Turken Gida Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   25 / 55

72K to 75K   out of 163.1K words

na sake yi ba zai taɓa fahimta ta ba.

"Nawa ne duka kudin ki da ke hannuna?

Ko kallon shi ban yi ba saboda haushi.

"Ki rubuta ki tura mini cikin satin nan zan tura miki kuɗin ki ba na so ki sake yi mini kallon wanda bai yi miki adalci ba."

Tsaki na so na ja masa sai na fasa ni na ɗauka ma zai ce ne yau yau ɗin nan zai tura mini kudin ganin yadda ya yi zuciya.

"Sai maganar Daughter kin ce wai ita da ta zo a bayan ki ga ta nan na buɗe mata shago businness ɗin ta na ta haɓbaka. To ina so na faɗa miki ko na ce tunasarwa ce tun da kin sani sai dai in kin runtse ido ne saboda wata munufarki, ko da na auri Daughter da kuɗin ta na ganta mijinta ya mutu ya bar mata gado. Da kuɗin ta da buɗe shago, ni dai na taimaka mata wajen neman shago da sauran su amma wallahi tallahi ba sisi na a cikin kasuwamcin ta ban rantse miki domin ina jin tsoron ki ba sai domin na fita daga zargin da kike yi mini na rashin adalci."

Ban san tsakin da na ke riƙewa ya fito ba sai da na ga ya kalleni cikin mamaki kafin ya ce" Ni kike yi ma Tsaki Sadiya? Ni Yusuf?

Da zan ce ya yi haƙuri sai na fasa na yi masa banza. Na gama ba ma Yunma Nono na rufe rigata na ɗora ta a saman jikina na ja key zan ta da mota Yallaɓai ya make mini hannu yana yi mini ihu a saman kaina.

"Ni kike yiwa Tsaki Sadiya? Rashin kunya za ki yi mini?

Sai kawai na koma na jingina da kujeran mota ina sauke numfashi, sai tsorata mini yarinya yake yi da ihun shi.

"Na gode kin ji ko? Tun kina yarinyarki ba ki yi mini rashin kunya sai yanzu da girma ya kama ki ko Sadiya?

Ya faɗa har ya na nuna ni sai ma ya ba ni dariya har sai da na ɗan dara shi kuma sai ya jijjiga kansa kawai bai ƙara maagana ba sai ma ficewarsa da ya yi a motar ban kira shi ba na ta da mota na zo na wuce sa, na koma gida ina ta jiran shi duk da wata zuciyar na faɗa mini ba zai dawo ba tun da ya yi fushi haka ko aka yi bai shigo gidan ba daga can ya yi gaba da man a gidan Gimbiya yake, sai washegari ne zai dawo gidana kuma har sai washegarin da dare na gan shi, haka ya shigo mini gida a daƙune ina gaishe shi da kyar ya amsa kamar na faɗa masa cuta.

Daga shi sai yaran shi ya riƙa mgana. Shi da Jidda sun kai har wajen sha biyun dare yana mata solving Quention paper na Neco wancan shekaran. Tun da sun kusa gama WEAC bai wuce paper biyu su gama ba za su fara Neco kafin babban salla shi ya sa ba ta samun natsuwa ko da yaushe cikin karatu suke yi. Ni dai ganin ba a yi da ni ya sa na kama kaina na ja jikina ni da Yumna muka shiga ciki muka kwanta sai cikin dare da na farka ne na gan shi rumgume da Yumna ni uwar Yumna tun da ana fushi da ni, ni kaina kamar jikina ya sani duk mugun barci yau ban ganganra jikinsa ba. Da safe ma haka ya yi mini wani nuku nuku da fuska ni dai ina ganin ikon Allah har ya koma gidan Gimbiya ba ma yar daɗi da shi, da farko na so na biye masa a yi zaman doya da manjan sai daga baya na zauna na yi tunanin ban kyauta ko domin tsakin da na yi masa shi zai fi tsaya masa a rai. Shi ya sa ranar da zai dawo gidana na ci kwalliya saboda ina son sulhu.

Ba ƙaramin kai zuciyata nesa na yi ba ina bashi haƙuri yana yi mini cin mgani. Kallona ya yi kafin ya ce" Uhm ni yau na ke magana Sadiya ki kalle ni ki yi mini tsaki? Haka na lalace daman a idanuwan ki?

"Ka yi haƙuri tsakin ya suɓuce mini ne."

Duk da haƙurin da na yi ta bashi bai saka ya hakura duka ba amma dai ya ɗan sassauta tun da har a daran ma ya neme ni mun yi ɓarnan ruwan da safe kuka ya tashi ya na sake yi mini cin magani ni dai na ce ai na ga ta kaina. Bai saki ba sai da ya fi sati yana yi mini isa isa daga ƙarshe dai ya haƙura don kan shi ya sauko amma ko yaya abin ya faɗo masa a rai sai ya yi ƙyafci a cewarsa ba abin da ya kai tsaki reni. Ya tsani ko wanda ya girme shi ne ya yi masa tsaƙi ballanta ni da nake ƙarƙashinsa ni dai nawa cewar ai ban haƙuri ne, ya dawo yana yi mini burga na yi lissafin kuɗina ya biya ni na yi banza da shi, daman can jin ta baki ne muna shiryawa sai shuru kuma bai ƙara ta da maganar ba. Shike nan na samu faɗan mu ya wuce sannan maganar biyan bashi dai ya sha ruwa daga lokacin da man can ba biya na zai yi ba, barazana ne kawai.

Sallar babban salla ne ke ta matsowa muna ta shiri. Daman da sallar ne muke haɗuwa gabaɗayanmu a gida wannan ma salla hakan ce ta faru an hadu gabaɗaya an yi hiran zuumci an yi wasa an yi dariya an yi faɗa an kuma shirya. In ka ganni ni da Ma'u ba za ka taɓa cewa mun taɓa samun matsala ba a baya. Ma'u ta na faɗa mini Amarya da Hajiya Zainab sun haɗa mata kai, na ce ta yi haƙuri duk ta kau da kai haɗuwa in ba ta Allah ba ce tana zaune za ta ji kan su. Duk da ta fara kwantar da hankalinta amma har yanzu Ma'u ba ta mai da jikinta ba, sannan Alhajin ya daina rawan jikin da ya ke yi a kanta a da duk in da Ma'u za ta je in bai kai ta direba zai kaita amma yanzi har ta saba yawo a cikin adaidaita. Ni da na ga ta yi fari ma na ɗauka tana da ciki ne sai da na tambayeta ta rantse mini ba ta da ciki a lokacin ma jini take yi. Marwan Ya Aina ce cikinta har ya fito ita ke gaba sai Rahila ta kunsa ƙarami.

Sai a Gwammaja muka haɗu da Gimbiya rabo na da ita tun wani zuwa da na yi gai da Nene bayan sunan Yunma muka haɗu sai da salla kuma muka sake haɗuwa. Ta yi fari ta ƙara zama wata katuwa ni dai sai na ga kamar ciki gare ta ban dai furta ma kowa ba. Da man ai ta yaye Anwar yana yawon shi ko'ina suna ganina da ga shi har Khalipa suka rumgumeni suna kiran Umma daman haka Khalipa ke kirana saboda ya ji a bakin su Jidda. Shi ya sa sai Anwar shima ya kama sunan. Nan muka yini gabaɗaya ni ban bi ta kanta ba tun bayan da muka gaisa muna ɗakin Maman farko ni da su Munnira muna ta hiran mu sai dare Yallaɓai ya zo ya ɗauke mu daman gidanta yake, mu aka fara saukewa sannan suka yi mana sai da safe suka wuce gidan su.

Nun yi babbar salla a watan june ne. Lokacin Yunma na cikin watan ta na bakwai ne har ta fara wayau tun yaushe har ina koya mata zama. Tana wayau tana ƙara zama burtuka yanzu Baby da nishi take iya ɗaukanta. Jidda tuni har sun fara Neco Baby ce kawai ke zuwa makaranta kullun ita in ba su da paper tana gida. Ta ɗauke mini komai ita ke aikin gida gabaɗaya ni sai dai kawai na ci na kwanta, Yallaɓai ya yi ta mini tsiya wai daman abin da na ke so kenan na ce to sai dai ya yi haƙuri tun da raina ya kai kuma na haifa.

Ni bai faɗa mini Gimbiya na da ciki ba amma tun ganin da na yi mata da salla na zargi haka. Sai da Jamila ta shigo anguwar mu wani gaisuwa gidan abokin mijinta ta shigo gidana ta ke faɗa mini ashe kuma Gimbiya ciki gareta? Na ce ban sani ba wallahi.

"Tab ciki ko gashi nan har ya fito ba ki gan shi a jikinta da salla ba ne da kuka haɗu?

"Ban lura ba"

Na faɗa ba tare da na sake yin wata magana.

"Ai ko ciki gare ta. Da Suwaiba ta yi magana ta ce ba an ce likita ya ce ta huta ba Anty Bahijja ta ce likita ai ba Allah ba ne. Lafiyan ta ƙalau kuma za ta iya haihuwa da kanta gwara ta yi ta haihuwa tun da Mijinta mai son ƴaƴa ne"

"Ba shakka"

Na faɗa ina jinjina kai, na rasa me zan ce ma. Ita dai Gimbiya haihuwa ce a gabanta ita a dole sai ta fini yawan ƴaƴa a raina na ce ta yi ta haihuwa ko duniya za ta haifa ba ta gaba na. Na tuna ko bayan haihuwan Anwar ni da Yallaɓai mun yi magana ya ce za ta yi planning ko na shekara biyu saboda dokar likita ban sani ba ko ba su yi tsarin iyalin ba ne. Shuru na yi da bakina na yi kamar ban ji ba ko Yallaɓan da bai faɗa mini ba nima ban nuna masa na ji ba, kowa kuma ban yi maganar da shi hatta ko da su Munnira. Sai ma Hauwa ce ta kira ni a waya ta na faɗa mini  a Rano ta ji labarin Gimbiya na da ciki na ce mata e da gaske ne.

"Ba likita ya ce ta huta ba?

"Ba ta son hutun ne Hauwa. Ki barta ta yi haihuwanta."

"Allah ya sauwake."

Haka muka rufe maganar muka shiga wata, mun ɗan jima muna magana kafim mu yi sallama Munnira ma da ta ji ba ta yi mini maagana ba sai da na je gidanta ranar daga asibiti na kai Yumna tana da fama da ciwon ciki, shi ne muke maganar da ita.

"Ai kishiyar nan taki munasura ce Sadiya. Ta ce ita haihuwa yanzu ta fara a gidan Tafida ba ta ma yi komai ba tukunna."

"Allah haka ta ce?

Munnira ta ce"Haka ta ce, ta ke faɗa a gidan su nima Hauwa ce ke faɗa mini da ta je gidan su ta ji maganar."

"To Allah ya ba ta masu albarka"

"Addu'a za ki yi mata?

"To zan ce ne kar Allah Ya ba ta masu albarka ne Munnira? Allah ya ba ta masu albarka ko ba komai ai ai ƴa'ƴan Yallaɓai ne. Kuma duk saurin ta sai dai a kira su ƙannen su Jidda ba dai yayyen su ba"

"Wannan gaskiya ne."

"To kin gani. Ku bar ta lokaci ne wata rana sai labari."

Har na baro gidan Munnira ba mu ƙara ma ta da hiran Gimbiya ba, ni ma da na dawo na cire abin a raina na watsar nima na gode ma Ubangiji tun da har ya ba ni biyu ya kuma ƙara mini a lokacin da na cire tsammani, ita takamar tana da ya'ya maza ita ce ta haihu ni tun da mata ne yarana ban haihu ba ko alama ba ta gabana harkan rayuwata kawai na ke yi. Kuma yadda shima ya yi shuru bai taɓa mini maganar nima ban yi masa ba sai ranar da ya ke gidanta har dare bai zo ya duba mu kamar yadda ya saba sai a washegari da safe ya zo yana faɗa mini a jiyan Gimbiya ce ba lafiya a asibiti suka yini, amma an sallamota tana gida in na samu lokaci na shirya mu je ni da yara mu duba ta a gida.

Kamar zan je sai mun samu lokacin sabo da ban manta wulaƙancin da ta yi mini da cikin Yumna ba ni ko ba zan ƙara rawan jiki a kanta ba. Na ce masa za mu je ranar da su Jidda ke gida na masa Allah ya ƙara lafiya amma ko gaisheta ban ce ya yi ba. Kwana biyu tsakani ranar lahadi Jidda na gida ta je Hadda ba ta dafe ba ta dawo tun da sun gama haɗa Qur'anin su suna bita ne kafin a yi musu waliman sauka. Daman a gidan ya kwana yana ganin su dukkansu a gida sai ya ce mu shirya  mu je mu duba ta daman na kudira a raina ba zan je ba. Sai kawai na nemi waje na kwanta na ce ba na jin dadi wai to bari a fasa sai gobe in na samu sauƙi.

"A'a ku tafi kawai ku gaishe ta."

Na faɗa ina daga kwance a saman gado
Sai ya ce to bari su tafi amma har da Yunma Baby ta ɗauka suka tafi, tun bayan la'asar sai dare suka dawo sai ga su da yara niki niki Anwar da Khalepa da kayan su, sannan ba su dawo da Jidda ba wai tana can za ta kwana saboda Gimbiyar ita kadai ce yaran ma tace a kawo mini su sun dame ta da hayaniya ga shi ba ta da lafiya.

"Topha. Ai nima ba ni da lafiyan kuma daman Jidda ce ƙarfin aikin gidan yanzu."

Na faɗa a tsume bayan duk ya gama rattabo mini bayaninsa. Wato ga jaka dole ta ce a kawo mini yara.

"Ga Baby za ta taimaka miki da wani abun. Ita ma Jidda zuwa jibi za ta dawo tun da ranar laraba suna da jarabawa."

Takaici ma ya hana ni mgana, tun da yaran nan suka zo hutu na ya ƙare tun da Jidda ba ta nan dole na ke tashi da safe na yi musu shirin makaranta. Har Anwar da ke ɗan shekara biyu an saka shi makaranta ajin yara ban sani ba da man a can uwar su ke kai su yanzu kuma tun da suna gidana Salisu ne.
Ko Yallaɓai in bai fita da wuri ba, sai da Jidda ta kwana uku ta dawo da na ke tambayanta Antyn ta su a kwance take?
Sai ta ce mini.

"Wani kwance Umma? Ta ji sauki fa ta yi ta chart da waye wayenta abinci ne ma in ta ci wani lokacin ta ke Amai."

Jinjina kai kawai na yi, a raina na ce ban ga laifinta ba wanda ya samu rana ga igiya ai sai ya yi ta shanya. Yallabai ne ya ɗaure mata gindin yara kuma na yi magana ya ga ɓakina. Amma me ya sa bai kai su gidan Naja ko Anty Bahijja ba? Sai ni ko wacce suka raina to ai ya yi kyau ni kaɗai ranar na rika masifa a cikin gida kuma har lokacin bai faɗa mini ciki gare ta ba, nima ban tambaya ba sai ranar da ya ke gidana har mun yi shirun kwanciya ya fita ɗakin yara sai ga shi ni kuma ina kwance ina ba ma Yumna Nono ta farka ta fara mini jananun kuka.

"Meke damun Gimbiya ne haka da take ta rashin lafiya?

Da gayya na yi masa tambayan ya na sauya kayan jikinsa zuwa na barci yake amsa mini.

"Laulayi ne."

"Laulayi?

Na maimaita cikin sigan tambaya.

"E ciki gare ta. Ba ki sani ba?

Sai da na balla masa wata uwar harara kafin na ce" Na sani mana tun da ka sanar da ni."
Sai ya yi dariya lokaci ɗaya yana hayo gadom har kusa da ni, hannunsa ya sa ya ɗan shafa fuskar Yumna zuwa jikinta.

"Kar ka ja ta da wasan ka. Ka ja mana tsayuwar daren dole."
.

Dariya ya fara yi ni kuma na kanne ina fadin" Ahto domin kai zan haɗa da ita na yi kwanciya ta wallahi."

"Na ji ba komai. Ai na iya reno nima."

"Ka iya fa."

Na faɗa cikin gatse,shi kuma yana ta mini dariya.
Ganin na gimtse fuska ne ya sa ya saussauta murya ya na faɗin" Da gaske ba ki san Daughter na da ciki ba?
"Na sani na ce ba ka faɗa mini ba?

Na faɗa ina masa wani kallo.

"Yi hakuri ma yar da wuƙar wallahi na ɗauka fa kin sani shi ya sa ba mu yi maganar da ke ba."

Uhm"

Na faɗa kafin na ce" Allah Ya raba lafiya.'

"Amin ai da sauƙi ma bai wahalar da ita kamar cikin Anwar ba."

Na yi masa banza na cigaba da ba ma Yunma Nono.

"Kin san likita ya ce ta huta. To da na yi mata mganar ko za ta yi tsarin iyali ne ai kin san mun ma yi maganar da ke ko?

Ya faɗa yana kallona sai na gyaɗa masa sai ya cigaba da faɗin" Sai ta ce ita ba za ta yi ba. Wai ba ta son yi saboda ba ta so ta yi itama ta samu matsala irin na ki."

"Jar Uba!

Ban san na yi ashar ba sai da na ji ya fito. Yallabai ya yi ƙasake yana kallona. Cire Yumna na yi daga nono na kwantar da ita gefe ina kallon Yallaɓai.

"Zagi kuma Sadiya?

"Dole na yi ashar na ga matarka na neman rena mini wayau ne."

"Na me fa?

Ya faɗa shima ya ɗan sauya yanayin shi.

"Saboda ta raina ni sai ta yi kwantance da ni ni kaɗai ce macen da ta taɓa tsarin iyali ya sakar mata matsala? Ko tsarin jikin mu da jinin mu ɗaya ne. Wata ƙila ita in ta yi sai ta wanye lafiya ai komai na Allah ne amma don tsabar renin wayau sai ta fake da ni? Ina ruwanta to da rayuwata"

"Ki tsaya ki fahimci ne ita fa ba haka take nufi ba."

"Ya take nufi? Kar ka wani kare mata. To ni ba ni da wata matsala ba kuma zan gani ba in sha Allahu sako na baka ka sanar da ita ni Sadiya ba ni da matsala ban kuma tare da ita wanda ke ƙababa mini ita ma ya je Aniyarsa ta bisa wallahi."

Na ƙarishe faɗa a fusace saboda raina ya gama baci ina gidana amma ta na can tana raina mini wayau.

"Topha ni ce Aniyata ta bi ni ko Daughter?

"Oho ni dai na ce ba ni da matsala mai neman kuma goga mini ita sai ta faɗa kan shi Ehe."

Na fada ina sauka daga gadon gadon bi na ya yi da kallo ya yi kafin ya ce" Yi hakuri

25 / 55