Turken Gida Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   28 / 55

81K to 84K   out of 163.1K words

ji haushi amma ban damu ba daga baya na watsar da abin. Washegari muka koma gida Kano kuma ko a labari ban taba faɗa ma Yallaɓai ba.

*****

Yallaɓai tuni ya zagaye filin shi an saka get har an fara gini gadan-gadan domin yanzu Yallaɓai kuɗi yake samu mahaukata. Kwangiloli sama da biyar yake yi a lokaci ɗaya.
Ba zato ba tsammani ban ma saka rai ba Yallaɓai ya siya mini mota a watan November ranar goma ga wata ranar da Yunma ta cika shekara ɗaya. Har na shirya mata party a gida Jidda ta yi mata cake tun da yanzu ta ƙware, sai ga Yallabai da maƙullin mota ya siya mini vibe fara, amma ba sabuwa ba ce sai dai ba ta sha miya ba. Na daka tsalle na ruƙumƙume Yallaɓai ina faman ihu da murna ni da yara shima farinciki yake yi ganin yadda gabaɗaya na rikice saboda murna.

"Mota ka siya mini Yallaɓai? Innalillahi."

Na ke faɗa na ma kasa mgana saboda murna da farimciki.

"Mu je ki ganta tana haraba. Ita na tuƙo, tawa na ce Musbahu ya taho mini da ita daga baya."

Ai sai gani ni da yara muna rige-rigen fita har da Yumna dake tafiya itama har ana neman ture ta Yallaɓai ya sunkuto ta ya biyo bayana.

Da na ga motata sai na dafa ta kawai na fashe da kuka.

"Yallaɓai wannan mota ta ce?

Shi da yara suna ta mini dariya ganin ina kuka sai ya ƙariso ya rumgumeni shi da Yumna yana bubbuga bayana lokaci ɗaya yana faɗin" Kin yi mota saura ki je ki sauke farali My Sady."

"Yallaɓai har saudiya za ka biya mini?

"In sha Allahu Sadiya ta."

Ai sai na ƙara fashewa da kuka na rumgume Yallaɓai na ƙamƙame shi ina ɗaga murya cikin kuka amma na kasa magana.

"Shii. Bar kuka yau ranar farimciki ne ok?

Ya faɗa yana ɗago fuskata ya fara share mini hawaye. Yumna na ta ya shi.
"Kin ga har Yumna ma ba ta son ganin Umman ta na kuka."

"Yallaɓai kukan farinciki ne"

Na faɗa wasu hawaye, na gangaro mini na farinciki.

"To za ki karar da hawayen na ki ne a yau? Ki adana su saboda ba ki ga komai ba. Tun da Ubangiji ya wadata ni ni kuma zan yi ta saka ki farinciki har ƙarshen rayuwar mu Sadiya ta."

A gaban yara na yi ɗage na sumbaci bakin Yallaɓai sannan na sake shi ina kallon shi kafin na ce.

"Na gode Yallaɓai. Ubangiji ya yi ma dukiyarka albarka. Na gode."

Na faɗa ina ƙara gocewa da kuka Yunma ma sai ta fara. Baby da Jidda na can suna santin mota, ko ta kan mu ba su bi ba,

"Bar kuka nan kin ga Yunma ta fara."

Ya faɗa yana bubbuga bayana. Amma na kasa tsaida hawayena. Sai da ya share mini sannan ya saka ni na shiga motar na yi bismilla da addu'a..

"Allah ya tsare Hanya Madam me"

Yallabai ya faɗa yana lekowa ta window
Yunma ta ya fito ni, na karɓeta ina fadin" Amin Sadaukina "
Babby har ta kame a gaba Jidda dai baya ta buɗe ta shiga tana faɗin.

"Umma tubuli Allah ya sa ki kashe ta lafiya."

"Amin Amin Jidda. Yallaɓai saura Jidda ka siya mata ta ta motar"

"Da a ce nan garin za ta yi makaranta da na siya mata amma tun da zariya ne sai dai in ta gama in sha Allahu."

"Allah ya amimce Yallaɓai na."

Jidda ta kalli Babanta kafin ta ce" Mun gode Yallabai Allah ya karo buɗi."

Baby ta ƙyalƙyace da dariya kafin ta ce" Abba Yallaɓai "

Ni da shi muka yi dariya gabaɗaya.
Daran nan da kyar na iya barci gani na ke yi kamar mafarki waahegari ni na kai Baby makaranta a mota ta, daga can ɗorayi na dira Yallaɓai na bari a gida shi da Jidda daman na ce sai in da mai ya ƙare.

Sai da su Gwaggo su ka ganni da mota na ce su fita ita da Alhajinmu suna ta murna da saka albarka. Daga nan sai gidan Ya Abubakar shima na kai masa ya gani. Na je har gidan Ya Aina na nuna mata sannan na koma gida na ɗauki hoton motar na yi status da ita sannan na yi caption a kasa da cewa.

"Alhamdulillah. Yallaɓaina ya gwangwaje ni da mota jiya. Matar Yallaɓai ta yi mota jama'a ku ta ya ni murna."

Nan da nan aka yi mini caa Sadiya kin yi mota! Congratulaton Mimiaco ta ce kin chanchanta ta Yallabai. Ita ce kaɗai ta yi mini murna sai su suwaiba da Nasara da Jamila. Gimbiya ta gani amma ko Allah ya tsare ba ta ce ba, Ya Hamza ya turo mini rawa kafin ya ce" Lalle Yallaɓai ya iya gwangwaja danƙari. Allah ya tsare "

Adanan kuwa faɗi yake yi" Ya Sadiya kin rigani yin mota? Na ce to ka zauna ni ai na yi gaba.
Su Maijidda da Samira suna ta mini fatan alheri.
Munnira da Hauwa gida suka zo yi mini murna, da za su tafi na tuka su na kai kowacce gidan ta. Ni fa tun da na yi mota na dai na zaman gidan ni ce can ni ce nan, har Jidda ni ke kai ta wajen koyon kwalliyarta tun da sun gama na snacks, sati mai zuwa ma zata je zariya yin POS UME. Ni ce har Gwammaja na kai ma su Nene mota suka saka albarka. Lokacin Jawahir da Umma Salma sun zo ganin gida suma sun saka albarka suka ce ai na caancanci mota na kuma chanchanci na shiga na fita. Yallaɓai ai nawa ne an sha gwagwamarya.

Wajen sati biyu ban zauna a gida ba, Yallaɓai ya gaji ya ce na zauna na huta har abada fa motar nan tawa ce sannan na hakura gani nake yi kamar zai ce na kawo key ɗin an fasa za a mayar ma da masu shi. Faridan Tariq ta ce itama a satin Tariq ya siya mata na ce mun yi amarya a tare. Anty Zabba da muka yi waya ta ce ta yi mini murna yayan shi da ya ji sai ya ce ya kyauta muka yi ɗan tsegumi har tana ce mini yanzu sai Gimbiya ta daina yi mini gani gani anan ne ma na ke faɗa mata ita da su Anty Bahijja ba su yi mini murna ba.
Ta ce na raba su hassada ne da bakin ciki na ce sai dai ya koma musu kuwa. Ba sa gabana ta ce ya fi haka.

Ni ina gida ban san wainar da ake toyawa ba. A satin da Jidda ta tafi Zariya gidan Ya Hamza ta sauka bayan ta gama jarabawar ba ta dawo Ya Hamza ya ce sai sakamako ya fito za ta dawo. A Safiyar litin Ni kaɗai a gida Baby na makaranta daga ni  sai Yumna da ta koyi shegen ɓarna tana tafiya turba turɓa da ƙyar, Yallaɓai ba gidana ya kwana ba bai kuma shigo da safe ba sai na yi tunanin fitan gaggawa ce ta kama shi, da man wani lokacin in bai samu dama ba sai dai mu yi gaisuwar ta waya.

Wajen sha ɗaya na safe Sameena ta kira waya muka gaisa tana yi mini murna. Har ina mata tsiyan ta makara ta ce mini wallahi ba ta ji labari ba sai satin nan da ta je gida ta ji ana ta rigima kan motar.  Ashe har yaji Gimbiya ta yi akan Yallaɓai ya siya mini mota. Saboda ta yi masa maganar siyayyan kayan haihuwa ya ce ta jira sai ya siya mini mota sannan zai dawo kanta shi ne ta suka yi tsiya fata fata har ta yi yaji. Kwananta hudu a gida amma ta dawo shekaranjiya yara ma can Gwamnaja aka kai su wajen Nene.

Na yi ta mamaki domin Yallaɓai bai ba ni wata alama ba, tun da ni dai bai zo gidana ya kwana ba ashe shi kaɗai ya riƙa kwana don kar na fahimci wani abu. Sameena ta ce tana gidan shekaranjiya asabar Yallabai ya je can Rano tare da Kawu aka zauna ana ma yar da magana Gimbiya tana ta kuka tana faɗin ba ya yi mata adalci komai ni komai kamar na shanye sa shi ne ya ce e na shanye sa ne, itama za ta iya shanye sai bai hana ta ba mota ne ya siya mini haihuwa kuma tun da ba gobe ba ne ta jira ta gani in bai ba ta kudin siyayyan ba sai ta yi magana. Sai da Tafidan Rano ya shiga maganar sannan ta biyo sa suka dawo gida tare.

Na jinjina lamarin Gimbiya a raina sosai. Hasashena ya kasa hasaso mini tsanar da matar nan ta yi mini ta zo ta same ni da mijina amma tana neman ta hana ni zaman lafiya! Kwana na yi ina auna abin a kasan raina wai ta yi ya ji saboda an siya mini mota. A bakin Sameena na ke ji tana cewa itama ai ta yi ta yi ya sauya mata mota ya ƙi. Amma ni ya siya mini shi kuma ya ce ita tana da shi, ni kuma ban da shi shi ya sa ya fara siya mini tun da ni ce uwargida. Ta jira in ya samu kuɗi sai ya sauya mana gabaɗaya ta ce Hajiyarsu na ta yi mata faɗan ita ba ta ga ƙoƙarin da ya ke yi ba miye don ya siya ma matarsa mota shekara nawa suna tare bai siya mata ba sai yanzu? Ita na za ta gode ma Allah da ni'imar da ya yi mata sai ta bari sheɗan na yi mata susa a kunne. Ta bakin Sameena ta ce bakin ciki ƙiri kiri Gimbiya ta nuna akan an siya mini mota. Ni ko da gayya na ce ta ko fara gani in sha Allahu sai dai ta mutu in ba za ta iya ba ta fi ta bar ni gidana da mijina daman a ciki ta zo ta ganni na matsa mata amma shi ne za ta yi mini butulci.

Kamar in yi ma Yallaɓai magana sai na fasa ganin shi bai faɗa mini amma na riƙe ta a raina, a satin da na ji maganar muka haɗu a Gwamnaja Maman farko ce ta zame daga bene ta samu gocewa shi ne na je dubata kuma da motar na je  a ɗakin Nene a gaban Anty Bahijja da ita kanta Nenen na kalli Gimbiya na ce mata.

"Gimbiya Yallaɓai ya siya mini mota kowa ya yi mini murna ban da ke ko ba ki sani ba ne?

Da gayya na faɗi haka, ai sai ta ji kunya ta fara kame kamen wai kwana biyun nan ba ta ji daɗi ba ne ta so ma ta zo har gida ne ta yi mini murna. Kallonta kawai na ke yi ni sai na raina wayan ta. Matar da ke da shago guda amma ɗan abin da Yallaɓai yake yi mini ya hana ta sukuni.

"Allah Ya sanya alheri."

Na amsa da Amin ina kaɗa key ɗin hannuna.

"Kema Anty Bahijja ba ki yi mini murna ba."

Duk na kunyata su, ita da yake akwai isa kai tsaye ta ce" Kin kawo mini ita har gida ne kika ga ban yi miki murna ba?
Sai na nuna mata na fita iya bariki kai tsaye na ce" Ban kai miki gida ba amma yau ga ta can a haraba na zo da ita. In za ki fita ki duba ta, ki saka albarka Anty Bahijja."

Sai ta kasa magana Nene na wajen ta saka baki ta ce ba su kyauta. Abin alheri ne ya same ni yana da kyau su yi mini murna sai ga shi jiki an sanyaye da zan tafi suka fita ganin motar suna saka albarka na ciki na ciki. Halima ina haraba ta shigo yadda ba ta gaisheni ba, nima ban nuna na ganta ba, na shige mota ta ni da Yumna na yi tafiyata suka bini da kallo har na fice a raina na ce ku yi ku gama. Babu yadda kuka iya da ni nan gani nan bari ɗumammen Manya.


*Janafty**TKGB3M013*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX


Assalamu Alaikum Fanmily, mun fara saro muku kayan Kitchen ko wani nau'i, duk abin da kuke bukata na gyaran Kitchen ɗin Amarya da uwargida duk za ku same su a JANAFTY KITCHEN ITEMS, kayan mu masu kyau ne da inganci sannan za ku same su akan rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina a falin Nigerian nan. Domin karin bayani ku tuntuɓe mu ta waɗannan lambobin kamar haka.
09069067488.
+234 706 234 9732

Muna maraba da masu siya ɗaya ko sari🥰

Shuru na yi da bakina kamar yadda Yallaɓai ya yi shuru bai faɗa mini ko ya nuna mini sun samu matsala da matarsa saboda ya siya mini mota. Nima sai na yi kamar ban ji wata magana ba na cigaba da sabgogin gabana. Addu'a kawai nake yi ma Jidda akan Allah ya ba ta sa'a ta samu gurɓin karatu a jami'ar bayero saboda ta ƙwallafa rai sosai akan makarantar.

Cikin ikon Allah satin ta ɗaya a Zaria Khaleesat ta kira ni tana faɗa mini Jidda ta ci Jarabawar da ta yi, na yi ta murna da farinciki Yallaɓai na dawowa na faɗa masa sai ya ce mini Jiddan ta kira shi ta faɗa masa, har yana cika baki da cewa shi da man ya san abin da ya haifa he is sure za ta tsallake, baki na saki ina kallon Yallaɓai yana yaɓon ƴar sa, har yana kallona yana ce mini ƙwakwalwarsa ta biyo shi ya sa take da hazaƙa.

"Me kake nufi Yallaɓai?

"Ni ai ban ce komai ba na dai ce Jidda ƙoƙarina ta ɗauko. Shi ya sa duk abin da ta yi ma himma take samun nasara da taimakon Ubangiji."

Ya faɗa yana ƴ'ar dariya.

"Allah Ya ba mu sa'a."

Na faɗa kawai saboda ba na so maganar ta yi tsayi amma Yallaɓai bai so haka ba kawai sai ya kalleni yana sake faɗin" Amma kin ga Baby ina jin kanki ta ɗauko sam ba ta kai Jidda ƙoƙari"

"Au ni daƙikiya ce kake so ka ce ko Yallaɓai?

Na faɗa ina masa wani kallo sai ya fara dariya yana faɗin" Ni yaushe na ce miki daƙiƙiya?
Ban bari ya cigaba da magana ba na yi wucewata ina faɗin" Sai kuma ka yi. Na gode da cin mutumci Yallaɓai. Ka ji na ce Na gode."
Jin yadda na yi maganar ya san na yi fushi sai ya biyo ni ciki yana rage mini murya, da ƙyar na haƙura sai da ya yi mini rantsuwa da cewa da wasa yake yi sannan na aminta da shi har na saki fuska muka cigaba da hira. Daman da daddare ne ya zo yi mana sallama tun da gidan Gimbiya zai kwana yau da gobe.

Ranar jumma'a Jidda ta dawo, gidan Khaleesat na saka aka aika mini da saƙon hijabai ta taho mini da shi, ta dawo a jigace ta sha wuya motarsu ta yi ta lalacewa a hanya sai mangariba ta iso. Yallaɓai ya kirani ya fi sau biyar yana yi mini masifan ya zan haɗa yarinya da kaya na san ba ta taɓa tafiya waje mai nisa ba, ko da za ta tafin ma da kyar ya bari da ace baya da wani abin da zai yi shi zai kaita. Amma sai da ya kaita  tasha yana jadadda mata ta kula da kanta, kafin ta kai ko ban san sau nawa ya kira ta a waya ba, to yau ma za ta dawo ya yi ta kiranta daga baya sai ya daina samun ta a waya shi ne zai sauke faɗan shi a kaina, tun ballatana da Jiddan ba ta taso da wuri ba saboda jiran sakona. Ai ni sai shuru da ba da haƙuri tun da dai ba ni da gaskiya. Sai da ta shigo gidan nan na samu sauke numfashin salama na kira Yallaɓai na faɗa masa duk da haka bai fasa faɗin abin da ke ran shi ba.

"Sai yanzu ta iso? Sadiya ba ki kyauta mini ba, kawai ki haɗa yarinya da kaya ki wahalar da ita fisabillahi kin kyauta kenan?

"Na ce ka yi haƙuri Yallaɓai ganin za ta dawo ne ya sa na ce ta karɓa ta taho mini da shi."

"Ni dai ba na so. Kar ƙi kara yin haka. Ba ta fa taɓa tafiya ta yi ita kaɗai ba"

Mamakinsa ya kama ni, Jidda kamar wata ƙaramar yarinya ni dai shuru na yi har ya gama bambamin sa ya kashe wayar ban ƙara ce masa komai ba, tun da tun ɗazu nake ba shi haƙuri amma kamar ya haƙura sai kuma da ya ji ba ta dawo ba sai ya fara mini masifan wai ni na ja. Ni fa daman na sani Jidda a wajen Yallaɓai ta musamman ce, in dai lamarin da ya shafe ta ba ya zaune ba ya tsaye, ya yi ta wani kafa kafa da ita kamar wata ƙaramar yarinya. Ai ban ma ga kafa kafa ba sai da ya dawo gidan haka ya zaunar da ita yana tambayanta ta sha wahala? Ta gaji ne ba dai ta samu wata matsala ba ko?

Tana dariya tana faɗa masa ita lafiyanta ƙalau, ba ta samu wata matsala ba kawai lalacewar motar ne, har yana tattaɓa wuyanta, ya ji ko tana da zazzaɓi, ni dai ina gefe ina kallon ikon Allah na kasa mgana. Na ɗauka Yallaɓai ya gama faɗan shi amma ina yana ganin hilimin saƙon da Jidda ta taho da shi faɗan shi ya dawo farko wai da gangan na yi kamar Jidda ne zan saka ta ɗauko uban kaya haka? Wai har Yallaɓai na faɗin an ya ina da tausayi kuwa?

Baki na saki kafin na rufe ina faɗin" To wai duk wannan faɗan na mene kuma Yallaɓai? Ina ce ba ga Jiddan ta dawo ba? Kuma ita Jiddan yarinya ce kar ka manta she is 19yrs kuma jami'a za ta shiga so Jidda ba yarinya ba ce, ka ma daina jijiyan wuya ko Baby ta wuce yarinya ballantana Jidda."

Na faɗa cikin jin haushin sa, to ya dame ni magana ta ƙi ta ƙare kamar cin kwan makauniya, maimakon ya yi shuru sai ya ma ya harzuƙa ya fara faɗin duk haƙurin da na ba shi na ƙarya ne tun da ban yi nadaman abin da na yi ba ina cewa wai Jidda ba yarinya ba ce.

"Za ki haɗa da kanki ne? Kin ga ko har yanzu yarinya ce."

"Jaririya ce Nono take

28 / 55