za a sha da lemu a wajen. Kayan da ya yi oder suka iso kamar su kujerun ofishoshi da I.C, cafet da sauran su a ƙarshen watan Febuary kayan suka sauka daman kuma ranar lunching goma ga watan March ne. Ranar lahadi za a fara taron goma na safe zuwa ƙarfe ɗaya na rana.
Ya ɗauki Nene da su Maman Farko ya kai su wajen sun gani sun yi murna da addu'o'i. Alhajinmu da Gwaggo da na je na faɗa musu sun kira shi sun yi masa fatan alheri yana ta jin daɗi. Shi dai ya ce walimarsa ta maza ne amma in za mu yi gayya a gida ƴan uwa a zo a yi murna bai hana ba, shi ya sa duk na faɗa ma yan gidanmu. Sai su Munnira sauran tawagan gidan su Yallaɓai yan bangaren Gimbiya ne. Ni Jamila da Suwaiba ne daman na sa ka ran in ma za su fito ranar kenan. Da bakin shi ya ke faɗa mini Gimbiya kayan snaks ta yi mishi har da ƙananun kofunan mug da sunan kamfani, ni kuma lokacin ba ni da kuɗi. Duk na ci ubansu da sunan Yumna hijaban ma tun da na haihu sau ɗaya aka kawo mini. Ba domin Gimbiya ta yi ba a'a sai domin nima matarsa ce kuma ya kamata nima na nuna nawa bajintar. Da na yi tunanin memo amma sai Adnan ya faɗa mini su Anty Bahijja sun yi masa Memo, sai na ce tun da har an yi memo da mug ni bari na yi jaka wacce za a saka gift ɗin a ciki ba ni da kuɗi amma haka na yi ƙarma ƙarma sai da Ya Auwal ya cika mini wajen 30k sannan na ba da a ka yi masa guda hamsin ta hannun Adnan.
Jakar ta kwali ce an saka sunan kamfanin ne.
Congratulaton Md Yusuf Muhammad Inuwa on your opening ceremoney of your company. Hm Tafida and son's Limited.
Cut ceey. "Miss Sadiya Yusuf Muhammad, Hauwa'u Yusuf Muhammad, Maimunatu Yusuf Muhammad and Rukyyatu Yusuf Muhammad.
Bai sani ba, kuma na ce kar Adnan ya faɗa masa sai ranar kawai sai dai ya gani. Bangaren abincin sadaka ni ya bar ma ragama buhun shinkafa za a dafa da wake, sai na raba biyu rabi na ba ma Maman Saude aikin rabin kuma sai na ba ma Maman Naana mai yi mana kitso. Na ce in sun yi su raba shi ga almajirai sadaka ce. Bangaren kayan da zai saka kuma ranar ya zo ya na cw mini da ya saka suit ko manyan kaya wanne ya fi? Ni kuma na ce ya saka manyan kaya zai fi ƙwarjini. Sai ya ce shima haka ya ce amma Gimbiya ta ce suit zai saka har ta siya masa ma ni kuma jin haka ya sa na ce duk wanda ya yi masa ya saka zai yi kyau tun da da man shi ɗin mai kyau ne. Sai ya ce kawai shi dai zai saka manyan kaya. Ya nuna min wata dakakkiyar gezner fara da ya siya ya ba da ɗinki har da babban riga. Sannan ya siya cover shoe baki mai kyau da hula dara sai agogon fata mai tsada. Ranar dai Yallaɓai sai wanda ya gan shi kawai amma kyau ne zai yi har sai ya gaji da kyau.
Tuni status ya ɗauka yan gidan su kaf sun ɗora katin gayyatan suna ta ya shi murna. Nima na dora har Samira ta yi min magana ko mata na zuwa na ce mata e amma mata gida ne, nan take ta ce mini za ta yi ma Hauwa magana wata ƙila su shigo fatan alheri. Su Ya Hamza duk na tura musu sai aka ci sa'a a satin zai shigo Kano ya ba ni tabbacin zai je Ya Auwal dai a waya ya kira Yallaɓai ya yi masa murna. Amma Ya Muntari da Ya Abubakar da Datti duk sun ce za su je. Sai jin daɗi nake yi domin ni kaɗai na san dararen da Yallaɓai ya ɓata bai samu barci ba saboda zuwan wannan ranar mai ɗimɓin tarihi.
****.
.
RANAR TARO.
10 March. 2021.
Lahadi.
Ko da ba a gidana Yallaɓai ya kwana ba amma ya biyo ta gidana ya yi mini sallama ni da yara muka rumgume shi domin ta ya shi murna a wannan rana mai matukar muhimmamci a gare shi.
Kun ga Yallaɓai? Cancaɗi ni kaina sai da na saki baki da hanci ina kallon shi. Domin ya dawo min wani ɗan saurayi ɗan shekara talatin. Da man ya na son fararen kaya ko don ya san suna yi masa kyau ne oho? Har da wani farin gilashi su Yallaɓai manya an fito sharr. Tare da Kawu Abba shima ya sha Babban riga. Ya kuma kyauta domin da Marwa ya taho mini duk da tana ta fama da laulayin ciki. Tariq na hanya bai riga ya iso ba. Hadda su Khalipa su kan yan kanti suka saka da su za a je ni kam ni da ƴa'ƴana ko ba mu je ba mun cakare a gida har ko da Yumna na mata gayu kuma itama sai da Yallaɓai ya ɗauke ta na ce murna ta ke taya shi tun da tana jin muryansa ta fara harba ƙafafu.
Sun fita gidana tara da wani abu ba a fara taron ba sai sha ɗaya na safe. Har sarkin Rano ya zo da Tafidan Rano kanin mahaifin Gimbiya. Ta waya muke ganin komai live Adnan ke yi da wayarsa ya na turawa a group ɗin gidan su. Irin su Musbahu suna ta hotuna suna ɗorawa. Sun gayyaci yan jaridu da masu Video da hotuna. Muna gida amma kamar mu yi tsuntsuwa mu gan mu a wajen Baby sai tsallen murna take yi, su Ma'u da Rahila ne suka zo mini sai su Munnir. Hauwa ta ma dafa shinkafar jalop mai nama muka ci muka sha da lemu. Suma duka mazajensu na can wajen taron
Kafin a fara Yallaɓai ya turo min saƙo. Saƙon da na maimaita shi sama da sau goma saboda daɗin kalaman na shi. saƙon da ya samu wajem zama na musamman a ƙasan zuciyata.
"Sadiya ta ki sani kome yau na zama Nene ce sila tun da ita ce ta haife ni. Amma ina so ki sani bayan ita ke ce mace ta farko da kika bani ƙwarin gwiwa. Na gode Sadiya ta. Adnan ya nuna min abin da kika yi mini. Ina rubuta miki wannan saƙon cike da godiya a bakina. Zuciyata cike da ƙaunarki. Hawayen farincikin kasancewarki matata sun tarun mini a ƙwarmin idanuwana."
Nima sai na ji taruwan ƙwalla kafin na fita daga shauƙin da na shiga wani saƙon na shi ya sake shigo mini.
"A yau a wannan rana mai muhimmaci nake so na faɗa miki ni ke ce abu mafi muhimmanci da na mallaka a rayuwata. Na gode Abar ƙaunata. Yusuf na ƙaunarki. Ki tuna haka Halimatussadiya."
Sai kawai na samu kaina da ƙwalla, har sai da na saka hannu na share Allah ya sa ni kaɗai ne a ciki daga ni sai Yumna. Ita na ja na rungume ni ina jin wani irin shauƙi na motsawa daga ƙasan zuciyata.
An fara taro cikin nasara bayan an nuno hoton Yallaɓai ya yanka igiyar nan da almaka shi, tare da addu'oi. Sannan a ka shiga ciki da a ka ƙawata shi da kujeru da kanofi.
Manyan baki sun yi jawabai sosai na godiya da jinjina da burgewa. Kawu ya ba da labarin Yallaɓai. Tariq ya ƙara da irin gwagwarmayan da ya sha kafin ya kawo yau. Sannan ya yi amfani da haka wajen zaburar da matasa domin su nemi na kansu. Ya faɗi har tarin alherin da Yallaɓai ya cimma a shekaru ashirin da wani abu . Mafi rinjayen ciki samar da matasa aiki daga karƙashinsa sannan da gina wannan ma'aikatan bayan ya fara da kama hayan ƙaramin shago sai gashi yau ya mallaki ƙaton waje da sunan mallakin shi. Ya Usman ya yi jawabi a matsayin babba Yaya.
"Yusuf ƙanina ne amma zan iya cewa ya fini jajircewa. Ni gidan soja kawai na sani amma shi ya san gwagwamarya. Ya san zane ya san gine gine, ya san ya ɗau kankare akan sa. Sanadin shi matasa da dama sun samu aikin yi. Ciki har da ƙanin mu dake aiki a ƙarkashin sa. Abin da zan ce shi ne Yusuf is a good Exmples ga matansa mu. Ku tashi ku nema. Ku jajirce in kuka gwada kuka faɗi ku sake miƙewa ku cigaba da tafiya. Watan wata rana za mu iya samun kamar Yusuf ko ma waɗanda suka zarta shi da samun ɗaukaka sanadin jajircewarsa. Congratulations My Bro. Allah Ubangiji ya sa nan da shekaru goma duka arewa kowacce state kana da reshe Amin."
Sai tafi raf! Mu kan mu mun zagaye waya muna kallo kamar mu yi hawaye. Mimisco ce ta ɗora jawabin a status har mijinta ma ya je shima ya yi jawabi, daga ƙarshe ne Yallaɓai ya yi jawabinsa. Da farko ya yi sallama sannan ya yi salati ga Annabi(SAW) sannan ya gangaro wajen gode ma iyayen shi. Tare da addu'an Allah ya jiƙan Marigayi Muhammad Inuwa.
Mace ta farko bayan Nene ni ce wacce Yallaɓai ya gode mawa. Wallahi ina kallo ina hawaye ban sani ba su Munnira na ta minI sowa amma ni ina hawayen farinciki.
"Zan miƙa sakon godiyata zuwa ga Matata Uwargidana. Sadiya Sulaiman Yashe(Mrs Yusuf Muhamma Inuwa) bayan iyayena da ƴan uwana. Ita ce macen da ta yi gwagwamaryan rayuwa da ni cikin samu da rashi. Sadiya ta kasance wata mace mai hikima da baiwa. Wannan sunan kamfanin idea ɗin ta ne, duk da burina ne amma da shawaranta yau na kai ga gaci. Sunan da ke jikin wannan kamfanin ma nata ne. Ita ta samar da shi. HM TAFIDA ba mallakina ba ne ni kaɗai. Namu ne ni da ita da ƴaƴanmu. Ni zan kasance Md a idanuwanku amma asalin mai juya kujeran tana gida. Miss Sadiya Yusuf Muhammad ina miki jinjina ina kuma ta ya ki murna. Da girmamawa ina mai sanar dake MUN YI NASARA"
Ya faɗa sannan ya ɗaga hannu sai ihu da tafi. Daga nan Vedio ya yanke tuni na ɗauka na saka a status ɗina na ma kasa magana sai emojin kuka na saka. Munnira faɗi take yi" Wallahi gaskiya ya fada. Da bai ambace ki ba da ya yi butulci."
Ni dai ina ta sharan ƙwallar farinciki. Sauran jawabin na shi godiya ne ga amininsa guda biyu Tariq da kawu sai ƴan uwan shi gabaɗaya sannan ya jinjina ma Musabahu domin da jajircewan shi suka samu nasara. Daga ƙarshe ya yi godiya ga matasan da ke aiki a ƙarkashinsa domin ya ce ba domin su ba, da bai yi nasara a yau ba a ƙarshen ƙarshen dai ya kira sunanayen su Jidda da su Khalipa da Gimbiya ya gode musu a cewarsa suma suna cikin labarin nasarar shi a wannan ranar. Kafin taron ya tashi sai da matasan da yake aiki da su bangaren gine gine suka bashi award na takarda da gilashi sannan aka tashi taron za a ci abinci a raba gift shike nan taro ya tashi.
Ni Yallaɓai ya gama mini komai. Na maimaita kallon jawabin sa ban san iyaka ba. Ya Hamza sai da ya kira ni ina ɗauka ya ce" To Miss Sadiya yau ta sha godiya wajen Mr. Yusuf. Ya dai ce ke ce Md shi acting Md ne."
Sai kawai na hau dariya shima ya na taya ni.
Nan ya fara mini nasiha ya na fadin" Kin yi abu mai kyau ko Alhajinmu in ya ji zai ya ba miki kin tsaya ma mijinki. Da daɗi ba daɗi yau kun yi nasara. Congratulatons"
Saƙonni sai da suka yi mini yawa nima murna ake taya ni. Tabbas ni ma na samu nasara. Datti daga wajen taro gidana ya taho ya na ta sake ba ni labari. Shima ya taho da jakarsa na gift faɗi yake yi" Ya Sadiya Yallaɓai ya gama tashin kaina da jawabin sa. Danƙari."
Kowa sai ya ce abin ya burgeshi ba kamar wasu mazan butulu masu manta alheri ba. Ni kam Yallaɓai bai manta da ni ba ranar ba a gidana yake ba amma da daddare bayan sun sallami baki sai da ya zo gidana lokacin duk an watse daga ni sai yara. Marwa ma tun dazu Kawu ya zo ya ɗauketa.
Baby ta yi barci Jidda ce ta ce sai ta jira Abban ta. Ai ko muna jin buɗe get ni da ita muka fita. Ni saboda zumuɗi da sauri a falo na baro Yunma. Sai ga ni, ni da Jidda muna rige rigen faɗa ma Yallaɓai. Ture Jidda ya yi yana faɗin" Jidda ya za ki ture mini mata kuma"
Tana dariyan farinciki ta ce" Congratulations Abba. You make us proud Today."
Sai ya sake ni ya rugumeta sannan ya ɗago ya dafa kafaɗunta yana faɗin.
"Thank you Fav Daughter."
Ni ko sai da na sumbaci gefe kumatunsa sannan na ce" Da ikon Allah ka fara hawa matakin nasara kenan."
"Amin My Sady."
Ya faɗa ya na mini mirmishi, ya shiga gidan amma ruwa kawai ya sha ya tafi bayan na ce gobe ni zan ba shi na wa gift ɗin.
"Mai daɗi ko Sadiya ta?
"Sosai ma. Ya fi mazan ƙwaila."
"Ina godiya Hajiya ta."
Muka raka shi har haraba muna ɗaga masa hannu.
Na cika alƙwari domin washe gari da ya dawo gidana ban nuna masa gajiyawa ta ba sosai na saki jiki muka yi ma ruwa tas. Ƙarshen shi ne kawai ba mu gani ba. Tabbas kwans biyun da ya yi a gidana na saka su a cikin tarihin rayuwar auran mu.
Ni ban sani ba ashe kalaman da Yallaɓai ya yi a kaina Gimbiya kishi ya kusa kashe ta a cewarta ita bai ambaceta ba sai daga ƙarshe. Nima Sameena ta kira ni tana mini tsegumi ta ce a group ɗin su na gida Gimbiyar ta yi maganar da aka turo jawabin ta ce ai ita saboda haushi ba ta ma gama saurara ba. Na yi dariya na ce to me ta ke tsammani? Ya ya yabe ta sama da ni? To ta jira tukunna da sauran lokaci.
Nima na samu gift ɗin tun da ya yi saura kaf yan gidanmu sai da na ba su, na ba ma Hauwa da Munnira da Mubeena har Ya Auwal na ba ma Datti na shi ya kai mishi. Amina kuma ta kira ni a waya ta ce sai na ijiye mata mug ɗin da Memo na ce an gama. Na ɗaga akwatina na saka mata. Sauran kuma na ba ma su Jidda nima na ijiye ko domin tarihi.
Hankula sun kwanta. Tun da an yi taro lafiya an gama lafiya. Ni kan sai da na hi sati ina saka jawabin Yallaɓai a status ɗina, da hotuna kar ku ga laifina yaɓo na aka yi, dole na yi ta sakawa ina jin dadi. Na kuma san na tura ma Gimbiya haushi. Ya Auwal har sai da ya gaji ya ce sun gaji da gani har sun haddace. Na ce su cigaba da gani suna haddacewa sai an yi wata zan dai na sakawa. Kuma haka aka yi ko bai kai wata ba an kusa. Tuni aiki ya kamkama a sabon kamfani sai hamdala kuma kamar an buɗe a sa'a kwangololi suna ta zuwa saman tuberin Yallaɓai. Abin sai godiya kawai.
Fara aikin babban kamfanin Yallaɓai da wattani biyu muka fara azumin watan ramadana. Kafin azumin Gimbiya ta yaye Anwar a ka kai shi can Rano. Yallaɓai na ji ya na faɗa a nan na ji tun da ba ta faɗa mini ba. Mun yi azumi ashirin da tara mun yi salla a satin salla Jidda suka zana Jamb kuma cikin ikon Allah ta samu 220. Ta cancanta domin ba ta da wasa. Ba daɗewa kuma suka fara WAEC su Jidda an zama yan mata za ta yi graduation zai zama tana da shekara sha takwas cikin na sha tara. Baby kuma za ta shiga Jss2 tana da shekara sha biyu kenan. Na roki Yallaɓai da cewa ya bari na haɗa ma Jidda Waliman gama makaranta har yanzu dai bai ce komai ba. Ya ce sai ya yi tunani. Na lura tun da Yallabai ya koma babban ma'aikata ba ya son kashe kuɗi. Kuma sai ya kashe domin walima zan shirya ma Jidda in ta gama jarabawa kuma da kudinsa za a yi komai in sha Allahu.
*Janafty**TKGB3K011*
Ganin hankula sun kwanta ya sa ranar wata laraba Yallaɓai na gidana muna falon shi bayan mun gama ƙaryawa. Yumna na hannun shi yana yi mata wasa tana ta bangala masa dariyan su na yara.
"Yallaɓai."
"Uhm"
Ya amsa mini hankalin shi na wajen Yumna ɗaga ta sama yake yi yana cillata tana dariya. Yallaɓai ba ya ba ni mamaki in dai akan yara ne, haka yake zai iya ɓata lokacin sa mai tsawo shi da yaran shi ba shi da wannan damuwan in dai yana gidan to Yumna na hannun shi su yi ta kara kaina a kanta shi da Baby.
"Ya maganar koya mini mota? Kyan dai alƙwari cikawa. Yanzu na haihu ba ni da ciki"
Na faɗa ina kallon shi ina daga kujera mai zaman mutum ɗaya shi kuma yana zaune a saman mai zaman mutum uku ne shi da Yumna.
Kallona ya yi kafin ya ce" Ko ba ki da ciki ai kina da goyo ko?
"Goyo kuma? Yumna ce za ta hana ni koyon mota Yallaɓai?
Na faɗa ina cikin mamakin sa, har ina ɗan haɗe rai domin sai na ga kamar ba ya so kwata kwata ya koya mini motar nan to bai isa ba in ba zai koya mini ba ya ba ni dama na yi ma Musbahu ko Adnan magana su koya mini.
"Ki bari ta ƙara wayau zuwa ki yaye ta mana. Amma ai yanzu ba ki da natsuwar koyon tuki ko Yumna?
Ya faɗa yana kallonta sannan ya nuno mata ni yana faɗin"ki yi ma Umman ki bore wai za ta koyi tuki ba ki yi wayau ba! Ki ce baki yarda ba."
Kamar tana ji sai ko ta fara wuntsila kafafunta tana wani abu irin na su na jarirai da suke cikin wattanin haihuwa ba su shekara ba.
"Yauwa. Yumna ma ta ce ba ta amince ba sai ta girma."
"Tabɗijam! Ai lokacin ma na ƙware a tuki har Zaria ma ina tuƙa kaina