai da Yallaɓai ya shigo ciki da kansa. Ji kawai na yi an ruƙumƙumeni ta baya tunda na ji  kansa a saman wuyana na san shi ne in Yumna ce kafafuwana take rumguma
Sama sama na yi sallama da Saude ina ture Yallaɓai.

"Ke ba ki iya zuwa tarban miji ba ko?

Hararan shi na yi kafin na ce" Mijin wa?

"Mijin Sadiya mana."

Ina dariya na ce" Ai ni na bar ma su  Rabi'atu kai."
"Wallahi ba ki isa ba"
Ya faɗa kai tsaye har yana wani shan mur sai ya ba ni dariya.
"Ahto ban yarda ban kuma lumta ba. In ke za ki iya haƙuri da ni, ni ba zan iya haƙuri da ke ba My Sady"
Ya faɗa yana ƙara rumgumomi wannan karan ban kwabe niyarsa ba nima sai na rumgumeshi ƙamƙameni ya yi yana shinshinan ƙamshina.

"I miss you"

"Na yi kewar dumin jikin ki.'

Ya sake faɗa yana shafa bayana zuwa ƙuguna.

"Na yi kewar ban ruwa a nan."

Hannun shi na ture ina faɗin" Wani kewa? Kai da ka samu sabon lambu ba irin nawa tsohon da ya ji tsatsa ba."
Kallona ya yi cikin ido kafin ya ce" Haka nan na ke son shi, ai tun yana sabon shi ni na riƙa gurzan shi har ya yi tsatsan kin ga ko dole na so shi a haka"
Na buɗe baki zan yi magana ya matse ni ya haɗe bakin mu sai da ya tsotse jan bakina tas sannan ya sake ni ni da shi gabaɗayanmu muna sauke numfashi.

"I miss everthing about you Sadiya ta. Har da wannan jan bakin."

Ya faɗa yana shafa bakin sa, baki na tura masa ina ƙunkƙuni

"In kika sake tura mini baki wallahi zan turmushe ki sai na yi ɓarnan ruwa."

Ai ina jin haka da gudu na fice ina jin sa yana ƙayƙyatan dariya.
Sai da na daidaita kaina har ɗaurina ya kwance sai da na sake yin wani sannan na fita can falo, na iske Rabi'atu da su Baby, ta saka dogon hijabin ta har kasa sannan ba ta yi kwalliya ba amma da ka ganta fuskar nan ta yi fresh alamun dai ana shan amarci.
Gimbiya ko na gefe ta kame a kan kujera mai zaman mutum ɗaya an ci gayu da mayafi a saman kafaɗa, Ammar na hannunta Amwar na gefenta Khalipa ne kawai tare da su Baby.

Rabi'atu na ganina ta fara gaisheni cikin girmamawa na amsa ina tambayanta baƙunta ta sunkunyar da kai. Gimbiya ko ni da gidana ni ce na fara gaisheta ta amsa kamar ba ta so. Ban damu ba Yallaɓai na fitowa na ce na haɗa mana dinner mu fara da cin abinci.
A gaban su ya ɗan rumgumo gefen kafaɗata ya sumbaceni kafin ya ce" Allah ya yi ma matata Sadiya albarlka"
Na amsa da Amin Rabi'atu ta yi gaba ita da su Yumna Gimbiya ce a wajen amma ba ta amsa ba ina ganin ma tana hararan mu ko shi ne ya ja mini ban sani ba.

Dukkanmu har da yaran muka zauma a dining muka ci abincin. Gimbiya kunin aya kawai ta sha ta tashi ta koma saman kujeran falon ta ce ita dai ta ƙoshi. Ni da Yallaɓai ne a wajen ke ta hira sai ni in na sako Rabi'a ciki ta ɗan yi mirmishi kuma ta ci abincin sosai ta sha kunin aya. Da ma ina cewa ta ci mana ta daina baƙunta nan ma ai gida ne.

"Za ta ci fa, a can gida in kika aiko mana da abinci ta riƙa santin  cewa gaskiya Umma ta iya girki "

Ya faɗa yana kwaikwayonta ni da shi muna ta dariya ita ko ta sunne kai, ina son ta tana da kunya sosai. Anan ne na ke masa taɗin ashe ya kai ta wajen Alhaji.

"To ni da babana kuma? Ko sai na tambayi izini."

Ina dariya na ce ba ruwana, mun tattauna mganar makaranta ya ce ai itama Rabi'atu cikin satin za ta shiga cikin makaranra ta yi risgtration suma sun koma sai ina zolayansa na ce shi zai kai ta?

"A'a sati ɗaya ban je aiki ba gobe zan koma office. Amma ina tunanin na haɗa ta da Musbabu ko Adnan"

Ni ko na ce sai dai Adnan din Musbahu ma ayyuka sun yi masa yawa ita ko tana gefe ta ce ai za ta iya fa ita kaɗai, sai ya ce bari dai ya gani in ba buJata sai ya haɗata da direba. Baby ta yi zencen nata makarantan ya ce gobe zai shiga makaranta ta zama cikin shiri za ta fara SS1.
Ni ko na ce ga Yumna a saka mini ita a Ajin yara.

"Mugunta ko? Wannan jarriyar ne zan kai makaranta to ni ba da ni za a yi haka ba "

Ina dariya wai Yumna ce jaririya ina roƙon Yallabai ya kai ta bakinta ya buɗe da karatu ya ce sai  ta kai shekara huɗu zai saka ta a makaranta wai Baby ta riƙa koya mata a gida tun da na ga ya dage na yi shuru na san ba zai amince ba.
Muna gama cin abincin na saka Baby ta gyara wajen sannan Yallaɓai ya ce duty ɗin ta ta tattara yara su koma can falon su a zauna lafiya ban da hayaniya har Ammar sai ta karɓe shi hannun Gimbiya ta tafi da shi can falon su, saboda ya ce kar a yi hayaniya shi ya sa suka yi shuru kamar ba su a gidan.

Farko Yallaɓai ya buɗe taro da addu'a sannan ya yi nasihohin shi, da tunasarwan cewa dukkanmu ya aure mu ne domin yana son mu ne, Gimbiya da  ya aurota ni ban gaza ba haka itama Rabi'atun ya faɗa mata Gimbiya ba ta gaza ba. Duka matsayin mu ɗaya mu yi haƙuri mu zauna lafiya mu rike juna da Amana. Ya ce ni ce Babba ya san ina ƙokari to don Allah na ƙara Rabi'atu ƙarama ce a cikin mu, mu zauna da ita bisa gaskiya da Amana.
Ya ba mu damar magana ni dai na ce in sha Allahu ba matsala daga bangarena Gimbiyar ma ta ce haka itama Rabi'antun ta ce haka sannan ya yi mata gargaɗin ko ba aure ba a shekaru mun girme mata ta yi mana biyayya in ya ji saɓanin haka zai saɓa mata ta ce hakan ba zai faru ba.

"To na ji daɗin  haka. Maganar rabon kwana mu bar shi 2dys ɗin ne ko ya ya?

  Sai na ce a bar shi a haka ɗin ai ya yi.
Amma sai Gimbiya ta ce ba ta yarda ba sai dai a ma yar da shi kwana ɗaya.

"Miye wani kwana ɗaya,? Da ba biyun kuke yi ke da Sadiya ba?

"Da ka ce yanzu ko mun ƙaru gwara ɗayan saboda kar a cuci kowa."

Gimbiya ta faɗa cikin gatsali, zai fara faɗa na dakatar da shi da cewa" Ba komai a yi kwana ɗayan ai duk ɗaya ne."
Bai haƙura ba yana so ya dai yi magana na ce"Ka yi haƙuri a bar shi a haka don Allah"
Jin haka yasa sai ya yi shuru. Zaman dai haka ya shi ba wani kwarjini, shi da ya kawo su  shi ya ɗauke su ya ma yar da su yafi awa da tafiya sannan ya dawo ni kuma ban tuhume shi a in da ya tsaya ba da kan shi yake faɗa mini Rabi'atu ke kuka wai tsoro ba za ta iya kwana ita kaɗai ba, shine ya tsaya yana lallashinta da nuna mata ga Gimbiya a gidan kar ta ji tsoro.

"Allah sarki. E kafin ta saba ko a gida ta ɗauko yarinyar da za ta ɗan rika taya ta kwana in baka gidan."

"E mun yi wannan mganar to can gidan baffan nata ba yara fa, ni da man Baby na ce ta riƙa zuwa tana taya ta kwana kafin ta saba."

Na ma kasa mgana ni shike nan ya'yana Yallaɓai yana raba su tsakanin matansa ba tare da izinina ba kala ban ce masa ba.
Mu ka yi shirin kwanciya amma bai bar mu mun kwanta ba sai da ya yi ɓarnan ruwa har yana yi mini sambatun ya yi kewar gidan ruwan shi a raina na ce ka ji da shi dai da asuba ma ya koma ruwa. Da safe kuma tun safe ya yi shiri ya tafi office da yamma da ya dawo ya biyo ta nan gidan ya ɗauki wasu kaya sannan ya wuce can gidan yana ƙara jadadda mini na fara shirin tariya, a nan ne ma ya ke faɗa mini gidan da Gimbiya ta tashi Kawu ya bashi shawaran ya saka yan haya, ni dai na ce kar ya saka yan haya a gidana don Allah.

"To a bar miki za ki rika zuwa partime kenan?

Na ce masa e, saboda ina son gidan ya fita yana dariya wai duk abuna sai na tashi na koma sabon gida na samu cigaba ni ina noƙewa bai san yadda na ke son gidan nan ba ne ne har raina ni kaɗai ce fa anan can ko da gayyar kishiyoyi. Ganin ya matsa ya sa dole na fara shiri Baby dai ta koma makaranta an zama manya yanzu, ni dai labulayan na samu na siya sai cafet na falo biyu sauran kuma na tattara aka kai wanki na ce na yi amfani da su. Yallaɓai na yi ma maganar falo guda ɗaya ba kujeru ban saka rai ba ya ce na yi magana nawa za a yi saffa saffa gado da kujeru da gudu na je na tambayo, can ɗan kusa da gidanmu na Dorayi ne kafinta  ya ce 800k na zo na faɗa masa ya ce a yi mini ganin na samu sauƙi na ce a yi mini ƙaramin gado da wardrope na ɗayan bedroom ɗin sauran kuma kaya na kuma da su zan koma, na so tariyan ya zama bayan biki ko da wata ɗaya ne amma bai samu ba sai da ya kai wajen bayan biki da wajen wata biyu sannan saboda an ƙarisa aiki a shashena. Allah ya taimake ni bangarena na haɗe da bangaeen Yallabai ne. Na Rabi'atu ne da Gimbiya suke a haɗe.

Ranar wata asabar ce na tare a sabon gida. Da man tun satin mota ta zo ta kwashe kayana zuwa can gidan y'an uwana suka taya ni muka gyara komai. Ban yi gayya ba daga ni sai su Munnira sai y'an gidanmu sai Marwa da ta zo, sai dangin Yallaɓai, mun dai yi girki saboda ma su zuwa. Bangarena babban bangarene kamar gidana sai dai nan na samu ƙaruwan falo da ɗakuna amma duk samfur ɗaya ne. Dining na so na yi sabo rashin kuɗi ya sa na dawo da tsoho. Amma zencen gaskiya gidan ya yi kyau Yallaɓai ya kashe kuɗi sosai masha Allah. Gimbiya tun da ta leko sau ɗaya ban ƙara ganin ta ba Rabi'atu kuma tana zuwa makaranta amma in dai ta dawo ta nan tare da mu da ita duk muka gyara ɗakuna na.

Gaskiyan magana ba ruwanta ba ta da hayaniya ga kunya. Hatta su Munnira sai da suka yabe ta ga girmama na gaba da ita. Su Suwaiba da su Jamila duk sun zo mini amma ban ga su Anty Bahijja ba Mimisco ta zo ta ga waje ta saka albarka. Maƙotana na can anguwan da na shiga na yi musu sallama suma sun zo mini ganin gida sun saka albarka. Ga wargajejen fili, ga motata, ga na Gimbiya ga na Yallaɓai amma ko rabi ba a cika ba sannan ga maigadi, na yi hoton shashena na tura group ɗin gidanmu su Ya Hamza suka ga gaggani, suka saka albarka Amina na ta santi ta ce wallahi shashema duk ya fi kyau haka su Munnira suka ce, har fentina ya fi kyau sannan Yallaɓai ya siya mana manyan palasma guda biyu ni ɗaya Gimbiya ɗaya. Sai na yi amfani da na tsohon na falona a falon yara na tsohon  faalon Yallaɓai kuma na saka shi a falona na yanzun sabon kuma na saka shi a sabon falon Yallaɓai.

Sai na raba abun falon farko na Yallaɓai ne na biyu kuma nawa na ukun na yara. Bedroon na farko na nawa ni da Yallaɓai na biyu kuma na yara sauran kuma sai na bar shi a na baki. Sannan kitchen ɗina na nan wargajaje har fridge dina da frizer anan na saka su disspanser ne kawai na saka a falon Yallaɓai.
A satin kaf ban samu fita ba ana ta leƙo mini Allah ya sanya alheri, Baby da Yumna kamar an saka su a aljannah. Sun haɗe gida ɗaya da su Khalipa in sun dawo makaranta haka za su yi ta wasa a haraba.
Rabi'atu kuma in dai tana gidan ba ta je makaranta ba tana tare da yaran
Ni da ita zaman mu lafiya. Amma Gimbiya ta ware kanta gefe, ni da man ba ta yi da ni ballatana Rabi'atu yar baya baya. Ban san tsakanin ta da Yallaɓai ba tun da ba faɗa mini abin da ke faruwa a tsakaninsa yake yi ba.

Ba ni na fara fita ba sai da aka shiga satin bikin Datti sannan muka fara zaryan zuwa Ɗorayi.



*Janafty**TKGB3020*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX


Assalamu Alaikum Fanmily, mun fara saro muku kayan Kitchen ko wani nau'i, duk abin da kuke bukata na gyaran Kitchen ɗin Amarya da uwargida duk za ku same su a JANAFTY KITCHEN ITEMS, kayan mu masu kyau ne da inganci sannan za ku same su akan rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina a falin Nigerian nan. Domin karin bayani ku tuntuɓe mu ta waɗannan lambobin kamar haka.
09069067488.
+234 706 234 9732

Muna maraba da masu siya ɗaya ko sari🥰

Bikin Datti ya taho gadan-gadan mu mun ɗauka ma za a ɗaga bikin ne ganin ba a yi shirye-shiryen komai ba amma su Ya Hamza suka ce ba za a ɗaga ba tun da Datti ya kusa gama haɗa lefensa ta hannun Anty Laila a can  Abuja. Gidan da za su zauna kuma haya ya kama anan garin Kaduna kusa da ma'aikatansu.

Ya Hamza ya turo da kuɗi Ya Abubakar da Ya Muntari sun yi ja gaba an yi fentin gidanmu ciki da bai. Sannan an gyara ɗakin Mama an yi waje da wasu kariki tai an rufe shi saboda nan Amarya za ta sauka sai sun yi sati sannan za su wuce Kaduna ita da angonta. Duk da can za a yi mata jere amma Kano za a fara kawo ta in ji Datti. Kuma y'an uwansa suka yi naam da haka mu da man namu kawai to ne da bi, saboda ƙurewar lokaci shi ya sa ba mu tara kuɗi masu yawa ba amma kowa ya yi abin da zai iya dai'dai ƙarfin sa mun damƙa ma Datti, amma ni da Amina mun ƙara masa da leshi guda biyu da atamfa aka ƙara cikin lefen shi. Gida da man su Ya Hamza sun ɗauke komai hatta da abincin da za a ci har a gama biki, balle kuma Alhajinmu na da hatsi a store sai abubuwa suka taho mana da sauƙi.

Ana saura kwana huɗu aka kai lefe. Daga Abuja Laila suka kawo shi Zaria bayan duk mun gama ganiwashegari ni da Ya Murja da Ya Aina  da Inna Mariya muka tafi da su Kaduna muka haɗu da Amina a gidanta sannan direban mijinta ya tuƙamu zuwa gidan su Amaryan mai suna Badariya. Mun samu kyakyawan tarba sai godiya akwati bakwai muka kai kuma mun yi daidai abin da ya kamata wanda ba za a raina ba. Kuma ba su raina ba ɗin mun ci mun sha har da guzuri sannan sun bamu tuƙwaici muka ce ma ba za mu karɓa ba suka matsa mana. A gidan Amina muka kwana sai washegari har da ita da yara muka tattaro Kano gabaɗaya. Muna zuwa muka iske mutanen Zaria sun iso da mutanen Yashe gida ya fara ɗaukan harama. Dangin Mama na gandun albasa da man ni ce na sanar da su bikin suna ta faɗa domin ba a faɗa musu da wuri ba amma duk da haka sun haɗa kudaɗe sun aiko mana da shi, har gobe ba su yada wannan zumuncin ba.

Jidda ta kira ni a waya har tana mini shagwaɓa wai na bar ta tazo bikin Uncle Datti na ce mata ni ba ruwana ta kira babanta, ita kanta ta san ɓata ma kanta lokaci ne ba zai bar ta ba, nan da nan ya ce ta zauna makaranta ta yi karatunta ga bikin Adnan nan in ya ga cancantar ta taho zai tura aje a ɗaukota. Ta kirani kamar ta yi kuka tana faɗa mini ina yi mata dariya. Sai a lokacin ma take

44 / 55