Turken Gida Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   35 / 55

102K to 105K   out of 163.1K words

"
"Ba gidan ki za ki koma ba? In kin je can sai ki yi. Maza tashi kafin Alhaji ya ji ya leƙo da kansa kin san halin shi."
Ba ni da yadda zan yi haka nan na yanke ba ma Yumna Nono Gwaggo ta karɓeta tana yi mata wasa.

Kayana na je na saka na ɗauko hijabina na saka. Baby tuni ta fita wajen babanta Marwa na yi ma magana ko yanzu za su wuce ta ce zai kaita gida ta gai da Ya Aina. Amma kafin su wuce za ta biyo gidan tun da akwai kayanta a can na ce mata toh. Na karɓi Yumna hannun Gwaggo na shiga yi ma Alhajin mu sallama.

"Allah ya yi miki albarka. Mijinki ya yi ta bani haƙuri sharrin shedan ne Allah ya tsare na gaba.'

Na ce Amin sannan ya yi ma Yumna wasa, har yana ba ta 500 ya ce kuɗin zance ne. Na karɓan mata ina masa godiya. Koda na fita kofar gida suna jikin motar Yallaɓai shi da Kawu suna mgana amma kowannen su da motar shi ya zo. Baby na cikin mota da alamu ni suke jira.

Ba domin Kawu ba wallahi shigewata mota zan yi amma saboda shi na tsaya ina gaishe shi.

"Lafiya lau Surukata. Ashe kuma abin da wannann mara mutumcin ya yi miki kenan?

Sai na kasa magana amma na kauda kaina bana son ma mu haɗa ido da Yallaɓai.

"Ai da kin kirani wallahi sai na shigar miki. Amma ko yanzu na yi mata faɗa na ce kuma ya gode ma Allah ma ya samu surukai na gari in wani ne Alhaji ai ko kallon sa ba zai yi ba. Maimakon haka ma sai ya karrama mu, muna bashi haƙuri muma yana ba mu."

Nan ma na yi shuru kaina na kasa, Yumna ce ma ke miƙa ma Yallabai hannu tana faɗin Aba da sauri na janyeta ina ƙara haɗe raina.

"Ki yi haƙuri kin ji ko? Fushi ne da shedan suka yi tasri a kan shi amma ya tuba ya ce ba zai ƙara ba."

Sai na ɗan kalle shi ta gefen ido kansa na ƙasa yana ɗan mirmishi kamar ba shi ne ya yi mini wulakanci ba jiya.

"Ba komai. Allah ya kyauta na gaba.'

Suka amsa da Amin gabaɗaya. Shi ya buɗe mini gaban mota na ƙi shiga na faɗa baya kusa da Baby. Mun tafi muka bar Kawu anan amma ya ce za su biyo kafin su wuce. Muna tafe a hanya yana ta kallona ta madubin gaban mota ni ko na yi cuɗun ciɗun da fuska bai ga fuskar ma wata mgana ba.
Haka muka isa gida ni ko jiran shi ban yi ba na yi wuce wata cikin gida. Ya biyo ni har ɗaki yana so ya yi mini magana na bar masa yarsa nan saman gado na faɗa tiolet na banko masa ƙofa ai ban fito ba sai da na ji ƙaran jan get alamin ya fita sannan na fito ina jan tsaki.

Sai da na yi wanka sannan na duba gidan. Kitchen dai ya sha kyau Baby na saka ta gyara shi ta goge da falon su. Falon Yallaɓai ko ta kan shi ban bi ba girki ma doya na ce Baby ta fre mana ta sulala mu ci da mai da yaji sai bayan azhar na duba wayata. Hauwa da Munnira sun kikkirani da Rahila sai Suwaiba.
Munnira na fara kira ba ta ɗauka ba sai na kira Hauwa. Ita ke faɗa mini Mutaƙka ya yi fata fata jiya akan abin da ya faru, ni tsabar haushi ban san lokacin da na ce.

"Ku fita hanyata ku fara aminta da Gimbiya shine faɗan na su."

"Wani irin magaana ne wannan? Ai ba su isa ba. Shima ai na faɗa masa ba zai yuyu ba sai ya ce wai shi bai ne na rabu dake ba amma na daina wulakanta Gimbiya saboda ke Ya Tafida ya ce ba ya jin daɗin haka."

"Kar Allah ya sa ya ji daɗin mana.'

Na faɗa cikin ɓacin rai, ban faɗa mata na je gida har na kwana ba amma na faɗa mun hau ramar da ba ta da ganye mun fado a jiya da daddare ni da Yallaɓai.

"Kai Gimbiya ba ta ji daɗi ba. Ta haɗa karya da gaskiya.'

"Daga shi har ita in sun fasa sun raina Ubangijin su.'

Sai da na faɗa sannan na rufe baki ina waige-waige ni kaɗai sai da na yi dariya Hauwa ma sai da ta dara."

"Haushi take ji kuna tare da ni, ba ma ita ba har su Anty Bahijja ma. Kuma sai dai su mutu wallahi.'

Hauwa ta ce kwarai mun daɗe muna mgana kiran wayar Munnira ne ya katse mu. Ta ce mini Ashe ta koma tun safe,Marwa fa? Na ce mijinta ya zo ɗaukanta ta je gida ta dawo.

Munnira zage-zage ta dinga yi tana faɗa mimi hauka hauka ta yi ma Nasir jiya ya zo yana ce mata ita ke hassada fitina tsakanin matan Yaya Tafida."
"Ai ko jiya ya ga tijara. Na fashe kamar tayagas faaa faaa. Haka nake yi ta in da na ke shiga ba ta nan nake fita ba. Ai daga karshe sai ya dawo yana bani haƙuri."

Ina dariya na ce" Duk haka suke suna da son kan su. Amma ba su da laifi abin da Yallaɓai ya faɗa musu. Za a ce ke ce ke da fitina ya ja miki kunne."
"To ai ba shi kaɗai ba hadda su Anty Bahijja, a group ɗin gidan su je ki gani sai abin da suka manta ba su fada mana ba, na fara ma yar da martani Mimisco ta kira ni ta ce kar na sake magama shi ya sa na yi shuru."

"Au kuma?

"Wallahi kunna data ki sha kallo."

Ba musu na yanke wayar na kunna data. Sai da na bari saƙonnin duk sun gama shigowa a group din gidan su Yallabai Iyalan Marigayi Muhammad Inuwa02. Mata ne kaɗao sai mi surukai a ciki mazan suna can na farkon.
An yi ta cin kasuwa akan mu har Yayar Gimbiya da ba ta zo ma sunan ba, tana ta mganar cewa ba za su yarda da duka ba ko su Anty Bahijja su ɗau mataki ko su su ɗauka da kan su.

Ita ko yar kanzagi Anty Bahijja ta ce ai Tafida tuni ya ɗauka mataki dukkanmu an ja mana kunne. Anty Maimuna ta fito ta ce ba lafin kowa ba ne sai ni Munnira ta ce ko gobe yarinya ta sake mata rashin kunya sai ta mata dukan tsiya. Anty Maimuna ta ce ta yi mata rashin kunya Nasir zai ji, group ya koma faɗi in faɗa har sun jj labarin abin da ya faru. A cewar Jamila ta ce Gimbiya da bakinta tafaɗa mata ni da su Munnira taron dangin muka yi mata ita da yan uwanta Suwaiba ta yi taggin ta ce ƙarya ne tana wajen ta yi Vn wajen mimtina sha tana bayanin abin da ya faru ni ina fara ji ma haushi ya sa na kashe gabaɗaya.

An yi manganganu har Ant Zabba ta tanka ta ce in dai har gida muka je muka dake su ba mu kyauta ba.. amma ya kamata a yi bincike domim a samu sulhu. Mimisco ta tawatar ganin abin na nemen ya zama rigima ta ce kar wanda ya ƙara mgana. Ba ni da damar ma yar da martani shi ya sa na yi shuru.
Kafin ma na kashe datan sai ga kiran Mimisco na ɗauka muka gaisa sannan ta tambayeni abin da ya faru duk na zayyane mata, ta ce gaskiya suma ba su kyauta amma Munmira ma ba ta kyauta da tun farko ba ta tanka su ba. Ta yi mini faɗa sosai ta ce bai kamata ina barin ƙananun abubuwa suna shan gabana ba. Na yi gaba fa sai dai a biyo bayana. Na ji daɗin magana da ita shi ya sa duk cikin yayyen Yallaɓai Mimisco na dabam ce a wajena. Ta ce ko an buɗe gidan kar na tanka ma kowa na yi shuru kawai itama amsa ce. Nan take na yi mata alƙawarin ba zan yi magana ba ta yi mini godiya muka yi sallama.

Mun gama wayar kenan ina shirin ajiyeta bayan na kashe data Jidda ta kira ni kwana biyu ba mu gaisa.
Bayan gaisuwa da tambayan makaranta ta kira sunana.

"Umma."

"Na'am Jidda."

"Me ya faru tsakanin ki da Abba ne?

Cikin mamaki na ce" Me kika gani?

"To ya kira ni yanzu ba daɗewa yana faɗa mini ya yi miki laifi kina fushi da shi na kira ki na baki haƙuri"

"In ji baban na ki?

"E Umma. Don Allah ki yi masa haƙuri ba ki ji muryan Abba ba duk ya damu."

Sai na yi mirmishi kafin na ce" Bayan nan bai faɗa miki komai ba? Bai faɗa miki laifin da ya yi ba?

Tana dariya ta ce."Umma ba sai ya faɗa mini ni dai kawai ya ce kina fushi da shi na kira ki na ce ki yafe masa ki kula shi."

"To."

"Don Allah Umma."

"Na ce to ko?

Na faɗa a ɗan hasale.

"To ai Umma na san halin ki ne yanzu sai ki fara gaba da shi, yana mgana kina yin banza da shi. Allah Abba abin tausayi ne fa Umma in dai a kan ki ne."

"Ƙaniyarki Jidda."

Na fada ina danne dariyata itama dariyan ta ke yi.

"Ke har kin san abin tausayi a kaina? Zan ci mutimcin ki fa"

"Wallahi Umma in ba ki yi masa mgana da ya ganki duk sai ya ruɗe"

"Sai anjuma Jidda"

Na faɗa mirmishi, jin tana yi mini shaƙiyanci.

"Umma a duba mini my Abbana don Allah."

Kawai sai na yi tsaki na kashe wayar, har ta saka ni mirmishi wai Yallabai ne da kiran Jidda yana cewa ta ba ni haƙuri, ba ma wannan ba yaran mu fa yanzu duk motsin mu suna ankare damu  ji dai Jidda da na ke ganinta shuru shuru ashe tana ankare da komai. Wayar da muka yi da ita sai na ji zuciyata ya ɗan sauka
Ina cikin ɗaki Marwa ta zo, ba ta wani daɗe ba amma ssi da na zuba mata doya ta tafin ma Kawu da shi tun da yana so amma ya ce ba za su tsaya ba akwatinta ta ɗauka na raka ta har haraba na ba ma Afra 1k na ce ita 500 Abadalla ma haka tana ta mini godiya. Kawu daman a can waje ya yi parking ɗin motar shi.

Yallaɓai na neman shiri da wuri ya dawo ana yin sallar mangariba ya siyo mini fura da kayan marmari ban sake masa gwiwa ba amma dai na karɓa kadahan kadahan. Lokacin na yi wanka abinci kuma daman farar shinkafa na dafa da daddaren ina da sauran miya, saboda na san muna faɗa sai na ji gayu na tsuke cikin riga da wando ina tafe mazaunena suna kaɗawa. Ai da ƙyar ya fita sallar isha'i yana dawowa ina ciki Yumna na wajen Baby ya ritsani yakulle kofa.

"Sadiya so kike yi na haukace a kan ki ko?

Ina tssye lokaci ɗaya ina ninke darduman da na idar da salla a kanta na ce" Sai dai in matarka ce za ta haukata ka. Amma ni Sadiya ai ban kai wannan matsayin ba.'
Ban san ya ƙariso gabana ba sai da na ji ya ruƙumƙume ni daga tsayen yana mai faɗin" Ki yi haƙuri ki yafe mini na yi kuskuren da na zo na yi miki magana cikin fushi. Am sorry please."

Na yi banza da shi, amma dai ban yi ƙoƙarin kwace jikina ba. Ya juyo da ni muna kallon juna ya saka hannu ya zare mini hijabin jikina yana bina da wani kallo duk ban yi masa mgana ba.

"Kike cewa ba ki isa ba Sadiya ta? To wai wata kuma isar kike so na nuna miki da za ki san ni a wajena kin isa kin iss. Ke ɗin isa ce kafin ma isar ta iso."

A tsume na kalle shi kafin na ce" ai ka gama nuna mini isata tun da jiya ka ce na bar maka gida.'
Sai kawai ya riƙo hannuna duka buyin cikin na shi ya matse yan faɗin" Na rantse da wanda raina ke hannun shi. Lokacin da kika ce in na ce ki tafi za ki tafi na faɗa ne domin na ga zaki iya tafiya ki bar ni Sadiya? Sai na ga wai kin tafi? Lokacin da kika fita wallahi ji na yi kaina ya yi wani girimgirim Sadiya na shiga tashin hankali. Me ya sa za ki yi mini irin wannan gatsen fisabillahi"?

"Gatsen me? Kai ka ce na tafi ba za ka hana ni ba."

"Na gwada ne, na gwada ki na ɗauka kema a wasa kika faɗa "

Kallon sa na yi ina wata dariya kafin na ce" Wasa? Ni ka ga wasa a magana ne."
"Wallahi ban gani ba. Kin ba ni tabbaci jiya. Ni dai kar ki ƙara yi mini irin haka bana so. Sai ki saka ai zuciyata ta buga."
Na buɗe baki zan yi magana ya haɗe bakin mu waje ɗaya yana tallafo kaina na yi masa tsaye ƙiƙam shi ya sa sumbatar ba ta yi armashi ba.

"Ki tallafe ni ma Sadiya ta."

Ya faɗa cikin karyewan sauti a yanayin shi kaɗai da na kalla na san tallafan yake so.

"Me zan maka? Yara na falo fa?

Ƙamƙameni ya yi yana faɗin" Na kulle ɗakin ba za su shigo ba "
Ganin ina kallon shi ya sa kamar zai yi kuka ya marairaice mini yana faɗin" Don Allah I need you sosai."
Sai na kasa musa massa ya ja na ya yi zuwa kan gado yana mai ƙamkame hannuwana. Duk yadda na so na basar da shi na kasa Yusuf ne fa?  Yusuf ɗin da na sani tun yana matashin sa. Sai kawai nima na tallabe shi, na saki jiki na ba shi abin da yake so.

Bayam mun natsa tun kafin mu kai ga wanka ina saman ƙirjinsa ya rumgumeni yana faɗin" Ki yi haƙurin kin ji ko? Ke mai hakuri ce ki ƙara akan na baya. Mimisco ta kira ni , Suwaiba ma duk sun sake yi mini bayani na gamsu. Itama Daughter zan yi mata faɗa kowa ya yi hakuri domin a zauna lafiya kin ji"
Na yi kamar ban ji ba sai da ya ƙara faɗn" Kin ji ko?

"Na ji."

"Ba ki yafe mini ba ko?

"Uhm"

Sai ya sumbaci goshina kafin ya ce.

" Ina kaunar ki."

"Ina sonka Yusuf ɗina."

Na faɗa ina sake rumgumoshi kamar na saka shi a aljanma haka ya ƙamƙameni yana faɗin

"Na gode Abar ƙaunata Ubangiji ya bar mu tare har mutuwa. Mutuwan ma ta ɗauke mu rana ɗaya"
Ina mirmishi na amsa da Amin.
Mun so mu shagala sai muka ji kukan Yumna a kofar ɗaki tana kiran sunana.

Uma
"Uma.

Ni da Yallaɓai muka kalli juna muka kwashe da dariyan nishaɗi.

*Janafty**TKGB3016*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX


Assalamu Alaikum Fanmily, mun fara saro muku kayan Kitchen ko wani nau'i, duk abin da kuke bukata na gyaran Kitchen ɗin Amarya da uwargida duk za ku same su a JANAFTY KITCHEN ITEMS, kayan mu masu kyau ne da inganci sannan za ku same su akan rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina a falin Nigerian nan. Domin karin bayani ku tuntuɓe mu ta waɗannan lambobin kamar haka.
09069067488.
+234 706 234 9732

Muna maraba da masu siya ɗaya ko sari🥰

Shike nan faɗan mu ya ƙare ni da Yallaɓai amma lokaci bayan lokacin in muna zaune da ya yi magana zan kalle shi na ce" Ni ai Yallaɓai ka ga ƙarar mini da ruwan kaina. Ni da ka kalla ido cikin ido ka ce mini ina da mugun nufi akan matarka. Wallahi na kasa mantawa da wannan maganar"
In na faɗi haka sai ya marairaice yana lallashina shi a dole sai na manta duk kalaman da ya yi amfani da su a kaina.

"Me ya sa ba ki mantuwa ne Sadiya? Maganganun da na faɗa cikin fushi kema kin san ba a son raina ba ne. In ma na ce kina da mugun nufi ai kaina na yi mawa. Tun da tsawon shekarun da muke tare da ke ban amfana da komai ba sai alheri. Ki yi haƙuri don Allah ki daina dawo da maganar da ta wuce."
In ya faɗi haka sai na tura masa baki na ce" Uhm, ai ka san da haka ka manta ka yi ta manganganu."

"Ki yi mini afuwa ki yafe mini. Halin ɗan adam ne na ajizanci."

  Haka ya kan faɗi in na ta da maganar kuma ba wai ban yafe ba ne na yafe amma na kasa mantawa in na ga yana yi mini rawam ƙafa sai na kalle shi na tuna masa maganar. Tun yana lallashi da sake ban hakuri watarana ma shuru yake yi mini amma ya kan ce Allah na sama yana gani kuskure ne ya yi kuma ba wanda ya wuce ya yi kuskure.
Har cewa ya yi sharrin sheɗan ne ranar ina ta tsintsira dariya shi kuma sai ya yi fuska yana hararata.

  Kwana biyu kamar na manta da maganar kawai ranar yana gidana da daddare muna falon muna kallo, Yumna ta yi barci tana ɗakin su Baby, sai za mu kwanta zan je na ɗaukota.
Wani American film muke kallo daman sune fina finan Yallaɓai ni kwata kwata ba sa burgeni sabo da shi ne ma na ke kallo, in ya ga na yi shuru sai ya yi ta mini bayani iyakata Umh da Hmm to ni bai san ba na son wannan bayanin ba, da zai ƙyale ni da na ji daɗi amma ba zai gane ba ni kuma ba na son na kushe ƙokarinsa. Yana cikin ba ni labarin film din ne ya gangaro kan karatu shi ne ma yake faɗa mini ya nemi gurbin PHD a Universty of Ibadan har ya samu.

Baki na buɗe kafin na kalle shi ina faɗin" Lalle Yallaɓai can Ibadan ɗin za ka koma?
"A'a ai online ne karatun sai in za a yi jarabawa zan je."
"Allah ya ba da sa'a."
Ya amsa da Amin Amin.
"Saura ni Yallaɓai maganar komawata master"
"Ina za ki je da Yumna? Ki bari ki yayeta sai ki koma."

Na kalli Yallabai shima ya kalleni, ai yadda ya ga ina kallon shi ne ya sa ya yi dariya kafin ya ce" Wallahi da gaske na ke yi. Zan hana ki komawa makaranta ne? Ko Daughter na faɗa mata in har za ta koma ni ba ni da damuwa."
Shuru kawai na yi masa na ma kasa mgana ina zencen makarantana yana kawo mini zencen wata matar shi, tsaki

35 / 55