Jidda na ci gare ta kamar mahaifinta in suka saka kansu a abu agaba sai sun ga sun cin ma nasara.
Ranar kawai Yallaɓai ya ce mu shirya da ni da yara gabaɗaya har da Gimbiya mu je mu ga ma'aikata sannan mu ƙarisa mu ga filin da ya siya tuntuni wanda zai gina ma gida da zai haɗe mu gabaɗaya. Ranar lahadi ne kuma ba a gidana yake ba yana gidan Gimbiya ne. Jidda ma ya hana ta zuwa lesson ɗin ta da ake yi musu a makaranta saboda fitan da za mu yi, mun cakaree gabaɗayan mu har Yumna na yi mata gayu, shi muka rika jira tun da yana can gidan ne sai ya kwaso su sai ya zo mu wuce ta gidana.
Sai da suka ɓata mana lokaci sannan suka zo. Gimbiya an ci gayu abaya ta saka ta yane mayafin a saman kanta ta saka wani takalmi mai rufi har da uban gilashi su Khalipa ma sun ci gayu cikin riga da wando yan kanti. Ni daman doguwar rigar atamfa na saka ɗinkin kaftan na saka mayafi kalan kayan sai na saka takalmina baki mai saukakken tudu. Jidda ma haka ita dai Baby pakistan ne riga da wando a jikinta da breziya Hijab. Tana kuma riƙe da Yumna ni ce ke ɗauke da jaka da na sako mata ruwa da ƙyallen goge tumbulunta tun da tumbuli take yi shi ya sa take yi kiba kamar ana hurata.
Mun gaisa sama sama da ta so ta shige gidan gaba ne sai kuma ta fasa ta shiga baya da yara. Ni ko ba ta san mota ba ta dame ni ba, mijin ma gabaɗaya na raba shi ballantana wata motar banza. Muna tafe ni da shi muna hira shi ne ma yake sako ta a cikin maganarmu shima ɗin a daƙune take amsa mishi ban san me aka yi mata ba, ko Yumna ba ta ɗauka ba nima ban tura mata ba. Na fahimci bata kaunar fita ta haɗamu ni da mijina ta aure mini shi, ni ban yi kishi ba sai ita? Mamaki
take ba ni in dai fita ta haɗamu gabaɗaya ta riƙa cin mgani kenan. Ni ba na ta ita in muka gaisa ban ƙara jan ta da magana sai dai in har ita ce ta sake yi minI magana. Ina da aji ba zan zauna ina bin kishiya ba. Har muka isa hira muke yi da Yallaɓai yana faɗa mini yanzu ƙasa za su fara amfani da shi sama sai zuwa gaba. Wancan kuma wajen tun da ya siye shi tuntuni yanzu yana matsayin mallakin shi ne. Zai ba da hayan saman ƙasan kuma yana tunanin abin da zai saka a wajen.
"Yallaɓai to ka buɗe shagon sai da kayan gine gine mana "
Yana tuki ne amma sai da ya juyo yana kallona.
"E mana. Na ga kai ma in ka buɗe amfaninka ne tun da in kwangila ta samu suma kayan ginin siyansu kake yi."
Sai ya jinjina kai alamun gamsuwa kafin ya ɗan waiwaya baya yana faɗin" Ke fa Daughter ba ki ce komai ba?
"Me zan ce?
"Ke ma ki ba ni shawara. Kin ga Sadiya ta. Kusan komai da zan yi in na nemi shawaranta tana kawo mini shawarwari masu kyau kuma in na yi amfani da su ina ganin alfanu sosai."
"To ba gashi ta baka ba"
Ta faɗa har a muryanta haushin ta bai boyu ba.
"Duk da haka kema ina son jin na ki shawaran"
Shuru ta yi kamar ba za ta yi magana ba sai da ya sake yi mata magana sannan ta ce" Ni a ganina me zai hana ka buɗe shagon provision tun da wajen a bakin titi ne."
Jinjina kai ya yi kafin ya ce" Good. Ke ma kin kawo point amma na Sadiya ya fi muhummanci. Bari mu fara da na ta, daga baya in komai ya tafi daidai sai a buɗe shagon provision ɗin"
"Ka san shawaran ta za ka ɗauka me ya sa ka na ce sai na yi magana?
Ta faɗa a zafafe.
"Saboda kema kina da haƙƙi a kan haka."
"Uhm"
Kawai ta ce ba ta ƙara magana ba, ni ko ina zaune kamar zan yi magana sai na kwaɓi kaina. Yara ma ba sa jin abin da muke tattaunawa suna ta wasannin su. Gwara ma Jidda amma ita hankalinta na kan Tab ɗin da ke hannunta. Na yi na yi da Yallaɓai ya siya mata waya ya ce sai ta shiga Jami'a. Tab ɗin daman shi saboda karatu ya siya mata. Ko rigister ɗin jam da sim ɗin Yallaɓai ta yi amfani wani lokacin yana da tsauri wani lokacin kuma yana da sauƙin kai.
Har muka isa ma'aikata ba ta ƙara magana ba sai ma amsa wayarta da ta riƙa yi lokaci bayan lokaci.
Ƙwarai waje ya yi kyau fiye da labari da gani a hoto. Kafin shiga ma'aikatan akwai babban get in da masu gadi ke tsaro har mutum biyu saboda sace sacen kayan aiki. Sannan daga gefe an makala wani allo da aka yi ma rubutu kamar na zaiba mai ɗauke da sunan ma'aikatan HM TAFIDA AND SON'S LIMITED"
Ma'aikatan na nan a kan titiN zaria road gaba kaɗan da in da office ɗin su yake na yanzu. Kuma wajen babba ne akwai fili a haraba da zai ci kimanin motoci sama da goma. Sannan an yi shuke-shuke daman Yallaɓai na son shuke-shuke. Ko'ina sai da Yallaɓai ya zagaya damu an gama komai fenti ne ma ake ƙarisawa a wani wajen. Office ɗin Yallaɓai babban yana benen sama ne amma tun da ba yanzu za su fara amfani da can ɗin ba sai ya samu wani a ƙasa da aka saka masa suna da zane kamar na zaiba wato Managin Director Md. Har office ɗin Musbahu na gani shima makeke na ce tabbas ya cancanta har sama mun haura shi dai ba a ƙarisa ba amma ma'aikata suna kan aiki. Akwai ɗakin hutawa da sauran su ba abin da dai ma'aikatan ba ta mallaka ba sai godiya.
Ina kallon Yallaɓai ina tuna a farkon auren mu in ya ce mini shi ba ya son aiki a ƙarƙashin wani ya fi son aiki na ƙashin kanshi. In ya ce mini ya na son gina kamfanin shi na zane zane da abin da ya shafi kwangilan gine-gine a shaci faɗi nake ɗaukan duka mganganunsa. Ban taɓa tunanin bayan shekaru ashirin Yallaɓai zai cimma burin sa ba. Sai ga shi ya cimma burin sa da nasara tabbas ya yi aiki taƙuri sannan ya jajirce wahala da rashin kuɗi bai sa ya nuna gazawarsa ba. A gaban yara a gaban Gimbiya na rumgume shi sannan na bashi sumbata a gefen kumatun shi, ina mai faɗin.
"Congratulation Yallaɓaina. Im so proud of you."
Na faɗa ina yi masa wani irin ƙayattacen mirmishi.
Sai ya sake riƙo ni gefen kafaɗansa na dama yana mai kallona ya ce.
" Amin. Nima ina alfari dake Sadiya ta. Duk matakin da wannan kamfanin zai kai ke ce a gaba. Kin ba ni dukkan gudummuwar da macen ƙwarai ke ba ma mijinta. Thank you so much haƙika da ban haɗu da ke a shekaru ashirin a baya ba da na tafka babban asara rasa mace kamar ki."
Sai na ji wani farin ciki ya lulluɓe ni har ina ƙara narkewa a jikin shi, Jidda na gefe sai ji muka yi ƙyars ta yi mana hoto. Baby da su Khalipa ba su san ma me ake yi ba suna can suna wasa.
"Jidda Allah ya sa hoton ya yi kyau."
Na faɗa ina dariya. Yallaɓai ko sai faɗin yake yi ta ƙara yi mana wani.
"Kun yi kyau sosai Umma da Abba."
"Mun gode yar albarka ta wajen Abban ta"
Yallaɓai ya faɗa har yana ɗaga mata babban yatsan shi alamun jinjina.
Jidda na ta ɗaukan mu hoto kwata kwata na sha'afa da Gimbiya sai da ta yi tsaki na ji sannan na juya muka haɗa ido, wallahi na gan ta harara ta, ta yi sannan ta yi motsi da bakinta ta ɓata rai, duk da na ga abin da ta yi mini ban riƙe shi a wani abu ba sai na juya ina kallon Yallaɓai kafin na ce
"Mun manta da Amarya. Kira ta a yi mana hoton tare mana."
Saboda ba lallai in ni na yi mata magana ta saurare ni ba. Wataƙila za ta iya ganin hakan a matsayin cin fuska.
"Haka ne. Daughter taho mu yo hoto in an gama sai mu yi da yaran gabaɗaya."
Amma sai ta yi kamar ba ta ji ba, sai ma ta juya yana kiran ta ta yi banza dashi ta fita daga office ɗin na shi, da muke ciki Jidda na ɗaukan mu hoto.
"Ka je ka yo lallashi Yallaɓai."
Na faɗa ina kallon sa. Ni kaina yaƙe nake yi amma a ƙasan zuciyata ina jin wani abu kamar kishi na motsa mini.
"Me a ka yi mata? Ƙyaleta."
Ya faɗa ne kawai amma sai na ga hankalinshi ya tafi a kallon ƙofa ko za ta dawo sai na ƙara roƙon sa da ya je ya ba ta hakuri ta zo a yi musu hoton.
"Ƙyale ta kawai."
Jin abin da ya sake faɗa ya sa sai na kama kaina ban ƙara yi masa magana ba. Ina lura dashi saboda fushin da ta yi ya sa sama sama muka yi hotuna da sauran yaran sai ya ce a bar shi haka ya na so mu je filin can mu gani ya mai da mu gida yana da wajen zuwa. Ko da muka fito tana cikin mota kila da ace da motarta ta zo sai dai su haɗu a gida. Ya yi sallama da masu gadin sannan muka tafi a cikin motan ma Khalipa sai da ya sha mari wai ya ta ka mata kafa.
"Kawai saboda ya taka ki sai ki yi masa irin wannan marin haka?
Yallabai ya faɗa cikin mamaki, ni kaina ban yi maagana ba ne amma marin da ta yi masa ya yi tsauri a bi sa dai laifin da ya yi.
Yaron sai ya fashe da kuka Baby ce ke lallashin sa.
"Sorry. Khalipa sorry."
Amma sai ƙara ɓare ma mutane baki yake yi, ni dai na sake tallafan Yumna dake hannuna da ta yi barci faɗan da ba ruwanka daɗin kallo ne dashi.
"Kar ki sake yi masa irin wannan marin."
"Ya yi laifi kar a hukunta shi?
Ta faɗa a zafafe ni a tunanina ko dai daman suna faɗa ne kafin su fito? Domin na ga a zafafe take kamar za ta kai duka.
"Ni dai na faɗa miki kar ki sake. Ba a hana ki yi masa hukunci ba amma ba mari irin haka ba."
"Na ji."
Ta ce a ƙasa ƙasa, shima sai na ga ya yi wani ƙyaci na ɓacin rai a raina na ce can ta matse muku. Tafe tafe sai ga mu a anguwar Alu veneu in da Yallaɓai ya siya wawaken fili. Mun sauka daga mota dukkan mu muka shiga filin babba ne Yallaɓai ke nuna mana yadda fasalin ginin zai kama. Ya tabbatar mana da kan shi zai yi zanen gidan shi, ya yi masa irin fasalin da ya ke so a cewarsa yanzu ginin ne a gaban shi bayan taron lunching na buɗe kamfanin shi za a fara yin katanga a saka get sai kuma a fara gini.
"Flat huɗu zan yi a cikin filin nan in sha Allahu."
"Kuma duk a gida ɗaya nufina a haɗe?
Na faɗa ina kallon filin, babba ne amma flat huɗu na su waye?
"E mana. Naki ɗaya na Daughter ɗaya. Ɗaya nawa ɗayan kuma ko saboda baƙi."
Ina shirin sake magana Gimbiya ta yi zaraf ta ce.
" Me ye amfanin yin shashen baƙi tun da ga shashen ka? Infact ma mu kan mu na san akwai spare room a bangarorin mu."
Sai na zama ƴar kallo, domin kai tsaye Yallaɓai ya ce" Duk da haka flat huɗu zan yi."
"Babu amfanin yin haka."
Ta bashi amsa sai ya share ta bai yi magana ba.
Ni kuma da ƙarin bayani sai na ce" Yana da amfani ko saboda su Khalipa in sun tasa zai musu amfani.
"To kin ji ma."
Ya faɗa cike da ƙarfin gwiwa. Amma ita duk ba ta gamsu ba na san fargabanta kar Yallaɓai ya ce zai ƙara aure amma saboda na ƙara samun tabbacin sai na tsaƙalo maganar.
"Yallaɓai ko dai shashen ɗin Amarya ne."
Yadda ta yi saurin kallona da razana a yanayin ta shi bai yi haka ba sai ma dariya da ya yi kafin ya ce" Wannan kuma lamari ne na Ubangiji. In ya kaddaro mini zan gode masa."
"Yallaɓai dai zai yi ginin mata huɗu ne. Wata ƙila shashen naka ma in ka ji ra'ayin aure zai tashi a naka ya koma nata."
Ni na faɗa amma yana ta dariyan nishaɗi.
"Ke ko?
Ya faɗa ya na nuna ni da hannu. Nima dariyan nake yi ina faɗin" To ai gaskiya ne."
Gimbiya na tsaye amma ta kasa magana sai dai ina kallonta ta gefen ido ta ƙara kumbura. Har tana wani kifta idanuwana kamar na yi dariya sai na kanne. Yaran suna can gefe Khalipa da Baby suna ta wasan ƙasa Jidda na tsawarta musu har da Anwar da shima yana tafiyan shi ko'ina.
Ban ɗauka za ta yi magana ba tun da har muka baro wajen muka shiga mota. Muna hanya zai fara sauke mu gida Gimbiya ta kira sunana daga bayan mota.
"Madam"
Da man haka take kira na ko ta ce Maman jidda.
"Na'am"
Na amsa mata ina ɗan waiwayawa bayan in da take zaune ita da yara.
"Kina ta wani dariya yana faɗa miki in aure na cikin kaddaransa zai ƙara."
Sai na saki dariyan nishaɗi kafin na ce" To kuka kike so na yi?
"Amma bai kamata ki yi masa dariya ba."
"Ikon Allah."
Ni da shi muka haɗa baki wajen faɗa.
"Ka gama aure Daddy. Ni da Madam mun ishe ka in sha Allahu."
"Gaskiya ne."
Na biye mata ina ƴar dariya.
"Ba ku isa ba. Ku ji minI ƙarfin hali ni na ce kun ishe ni ne?
"Ko ba ka ce ba mu mun ce ko Madam?
Ta faɗa tana sako ni a ciki.
"Tabbas. Yallaɓai mun rufe ƙofa. Gimbiya ce a madadin biyu nima a madadin biyu shike nan mun cike maka ƙofa."
Na ƙarishe faɗa ina dariya.
"Shi kenan ko."
Ta faɗa cikin jadadadawa.
"To ba ku isa ba."
Ya faɗa yana wani haɗe rai irin da gaske nake yi ɗin.
"Mun isa har ma mun yi yawa."
"Haka kuka ce?
"E haka muka ce."
Ta mayar masa da martanin cikin nuna da gaske take yi.
"Ok we shall see."
"See me?ba abin da za mu gani sai alheri wallahi ko ɗauko auro ka yi ni da Madam sai mun ruguza shi. Mu ai ka gama auro wata mace kuma a duniya tun da ka aure mu."
A yadda take magana kaɗai ya isa a fahimci da gaske take yi. Har suka sauke mu a gida ina jinjina zafin kishin Gimbiya. Wato wata rana in har Yallaɓai ya ɗauko auro akwai yaƙin duniya na uku ita da Yallaɓai kanbu! Da abin na kwana a zuciyata gari na wayewa na kira Munnira na tsegunta mata yadda muka kwashe da Gimbiya jiya. Matar nan da ta laulayo ashar sai da na ce.
" Ke Munnira ki ji tsoron Allah wannan ashar ɗin fa?"
Na faɗa ina dariya saboda na ga ta ma fini kambama lamarin.
"To ba dole na danno ashar ba. Ba a aure ita aka auro ta! Ba a yin kishiya ke kika bari aka yo miki da ita? Ba na son iskancin banza."
Ina ƙyatata dariya na ce" Ita ai za ta zo a matsayin kishiyar wata amma ita ba za ta bari a kawo mata wata a matsayin kishiya ba."
Munnira ta ce" Taɗijam! Tana da aiki ni tun da har aka yi miki da ita fata na yanzu itama ayo mata ta ji in da daɗi."
Ina dariya na ce" To waya sanin ko zai ƙara."
"To ke ba ki ga alamu ba?
"Ban gani ba amma in dai ana maganar za ki gan shi cikin nishaɗi ba ya ƙoran maganar gaskiya."
"An gama magana. Tafida in ya ga wata yar shila zai yi tunanin ƙara aure."
"Zai iya yuyuwa tun da ya iya yi mini kishiya itama ba abin mamaki ba ne don ya yo mata."
"Namijin kenen. Uhm Maza mutanen mu."
Muna ta dariya ni da ita, har ina tsokanarta in Nasir ya gano wata yar jan fata haka.
"Ta zo ai ba a kaina za ta zauna ba."
Na yi mamaki jin haka Munnira ta yi sanyi.
"Ke kuma yau? Kin saduda ne yanzu ta shigo."
"To na ga ko ka yi haukan ma in suka yi niyya sai sun yi."
Na kwashe da dariya ina faɗin" In dai ji maza kawai matar nan bana son sadudan ƙarya"
Itama dariyan take yi mun daɗe muna mgana kafin mu yi sallama. Da Yallaɓai ya dawo gidana sai da na yi masa taɗin da cewa" Kai Gimbiyar taka ba ta son kishiya. Sai ka shirya in dai za ka ƙara aure za ta yi maka daru."
"Za ma ta yi ta gama ne. Tun da har na iya yi miki kishiya ita nata mai sauƙi ne."
Amsar da ya ba ni kenan, sai na kalle shi kawai ina dariya. Ban sani ba amma haka kurun na ke ji a jikina watan wata rana Yallaɓai zai iya ƙara aure ko bai cike gurbin ba. Wata ƙila kuma ya yi gadon marigayi mahaifin su. Tun da jajirtattace ne, sannan yanzu ya samu buɗin da riƙe mata sama da biyu ba zai zama wahala a gare shi ba.
Maganar lunching ɗin kamfanin Yallaɓai ya ta so. Ya ce ya na so a yi komai a gama kafin azumi. Shi ya sa ya ke ta shirin sa muma muna taya shi. Sanin rana ce babba a gare shi, ya yi katin gayyata kuma ya gayyaci mutane sosai abokan karatun shi, abokan harkokin shi, ƴan uwan shi na nesa da na kusa. Ya gayyaci yan siyasa amma ba sosai ba, Kawu Abba da Tariq sun yi gayya suma daga bangaren su. Tun da shi Tariq a matsayin shi na lauyan kamfani shima ya gayyato ƴan uwan shi lauyoyi. Kaf ƴan uwan shi maza za su hallarta hatta Ya Usman da ke nesa. A hankali yake ta shirin sa mun yi shawara da shi, akan za a yi abincin na sadaka sannan zai ba da a yi masa saukan Qur'ani acan ma'aikatan kafin a fara amfani da shi ya ce mini To. Abincin da lunching kuma Mimisco ta ce za ta ɗauki nauyin komai da komai har da ruwan da