faso gari na dai na garari a cikin Adaidaita sahu."
"Yaushe ne kike garari a cikin adaidaita sahu Sadiya?
"Ba na yi ne?
Na juya a fusace ina tambayarsa.
"Fisabillahi fa Sadiya"
Gani na yi magana da shi ma ƙara ɓata minu rai yake yi ya sa kawai na tashi na sauya kujeran zama na bar shi yana mini dariya. Tunani nake yi wata ƙila shi da matarsa sun shirya ne can kwanaki bai ko zencen ta in ma zencen ya zama dole sunanta ya ke kira kai tsaye. Yau ko tun da ya kira ta da sunan da ya ke kiran ta dashi na san sun shirya. Saurin kauda tunanin na yi ina mai faɗin miji da mata sai Allah tuni zai lallasheta su shirya har yana wani ɗaukan hoton mota ya na nuna mini saboda iyayi.
Ina ta hararan shi ta gefen ido lokacin yana amsa waya ne. Bayan ya gama kawai sai ya ɗau remot ya chanza tasha. Daga MBCBOLLYWOOD suna haska wani indian film mai suna Khabi kushi kabhi gham. Tsohon film ne mun kalle shi tun muna da ɗan wayau ina son film ɗin kawai ina cikin kallo Yallaɓai ya sauya mini tasha ya kai can wani tashar turawa a na rawa.
"Haba Yallaɓai ya za ka sauya mini tasha?
Na faɗa a ƙufule sai kawai ya kalle ni bai yi magana ba ni kuma na mike a fusace na je na karɓe romot ɗin hannun shi na mayar tashar da nake sannan na koma na zauna ina girgiza ƙafafuwana saboda yadda na ke jin ɓacin raina nw hauhawa.
"Allah ya ba ki haƙuri ban san kallo kike yi ba."
"Kallo na ke yi mana. Ko da ka shigo ba shi ka iske ni ina yi ba?
Na faɗa ina mai ƙure sa da ido fahintar da ya yi a fusace nake da shi ya sa koma ya jingina a jikin kushin ɗin kujeran ya na mai dannne dariyan shi.
"To miye abin faɗa anan? Na ce ki yi haƙuri ban sani ba ne?
Ɗauke kai na yi na mai da hankalina wajen kallon. Shi kuma ina ganin shi yana ta dariya ƙasa ƙasa.
"Na gode Yallaɓai na zama abin dariya a wajen ka "
"Kai na shiga uku. Wai dariyan ma ba zan yi ba?
"E in dai a gaba na ne to zan ce ni kake yi ma dariya?
Na ƙarishe faɗa ina zaro masa ido sai kawai ya koma ya kwanta a saman kujeran har yana miƙe kafa kafin ya ce" Ke dai ke ce yanzu kin koma rigimmaniya abu kaɗan sai ki yi zuciya ki hau faɗa. Allah ya baki haƙuri ni kin ga ma barci na ke ji"
"Ka je ɗaki mana. Nan ai ba wajen barci ba ne"
"Ni da gidana sai an zaɓa mini in da zan kwanta?
Ina ƙoƙarin mgana ya yi saurin dakatar da ni yana daga kwancen bai taso ba ya ce.
"Ki ƙyale ni na yi barci Sadiya. Ba zan iya da rigimar ki ba."
Jin haka ya sa na yi shuru ban ƙara masa mgana ba. Zuwa can sai na ga kamar da gasken barcin ne ke fizgan sa, sai na rage ƙaran talabijin ɗin domin kamar ya dame shi. Daga baya ma da na ya fara barcin hani'an sai na kashe kallon a nan falo na koma falon su Jidda na kunna na cigaba. Har ta gama soya dankalin mu ka ci ni da ita. Baby na ɗakin su daga wasa ta bingire da barci sai la'asar na saka Jidda ta tashe su. Yallaɓai ma sai da na tashe shi sannan ya iya tashi da gaske yake yi yana da gajiya a jikinsa. Duk sai ya ba ni tausayi yana da ƙoƙari sannan ni kaina zan iya ba da shaidar mijina jajirtattace ne. Sai na ce masa ya bari da daddare ya sake wanka da ruwan zafi na ƙara shafe masa jikinsa da man zafi in sha Allahu zuwa gobe ƙasusuwan na shi da suka rirriƙe za su sake shi ya ce da ko ya yi ta saka mini albarka.
Haka ko na yi masa zuwa washe gari tun asuba da muka tashi salla ya ce minI ya ji daɗin jikinsa. Ni kuma sai na mayar masa da martanin ya riƙa siyan man zafi ko ya na can gidan Gimbiya ne in ya ji kasusuwansa sun riƙe sai ya gasa jikinsa ta shafa masa. Nan ta ke ya ce ai tun da ya ji daɗin sa shi zai riƙa siya.
Haka rayuwar dai ta cigaba da gangarawa yau a ji daɗi gobe a damu akasin sa. Gefe ɗaya ina cigaba da renon cikina da ya yi wani irin girma na ban mamaki ni ma ya mai da ni wata ƙatuwa. Shi ya sa ba na son fita sai ya zama dole. Daga asibiti sai gida ko Ɗorayi na daɗe ban je ba. Tun wani zuwa da na yi daga asibiti na biya na gai da su Gwaggo ban koma ba amma dai ina mgana da su Ya Aina ta waya muna gaisawa.
Siyayya kayan haihuwa kuɗi Yallaɓai ya ba ni muka je kasuwa ni da Jidda muka siyo komai da komai sai abin da ba a rasa ba. Da ya ke tun scan ɗin da na yi ya nuna mace zan haifa kuma ko Yallaɓai ban faɗa mawa ba. A raina na ji ko da macen na samu tabbas zan yi ma Allah godiya. Tun da ya yi min ni',ima a farko a yanzu ma ya sake zaɓo ni cikin dubu ya sake ba ni wannan ni'imar. Itama Jidda zencen ta kenan Umma ki hai fa mana baby mai kyau mu yi ta renon ta ni da Baby. Itama Babyn macen ta ke so Yallaɓai kuma daman bai da zaɓi duk abin da na haifa ya na maraba dashi.
Cikina na shiga wata na bakwai sai ya fara yin ƙasa. Mutane da dama sai su yi ta cewa namiji zan haifa saboda yanayin girma cikin. Ni kaina ina mamakin girman shi, ban taɓa yin ciki mai girman shi ba, ko na Jidda da ya ke na farko ne, jikina ya bi gwara ma na Baby ya ɗan yi girma. Amma shi wannan girman shi na dabam ne. Ban taɓa saka ma zuciyata ina son sai na haifi namiji ba. Abin da nake addu'a a duka khamsul salawati ɗina shi ne Allah ya sauke ni lafiya. Jinsin namiji ko macen duk wanda Allah ya ba ni, ni mai gode ma ni'imarsa ne.
Kuma ni ban taɓa lura da cikin nan muni ya saka ni ba. Ban cika kallon madubi ba ta kaina na ke yi. Sai da za mu je gai da Mimisco ta yi fama da zazzabi ni da Yallaɓai da yara. Su sun rigani fita ni kuma na tsaya ɗauko makullin gida da hijabina har ƙasa na tsaya rufe gida tuni na ce ma Yallaɓai ya samo mana megadi ya ƙi. Wai a wannan a kurkin gidan ne sai ya wani saka megadi? Na bari in ya gina wancan babban gida sai ya ɗauki megadi amma ba a nan ba.
Na fara takawa sannu a hankali zuwa wajen mota. Sai da na ƙariso na ji Yallaɓai na dariya shi da ƴa'ƴan shi. Ban ɗauka da ni suke ba na ɗauka labari ya ke ba su na abin dariya shi ya sa ban damu ba na buɗe mota da ƙyar na shiga na zauna a bangaren mai zaman banza na gidan gaba sai da na gyara zama sannan na ce.
"Na ce motar na kama da za a hau foo ka ji haushina Yallaɓai. Yanzu don Allah ga irin mu masu lalura ai sai yaro ya jirgice a ciki saboda wannan motar ta ka."
Sai na ji sun ƙara kwashe minI da dariya har da Jidda da nake gani saliha ba ruwanta. Sai na waiwaya ina kallon su nima ina ta ya su dariyan. A tunanina maganar da na yi ta saka su dariya ashe ni ce suke yi ma dariya kamar sun samu cortoon.
"Yallaɓai."
Na kira sunan shi cikin mamaki ganin yadda yake dariya har ya na kwantar da kan shi saman sitiyari. Na fara zargin da ni yake saboda na ga sai ya kalle ni sai ya ƙara tsintsirewa da dariya.
"Me kika gani?
Ya faɗa ya na kuma cigaba da dariyan. Sai na ɗan tsume kawai na juya ina kallon gefen window ni kam ai na daina biye ma Yallaɓai tun da ya ce mini wai nishaɗi na ke bashi. Haka kurum zai ta sa ni yana mini dariya ko ya yi ta ja na da mgana ko faɗa sai na fara masifa sai ya koma gefe yana mini dariya. Tun da na fahimci mahaukaciya ya ke son mai da ni na fita sha'anin sa. In ya na dariyan shi ba na bi ta kansa.
"Wai uban wa kuke yi ma dariya?
Na faɗa cikin ƙufula. Ganin har su Jidda ban daina jin tashin dariyan su ƙasa ƙasa ba.
Sai suka yi tsit kamar ruwa ya ci su. Yallaɓai kuma ba ni da yadda zan yi dashi shi ya sa na kallon shi a ɗage sannan na ɗauke kaina sama ina hura hanci.
"Me suka yi miki? Ba su suka kai zomon ba."
"To dariyan me kuke yi? Haka kurum ku ta sani kuna yi mini dariya?
Na faɗa har ina yarfa hannu. Zaune kawai na yi ina kallon Yallaɓai na kallona ya na cigaba da dariyan sa. Tuni na harzuƙa na cika saura kiris na fashe.
"Me ye abin dariya a jikina?
Na faɗa ina kallon shi ganin da ya yi a fusace na yi maganar ya san yanzu nan zan birkice musu. Ya kuma san halina ba ni da sauƙi.
"Wai. Sannu Hajiya Dubu."
Ya faɗa ya na kallona har ya na ƙwarewa saboda dariya. A raina na ce Allah ya ƙara. Saboda ai dariyan ta mugunta ce.
"Ban taɓa tunanin sunan da Alhaji ke kiran ki dashi ya dace da ke ba sai yau."
Sai kawai na koma ina bin kaina da kallo. Rarrashin kaina na ke kar na kai ma Yallaɓai duka. Sunan nan ban da Alhajinmu da Gwaggo na haramta ma kowa ya kira ni da sunan nan saboda ba na so. In wanda na ke jin kunya ne ba na mgana amma in har ba na jin kunyar nan ta ke zan maka in karin da cewa ni ba sunana Dubu ba. Yallaɓai bai cika tsokana da sunan ba sabo da ya san yadda na fi tsanar sunan gwara ma a kira ni da Sadiya ƴar laushi. Amma yau
Saboda cin mutumci yana kirana da shi a gaban ƴa'ƴa na bayan ya tara su suna yi mini dariya.
Da dai na fahimci yadda ciki ya mai da ni suke yi ma dariya sai ban ƙara magana ba. Ya gama dariyan shi ya na tsokanata da mgana na yi masa banza. Su jidda kan sun yi tsit sun san halina wallahi yarinya ta ƙara mgana sai na yi mata bugun tsiya. Tun da uban su ba zai dakun mini ba to ai su ni na haife su zan yi iya hawa ruwan cikin yarinya na yi mata lilis ba mai ce mini me ya sa? Baby ta fi shan dukana domin da cikin nan ban san a dadin dundu da rankwashi nawa ta sha ba. Ita Jidda ba ta cika laifi ba ina son yarinyar ta na da gudun zuciyar iyayenta.
Bar muka isa gidan Mimisco a tsume nake. Ita kanta sai da ta yi maganar ta ga raina a ɓace me aka yi mini. Cikin jin haushi na ce" Wai Yallaɓai ke mini dariya saboda ciki ya sa duk na zama cus. Har yana tara su Jidda suna kallona suna mini dariya.
Tsabar yadda abin ya tsaya min a rai sai da na ji hawaye sun kawo minI. Ita ko da yake ta san irin yanayin nan da nan ta fara masa faɗa.
"Kai shike nan haka ake yi? Sai ka yi ta mata dariya? Waye silan da ta koma haka in ba kai ba? Ka daina tun da ta ce ba ta so don Allah Tafida ka daina. Ka san yanayin masu ciki sai a hankali in suka ce ba su so abu gwara a bar shi zai fi alheri."
"To na bari shi kenan?
Ya faɗa ya na kallona kuma ya na ƙara mini dariyan yadda zuciyata ta kawo a lokacin duk da a gaban yayarsa ne sai da na shammace sa na kai masa bugu a gadon bayan sa lokaci ɗaya kuma na fashe da kuka domin ji na yi in ban yi kuka ba kamar zan mutu saboda haushi.
"Kin gan ta ko Mimisco? To kuma ta dake ni, ni ban yi kuka ba sai ita?
"Tashi ka fita ka ba mu wuri."
Da haka ta fattake shi,ya fita can falon mijinta ni kuma sai ta koma ta ba ni haƙuri.
"Ki yi haƙuri Sadiya. Kin ji ko?
"Mimisco na gaji da abin da Yallaɓai ya ke yi mini a cikin gidan nan. Abu kaɗan sai ya ta sa ni a gaba ya na mini dariya."
Na gama faɗa bilhaƙki da gaskiya ina sharen ƙwalla sai ta taso ta zo gefena ta zauna ta na bubbuga bayana alamun lallashi.
"Ƙyale shi. Tsokanar ki yake yi kuma jin daɗi yake yi fa. Ki daina biye masa kin ji ko?
Ina sharan ƙwalla na ce" Da man nima ai ba na biye masa "
Ita ta yi ta lallashina ta ba ni haƙuri, mun yi awa ɗaya da wani abu sannan muka yi shirin tafiya ita da megidanta da yara suka rakomu har bakin mota suna ɗaga mana hannu
"Allah ya huci zuciyar gimbiyar Tafida."
Ya faɗa bayan mun fara tafiya. Ganin na yi masa fuska ina hura hanci ba annuri a fuskata kwata kwata. Kaina na mai da barayin window ina kallon giftawan motoci na yi kamar ban ji sa ba sai ya ƙyale ni ya koma suna mgana da Jidda kan mganar buɗe gari sai na karkata kunnina ina jin su.
"Cutar ta fara sauƙi. Tun da an nemi kariya ina tunanin ba zai wuce wata biyu ba za a buɗe gari ku koma makaranta."
"Allah ya sa Abba. Amma har na gaji da zaman gida. Da yanzu ina level 1 fa Abba."
Ta faɗa cikin ƴar shagwaɓa. Sai Yallaɓai ya yi dariya kafin ya ce" Allah ya tsara Nene ta. Kar ki damu za ki shiga makaranta a shekara mai zuwa in sha Allahu."
Ina jin su amma tun da ina jin haushin shi ban nuna ma na ji ba. Ban yi wani murna ba da na kalli cikina sai ƙarsashina ya ragu ina zan je da wannan cikin? In ma na haihu ba hutu ba ne har sai na yi yaye. Wataƙila Yallaɓai ya yi ta addu'a ne shi ya sa ba ni da rabon komawa makaranta.
Muna cikin motar kafin mu kai gida na ji Baby na tambayan shi ina su Khalipa sai a lokacin Gimbiyar ta faɗo mini a rai. Kwana biyu ba mu haɗu ba sai na ji ya na cewa ba sa gari sun tafi Rano da yara jiya. Har Jidda ke faɗin yaushe za a saka Khalipa a makaranta? Ya ce da zaran an buɗe makarantu.
Har muka kai gida ina tunanin wani abu. Tuni Gimbiya ta janye ƴaƴanta daga zuwa gidana. Wato na gama cin wahala da su musamman ma Khalipa shi ne yanzu za ta nuna min ita ƴaƴanta ne. Shi kan shi Yallaɓai ya daina tarkato mun su. Wata ƙila ta nuna ba ta so ne sai ya bar ta da ƴaƴanta haka nake tunani. Su Jidda ma ta daina neman su nima ba na cewa su je gidanta. Gwara Baby ma da Jidda. Ita ba ta son zuwa ma kwata kwata. Yallabai ma ba ya matsa musu abin da na fahimta kowa ya zauna in da yake kawai. Kuma Gimbiya yadda take kishi da ni ina da tabbacin ni da ta aure mini miji bana yi da ita. Ta so ni ta riƙa juya ni ta ba ni umarni ta zama ita ke tafiyar da rayuwar Yallaɓai gabaɗaya sai kuma ba ta samu wannan damar ba. Baƙin cikinta Yallaɓai ya nuna ina da daraja. Sai ta ke ganin ya fi sona a kanta nima kuma ina ganin ya na son ta. Daga baya sai na fahimci maza in suna da mace fiye da ɗaya to zargin an fi wata a kaina ba zai bar zukatan mu. Duk yadda ya so ya yi adalci sai wata ta ce ya cuceta. Haka rayuwar namiji mai mace fiye da ɗaya yake.
Ni dai na riƙe maganar da Alhajin mu ya yi mini na zama da ita da zuciya ɗaya. Ruwan ta ne ta zauna da ni da wani manufa ni dai na riƙe Allah kuma shi ne ke yi mini jagoranci a duka lamurana.
Har muka koma gida ina cin mgani ina ta hura hanci. Ban ɗauka zan haƙura da wuri ba sai gashi a daran ya lallasheni na haƙura amma da sharaɗin ba zai ƙara mini dariya ba in ya ƙara duk matakin da na ɗauka ya amince. Sai ya fara cewa zan hana shi dariya ne? Na ce ba zan hana shi ba amma in dai a kaina ne na haramta masa. Da ya ga na tubure sai ya amince tun daga lokacin na samu lafiyan shi in ma zai yi dariyan to a bayan idanuwana yake yi. Tun kuma daga lokacin nake kallon kaina a madubi ina ganin duk na yi baƙi na lalace na yi muni. Sai na daina ganin laifin Yallaɓai in ya yi mini dariya. Tabbas halitta ta jirkice. Komai na fuskata ya yi girma ni kaina ina na ga hancina a madubi na shafa na ji ya buɗe fafa sai na yi ma kaina dariya. Ina ciki mai sauya halitta amma fa shi wannan cikin komai na shi wani sabon salon ya zo da shi.
****
*September*
A ƙarshen watan september lokacin cikina ya shiga wata na takwas kenan. Muka yi wayi gari a safiyar talata da rasuwar yaron Ya Abubakar na farko mai sunan Ya Hamza. Ciwon ciki daga dare zuwa safe, sun ɗauko shi da asuba zuwa asibiti suna hanya ma ya rasu. Yaro ne ɗan shekaru goma sa'an Baby ne ta ma ɗan girme shi da kaɗan.
Ya Aina ta kira ni ta faɗa mini ƙarfe shidda na safe ta ce na zo gida a nan za a yi masa