Turken Gida Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   12 / 55

33K to 36K   out of 163.1K words

ce me zai dame ni,? Ni da na yi farar haihuwa.."

"Shutup."

Ya katse ta bayan ya da ka mata tsawa. Sai ta yi shuru ta na wani nuƙufarci.

"Har kina sake maimaitawa?

"To ai na ga ba."

"Ki  rufe mini baki na ce ko?

Ya sake mata tsawa har ya na miƙewa kawai sai ta fashe da kuka tana faɗin" Ni shikenan ba za a bar ni na yi mgana ba. To da yake ita kake so ai ka bar ta ta yi mgana ni kuma da a ka tsana ina mgana kana mini tsawa."

"An hana ki ɗin. Kuma ba a son ki ɗin, an tsane ki, ki yi abin da za ki yi wawuya kawai "

Kamar famfio sai ta ƙara ma kukanta volume.

"Ki yi mini shuru na ce ko?

Ya sake faɗa a fusace dole ta kama bakinta ta koma tana haɗiyan zuciya.

Shima sai ya koma ya zauna yana sauke numfashi kafin ya kalleni yana faɗin" kin yi mini laifi Sadiya. Me ya sa da kika yi ta mata mgana tana miki wulaƙanci ba ki faɗa mini ba! Da tun lokacin zan faɗa mata ko ni da nake aurrn ki ba ki taɓa mini mgana na yi miki haka ba ballatana ita ? Sannan mganar tun da kika samu ciki ba kya laifi a wajena sai ki faɗa mata tun kafin ki samu ciki ke ɗin daman ba kya laifina a wajena ko za ta ɗau mataki ne? Wallahi da kin faɗa mini da na ci mata mutumci da ba ta isa ta tare ki da wata mgana ba."

"Ka yi hakuri."

"Kar ƙi kara ganinta ki ce za ki yi mata mgana. Umarni ne daga ni na ce duk in da kuka haɗu ita ce za ta fara gaishe ki "

"Tabɗijam"

"Ko ba za ki bi Umarnina ba ne?

Ya katse ta a fusace kamar zai kai mata duka.

"Na ji."

"Wallahi tallahi kika kuskura na sake jin kin yi sa'in sa da Sadiya sai na nuna miki kalata. Haba. Ke ba ki jin lallashi ne? Wani irin haƙuri ne ban baki ba ? In Sadiya ce wallahi umarni ɗaya nake ba ta ta bishi amma ke sai yanzu za ki fiddomin sabbin hallaya? Haka kike daman? Ko zuga ki a ke yi! To in ma zugi ne ba ki isa ki ce ni za ki juya ni ba. Ni ba batulu ba ne kafin na same ki da Sadiya kika ganni. Kin san faɗin tashin da muka sha tare kafin mu kawo a lokacin da kika aure ni? Kin san gwagwarmayan  da muka faro ta da ni da ita kafin zuwan ki? Ni ban raina ta ba sai ke? Ki raina mini mata sannan ki na neman ɓata mini ƴa'ƴana? Har kina dukan ƙirji da kin yi mini farar haihuwa? Na taɓa faɗa miki na bambamce tsakanin su Khalipa da su Jidda ne? Ban da ba ki da tunanin ba su Jidda na fara samu kafin su Khalipan ba? Dukkansu ƴa'ƴana ne kuma ina son  su amma mace ko namiji ba wanda ya fi wani a wajena. Na rantse da wanda raina ke hannun shi Saudatu in na ƙara samun labarin kin ce ke farar haihuwa kika yi sai na saɓa miki. Saɓawa mafi munin da ba ki taɓa sanin haka nake ba "

Ya dakata ya na sauke numfashi ita kuma tana ta kuka.

"Ki bata haƙuri. Kuma wallahi in kuka ƙara haɗuwa ko kallon banza kika yi mata in na ji labari ni da ke ne."

Ba ta da yadda ta iya ne ya sa ta ba ni haƙuri tana kuka.

"In ba ɗan adam da manta alheri ba wani wahala da kara ne Sadiya ba ta yi miki lokacin da kike da cikin Khalipa ba? Har kin manta yanzu ba ki da abin ciwa mutumci sai ita? To bari ki ji ki sani in kika tozarta Sadiya kamar ni kika tozarta. Tozartani kuma da-dai yake da kin tozarta auran ki. Ita da zuciya ɗaya take zaune da ke amma ke ki zo ki auran mata miji kuma ki hana ta zaman lafiya? To ba ki isa ba ki shiga taitayin ki da ni wallahi in ba haka ba ki kasa gane kaina"

Sai kuka take yi ta kasa mgana ina ga ba ta yi tunanin lamarin zai ɓare da ita kamar haka ɗin ba. Yallaɓai ta in da yake shiga ba ta nan yake fita ba har sai da ta koma tana ba ni tausayi.

"Ka yi haƙuri ma na Yallaɓai."

Na faɗa ina so ya bar mganar amma bai bari ba sai da ya gaji don kan shi sannan ya koma yana sauke numfashi.

"Itama ta yi haƙuri kan mganganun da ta ce Munnira ta faɗa mata."

"Ai ba mganar haƙuri duk mganar da ta faɗa gaskiya ta faɗa mata. Saboda haka ba wani mganar a bata ma haƙuri."

"A'a ka saka ta ba ni haƙuri nima ba laifin in na ba ta haƙuri."

Sai ya yi shuru ni kuma sai na juya ina kallonta kafin na ce" Ki yi haƙuri kan mganganun da na faɗa miki har da wanda ma su Munnira suka yi. Hakan ba za ta ƙara faruwa ba."
Ba ta yi mgana ba sai jan zuciya kawai take yi. Yallabai ya yi mgana ta ƙarshe shi ne kar ya sake jin labari makamcin wannan ya sake faruwa in hakan ya sake faruwa kowacce cikin mu ke da laifi zai haɗa mu ne gabaɗaya ya hukuntamu.

"In sha Allahu hakan ba zai ƙara faruwa ba. Ka yi haƙuri."

"Na gode Sadiya ta."

Haka ya ɗauke ta suka koma. Ni na san za su kwana ba zaman lafiya domin a fusace ta fita haraba yaran ma shi ya tsaya ya taho da su. Ni dai a raina na ce ku ƙarata faɗan da ba ruwan ai daɗin kallo ne da shi. Sannan daman in har ka rike gaskiya a je dai a dawo wata rana kai ke da nasara.
Tun da ya yi mana wannan sulhun ban ƙara bi ta kanta ba har aka zo a yi sallar babbar salla ba mu ƙara haɗuwa ba sai a Gwammaja a falon Nene da ya ke ba a sallar idi saboda corona yadda ta gaisheni ba fara'a nima haka na amsa mata cikin yanayin da ta gaisheni. Nene ta ji labari ta sake kiran mu har cikin ɗakin ta ni da Gimbiyar ta sake yi mana faɗa, ni dai na ce mata na yi mata alƙwarin hakan ba zai ƙara faruwa ba. Itama ta ce ta bari ba za ta ƙara ba.

Amma har muka bar gidan nan ba mu ƙara ma zama a inuwa ɗaya ba. Kowa na harkan gaban shi, Munnira ta dame ni sai da na faɗa musu tara  mu da Yallaɓai ya yi amma ban faɗa musu masifan da ya yi ta mata ba amma dai na sanar da su ya ce in muka ƙara haduwa ita ce za ta riƙa gaishe ni.

"Da kyau. Tafida daman ai Namiji ne."

Ni dai ban ce komai ba. Saboda namiji ne mai canza launi baƙin cikin sa kuma amarya da uwargida duk sun kurɓe sa. Shi ya sa don ya yi wannan faɗan zuwa Gimbiya bai saka na ji daɗin haka ba wata rana ni kaina zai iya yi mini haka kuma a gabanta. Abu ɗaya na ji daɗin shi yadda ya nuna mata shi a wajen shi daga mace har namiji duk ɗaya suke kuma ya nuna mata ina da daraja ta nan kawai ya burgeni.

*****

Haka lokaci ya ci gaba da tafiya tun ina sa ran za a buɗe gari har na fidda raina. To ko an buɗe gari ina mganar komawa makaranta ina fama da kaina. Jdda ma nake ji itama daga farko ne ta damu daga karshe sai ta saki jikinta kawai zaman gida dole. Ko Tahfiz ɗin su babu duk wata makaranta an daina yin ta in dai za ta haifar da cunkosun jama'a. Ni kuma gefe ɗaya ina cigaba da renon cikina da ya shiga watani shidda har na fara zuwa awo a nan asibitin Aminu Kano AKTH.

Cikina ya fito daga gani cikin zai yi girma wannan karon. Allah ya taimake ni lokacin da ya shiga watani biyar sai na dawo da cin abinci kamar gara shi ya sa cikin wata ɗaya na mai da jikina har na fara haɗa wata kiɓa. Kumatuna sun yi luhu luhu wuyana har ya na neman haɗewa saboda kiba. Abincin na ke ci kamar hauka a rana sama da sau huɗu har cikin dare, yanzu tea na saka ma ƙahon zuƙa madara ba ta sati ta ƙare har Yallabai sai da ya ce wato abincin da ban ci ba ne a baya na ke famshewa. Kowa ya ganni sai ya ce Sadiya cikin nan ya buɗa ki? Shi ya sa hancina da bakina suka yi girma saboda yadda fuskata ta ciko sosai.

***

Lahadi.
August, 2020.

Lahadin ƙarshe mako ne Yallaɓai a gidana yake tun ranar jumma'a ya je Abuja sao jiya da daddare ya dawo.  Can ma aiki ya samu na gina ma'aikatan sarrafa leda ba ya samun hutu sai a yi ƙarshen mako sama da biyar bai kwanta a gida ya huta ba. Jiya ma ya dawo da daddare mun daɗe muna hira saboda ni tun da cikina ya shiga wattanin sa na shidda na daina barcin dare sosai amma ina yi na rana hani'an.

Faɗa mini yake ba shi da kuɗi ya kwashe ya saka a ginin ma'aikatan shi, ga wannan aikin sai da ya ɗan ci bashi daɗin sa ma sun ce za su ba da rabin aiki rabi kuma sai an gama. Ga na Dutse bai kamallah ba amma an kusa sai ya raba yaran na shi uku. Biyu ya kai su Abuja. Kaɗan kuma suka zauna a Dutse suna ƙarisawa. Wasu kuma suna na ma'aikatan shi duk sauran aikin kaɗan ne. Kofofi ne suka rage sai fanti da sauran ɗan abin da ba a rasa ba a gama. Shi damuwar shi in an gama aiki furnitures ɗin da za a sanya a a wajen ne tunanin shi ya so ya yi oder ɗin ko da rabi ne amma bai samu ba sai na bashi shawaran ya bi komai a hankali in an gama aikin Dutse an gama biya sai ya yi oder ɗin ko rabi ne Allah bar shi daga  ya siya saura. A yadda ya faɗa mini yana so a farkon shekaran 2021 kamfanin shi ya fara aiki a sabon gini. Ni na yi ta kwantar masa da hamkali har wajen biyu na dare sannan muka kwanta da asuba kuma bayan mun idar da salla ya ce sai ya yi barnan ruwa. Ni dai ina tura baki aka yi a ka gama maganar gaskiya cikin nan ba ya son ɓarnan ruwan nan shi ya sa ya ce bai ji daɗin da ba irin cikin Baby na ƙara samu ba ina hararan shi na ce wato ya so ne ya ƙara samun damar da zai ta shagalin sa ya ce kamar na sani. Tun da ya kwanta ya ke barci har azahar.

Ganin azahar ta yi ya sa na tashe shi wajen ɗaya da rabi. Da ƙyar ya tashi ya yi sallah ya so ya koma barci na ce masa don Allah ya bari ya yi wanka ya karya. Wanka ma ni na taya shi na gaggasamai jiki saboda ya ce ko'ina ciwo suke yi masa.

'"Wai ni hala ƙankare nan kake ɗauka a saman kai ne?

"Ba na ɗauka amma in ta kama ina ɗauka. Kamar yadda suke yini a tsaye suna aiki nima a matsayina na Injiniya mai kula da aikin kamar haka ne a tsayen na ke yini."

Cikin tausayawa na ce" Sannu.  Allah ya tsare mana kai mijin mu."

Na faɗa ina danna masa kafaɗunsa lokacin ina sha masa vesiline ne.
Ya amsa da Amin yana dariya.

"Ko in shafa ma ka man zafi ne?

"Yauwa shafa mini Allah ya yi miki albarka."

Dirowan gado na jawo na ɗauko na fara sha fa masa kafaɗunsa zuwa bayansa ya na tambayana in da na samu man zafi na ce Gwaggo ta ba ni ta ce na riƙa shafawa a kafafuna da suke kumbura.

"Ba kumburi ba ne tsabar cin abinci ne ko?

Ya faɗa yana dariya sai na lakato na shafa masa a fuska ya ji zafinn yajin  ya sa ya kare fuskarsa yana faɗin" Makanta ni kike son yi Sadiya?
Ni kuma ina ta dariya ina faɗin" Ka kara cewa ina da cin abinci. Wai ba ɗanka ba ne ke saka ni cin ba?

"Shi ne."

Ya faɗa yana danne dariyan shi. Haka na gama shafa masa muna hira nima har sha fa mini ya yi a ƙafafun nawa sannan ya saka kaya. Yau a bedroon na kawo masa abin ƙarin bayan ya gama na kwashe na mai da kitchen su Jidda ma sai da suka biyo sa suka gaishe shi a ciki.

Nan na bar shi na je falo muna duba hijabai ni da Jidda. Jiya suka iso na ce ta ɗauko list mu cire ma waɗanda suka saka oder. Can na ɓata lokaci ko da na koma ɗaki na ɗauka zan gan shi ya na barci amma sai na iske shi zaune yana waya ina shigowa ma ya gama wayar.

"Yallaɓai ba ka kwanta ba?

"Yanzu waya ta tashe ni."

Sai na zauna kusa da shi ina matsa masa kafaɗanshi.

"Sun daina ciwo?

"Sun yi sauƙi."

Ya faɗa yana kallona. Sai na sake shi ina faɗin" Yallaɓai ni fa ina son ka fara koya mini mota."

Daga maganar arziƙi sai kawai na ga Yallaɓai ya kalleni ya wani kwashe dariya.

"Mota? A hakan ne za ki koyi mota?

Ya faɗa ya na kallon cikina. Sai na fusata a kuma fusacen na ce" E a hakan ko ba za ka koya mini ba ne?
Na fada ina haɗe fuskata ganin yana ta mini dariya sai ka ce na faɗin abin dariya.

"Ko ba za ka koya mini ba ne. Na je wajen da ake biya na koya?

"E to gaskiya domin ni ina na ga lokacin koya miki mota fisabilillahi Sadiya? Wai ma to ke kina da motar ne da kike son koya?

"Ba ni da shi amma ina da niyar siya ne"

"Da wani kuɗin?

Yallaɓai ya faɗa har yana tagumi.

"Da kuɗina mana"

"Kina da kuɗi ne da man?

Tambayoyinsa sun fara ƙular da ni ya sa a ɗan tsume na ce.

"Ai ba zaman banza nake yi ba kasan ina da sana'ata."

"Wai da riban hijaban ne za ki siya mota da man?

Sai kawai na kalle shi na kasa mgana. Me Yallaɓai zai yi in ba dariya ba har ya na duƙawa rike da ciki.

"Ke yanzu daman kin san riba ake samu haka tsagwa gwa shi ne ba ki faɗa mini na saka hannun jarina ba? To wai kamar nawa yanzu kika tara na siyan motan?

"Ban sani ba."

Na faɗa a fusace ina mikewa da cikina gaba. Har na bar ɗakin Yallaɓai na tintsira mini dariya abin ya yi mini ciwo. Kuma wallahi zan bashi mamaki da ni yake zencen.




*Janafty**TKG0B3F06*

Duk da na bar ma Yallaɓai ɗakin sai da ya ƙara biyo ni falon. Ina zaune ina cin dankalin hausa ɗanye kitchen na shiga na ga Jidda na ferewa wai shi ta ke sha'awa za ta soya ta ci nima nan take na ji ya shiga raina sai na ce kawai ta fere da ɗan yawa sai mu ci gabaɗaya. Shi ne kafin na taho na ɗauki wanda ta feren ƙarami na wanke na taho da shi falon Yallaɓai na zauna ina gutsira a hankali ina jin daɗin sa a bakina da cikina gabaɗaya.

"Aa Hajiyar mota nan kuma a ka dawo?

Wani kallo na yi masa amma ban yi magana ba. Yana dariya ya zagayo ya zauna a gefena yana faɗin.

"San mini dankalin"

Ya faɗa ya na kamo hannuna na yi saurin fizgewa ina ƙara haɗe rai.

"Ba za ki ba ni ba?

Nan ma na yi masa shuru. Saboda ganin har lokacin bai dai na yi mini dariya ba. Maganata ta zama a bar dariya a wajen shi shi ya fi ƙular da ni kuma ni har a cikin zuciyata da gaske nake yi zan koyi mota saboda nima ina son wata rana na ganni ina tuƙa mota da sunan tawa ce.

"To fushin duk na mene ne Madam?

"Ko duk  fushin na ce ba ni da lokacin koya miki mota ne?

Sai a lokacin na kalle shi ta gefen ido kafin na ce" Na me! Abu na kuɗi zan je na biya a koya mini kasha zaman ka."

"To ni me ya sa zan bari wani ƙaton banza ya koya ma matata mota?

"Haka ka so."

Na faɗa a tsume kuma cikin gatse sai ya gimtse dariyan sa lokaci ɗaya yana faɗin" Ba za a yi haka ba. Yanzu dai ki bari in na samu dama zuwa ki haihu sai na koya miki."
Na yi masa shuru ban ƙara magana ba amma ina ta gutsiran dankali da ƙarfi yana ƙara saboda haushi.

"Kan lokacin ma ƙila abubuwa sun warware na sauya mota sai kawai na bar miki nawa Hajiya ta."

"Ba na son wannan motar."

Na faɗa da sauri ina kallon shi fuskata ba fara'a saboda ni fa gani na ke yi kawai Yallaɓai zama ya yi ya na ci mini fuska.

"Sabo da mene ne?

"Ba na sonta ne. Mota kamar za ka hau foo?

"Foo kuuma?

Yallaɓai ya maimaita cikin alamun tambaya.
Sai na gyaɗa masa kai kafin na ce" E. Ni zan siya mota ta mai kyau irin ta mata."
Yallaɓai sai dariya yake yi yana kallona.

"Wai miye? Na zama abin dariya ne?

Na faɗa a tsume fuskata a murtike ba ko fara'a.

"Ke yanzu motar tawa ce kamar za a hau foo? Lalle kin ma raina mini wayau. Motar nan ma a gan ki a ciki duniya ne hajiya amma tun da kin raina shi kenan. Zan siya miki ta mata ko irin ta Daughter satin da ya wuce ta sauya mota wata Vibe mai kyau ta mata kina son irin ta na siya miki?

Bai ba ni zarafin mgana ba na ga ya ɗauko wayarsa ya latsa sai ga hoton motar yana nuna mini tana da kyau. Sai da na gama gani sannan na ture hannun shi ina faɗin" Ba na son irin ta. In ta shi siya ai ni na san irin wacce nake so"

Kawai sai ya riƙe baki cikin mamaki ni kuma sai na juya masa ƙeya ina faɗin" Kuma saura ka ce wai saboda matarka na da mota ne, nake son siya. Ni kawai ina so ne saboda nima na

12 / 55