sai an gama suna can kuma sai ga Sameena sai da muka rumgume ga shi dai ƙanwar Gimbiya ce amma tana ƙaunata saboda da Allah. Daga Rano ta ke sannan ta sauka a gidana. Su Munnira daman ai suna nan sai suna ya tashi. A ranar mai ƙunshi ta zo ta yi mini saloon kuma tun safe na je shagon Amesty ta yi mini. Har su Munnira sun ce za su yi ƙunshin. Can sai ga Saude ta iso itama sai na ji daɗi su Khaleesat ne sai gobe amma Laila Ya Auwal ya ce mini ta na hanya.
Gida ya kacame da ayuuka. Da yake za su yi waina sai sinasir da aikatau muka kai sannam za su yi alale da shinkafa jalop mai kaza. tun da akwai naman miya da Yallaɓai ya aiko da shi. Raguna kuma uku Yallaɓai zai yan ka ma Rukayy suma ragunan su Suwaiba na faɗa mini su Anty Bahijja suna ta surutu ni a bakin ta ma nake jin raguna biyu Ya Usman ya siya masa ɗayan kuma Mimisco ce kuma ya ce tun da da sunan Rukayya a ka ba da su to duka za a yanka mata su. Sannan nima na ba da a yi mini tsire sannan na saka mai yin ledojin kayana na hijabai ya buga mini na suna da jakar nan mai ɗauke da sunan Rukayyatu Yusuf Muhammad(Yumna) name on 17 November 2020.
Cut-ceey: Hauwa'u Yusuf Muhammad(Jidda) and Maimunatu Yusuf Muhammad(Baby)
Lemuka da ruwan roba katan katan Yallaɓai ya saka a ka sauke mini sanman ni kuma za mu yi zoɓo da kunin aya duk za mu saka a robobin ma su ɗauke da sunan Rukayyatu.
Wanda a ledan za a saka mutum da jalof ɗin shinkafa mai kaza sai tsire da zoɓo wannan na in zai tafi gida ne. Da yamma kwandon tumatir da solon tattasai da attarugu mai yawa Musbahu ya zo da shi tare da gyararrun kaji guda ashirin a buhu, lokacin su Anty Bahijja da su Gimbiya duk suna gidan ba aikin da suke yi sun kame a gefe suna tsegumi tare da taɓe baki ni ko kallo ba su ishe ni ba, da suka ga an kawo wannan kayan nan kamar su mutu sun ɗauka Yallaɓai ne ke ta kashe mini kuɗi tun da nima yar matsiyata ne ba ni da kuɗi. Ya Hamza da Ya Auwal sai suka suka haɗa mini 150k na kuɗi saboda na ce musu zan yi suna kuma Yallaɓai ba shi da kuɗi, abin da ya ba ni ba za su ishe ni ba, Shi ya sa suka tura mini kuɗi har Datti sai da ya tura mini 30k ya ce na ƙara. Kawu Abba 50k ya tura mini bayan Marwa ta zo mini da atamfofi masu tsada guda uuku da kayan jarirai. Amina ma turamen ta kawo mini da kayan jarirai Farida ita ma turminta huɗu da kayan jarirai sama da guda biyar, tun kafin goben ta yi gefen gadona ya fara cika da kaya sannan wasu ma hidiman su Munnira ke yi ba sa faɗa mini. Suma ita da Hauwa turame uku suka yi min da su pampers da kayan sanyi sannan sun ba da an yi mini yajin jego mai yawa mai daddawa.
Ina can cikin ɗaki ban sani ba Hauwa ta zo tana faɗa mini wai ashe sai da Anty Bahijja ta kira Musbahu tana tambayan shi ko Tafida ne ya ba da saƙo ya kawo? Shi kuma ya ce ni na tura masa kuɗi ba Yallaɓai ba ni tana faɗa minibsai da na bushe da dariya. Matar nan ba za ta bar ni na huta ba na yi alƙwarin in ta sake magana a gabana sai na mayar mata da martani ana cikin gida a na aiki su kuma suna zaunes sai ji da jiyarwa.
Bayan mangariba mai ɗinkin mu ya kawo mini sauran nawa da na yara sai na Farida da Amina. Ni na fita har haraban gida na karɓa muka yi maganar ƙarishen kuɗin ɗinki na dawo kenan falon Baby ta tare ni tana faɗin wai Anty Gimbiya ba ta zo da su Khalipa ba. Kayan ɗinkin da ke hannuna na miƙa ma Amina da ta zo ta tare ni da mgana na ce ta bari in zo.
Ina sanye da doguwar riga tsaraban makka ne cikin tsaraban Yallaɓai., rigar ba takai mini har ƙasa sosai ba tana da mayafinta shi ne ma jiki na, na yi kyau ɓulɓul da ni domin ga ruwan zafi daman sannan kuma na saka Aisha lame ta kawo mini mai da shower gel, kuma ina kula da jikina ina cin mai kyau ina shan mai kyau ni kaina na san na yi kyau da haihuwan Yumna sannan cikina ya fara komawa jikina ya yi cif sai na zama wata yar dumduma gwanin sha'awa kowa ya zo ya ganni sai ya ce mini na ƙara kyau da na haihu mene ne sirrin? Na ce Yallaɓai ne sirrina muna ta dariya.
A tsakiyar falon Yallaɓai na tsaya tun da nan suke zaune har da su Halima. Anty Maimuna ba ta zo ba itama Anty Bahijja gulma ne ya kawo ta. Yau ga shi Anty Bahijja na zaune amma bayan gaisuwa ba abin da ya ƙara haɗa su da Ma'u duniya juyi juyi. Gimbiya ta ƙura mini ido tana kallona ita kuma Naja da gayya take ce mini" Ka ga uwar gida a gidan Uncle Tafida"
Na yi mata fari ina faɗin" Faɗi ki ƙara Uwargida mai babban muƙami a wajen megida "
Sai ta yi shuru ai ba zan bari ta saƙa mini magana ba Gimbiya na kalla ina faɗin" Baby ta kawo min ƙaran ki."
Sai ta yi wani luu da ido kafin ta ce" Ni fa? Me ta ce miki na yi?
"Ta ce ba ki zo da Khalipa ba"
Anwar ma da za ta zo da shi ya na wajen Halima.
"Ayya ai Khalipa na Rano Anty Marliya da ta zo ya saka rigima sai ya bita sai kawai na ce su ta fi dashi."
Sai na jinjina kai kafin na ce" Amma ai da kin ce su zo da shi saboda suna ko?
Kawai karaf Halima ta saka bakinta.
"Don dai suna me ya sa zai dawo? Suna dai ba biki ba fisabilillahi."
"To nima shi na gani."
In ji Naja.
Anty Bahijja dai ba ta yi mgana ba, ni ko sai na juya ina kallon Halima kafin na ce" Aa. fa ba suna kawai ba wannan sunan ya sha bambam da sunan da kika saba zuwa ko gani Halima. Suna ne garurumin da baki taɓa ganin irin shi ba."
"Allah ko?
Ta faɗa cikin mamaki ni kuma sai na gyaɗa mata kai, muna cikin haka ne sai ga su baby da murna da akwati Laaila ta iso mutanen Abuja. Muka rumgume juna ina yi mata maraba ta gaggaisa da su Anty Bahijja. Yara wajen ɗaukan wata leda suka yagata kayan ciki ya zube kayan fulawa ne ta yo mini cincin da donot sai cake, ina ta faɗa sai ta ce ai namu ne ta zo mini da shi saboda gobe. Ta ce mini ma ta saka ƙanwarta ta yi mini meatpie gobe za ta kawo. Su Amina duk sun taho falon da suka ji tahowar Laila.
Munnira ta daddage ta rangaɗa guɗa Amina na ta ya ta. Ina ta dariyan farinciki na ce"Na gode Anty Laila."
"Ba komai an zama ɗaya. Kin ga yadda yayanki ya ruɗe. Ki yi ki gama aikin nan ki tafi kayan fulawan nan ma duk tare da shi muka shiga kasuwa muka siyo komai ina cewa ya bari na siya da kuɗina ya hana shi dai faɗi yake Sadiya ce ta haihu ta yi ma Mama takwara saboda haka muma za mu yi ma wannan haihuwan na ta kara."
A gaban su Anty Bahijja ta fiddo mini kayan suna. Atamfa biyu leshi ɗaya sai kayan jaririya guda bakwai bayan su pampers da mayuka da rigunan sanyi. Har su Aina sun ƙariso suna ta ɗaga kaya suna gani da farinciki. Amina ta ranguɗa guɗa tana faɗin" wannan yarinya ta ga gata. Ta shaida ita ɗin yar dangi ce gaba da baya."
"Tabbas yar dangi ce. Ya Hamza ya nuna bajintarsa ga Ya Auwal ma ya nuna na shi Ubangiji Allah ya bar zumumci."
Aka amsa da Amin gabaɗaya da gayya ba na ce" Kuma duk sun tura mini kuɗi duk da su na yi wasu hidiman."
Mu mun man ta da su Gimbiya a falon ma ballanta su ce da gayya mu ke yi sai da daga baya ne da muka haɗa ido da Gimbiyar sannan na ce bari nima na ɗan ɗana.
"Na daɗe da sanin ni yar dangi ce amma na ƙara ganin kara a haihuwan Rukayyatu. Na ga karamci a wajen ku yan uwana na gode. Alhajin mu ma buhun shinkafa cir shanshera ya ba ni saboda Rukayya"
Su Rahila har da kabbara
Ni kuma na cigaba da faɗin "Mijina ya yi mini dukkan gata na gode masa. Sannan ƙawayena da ku dangina gabaɗaya kun rufa mini asiri kuma ina mai gode maku uUbangiji ya ruɓanya muku."
Munnira da Amina sun fi kowa zaƙin murya wajen amsawa da Amin
Munnira har ta na faɗin wani abun ma sai gobe. Ta ba ni hannu muka tafa ni da ita. Gabaɗaya su Gimbiya sun gama muzanta Anty Bahijja ma ba san tafiyarta ba na ji daɗin haka saboda ta fahimci ba Yallaɓai kaɗai ya yi mini hidima ba, Gimbiyar ma sai wajen tara na dare suka fita tare da Naja da Halima sai bayan tafiyar su ne da muka zauna da Sameena nake jin wasu manganganu. Ni da ita ba mu taɓa zama mun yi maganar zama na da Gimbiya ba sai ranar. Kusan raba dare muka yi muna hira na faɗa mata wasu rigingimun da suka faru tsakanina da Gimbiya. Itama tana ba ni wasu labaran da ban san da su ba.
Ashe Gimbiya kishi take yi da ni da tana da iko da tuni ta koreni. A bakin Sameena nake jin ko maganar haihuwan ta ce Tafida sai rawam jiki yake yi a kaina kuɗin shi duk a kaina da yayana ya ke ƙarewa to daɗin abin ma dai ban yi irin haihuwanta ba mace na haifa. Haka ƙannenta suke ta faɗa da masu goya mata baya. Kuma wai a haihuwan nan da na yi sai da ta nemi ya ranta mata kuɗi ta biya kuɗin shipping, amma ya ce mata ba shi da kuɗi aamma ni ga shi nan ya ba ni kuɗi ina ta wadaƙa har suna na shirya mai kama da biki. Har cewa ta yi yadda Yallaɓai ke jin maganata ko Nene albarka.
Na yi dariya kafin na ce ma Sameena." Duk maganganun su Anty Bahijja a kaina ne itama ta ɗauka. Ni gaskiya na riƙe kuma shi ke riƙe da ni har gobe. Maganar hidimar suna kuma wallahi kayan abinci da kayan sawa kawai Yallaɓai ya yi mini. Sai sauran abin da ba a raasa ba. Maganar gaskiya nima na yi hidima da kuɗina sannan ku ma da muke tare kun yi mini amma ba kuɗin Yallaɓai ba ne balle hankalinsu ya tashi kar na karar da kuɗin ɗan'uwan su."
Sameena ta ce wallahi ita ta sani ita ko magana ta ji a kaina ba ta yarda. Lamarin Gimbiya ya daina ba ni mamaki tun da kishin take so a yi to za a yi. Sannan suna kuma za a yi sai dai ta mutu.
Ni Allah ya ji ƙaina da ban yi haƙuri a lokaci haihuwar Gimbiya ba, da tuni an buga mini tambari amma yau da na yi haƙuri ga shi komai ya wuce abin da Yallaɓai ya yi mata ko rabin shi bai yi mini a haihuwan Rukayya ba amma Na tsaya mata a ƙahon zuciya saboda kishi da baƙin ciki.
*Janafty**TKGB3I09*
RANAR SUNA.
Talata.
17,November. 2020.
A safiyar talata muka tashi da hidiman sunan Rukayyatu(Yumna). Da yake duka nan suka kwana tun asuba suka tashi da aikace aikace kafin ka ce kwabo an gama komai. Alele ne ma ƙarshen gamawa amma waina tun asuba suka fara suya tun da tun a daran jiya suka haɗa ƙullun wainar miya kuma da safen nan wuta kawai suka ta da mata tun jiya sun gama haɗa komai. Kafin azahar komai ya kammallah gida ya fes sannan duk mun yi wanka amma ba mu saka anko ba sai bayan ƙarfe biyu amma ni da yara da ba su je makaranta mun saka sabbin kaya muna walwali. Yunma ma tun safe a ka yi mata wanka a ka saka mata kyakyawan kayan jarirai masu kyau da safa da takalminta na yara mai kyau da hula cikin kayan da Yallaɓai ya ba ni kuɗi na siya mata ne.
Da safen nan ya zo ya gan mu har Amina ta matsa masa sai da ya tsaya muka yi hoto. Shima ya sha farar shadda har da babban riga har sai da na ce masa
" Yallabai hala kai ma walima za ka haɗa mana?
"A'a kawai na yi shigar fararen kaya ne domin nuna murnata a wannan ranar"
Abin da ya faɗa mini kenan na yi shuru kawai ina kallon shi ya yi kyau sosai. Sajen sa na shafo in da tsillin furfura suka fara fito masa, Yallaɓai fa yanzu shekarunsa wajen arba'in da takwas ne yana ƙoƙarin shiga gidan hamsin Allahu akbar jiya ba yau ba, ni ina ta kallon shi a matsayin ɗan saurayin da na aura ɗan shekaru ashirin da bakwai da takwas a duniya.
"Kallon fa Madam?
Shi kan shi ya gaji da kallon sa da nake yi sai da ya yi mini magana sai na yi mirmishi. Na isa gare shi na rumgume shi, shima sai ya kama ƙuguna ta baya yana faɗin" Wata Sadiya ta yi kewar Yusuf ɗin ta ko?
Ya faɗa yana sumbatar wuyana. Sai na noƙe ina ɗan mirmishi mun daɗe a haka muna shaƙan turaran juna sannan muka saki juna lokaci ɗaya muna masu kallon juna. Mun raja'a a kallon juna sai da shigowar Amina da kukan Yunma ya fargar da mu sannan muka saki juna na karɓeta na zauna gefen gado shima biyo ni ya yi shi ya zage min zip ɗin gaban riga ta na fito da nono ina ba ma Yunma. Yana zaune gefena muna hira yana faɗa mini Tariq da Kawu sun tura mai kuɗi wai ya ƙara na hidimar suna.
"Allah ya saka musu da alheri. To sai ka ƙara mini wani abu don Allah Yallaɓai."
Na faɗa har langwaɓe kaina sai ya wani kalle ni kafin ya ce" Da ga jin na ce an ba ni kuɗi sai ki ce na ba ki? Ke yanzu me ya rage ba ki yi ba ko ba ki siya ba?
"Yallaɓai ban ɗauko mai DJ da mai hoto ba fa"
Na ƙarishe faɗa cikin shagwaɓa har ina tura masa baki.
Yallaɓai sakin baki ya yi hakan bai ishe shi ba sai da ya riƙe haɓa yana faɗin" Kika ce me?
"Na ce DJ da mai hoto. Domin kasan Haihuwan Yumna na dabam ne za a sha shagali."
"To ni ba da ni ba."
"Acikin gida ne fa Yallaɓai ba matsala tun da duka taron na mata ne."
"Ba amince ba."
"Yallaɓai."
"Sadiya na ce ban amince ba ko?
Ya faɗa yana mai kallona a fuskarsa da maganarsa na fahimci ba wasa yake yi ba.
"To shike nan."
Na so na yi fushi ne amma sai na ga bai damu ba kawai ya miƙe yana saɓa babbar rigan shi. Duƙawa ya yi ya sumbaci goshin Yunma kafin ya dago nima ya sumbaci kumatuna lokaci ɗaya yana faɗin" Na tafi. Take care a yi suna lafiya."
Da dai na ga zai tafin sai na ce to ya taimaka mini da kuɗin zan kira ko mai hoton ne.
"Wani irin mai hoto kuma Sadiya? In hoto kike so ba ga wayoyi nan ba? Sai kin gaji da hotuna yau."
"Ni fa ba irin shi ba. Na camera nake so"
"Lalle."
Yallaɓai ya faɗa sannan ya cigaba da faɗin" Ni ba ni da kuɗi kin cika tsarabe tsarabe Sadiya. Suna ba dai a ci a sha ba ne? Kuma na tanadi abinci miye wani hoto? Hoton ma da a ka ce haramun ne?
Ni dai ai sai na kasa mgana ina ji ina gani Yallaɓai ya fice ya bar ni zaune bai ba ni ko sisi ba, to ya za a yi ya ba ni shi da ya ce hoto ma haramun ne. Dj dai tun da ya hana amma mai hoto kam zai zo daman mun yi magana da Samira class mate ɗina ita ce na taɓa zuwa sunan yaronta na ga an kira shi sai ta ce mini ƙanin mijinta ne. Na ɗauka zan samu wani abu a wajen Yallaɓai ne sai na ƙara tun da ban samu ba sai na ɗauka cikin kuɗina na tura mata rabi, anjuma da yamma zai zo, na samu kuɗi sosai ko Anty Zabba 20k ta tura mini ta ce ba yawa ni ko na ce mai yawan kenan, ina ta mata godiya. Har mai makeup na samu ita kuma ƙawar Anty Khaleesat ce tare suka yi makaranta ta yi mata mgana itama anjuma za ta zo ta yi mini kafin baƙi su fara suwa.
Kaf yan uwan Mama na gandun albasa sun taho mini suna. Kuma na ji daɗi sai na sauke su a ɗakin su Jidda. Falon Yallaɓai kuma na ce a bar ma dangin Yallaɓai saboda ba na son ƙananun mganganun falon su Jidda kuma yan gidanmu da sauran mutane ciki kuma ga bedroom ɗina na zauna ni da ƙawayena da mutanen arziƙi. An kawo sinasir da tsiren sannan tun jiya a ka haɗa da kunin aya suka ɗuɗɗura a gorinan suka saka sticker a fridge ma suka kwana ina ganin haka sai na kira su Ya Aina na ce su raba komai kashi uku, ɗaya namu ne da ƴan'uwan mu ɗaya kuma na yan uwan Yallaɓai ɗaya kuma ni da ƙawayena da yara tun da Baby ta ce mini yan ajin su za su zo Jidda dai na san hali ba gayya za ta yi ba.
Bayan na saka an diɓar ma su Gwaggo na ba da a ka kai musu sannan na saka Hauwa ta ɗibar ma Gwammaja suma suka aika da shi can wajen su Nene. Na saka suka ɗibar ma Yallaɓai na ce zam kira shi in yana office ne zan kira Musbahu da Adnan matan kuma na ce