Turken Gida Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   32 / 55

93K to 96K   out of 163.1K words

ta zo da safe ta je gida ta dawo.

"E mana da gayya ne. Tawagan uwargida ne ta bakin su, to wallahi mata ba ta isa ta watsa mana taro ba sai dai mu watse ta"

"Ke ai kin yi kaɗan ki watse mu Maryama sai dai ke mu watse ki wallahi. "

Ashe ta shige tsakanin Munnira da Maryama tana faɗin haka.

"Anty Munnira bar mini wannan faɗan koma gefe ki yi kallo"

Ta matsar da Munnira gefe tana nuna Maryama da yatsa kafin ta ce" Maryama karyan iskanci kike yi. Ni ce nan daidai da kugun ki wallahi "

Kawai sai ta saka hannu ta kabar da hannun Ashe tana faɗin" Ke Ashe kin sanni na san ki. Faɗan nan ba naki ba ne amma tun da kin shiga saboda yayarki Hauwa na ƙawar matar can mu zuba da ni da ke shege ka fasa."
Ta faɗa tana shan gaban Ashe har tana ture ta baya. Abu kamar wasa wasa ashe na gaske ne ni ina gefe rike da Yumna ina ta ma Munnira mganar su bari domin har da ita maryama na magana tana ma yar mata ita da Ashe har da Halima. Hauwa ma da wasu yan Rano suka je suna jan Ashe amma ta ce tun da rigima Maryama take so to ta tare shi ta same shi a wajen ta.

Gimbiya ma da ƴan'uwanta suna ta yi ma Maryam ɗin magana amma ba su ji ba.
Irin su Halima yan kan zagi suna faɗin daman da gayya ne.
Ga shi ba wasu manya Anty Bahijja ta tafi Anty Maimuna daman ba ta zo ba. Naja ce ta shiga tsakiyar su ta raba domin kaɗan ya rage afara kai ma juna duka.

"Miye haka? Daga suna na farinciki sai kuma ku ma yar mana da taro na tsiya.?
Ta faɗa cikin bacin rai kafin ta kalli Munnira tana faɗin" Anty Munni wannan ba girman ki ba ne don Allah ki ja tawagarki ku koma gefe domin a samu zaman lafiya."
Munnira kuma ta ce sun yi kaɗan daga abin arziki sai a nemi a ce sune suka zo da fitina.
Karaf wata ƙawar Gimbiya ta ce" Kune mana. Ina ruwan ki da waƙar da aka saka na uwargida ko na Amarya. Maganar gaskiya ku ne ba kwa son zaman lafiya. Ko kuma daman domin ku lalata mana suna kuka zo."

Munnira ta yi shewa ta dire da cewa an lalata su yi wani abun mana. Suwaiba na yi ma magana ita na samu ta jawo hannun Munnira amma sai Maryama ta ja tsiyar da cewa" Abin da ya kawo su kenan mana. Ga munafukar can ita ce ta turo su ita kuma ta koma gefe ta bakam kamar ba ta san me ke faruwa ba. Anty Gimbiya ki faɗa ma Kishiyarki ta ja tawagarta ta bar gidan nan kafin raina ya ɓaci a yi ɓaattaciya"

Maganar ta ba ni mamaki, sai kallo ya koma kaina duk sai na ji na muzanta. Naja ta zo gabana tana faɗin" Don Allah Anty Sadiya ki yi musu mgana su daina."
"Na yi musu magana mana Naja ko ba ki gani ba ne? Ni zan ce su zo suna ne su yi rigima da wata? Ku yi mini adalci mana"

"Ba wani adalci, ke ce munafukar da man tun da kika zo kika ga abubuwa sun tafi daidai kishin ki ya motsa ba haka aka so wai ƙanin miji yafi miji kyau."

Maryama ta faɗa tana wani girgiza jiki, sannan ta nuna Munnira da su Hauwa tana faɗin" Saboda baƙinciki sai ki ka yi amfani da waɗanan yan koren naki domin su wargazamana taro. To daga ke har su ba ku isa ba. Sai dai mu mu wargazaku mu kore ku tun da ba zaman lafiya ya kawo ku ba."

Baki na saki ina kallonta kafin in nuna kaina ina faɗin" Da ni kike?

"Akwai wata munnafukar ce bayan ke. Kin ga Anty Gimbiya na ta farar haihuwa. Bakin cikin ki ya kasa boyuwa sai da kika bayyana. To sai dai ki mutu aamma gida ya zama namu haka ma Yaya Tafidan shima namu ne sai mun ga dama mu ba da aron shi."

Maryama ta ba ni amsa ba tsoro ko tunanin wani. Kafafuwata suka fara rawa saboda ɓacin rai har ni na yi lalacewan da ƙanwar Gimbiya za ta ci zarafina. Yarinyar da ko Amina ta girme meta. Marwa ke rike ni tana cewa na yi haƙuri kar na tanka Suwaiba kuma tana yi ma Gimbiya mgana ta ja ma ƙanwarta kunne manganganunta suna tsauri da yawa.

"Me zan ce Anty Suwaiba? Ni ba zan hana ta ba domin duk abin da ta faɗa gsskiya. Taro na suka zo su watsa kuma sun ji daɗi.'

Kawai sai ta fashe da kuka munafunci, Munnira kuma ta fashe kawai sai ta dira kan ƙanwar Gimbiya ta shaƙo tana faɗin karya take yi, ai sune ma za su ce kishi ne ke damun yayarta domin duk wani abun da ta yi a wannan taron Sadiya ta kwaikwaya mu ba mu ce tana baƙin ciki ba sai mu ne za ki ce muna bakin ciki? To mun watse taron in ta isa sai ta yi wani abu ko ta ɗau mataki.
Ni ban san me ta buɗe baki ta faɗa ba, sai ji kawai na yi kaya kaya an fara kai duka Munnira ta fara kai ma Maryama Mari, ita kuma ta rama kawai sai suka fara dambe na ruɗe ina kiran sunan Munnira.

"Haba Munnira ba girman ki ba ne faɗa da wannan yarinyar."

Hauwa ta fada har da ni a masu rabo Yumna wajen Marwa na bar ta,ƴan'uwansu na Rano suna ta faɗa suka ce ga mota can ta dawo ɗaukan su za su wuce ba za su iya da masifa ba, da man yau za su koma, ita kuma Hadiza ganin ana faɗa da yayarta sai ta shiga suka yi ma Maryanma taron dangi suka kaita kasa. Gimbiya da Naja ganin haka suka shiga tsakani, wajen ƙokarin raba su Munnira idanuwanta ya rufe ta ture Gimbiya sai da ta faɗi gefe kusa da kujera hannunta ya bugu sai da ta yi ƙara. Kukanta ne ma ya raba faɗan sai kowa ya koma kanta Naja ta ɗaga ta irin kukan da Gimbiya ke yi ko dukanta aka yi sai kuka.

"Innalillahi shike nan sun karya ta burin su ya cika."

In ji wata cikin kawayen Gimbiyar.

"A kira Yaya Tafida mana shi sai ya zo ya ganin ma idanuwansa matarsa da Tawaganta za su nakasa masa mata."

In ji Halima, ni gabaɗaya kaina ya kulle ma, amma sai da na yi na Munnira masifa.

"Da wannan yarinyar ne zaki zo kina faɗa Munnira! Gaskiya wannan rashin sanin kimar kai ne "

Har ga Allah in na san abin da zai faru kenan da ban zo ba. Na ce su tattara mu tafi na je da niyyar na ba ma Gimbiya haƙuri ta juyar mini da kai tana faɗin" burin ki ya cika kin samu abin da kike so. Amma ki sani wallahi ba zan bar maganar nan haka ba."
Sai na ga ma tsayawa magana kamar ɓata bakina zan yi kawai sai na wuce. Har Ashe da Halima sai da na yi ma faɗa. Muka rankayo gabaɗaya zuwa waje muna fitowa Salisu na sauke Baby sai na ce kawai su juya. Motar na ce Munnira da Hadiza su shiga ya kai su gida ni kuma na ɗauko Hauwa da Ashe, tun da tace can za ta kwana sai Marwa da nima a gidana ta ce za ta kwana.
Suwaiba na cikin gidan mun bar,ta tana ban haƙuri.

"Munnira ta goga mini baƙin fanti a dangin Yallabai. Yanzu ko rantsuwa na yi ba za a yarda ba ni na saka Munnira dambe da ƙanwar Gimbiya ba "

Na faɗa cikin damuwa. Ni na san abin da na ke hange da man yaya lafiyan kura ballantana ta yi zawo. An ce ina baƙin ciki saboda ban haifi namiji ba kalaman sun yi mini dafi a zuciyata.

"Gaskiya ba ta kyauta ba. Haba ke kuma Ashe wallahi sai na faɗa ma Mama. Yanzu Sadiya kuka bar ma abin mgana."

Hauwa ta faɗa tana dungurar kan Ƙanwarta Ashe.
Tura baki ta yi kafin ta ce" Ni fa ban yi nadama ba. Ni Anty Munnira ma shigan sauri ta yi mini. Ni ce na so na yi ma Maryama bugun tsiya wallahi"

"Kuma bakin ki bai mutu ba ko?

Hauwa ta sake faɗa sai ta yi shuru ni kuma na ma kasa mgana hankalina ya tashi. Ba wai domin za a kira Yallaɓai ba sai domin ni ban je sunan nan da wata zuciya ba. Amma gashi abubuwa marasa daɗi sun faru Allah kaɗai ya san a yanayin da labarin nan zai fita.
Fuskata ba walwala na sauke su Hauwa a gida tana faɗa mini wai na kwantar da hankalina ko Yallaɓai ya zo zai fahimceni in na yi masa bayani kallonta kawai na yi. In har an so ya fahimcenin ba.

Mun koma gida muka iske Baby a ƙofar gida tana jiran mu ita da Salisun. Shi ya bude mini get na shiga da motata ciki.

"Umma me ya sa muka dawo! Ni ba zan je sunan Anty Gimbiyar ba ne?

Baby ta fara tare ni da mgana bayan na fito daga mota.

"Ni matsa ki ban waje kafin na gwabje ki."

Na faɗa a fusace saboda ta ba ni haushi. Marwa ce ta ja ta gefe tana yi mata mgana ni kuma na wuce cikin gida. A falon Yallaɓai na samu matsugunni ina mai da numfashi, gabaɗaya sai na tsargu kaina, wallahi ban ji daɗi ba ba kuma a son raina abin da ya faru ya faru ba. Ina zaune su Marwa suka shigo ko kallon su ban yi ba na tashi jaka da mayafi a hannu na shige ciki ina ji Yunma na kuka tana Uma na yi banza da ita.

Kwanciya na yi a kan gado kawai na rasa mafita. Tunanin maganar da zan harhaɗa na kare kaima a wajen Yallaɓai na ke yi amma da kamar wuya. Tun da a san tare nake da Munnira Allah ne kaɗai zai iya fitar da ni, na kasa haƙuri sai na ɗauki waya na kira wayar Yallaɓai bai ɗauka ba har sau uku a raina na ce shike nan wayar na hannuna sai ga kiran Suwaiba da sauri na ɗaga kiran

"Suwaiba sun kira Yallaɓan ne?

"E ya ce gashi nan a hanya zai zo. Ni dai na gaji da ba ma Gimbiya hakuri na baro gidan gani ni da Mubeena za mu samu adaidaita."

Ta amsa mini, sai na furzar da iskar bakina kafin na ce" Wallahi Suwaiba na kasa sukuni Allah ne kaɗai zai fidda ni a wannan sabgar."

"Gaskiya. Domin Gimbiya sai kuka take yi shima jaririn na kuka. Ina jin hannun nan da ta bugu ta yi gocewa ko targaɗe. Allah kaɗai ya san mganganun da za su faɗa masa in ya zo. Halima can na barta tana ta faɗin duk abin da ya faru da gayya ne ke ce kika shirya komai."

"Uhm"

Kawai na iya faɗa na kashe wayar. Daman ai ba ta kaunata tun marin da na yi mata na kore ta a gidana ni na san tana neman ranar ɗaukan fansa a wajena sai yau ta samu dama ai sai ta yi amfani da damarta da kyau da kyau.

Ina nan zaune Yallaɓai bai kirani ba har aka fara kiran sallar mangariba. Daga Marwa har Baby ba su neme ni ba nima ban nemi kowa ba. Tiolet na faɗa na yo alwala na so na ta yar da salla. Ina cikin yin salla na ji shigowar motar Yallaɓai da ƙaran buɗe get sai da gabana ya faɗi. Ya shigo falon farko ina tahiyar ƙarshe ina jin sa yana kirana suna da karfi daga ji ran shi a ɓace ya ke.

"Sadiya"

"Sadiya"

Ban zan iya sanin ko na ƙarishe salatin Annabi ba, na sallame salla, da hijabin jikina na fito daga bedroom na buɗe kofa na fito korido shima ya buɗe ta falo ya fito sai muka haɗe.

"Na'am. Ina salla ne lokacin da ka shigo."

"Me Daughter ta yi miki da za ki kwashi mutane ku je ku dake ta ita da ƙanwarta?

Baki na buɗe ina kallon Yallabai yadda ya yi mini tambayar a kausaahe alamun tabbaci ma gare shi ba hasashe ba. Sai na ma kasa mgana har na buɗe bakina sai kuma na yi shuru kawai.

"Ba da ke nake magana ba kin yi mini shuru kamar wani ɗan iska?

Ya faɗa yana mai yi mini ihu a saman kaina. Kawai sai na ɗaga ido ina mai ƙara kallonsa kafin na ce" Ni ban kwashi mutane su je su dake ta ba. Wa ya ce maka an dake ta? Ni dai na san Munnira sun yi faɗa da kanwarta ta shigo rabo ba ta sani ba ta ture ta shike nan abin da na sani. Kuma ni har ga Allah ba da yawuna Munnira ta yi abin da ta yi ba. Ni da hankalina zan kwashi mutane aje a yi tashin hankali? Me matarka ta yi mini da zafi da zan yi mata haka?

"Wa ya sanin miki. Duk abin da ya faru kina sane saboda ai su Munniran da Hauwa tare da ke suke. In kika tsawarta musu ai za su bari amma da ya ke kema akwai mugun nufi a ranki. Shi ya sa kika yi shuru sai da abu ya faru za ki zo kina faɗamini wai mai matata ta yi miki da zafi? Kika san abin da ta yi miki domin ni ba makaho ba ne tun haihuwan nan na ga take-taken ki, ko barka sai da na yi ta miki magana kika je, asibiti ma ba ki je kin duba ta ba sai da ta koma gida da na yi magana sai ki ce ba ki da lafiya. To duk na gama gano ki. Kin kuma kyauta da abin da kika yi. Saboda ke an targaɗa mini mata a banza a wofi na gode Sadiya kin ji ko? Na ce Na gode."

Ya faɗa cikin hargagi har yana yarfa hannu. Marwa da Baby suka fito da sauri daga dakin su Jidda suka gan mu cirko cirko ni da Yallabai.

"Ni ce mai mugun nufi a raina?. Ni Yusuf?

Na faɗa ina nuna kaina cikin tarim mamakinsa.

"E ke ce fa, kuma kin aiwatar da nufin ki, kin kyauta. Amma ki sani ba ita kika yi ma wannan tozarcin ba illa ni. In ma kin ji hauahi tana ta haihuwan Maza ni ba ki yi mini adalci ba. Domin na shafa faɗa miki da mazan da matan duk ɗaya ne a wajena me ya sa ba za ki yi mini kara Sadiya ki boye kishin ki ba? Abin da kika yi dai dai ne? Abin da kika yi sunan shi ne zubar da ƙima. Watarana in Saudatu ta gan ki   ba ta darajaki ba. Juzt bleme your self domin ke kika zubar da girmanki, ta bi kuma ta tattaka shi."

Wai Yallaɓai har yana nuna mini hannu yana gaggaya mini magana ina kallon shi kwarmin idanuwana suna cika da kwallah.

"Na ɗauka in ina da wani mugun nufi tun a shekaran baya zaka sani ba yanzu ba."

"Da ba ki da shi. Yanzu kika ɓullo da sabbin hallaya marasa kyau. Kin bari sheɗan na zugaki. Tare da su waɗanda kika rike a naki. Na daɗe da sanin saboda ke su Hauwa ba sa zumumci da Daughter amma ban taɓa magana ba. Kuma a adalci ai dake da ita duk ɗaya ne yadda za su yi miki haka za su yi mata. Duk na share wannan ban taba magana ba sai abu ya zo har da duka har gidan ta? To ba ki isa ba yadda kema ban kyaleki ba suma ba zan ƙyale su ba na kira Nasir da Mutaƙƙa kowannen su zai ja ma matarsa kunne. In dai ba za su dauke ki ɗaya da Matata ba to sai dai a raba wannan alaqar taku gabaɗaya tun da ba ta alheri ba ce sai ta sharri."

Ai ban san na kwashe da dariya ba, sai da na ga na yi ta cikin takaici da bakin ciki hawayen da suka zubo mini na share ina kallon Yallaɓai ido cikin ido kafin na ce"Wannan kuma wallahi ta yi kaɗan. Lokacin da tazo tare ta ganmu kuma wallahi tare za ta bar mu. Zama daram in ji mai naguda."

Na faɗa ina mai riƙe kuguna. Domin na lura an gama shiryaa mai mganganu ni zai zo ya tara mini gajiya to wallahi bai isa ba.

"Ni kike faɗa ma haka Sadiya?

"An faɗa maka sai me? Kai waye? Mijina!
Na yi wata bazawar dariya kafin na nuna shi ina faɗin" Mijina ne kai da muka yi zaman aure na shekari sama da ashirin ashe kai ba za ka iya sanin abin da zan iyawa aikatawa da wanda ba zan iya aikatawa ba? Wato duk abin da matarka da danginta suka faɗa akaina shi ne gaskiya a wajenka ko? To bari ka ji na faɗa maka ko na ce na ƙara tunasar dakai ko garke Gimbiya za ta haifa maka na Maza wallahi ko a gefen gyalena da yau ban haihu ba da bakin ciki ya kashe ni. Maganar zuwa barka ban yi niyya zuwa ba ne, duk ita a nata haihuwan ka fahimci ni ban je ba amma a lokacin da na haifi Yunma ba ka fahimci sai da ta ga dama ta zo ba? Ita ka same ta ka yi mata mgana kamar yadda ka yi mini? Wato sai ni ce marainiyar ka dole ka zo ka same ni ka sauke mini magana. To bari ka ji na rantse da wanda raina ke hanun shi ina dai dai dakai daga kai har munafukar matar taka."

"Sadiya."

"Yusuf"

Yadda ya kira sunana cikin tsawa nima haka na buɗe murya na kira sunan shi yana huci ina huci.
Sai kukan Yumna muka ji, can sai na Baby ko ni juyawa ban yi ba shine ya juya yana kallon su yara sun ga abin da ba su taba gani ba.

"Marwa ki ja yaran nan ku koma ciiki."

Ya faɗa yana sassauta muryan shi,

"A shiga da su ciki kuma? Daga baya kenan wai an yi sadaka da bazaawara. Ai sun gama ganin ka, kana ci ma uwarsu zarafi a kan wata banza a banza.'

Na faɗa ina haki saboda ɓacin rai.

"Kar ƙi kara ce mata Banza."

"Na ce banza a banza Yusuf

32 / 55