Turken Gida Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   4 / 55

9K to 12K   out of 163.1K words

sun shiga ya ke tafiya mun gaisa da shi ya yi min barka da dawowa ni kuma na ce ya gaida iyalan na shi, na rufe gida muka dawo cikin gida ni da ƴaƴana.

"Baby ciwo kika yi? Na ga kin rame ne?

Na faɗa ina tattaɓa wuyan ta lokacin da muka dawo cikin gida.

"Ta yi zazzaɓi na kwana biyu a gidan Anty Gimbiya."

Jidda ta ba ni amsa sai na zauna saman kujera na jawo Baby ta zauna saman cinyata ina shafa fuskarta na ke faɗin.

"Ayya sorry My princess Umma ta tafi ta bar ki ko?

Sai Baby ta fara tura baki tana faɗin" Umma ni dai kar ki ƙara tafiya ba ki tafi da ni ba ina ta kuka Abba sai ya yi ta cewa za ki dawo ba ki dawo ba sai da aka daɗe."
Dariya na yi ina mai rumgumeta kafin na ce" Ba zan ƙara tafiya na bar My princess ba in sha Allahu "
Jin haka ya sa ta fara tsallen murna ita dai Jidda na zaune ta na mirmishi. Ranar ni na ta ya Baby cire kayan makaranta ta saka na gida Jidda ma ta sauya ta fito na zubo mana abinci a filet muka ci tare. Na sha labarai wajen Baby duk abin da ya faru da ba na nan sai da ta faɗa mini Jidda na gefe ta na cin abincinta tak ba ta ce ba, ashe ranar da na tafi ranar daga makaranta ya ce salisu ya kai su sharaɗa ba su ma kwana a gidan ba kenan.

Bayan mun gama Jidda ta tattara komai ta kai kitchen ta kuma share in da muka ɓata. An kira mangariba muka yi alwala muka yi salla a falo, muka yi azkar sannan na ce mun dade ba mu yi karatun Qur'ani su ɗauko mu yi karatu.  Ba mu muka tsagaita da karatun ba sai da a ka kira sallar isha'i sannan muka dakata muka yi salla, muna idarwa na ce su yi aikin makaranta ni kuma sai na shiga ciki na ɗauki wayata ina dubawa sai na ga Yallaɓai ya yi min saƙo.

"Ya yi kyau."

Abin da ya ce kenan a saƙon na shi ƙaramin tsaki na ja na danna delete saƙon ya goge daga wayata. Data na kunna ina ganin saƙonni nata shigo mini ma su tambaya hijabai ne daga yan makarantar mu ta BUK daman suna siya tun da duk na yi musu tallah. Na amsa na yi ta ba su da cewa cikin satin nan za a kawo tun da ina Kaduna ma mun yi mgana da mai ɗinkin Hijaban lissafi kawai za mu yi na tura masa kuɗin shi, sannan na fara tunanin yadda zan in ganta kasuwancina  shi ya sa a I.G na yi ta following ɗin masu ƙananun kasuwanci domin na ga yadda suke marketing ɗin kayan su sai na fahimci ina bukatar suna da ledan da zan rika saka ma kowa hijabin shi in ya siya shima duk inganta kasuwanci ne, sannan ina bukatar ɗinka hijaban in diffirent styles ma'ana kowani yanayin ɗinki ya kasance ana samu bambamci sosai da ganin abu unique a hijaban da na ke siyarwa sannan akwai bukatar na ƙara da wani abu. Ni kaɗai na zauna ina ta tunanin da me zan kara? Na fi son abin da ni kaɗai na ke siyarwa ba ko ba ma ni kaɗai ba to ya kasance bai yi yawa ba. Lamarin ya kai har littafi da biro na ɗauko na fara rubutu har takalma na saka da atamfofi amma sai na ji hankalina bai kwanta da su ba sai kawai na saka under wears irin su pant, bra, sikat gajerun wanduna da dogaye tare da sleeping drees sai na ji na fi karkata anan sai na fara tunanin sunan da zan saka a jikin logon kasuwancina daga jarshe da na ga na matsa ma kaina da yawa sai na ijiye zuwa da safe amma waya na hannuna ina ta shige-shige ina ganin sunayen da mata ke sanya ma kasuwancin su very interesting.

Ina cikin shige- shige na sai ga kiran Surayya Dee Bojuwa herbel, da na ga kiran ta sai da na ji kunya na daɗe ban nema ta ba daman ina shirin neman ta ne muka samu matsala da Yallaɓai.  Ta ce kwana biyu ba ta ji motsina ba  shi ya sa ta kira ta ji ko lafiya
Ina dariya na ce" Lafiya ƙalau wallahi kwanaki can ne na kwanta asibiti da yake na samu ɓari."
"Subhanallahi Sannu. Allah ya kawo wani mai albarka."
Na amsa mata da Amin sai ta fara min mganar tun da na yi ɓari ai ya kamata na yi gyara sai na ce mata zan yi in sha Allahu amma ba ni da kuɗi a hannu in na samu zan yi mata mgana.

"Haba Matar injiniya. Ni dake ai ba haka tsakanin mu kawai ki yi lissafin abin da kike so mai delivery da safe sai ya kawo miki"
Sai na kasa ce mata komai tabbas mun saba ko ba ni da kuɗi a hannu ta na ba ni kaya in na samu sai na tura mata. In na ce zan yi mata wani bayani ba za ta taɓa ganewa ba sai kawai na ce zan tura mata whatsApp abubuwan da nake so da haka muka yi sallama.
Sai na yi zuru ina tunani to gyaran me zan yi? Na gyara ma wanda ya gaji da ni! Ko na ce na fara tsufa na rage daɗi shi ya sa yanzu Yallaɓai ya daina marmarina. Na so na sha kayan lambu ne su kankana da rake da za su ɗan ta da min ni'ima saboda amfanin kaina ba domin shi ba, amma ban yi niyyar siyan wani mgani na sha ba shi ya sa ma na share Surayya kawai ban tura mata ba, na dai kira Aisha lame na ce ta aiko min da lotion sai shower gel saboda na wajena saura kaɗan ya ƙare mun rabu da ita kan cewa da safe zan san ya mata kuɗin.

Hankalina ya yi kan wayata shi ya sa ko shigowar motar Yallaɓai ban ji ba sannan ban ji maganar yaran ba, ina kwance ruf da ciki a saman gado ya shigo ɗakin ba domin ban san shigowarsa gidan da ba da a ce na sani da ba zan taɓa ɗaga idanuwana na kalle shi ba amma tun da cikin rashin sani ne ina ɗagowa muka haɗa ido huɗu da shi, da sauri na mai da kaina kan wayata. Saboda sai da na gan shi sai na ji wani irin ƙunci na mamaye min zuciya. Na so na daure ma zuciyata ko sannu da zuwa na yi masa amma na kasa shi ya sa na yi kamar ban san da shigowarsa ɗakin ba shima ina ga ya na jiran ne na fara yi masa mgana shi ya sa har ya ijiye ƙaramar jakar hannunsa saman side drower ɗin gadon tare da agogon fatan da ya cire daga hannun shi ya fita bai ce min sannu ba nima ban ce masa ba ina kwance in da nake  ya dawo ya tuɓe kayan jikinsa daga shi sai gajerun wando ya koma tiolet duk ina kallon shi ta wutsiyar ido sannan na raka shi da hararan da bai san ina yi ba har kuma ya yi wankan shi ya fto ban ta shi ba, ya shafa mai sannan ya saka saukaƙkun kayan zaman gida ya fita can wajen su Jidda. Ni kuma na daɗe kan wayata sai wajen goma da rabi na kashe data nima na miƙe na faɗa tiolet na kama ruwa, sannan na zo na saka kayan barci na shafa ma wuyana da hannuna humra sannan na kwanta har ina kashe wutar bedroom ɗin kuma cikin ikon Allah barci ya ɗauke ni ban ta shi ba sai huɗu da rabi na asuba, na je na kama ruwa na yo alwala na zo na shimfiɗa sallaya na ta da salla, ina kan darduman Yallaɓai ya tashi lokacin an fara kiran sallar farko ni kuma na gama nafilfiluna ina ta jan casbaha ko kallo bai isheni ba kamar yadda shima bai nuna ma ya san ina gidan ba.

Ina idar da sallar asuba na tafi ɗakin su Jidda muka yi azkar da karatu bayan mun gama muka shiga kitchen ni da Jidda muka yi abin karyawa. Kuni na ji ina son sha tun jiya daman na jika geron sai na wanke na niƙa shi a blander Jidda kuma wanke wake shima na niƙa shi a blander, ni na dama kunin da tsamiya Jidda kuma ta fara tuyan ƙosan daga baya na karɓa na ce ta je ta shirya kar ta makara. Ni da ƴaƴana muka karya lokaci na yi Salisu ya zo ɗaukan su suka wuce ni ko daman na ci na ƙoshi sai na kishigiɗa a kan kujeran falon su Jidda tibin a kunne sai na ɗauki remot na sauya tasha zuwa arewa24 suna maimacin shirin daɗin kowa. Ina nan zaune ina kallo sai na ji motsin fitowar Yallaɓai ta wutsiyar ido na kalle shi, ya fito daga shi sai dogon wando da farar singlet Yallaɓai har wani kiba ya narka to in ba idona ƙarya ya yi min ba har da timbi ya fara ijiyewa ya samu duniya. Yau ɗin ma na so na daure na gaishe shi amma sai na ka sa ma na ƙara sautin talabijin ɗin a zuwan ko ya yi mini magana ma ba zan ji sa ba.

Ina zaune nan ya zo ya wuce ni zuwa kitchen ai ban gama mamaki ba sai ga shi ya fito da Mug cike da kunu sai filet shaƙe da ƙosai, daman ni ban shirya masa na sa a saman dining ba, a kitchen na bar komai shi ne ya shiga ya gani ya nema ma kansa mafita. Baki na saki ina kallon shi ya zo ya zauna saman kujeran dake fuskanta ta, har ya na haɗe kafafunwabaa ya kuma jawo center table ɗin da ke tsakiyar falon zuwa gaban shi ya ijiye mug ɗin kunun da filet ɗin da ya shaƙo kosan a ciki.
Remot na gefe na ya ta so ya zo ya ɗauka, ya sauya ta sha zuwa MbcAction. Ina ga ya so na yi magana ne sai kuma ya ga na mike tsam na wuce ciki na bar sa anan. Ban san yadda ya ƙare ba ina shiga ciki na kwanta sai barci tashi kawai na yi na ga bashi a gidan ya fita a raina na ce ɗan renin wayau ranar da yamma Salisu ya kawo min cefane shi na ba ma kuɗi ya je ya siyo mini kayan marmari na yi fruit salat na sha sannan na faɗa masa da safe direba zai kira shi za a kawo min hijabai daga Zariya zai karɓo daman tun da Musbahu ya yi aure sai na koma Salisu ke karɓan kayan a tasha.

Haka muka yi ta zaman doya da manja tsakanina da Yallaɓai in ya na gidana. In kuma ya na gidan Gimbiya ya kan zo duba mu da daddare. Har kuma ya gama zaman shi ya tafi ko ma ya ganni ba ma mgana. Ya san halina sarai na iya gaba shi kuma ina ga jirana yake na je na bashi haƙuri tun da ni na yi masa ba dai-dai ba ni kuma a raina na ce wallahi ya yi kaɗan ina yin abinci na ijiye masa na shi saman dining kuma ba kunya yake zama ya narka ma cikin sa. Na san har Jidda ta fahimci tsakanina da Abban na su ba zaman lafiya domin tun tasowarta ba haka ta ga muna gudanar da rayuwar mu ba, shi ya sa ta tsiri in ya shigo gidan ta biyo ni ɗaki ta na faɗa mini ga Abba ni kuma sai na ce ta je ga ni nan zuwa kuma haka zan yi ƙeme ƙeme na ƙi fita sai dai su in yana son wani abu ya ce su yi masa tun yarinyar bata fahimta ba har na fara fahimtar ba jituwa a tsakaninmu yanzu. Ranar da yana gidan Gimbiya ya zo mana sallama da daddare ina ɗaki ina rubuta waɗanda suka karɓi hijabai ba su ba ni kuɗi ta shigo tana faɗa mini ga Abba ya zo ya na falo.

Sai da na yi mata wani kallo sannan na ce" Ke in kika ƙara zuwa min ikina wani iyayin ga Abba ya zo sai na yi fata fata dake wallahi."
Sai Jidda ta kasa mgana ta tsaya ta na kallona kafin ta ce" Amma Umm."
"Fita ki ba ni waje. Shi bai san in da nake ba ne? Ko sai kin zo kina damuna? Ki sake dawo ki gani in ban yi miki bugun tsiya ba."
Ai Jidda da sauri ta fice tana mai rufomin ƙofa na bi ta da ƙwafa ina faɗin" Ka ji min munasiran yarinya."
Sai da yi kyafci sannan na cigaba da rubutuna amma a kasan raina ina jin zafi shi ai ya san in da nake, tun da bai neme ni ba ni kuma me ya sa zan nuna na san da zuwan shi?
Jira ya ke yi har yanzu na zo ina bashi haƙuri lalle ko bai san taurin kaina ba ne shi ya sa. Wallahi ba zan ba shi haƙuri ba, domin ni ban ga laifin da na yi masa ba. Sai ma shi ne ya yi min laifi da yake buƙatar ya ba ni haƙuri amma ya yi fuska yana jiran ne na fara ba shi haƙuri ai ko sai da ya bushe.

Da safe Amina ta kirani bayan mun gaisa tana mini tambayar banza wai na faɗa ma Yallaɓai na yi ɓari kuwa?
Ƙaramin tsaki na ja kafin na ce" Ban faɗa masa ba. Wani abu ne?
"Kai Ya Sadiya ai kamata ya sani ko?
"To ke sai ki faɗa masa tun da ya kamata ya sani ɗin"
Sai ta fara dariya ƙasa ƙasa ta na faɗin Allah ya ba ni haƙuri sai na fara masifa ina faɗin.
"Ai bai nemi ya sani ba, tun da na dawo ba ya mini mgana bai ma san ina rayuwa ba sai ni ce zan bishi ina faɗa masa na yi ɓari? A she ma yana gaba na kenan"

Sai Amina ta kashe wayarta ta bar ni ina ta masifa ni kaɗai. Haushin kowa na ke ji yanzu ina shiri zan je Ɗorayi, saboda Balaraba ta kirani kan zuwa Jigawa gobe sunan Saude daman na ce zan je, da safen ba a gidana ya kwana ba saƙo na tura masa kuma har na gama shirina na fita bai dawo mini da amsa ba. Sai da na fara biyawa gida na gaida Gwaggo Alhaji ba ya nan ya tafi Yashe duba gonakinsa. An kusa fara noma damina ta fara mana sallama na ɗan jima a gidan sannan na shiga gidan su Saude. Ma su zuwa sunan ƙannenta ne guda biyu sai ƙannen Saude da maƙota haka gobe za mu tafi sai jibi mu dawo tare da Sauden gabaɗaya tun da mijin ya amince ta dawo gida ta yi jegon ta.  Sai azahar na baro ɗorayi bayan na yi salla a gida shagon Amesty na biya na yi tsifa sannan na yi Saloon yau ma sai da ta yi mini mganar ya mganar buɗe shagona na ce mata ya na nan soon in sha Allahu.

Ban ji a raina zan haƙura da burina ba so kawai nake yi na tsaya da kafafuna amma sai na cika burina na buɗe shagon saloon in sha Allahu. Daga nan na dawo gida sai ma da na dawo gida ne na duba wayata na ga saƙon Yallaɓai na adawo lafiya a raina na ce aikin ɓur in ji tusa, na fara shirin tafiya jigawa suna. Daman tuni na siya Atamfa wajen Dija collection da pampers tare da rigan yaro sai na haɗa mata da setin mayukan jarirai, ina da ƴan kuɗaɗena da su na yi amfani da daddare daman Yallaɓai zai dawo gidana shi ya sa sai da na bari ya shigo gidan yana falo tare da su Jidda sai na fito na kira Jidda ta na zuwa na ce ta je ta faɗa ma Babanta gobe zan je Jigawa Saude ta haihu. Na ga ta tsaya ta na kallona amma yadda na haɗe rai ne ya sa ba ta samu damar mgana ba ta wuce ta koma falon ni kuma na koma bedroom na zauna ina jiran ta.

Can ba daɗewa sai ga shi ta dawo da kuɗi a hannunta sabbi yan dubu ta miƙa mini tana na faɗin" Abba ya ce Allah ya kiyaye hanya."
Ban karɓa ba na bi kuɗin da kallo kafin na ce" Wannan kuɗin fa?
"Shi ya ce na ba ki."
Karɓa na yi na kirga 10k ne cif kamar wata almajira ai ko siyayyan da na yi ma Saude ta fi karfin 10k ballanta a zo maganar kuɗin mota.

Mai da ma Jidda kuɗin na yi sai ta ƙi karɓa ta tsaya tana kallona.
"Ki mayar masa. Na gode."
Kuma yarinya sai ta ƙi karɓa wani kallo na yi mata kafin na ce" Ki karɓa mana."
Sai ta noƙe hannu tana faɗin" Umma kar ki yi haka"
Bai kamata Abba ya ba ki kuɗi kuma ki ce ba za ki karɓa ba."
Baki na saki kawai ina kallon Jidda. Wai ta na faɗa mini abin da ya kamace ni.

"Kuma Umma ni dai ba zan iya mayar masa ba sai dai ki mayar masa da kan ki"

Kafin ta rufe baki na watsa mata kuɗin a fusace na miƙe ina faɗin" Ke da kuɗin kar ki bari na buɗe idanuwana na gan ku a ɗakin nan. Ki kwashe su salim alim ki fice ki ba ni waje Jidda."
Amma sai ta tsaya za ta mini mgana ai ko na da ka mata tsawa ina faɗin.
"Ki fita na ce ko?
Sai ta duka ta tattara kudin ta fice cikin san yi jiki na dafe kaina ina tsaki, Jidda ma laifina ta ke gani, uban ta na yi min wulakanci tana ƙoƙarin kare masa saboda ba ta da tunani sakarya ce. Ni kaɗai a ɗaki ina ta masifa sai ma na tattara kayana da duk abin da zan buƙata na kai ɗayan ɗakin na can na kwana da asuba ma kuma mun haɗu na fito daga cikin ɗakin shi kuma ya fito daga tiolet muka kusa cin karo, ya yi

4 / 55