in sha Allahu."
Na faɗa cikin gatse har ina mele baki. Kallona ya yi ganin na haɗe rai ne ya sa ya fara ma yar da maganar wasa da dariya.
"Har garuruwa ma za ki riƙa zuwa kenan a motar kan ki?
"Ƙwarai da gaske. In sha Allahu."
"To Allah Ya tabbatar. "
Ya faɗa yana yi mini dariya sai na shaka ina hura hanci na sake kallon shi ina faɗin" Za ka cika alƙwari ne ko kuwa ka ba ni izinin na nemo wanda zai koya mini a mutumce?
"Au ni kenan ba a mutumce zan koya miki ba kenan?
"Ni dai ban ce ba"
"Kin ce mana."
Ya faɗa yana mai tsare ni da ido.
"To na ga sai kokarin yi mini wulaƙanci kake yi da na yi maka zencen koyon mota."
Sai ya yi murmishi kafin ya ta so daga in da yake zaune ya zo kusa da ni ya zauna Yunma kuma ya ɗora mini ita a saman cinyata shi kuma sai ya saka hannunsa na dama ya sagalo kafaɗata.
"Uhm to mene kuma na fushi? Ni na isa na ce ba zan yi miki abin da kike so ba?
Ina tura baki na ce" To gashi sai againsing ɗin maganar kake yi duk lokacin da na ta da maganar."
"Ni har na isa? Ke ba ki san wasa ba ne. Ko shike nan ni ba zan yi wasa da matata ba?
Ya faɗa ya na jan kumatuna. Gyara ma Yumna zama na yi a kan cinyata lokaci ɗaya ina fadin" To yaushe za mu fara?
"Mu bari weekend ko?
"Allah Ya kaimu da rai da lafiya."
Na amsa ina masa mirmishi.
Shima martanin mirmishi ya mayar mini, sannan ya ɗan ramƙwafa ya sumbaci ƙuncina lokaci ɗaya ya miƙe yana faɗin" Tukwaici me zan samu?
Ina dariya na ce" Me kake so?
"Abin daɗi mana."
Ya faɗa yana kashe mini ido ɗaya na san manufar shi ya sa na miƙe ina saɓa Yumna a saman kafaɗata lokaci ɗaya ina faɗin"To ka bari anjuma zan yi maka kyakyawan Tanadi"
"Uhm ni yanzu na ke so."
"Yanzu kuma?
Na faɗa cikin mamaki sabo da ko yau da asuba bai bar ni na huta ba. Amma wai yanzu ya na ƙoƙarin komawa ruwa. Matsowa ya yi kusa da ni ya rumgumo ƙuguna ya na faɗin" Muje ki ba ni, ina son na fita ne yau ina da baƙin da zan gani da ƙarfe sha ɗaya na safe."
"To ka je mana. In ka dawo ai abin daɗin ba zai gudu ba"
Ƙirjina ya taɓa har yana ɗan matsaawa har sai da na kalle shi, lumshe ido ya yi sannan ya buɗe yana yi mini wani kallon ƙasa ƙasa.
"Wai ba ka gajiya ne Yallaɓai?
Har ya na wani miƙa yana ta da power hannun shi kafin ya ce" Gajiya? Taɓ ni ai yanzu na ke jin kaina ma."
Taɓe baki na yi bai ƙyale ni ba sai turani gaba da ya hau yi da hannayensa a saman kafaɗuna. Bai kuma ƙyaleni ba sai da ya sake ɓaro mana wani ɓarnan ruwa sai bayan mun gama ne ya yi wanka da zai fita har yana faɗa mini saura na anjuma in ya dawo.
"Wani anjuman? Malam tuƙwaicin har guda nawa ne?
Da hannushi ya ƙirga mini guda uku, hararan shi na yi kafin na ce" Kai dai Yallaɓai sam yanzu ba ka yi mini abu don Allah sai ka dawo ka fanshe ko?
Maganata ta saka shi dariya har yana ƙyaƙyatawa.
"Na ji ba komai. Duk cikin cika sunnar ma'aiki ne(SAW)"
Ni da Yunma muna haraba mun rakosa ya karɓeta ya yi mata wasa ya sumbaceta sannan ya miko mini ita bayan ya haɗamu duka ya rumgume.
"Ki kular mini da kan ki Abar ƙaunata."
Ya faɗa yana kai mini sumba a gefen bakina.
Nima na mayar masa da martani kafin na ce.
"A dawo lafiya Allah Ya ba da sa'a."
"Amin My Sady."
Muna tsaye ya shiga mota ya ta da. Daman ya buɗe get ya fita sannan ya dawo ya rufe get ɗin duk muna tsaye ina ɗaga masa hannu shima yana ɗaga mini sai da na ji ƙara tashin motarsa sannan na koma cikin gida ni da Yumna.
Haka ko aka yi weekend na shiga Yallaɓai ya ce na shirya. Ranar farko ba da Yunma muka je ba wajen Baby na bar ta. jidda ba ta nan ta ta fi Tahfezz suna ta ƙoƙarin haɗa haddarsu ne gabaɗaya ba ta samun zama sosai. Ranar farko haka na yi ta rawan jiki da na hannu ban yi wani abun arziƙi ba da ya ke wani fili ne can gabanmu Yallaɓai ke koya mini anan, haka rana ta biyu tare da Yumna tun da Baby ta je Hadda itama Yallabai ke rike da ita ni kuma yana nuna mini yadda ake fara kunna mota da sauran su sai na yi kamar na gane in ya sakar mini sai na yi shirme kuma motar Auto ce shi ya sa za ta yi mini wahala amma ya ce wani sati zai saka Salisu ya kawo ta hannun shi tun da ita Munual ce za ta fi mini saukin koya.
A satin dai haka muka gama ban gane komai ba Yallaɓai na ta yi mini dariya amma daga baya da ya ga na damu sai ya bar dariyan ya koma ya na lallashina da ban baki. Ni har cewa na yi an ya ina da rabon tuka motar kaina kuwa! Tun da gashi nan ma motar ta gagare ni iyawa. Shi kuma yana lallashina da cewa zan iya in sha Allahu. To satin na biyu motar hannun Salisu ya karba ita dai kan an ga sauyi tun da ranar lahadi har ya sakar mini sitiyari amma fa da na fara tafiya sai na ruɗe na kasa yin kwana na saki kan mota Allah ya sa Yallaɓai na gefe riƙe da Yumna ya yi saurin rike kan motar da na halakamu, duk na ruɗe sai da kuma koma gida ya yi mini faɗan na daina ruɗewa na riƙa natsuwa ne in ba haka ba zan daɗe ban koyi abin da ke da sauƙi ba, kuma ya fahimci ina da tsoro to na fara cire wannan tsoron in ba haka ba, to ba zan iya ba.
Haka dai haka dai duk sati muna ta lallaɓawa kuma cikin ikon Allah na fara iya mota. Yallaɓai na sakar mini har na dawo damu gida ma. Ina ta murna da farimciki na iya mota na faɗa ma su Jidda suna ta mini ihun murna suma kar da Baby ta ji labari yan gidanmu kuma na ce mamaki zan ba su sai na yi mota na tuka kaina zuwa gidajen su su sha kallo. Sama da wata biyu Yallaɓai na koya mini mota kuma Alhamdulillah hannuna ya faɗa soaai fiye ma da tunanin shi tun da har cikin gari muna shiga na tuƙa mu, kuma na mayar da mu gida. Sannan har motarsa ma ina iya tukata yanzu lafiya lau.
Ranar wata lahadi ni kaɗai na fito, tun da motar yara saboda ina amfani da ita ya sa tun ranar Jumma'a in Salisu ya ɗauko su daga makaranta sai ya ba ni key sai kuma Monday zai dawo ya karɓa. To in dai Yallaɓai ba gidana yake ba kafin ya ƙariso in na gama ayyuka gida zan ɗauko Yumna mu fita a motar ina ɗan zagaya anguwa daga can sama zuwa kasa saboda dai hannuna ya ƙarawa faɗawa. To ranar ma ni kaɗai na fita kuma a gida na bar wayata sai da ina kan hanyar dawowa na haɗu da Yallaɓai a kasa yana tahowa lokaci ɗaya yana waya sai magana yake yi yana ɗaga hannu bai ma ganni ba ni ce na hango shi yana sanye da jallabiya da dogon baƙin wando. Jallabiyan mai kalan ruwan kasa ne har da wata hula ya saka rabin kai na rasa a ina Yallaɓai ya samo wannan hulan tun kwanakin nan na ga yana saka ta lokaci bayan lokaci.
Daga nesa na ke kallon shi, tun da na ɗan rage gudu. Yumna na kalla daga kwance a kan kujeran mai zaman banza. Sai na yi mirmishi kafin na ce" Yunma ga baban ki can"
Na faɗa ina mai ƙara kallon shi ta cikin gilashin mota tumbin da ya fara tarawa yake shafawa ya na faman magana a waya lura da yi bai ganni ba, kuma ni ya fito nema tun da ya je gidan ba na nan ya san na fito ne.
Hon na yi masa lokacin da na kawo kusa da shi, sai da ya juyo sannan na ɗaga masa hannu ina dariya. Sai ya rike baki yana kallona kafin ya yanke wayar. Tsaya wa na yi lokaci ɗaya ina sauke gilashin gefen da Yumna ke kwance.
"Hy ɗan saurayi ji mana "
Na faɗa ina kashe masa ido ɗaya. Sanye na ke da wando baki plazo da riga ƙarama amma na saka after dress a saman kayana na saka brieziya hijab na Baby ne ma na maƙalashi da zan fito. Yumna ma ta sha gayu abin ta sai tashin ƙamshi take yi.
"Eye Yan matana irin wannan cakarewa haka?
Ya faɗa yana yi mini mirmishi, lokaci ɗaya yana rike hannuwan Yumna itama ta rike shi gam ganin shi ya sa har ta fara wuntsila kafa tana masa gaurancin su na yara. Wai ita nan ta san me yi mata wasa haka take yi musu ita da Baby ta riga ta gane su in dai wajen yi mata wasa ne.
"Ya son ranka Ɗan saurayi."
"Raina fesa. Da kyau Hajiya ta."
Ya faɗa yana nuna mini babban yatsa alamun jinjina.
"Shigo na rage maka hanya."
Na faɗa ina masa dariya shima yana ta ya ni, buɗe masa motar na yi shi kuma ya shigo bayan ya ɗauki Yunma a saman jikinsa sai da muka fara tafiya na ji yana yi ma Yunma cakulckuli tana ta dariyan su na ihu irin na yara sannan na kalle shi ina faɗin" Yunma har ta gane ka kai da Baby in dai wajen wasa ne, in ba kwa kusa ta yi mini zillo tana son wasa ni ko na ce ba zan iya ba yarinya ki ji babanki ya zo."
Yana dariya ya ce" Me ya sa ba za ki yi mata wasa ba?
"Ban iya ba"
"Kin iya. Ke dai ba ki san yi mata ne, Yumna Umman ki ta iya wasa ba ta son yi miki ne kawai saboda haka kisan zaman da za ki yi da ita yauwa."
Kamar ta na jin sa ta yi zuru tana kallon shi, ni da shi muka kwashe da dariya ganin yadda ta wani yi nakwa nakwa da fuska kamar za ta yi kuka.
"Kar ka haɗa ni da uwata."
"To ki riƙa yi mata wasa. Irin wannan"
Ya faɗa yana shilla ta sama ya kuma caɓeta sai ga ta, tana bangala masa dariya.
"Aikin kenan daman shi ya sa in ta ganka ta yi ta zillo duk ka koya mata mugun wasa Yallaɓai."
"Dai dai kenan ma"
Muna tafe muna taɓa hira, ta kofar gida muka wuce mun kai farkon layi na sake kwana muka dawo sai a lokacin na lura ban ga motarsa ba.
"Ka shiga da motar ka cikin gida ne?
"A'a ba da ita na zo ba. Tun jiya tana gareji bakin mai ke zuba sai na kai ta aduba mini. Adaidaita na hayo."
Sai na gyaɗa kaina ban yi magana ba muna tafe sai ya kalleni kafin ya ce" Ehe Madam hannu fa ya faɗa."
Ina masa fari da ido na ce" To ya ka gani?
"Lafiya lau. Yanzu kam ba in da ba za iya tukamu ba."
"To Alhamdulillah saura motar kaina in sha Allahu."
"Akwai kuɗin siyan motan ne har yanzu?
Ya faɗa yana yi mini dariya ban ba shi amsa ba sai da muka isa gindin wata bishiya na yi parking na kashe motar sannan na kalle shi ina faɗin" Babu kam. Duk na ruguza jarina. Ina tunanin na riƙe wannan ko kai yara makaranta ne sai na rika kai su ina zuwa ina dawowa da su, tun da ina gida ba abin da na ke yi."
Bai yi magana ba amma dai ya kalleni, sai kuma ya ma yar da hankalin shi kan yi ma Yumna wasa.
"Ko Yallaɓai? Kafin na samu kudin siyan motar ko?
"A'a ba zai a yi haka ba"
"Me ya sa to?
Na tare shi ina mai kallon shi, sai ya dawo da hankalin shi kaina lokaci ɗaya yana faɗin" Saboda tuntuni motar nan tana hannun Salisu kuma kin ga ya tambayi izini tun a shekarun baya ya na ɗan haya da ita nan ƙauyakun kusa damu yana ɗan samun na cefane kawai sai rana tsaka na ce zan karɓa motata kin ga hakan ya dace?
Sai na yi shuru ina kallon shi ban yi magana ba amma dai gaskiya ya faɗa bai kyautu a karɓa ba.
"Shi ya sa ba zan karɓa ba. Kuma kin ga ya daɗe yana aiki tare da ni tun mashin ɗin sa har ya zo ya rasa mashin ɗin bayan na sauya mota sai na bar mishi wannan a hannun shi ba saboda kai su Jidda makaranta ba ne, saboda shima ya taimaki kan shi ne kin ga ne?
Sai na gyaɗa masa kai kafin na ce" Haka ne."
"To kin gani. Ki kwantar da hankalin ki in sha Allahu abubuwa suna ƙara warware mini zan siya miki mota in sha Allahu."
Kallon sa na ke yi domin ni na san alƙwarin Yallaɓai haka ya yi mini na buɗe shago har yau bai iya cika alƙawarin da ya ɗaukar mini ba.
"Kin yi shuru?
Sai na sauke ajiyar zuciya kafin na ce" Uhm Allah Ya sa."
"Amin ko ba ki yarda da abin da na ce ba ne? Wallahi zan siya miki ba ni na ce ba."
Ƙureni da ido ya yi ganin ina kallon shi ban ce komai ba.
"Ki yi mini magana mana ba na son wannan shurun fa"
"Yallaɓai ni dai ka daina yi mini alƙwari in dai ka san ba za ka iya cika mini ba"
Sai ya zura mini ido kawai bai yi magana ba.
"Ka daina lasa mini zuma a baki kuma ka tafi da sauran zumarka ban ƙara ganin ta."
"Wani alƙawari na yi miki ban cika ba Sadiya?
Ya faɗa a muryansa a natse ba maaganar wasa nima ko na gyara zama ina faɗin" Suna da yawa amma babban ciki ne na buɗe mini shagon Saloon. Ka samu damarmar maki da yawa a baya Yallaɓai amma ba ka cika mini alƙawarin da ka yi mini ba, duk da ba kyauta za ka buɗe mini ba da kuɗaɗena a hannunka amma abu ya gagara ko da yaushe sai dai ka ce kai ka yi alƙawari za ka buɗe mini amma shuru. Duba fa ka gani Gimbiya a bayana ta zo gashi yanzu har ta buɗe shago business ɗin ta na ta bunƙasa amma ni sai dai ka yi ta lasa mini zuma a baki. Ba domin na ɗan kama ma businness ɗin hijaban nan ba da har yau ina nan ina zaman jiran warrabuka."
Na gama faɗa a tsume, ban so na yi magana ba amma yau ne ya kai ni bango. Na gaji sai ya zauna ya yi ta cewa zai yi mini kaza zai yi mini kaza amma ya kusa cika alƙwari ko ɗaya da ya yi mini sai maganaa a fatar baki.
Shuru ya yi ya kasa mgana har yana dukar dakai.
"Ka yi haƙuri ban so na yi maganar nan ba. Ta kama ne."
"Kallon maƙaryaci ashe kike yi mini Sadiya ban sani ba?
Ya faɗa yana mai kallona.
"Ni dai ban ce ba."
"Haka ne mana. Kina mini kallon makaryaci sannan mara adalci ke ban buɗe miki shago ba amma na je na buɗe ma Daughter ko?
"Ni fa ba haka na ke nufi ba."
"Haka ne mana. Ga shi kin faɗa mini da ba ki fara ma sana'ar sai da hibajai ba da har yanzu kina nan kina zaman jiran warrabuka ko?
Ko ba haka kika ce ba?
Shuru kawai na yi ganin yana neman sauya mini mgana ta.
"Muje gida sai mu yi maganar a can"
Na faɗa ina kokarin ta da motar tsawa ya daka mini sai da Yumna ta firgirta ta fashe da kuka.
"Ba in da za mu je, anan kika fara ta kuma anan za mu ƙarƙare ta."
Ya faɗa da karfi har ya na buga kujeran mota ni gani na yi ma yana neman sakar mini da yarinya da ya sa da sauri na saka hannu na karɓeta ina rumgumeta ganin ta firgita tana ta kuka.
Rigata na ɗaga ina zaro mata Mama saboda in ba shi na ba ta ba, ba za ta daina kuka ba.
Ina ba ta Nono Yallaɓai ya ta sani a cikin motar nan yana ta yi mini masifa saboda ba ya son gaskiya. Eh mana rashin gaskiya in ba haka ba ai bai cika alƙawarin ba. Kawai yana kunfar baki ba shi da abin faɗa ko da zai kare kan shi da shi.
"Ni kike yi ma kallon maƙaryaci sannan macuci tun da kin ce abu ba kyauta ba tun da na cinye kuɗin ki kuma ban buɗe miki shago ba."
"Ni fa ban ce ka cinye mini kuɗi ba Yallabai ka tsaya ka fahimci maganar nan don Allah"
"Me zan fahimta! Bayan wanda na gama fahimta. Wato ke dai yanzu ma kina tunanin na zalunce na cinye miki kuɗi ban cika miki alƙawari ba ko?
Ya faɗa yana mai tsareni da ido.
"Haba mana Yallaɓai."
"Haba ko gaskiya"
Ya faɗa a fusace ni kawai sai na yi masa shuru ganin ya harzuƙa.
"To na gode ban taɓa tunanin irin kallon da kike yi mini ba kenan amma yanzu tun da kin furta mini kuma na ji zan yi lamarin tufkan hanci. Ki faɗa mini nawa ne kuɗin ki da kike tunanin na cinye, zan biya ki kuma ba na son ki yafe mini ko naira biyar a ciki in kuma kika yafe mini to ni wallahi ban yafe miki ba"
"Yallaɓai."
Na faɗa ina buɗe baki cikin mamakin kalaman shi. Daga magana sai ciɓi ya zama ƙari duk tsawon wannan shekarun da ban taɓa masa magana duk bai ga hallacin da na yi masa sai yau ne zai ce ni ce butulu saboda kawai na faɗa masa gaskiya.
"Kuma maganar buɗe shago kuma ni na yi niyya alƙawari ne kuma zan cika in sha Allahu. Na yi kuma ranstuwa da Wallahi tallahi zan buɗe miki shagon Saloon na muka mallaka miki shi halak malak in sha Allahu Sadiya."
Sai kawai na gyaɗa kai ban ce komai ba, na mai da kaina da hankalina wajen ba ma Yumna, saboda na fahimci ko magana