da inears. Kuma Alhamdulillah ina samun alheri matuƙa.
Ga shi cikina ya yi ƙasa na shiga watan haihuwana. EDD dina 17 November ne. Har ina ce ma Yallaɓai in na haihu zan haɗa mana da Wedding Annivesary na cikar auren mu shekara 20 wanda tun June muka cika shekarun lokacin ina ta kaina laulayi ya saka ni gaba ya sa ko maganar ma ban yi ba Yallaɓai daman ni nake tuna masa tun a baya ballantana yanzu da harkokinsa suka yi yawa.
*****
10. November 2020.
Tuesday. Talata.
Lafiya lau na tashi ko ciwon bayan da kwana biyu na kan tashi dashi yau ban ji sa ba. Yara duk sun tafi makaranta daga ni sai Yallaɓai a gida kwanan su uku a Abuja sai jiya ya dawo da daddare ya sauka a gidana daman daga can gidan Gimbiya tafiyar ta kama shi.
Lafiya lau muka karya, ya ce ba da wuri zai fita ba sai bayan azahar muna cikin bedroom Yallaɓai na kwance ni kuma ina zaune a gefen gado ina ware kayana da na yara sai na Yallabai da safen mai wanki ya kawo su. hira muke yi sama sama sai na ji shuru ashe barci ne ya ɗauke shi.
Sai na cigaba da aikina. Na kwashe kayana na jere cikin kwaba haka ma na Yallabai na su Jidda ne na ce bari na kai musu ɗakin su, sai dai ina in mikewa ne ya gagara. Ƙafafuwana sun riƙe, bayana ya ƙage, daman kafafun sun kumbura cikin ya sunkunya ya yi kasa ba ni ma da riga a jikina da ga ni sai zani zafi kawai na ji ina yawan ji tun da cikina ya shiga watan haihuwan shi.
Na yi ƙoƙarin dafa jikin gado na miƙe ai ban san lokacin na saki ƙara ba, wanda ya ta da Yallaɓai a firgce. Tuni har na duƙe a kasa ina riƙe bayana da na ji kamar ya tsage.
"Me ya faru?
Yallaɓai ya faɗa yana dirowa gabana.
"Baya na. Wayyo Yallaɓai bayana ya tsage."
Na faɗa cikin tsananin azaba har ina cije bakina. Yallaɓai na duba bayan nawa ne ni kuma ina ta wash wash kawai na ji ruwa na bin kafafuna ina dubawa sai na ga har faya ta fashe ai sai na zaro ido cikin ƙaraji nake faɗin.
"Haihuwa ce Yallaɓai. Haihuwa ce faya ta fashe."
Na faɗa ina makarƙyata jin yadda marata ke wani irin juyawa. Kusan fa na manta yadda haihuwa take shekaru goma ba wasa ba. Ji nake yi kamar ban taɓa haihuwa ba azaban da nake ji kamar ban taɓa jin irin shi ba.
"Innaliillahi haihuwa? To mu tafi asibiti ko?
Ya faɗa cikin ɗimuwa shi ma ya ruɗe kamar ni. Kawai sai na yi zaune kawai tuni zanin da ke jikina ya yi ta kanshi nima ina ta kaina na fahimci gajeruwar naguda zan yi. Haihuwa ce gadan gadan ta taho mini ban shirya ba.
"Ba lokaci Yallaɓai. Ba lokaci ka zo ka zoo.."
Na faɗa da ƙaraji jin abu na turowa ta gaba na. Kan ɗa ne ya turo, Yallaɓai ya ruɗe bai taɓa ganin haihuwa ba sai ranar shima da ya matso kusa na riƙe shi gam ina nishi amma bakina bai mutu ba.
"Zai fito. Zai fiiiiii.. too.."
Na faɗa ina karta kumbuna na a jikin fatar hannun Yallaɓai saboda nishin da nake yi, ga kan ɗa na ƙoƙarin fitowa da Yallaɓai ya leƙa ya gani sai ya ruɗe faɗi yake yi" Ga shi nan fa zai fito na shiga uku.".
Ya faɗa cikin fitan hayyaci..
Ni dai bam san yadda a ka yi ba domin kamar na shiɗe ne da na yi wani irin ƙarfafan nishi ina ƙara damke hannun Yallaɓai ihun har sai da muryata ta dishe. Sama sama na ji abu sulumf sulumf har sau biyu ya faɗo lokaci ɗaya da kukan jaririya
"Inyainya. Inya."
Sai na koma na kwanta a ƙasan tayels ɗin dake bedroom ɗin domin cafet ɗin yana da ga wajen ƙuguna ne, wajen kaina kuma tayels ne haka na ji jikina ya saki yaraf na kwanta kawai ina maida numfashi ina jin Yallaɓai cikin fitan hayyaci yana faɗin.
"Sadiya kin haihu. Wallahi kin haihu."
Muryansa cikin farinciki da wani irin ɗimuwa mara misali.
Ni kuma ina ta sauke ajiyar zuciya a jere ga zufa da ya wanke minu jiki kamar an kwarara mini ruwa. Haihuwa na yi cikin abin da bai gaza da mintina goma ba. Allahu akbar Allah shi ne Ubangiji mai yin yadda ya so a lokacin da ya so.
"Alhamdulillah."
Alhamdulillah'
Na ke faɗa a zucci da sarari saboda Ubangiji ya yi mini sutura na haihu a cikin ɗakina tare da mijina cikin lafiya da ƙarfina. Allah ne abin godiya.
*Janafty**TKGB3H08*
*Littafin TURKEN GIDA 1K ne on Telegram. 09069067488.*
Kina buƙatar kayan kitchens domin ƙawata Kitchen ɗin ki? Ya ke Uwargida kina buƙatar chanza ma megidan sabbin kwanukan cin abinci? Ko kina buƙatar sauya masa kofin shan ruwa? Ko kina so ki burgeshi da farantai masu kyau da yarari? Ko Amarya ce yar ƙwalisa da ke son ƙawata gidanta da kayan alfarma? To ku matso kusaa domin JANAFTY EXLUSIVE AVAILABLE Muna kawo muku ko wani nau'in kayan Kitchen da na kwalliya gida domin farincikin ku, kuma akan farashi mai rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina daga in da muke, ku tuntuɓemu ta wannan lambar domin ƙarin bayani.
09069067488
+234 706 234 9732
Ganin da na yi Yallaɓai a ruɗe yake, ni kuma jikina duk ya saki ina kwance itama jaririyan na kwance cikin ƙazanta tana ta callara kuka, tun lokacin da ta faɗo ta callara kuka na san cewa da gaske ƴa mace na sake haifa.
Sai na kira sunan Yallaɓai ya taho wajena sai na ce ya kamani cikin rawan jiki ya kamani na tashi zaune. Sai a lokacin na fahimci jaririyar tare da uwa mahaifa ta faɗo shi ya sa na ji fitowar abu sau biyu daga ƙasana.
Zanin da ke jikina da ya yi gefe na ce ya ɗauko jiki na rawa ya tashi ya ɗauko sannan na ce ya buɗe dirowan gadon mu ya ɗauko kit ɗin mu na magunguna akwai reza a ciki, bayan ya kawo mini na karɓa na rike jaririyan shi kuma na ce ya riƙe zanin na saka ta a cikin zanin tana hannun shi sannan na daidai ta na yanke cibiyar na ce ya matsa daga wajen tun da gabaɗaya mun yi dama dama daga ni har shi cikin kazantar haihuwa.
"Ya zan yi mata Sadiya?
Ya faɗa yana kallona ya na kuma riƙe da jaririyar.
"Ka naɗe ta a cikin zanin ka kwantar da ita a kan gado ka zo ka kama ni na tashi."
Haka ko a ka yi bayan ya kwantar da ita sai callara kukan jarirai take yi ya zo ya kamani na tashi tsaye. Na saka shi ya buɗe karamar akwatina in da na tara kayan haihuwa na ce ya ba ni na ɗaura. Bayan na ɗaura na ce ya je ya saka min ruwa a hiter tiolet da gudu ya fita ni kuma na tattaka ina ware ƙafa domin sai ina jin kamar na ƙaru ta ƙasana na isa in da yarinyar ke kwance na ƙura mata ido ina kallonta lalle dole ta ci sunan uwata. Domin a kammanni ma ni ta ɗauko.
Yallabai ya dawo ɗakin ya ganni tsaye ina kallon ta yana zuwa na kalle shi da mirmishi kafin na ce.
"Alhamdulillah mace na haifa Yallaɓai. Mace Allah ya sake ba mu"
Sai kawai ya rumgumeni bai damu da yanayin da nake ciki ba. Cikin tsananin farinciki ya ke faɗin.
"Alhamdulillah. Allah na gode maka da ya sake nuna mini wannan ranar"
Wai a haka don ƙarfin hali Yallaɓai sai da ya sumbaci bakina na ture shi ina faɗin" Ko minti goma ban yi da haihuwa ba Yallaɓai?
Sai ya yi mini dariya kawai bai ce komai ba.
Shi na saka ya kwashe kayan su Jidda dake zube akan gado ya saka musu cikin wardrope kar su ɓaci. Ba ni da tsummokarai sai kawai na ce ya kwaso doguwayen rigunan da na ɗinka na yi amfani da su lokacin ina da ciki waɗanda shi da kan shi ya saka musu suna da buhu in naɗe kazantar da su kawai a kai su bola bayan an wanke tun da sun gama amfani.
Jaririyar kuma na goge mata jiki da dotel, tare muka goge kazantar ni da Yallaɓai ina cewa ya bar shi yana mini faɗa wai na mayar da shi mara tausayi ta ya ina cikin wannan halin zan ce ya koma ya zauna yana kallona ai sai na yi shuru. Tas muka gyara wajen duk da ba sosai ba amma mun goge kazantar haihuwar. Ita kuma uwa mahaifa na ce ya je ya haƙa rami a haraba ya rufe. Ya ɗauka cikin wani zani ya fita dashi ya je ya rufe bayan ya dawo ya sake fita da cafet tun da a kan shi na haihu na ce ma Yallaɓai kawai a wurgar da shi ya ce a'a sai an wanke in zan yi kyauta da shi ne sai na yi amma ba zai bari a wurgar da shi ba.
A baho babba da ya ɗauko muka tara kayan da muka yi gogen-gogen na ce ya fita dashi can ta ƙotar kitchen.
"Kar ka ce kuma za ka wanke ka bari su Ya Aina su zo don Allah.'
Sai ya ce minI to, sai da ya dawo ne na ce ya miko mini wayata, tana falon su Jidda ya je ya ɗauko ya kawo mini jikin sa na rawa. Jaririyar na jikinsa ya nace sai da na ba shi ita.
"Kar ta ɓata ma ka jiki. Kasan gogewa kawai na yi ba a yi mata wanka ba.'
"To ai jikin nawa ya riga da ya ɓaci ba matsala in ta ƙara ɓatawa"
Sai da ya yi magana na lura shima dogon wandon da ke jikinsa duk ya ɓaci da jini har farar vest ɗin jikinshi wa ya ga maza yau sun yi aiki.
Ya Aina na kira na ce mata ta zo gida na haihu.
"Ke Sadiya"
"Wallahi da gaske Ya Aina. Na samu ƙaruwan mace."
Sai ta yi kabbara kafin ta ce min gata nan zuwa domin na ce ta yi sauri ko yarinyar ma ba a wanke ba
Sai da na gama wayar na duba lokaci sha biyu ne da wani abu zai iya zama gab da sha biyun na haihu ko kafin ma.
Saboda na kira Ya Aina ya sa na matsa Yallaɓai ya je ya yi wanka jikin sa ya ɓaci.
"To ke da ita fa?
"Za mu yi in Ya Aina ta zo.'
"Amma za mu je asibiti a duba mini ku ko?
Sai na yi dariya kawai ganin yadda ya kama jaririyar ya rumgume.
"Za mu je asibiti mana. Ka je ka yi wanka kafin ta zo"
Da kyar ya ba ni jaririyar nan ya tafi ya yi wanka nima ya bar ni rumgume da ita har lokacin ina yi ma Allah kirari. Ina jin jini na zuba ta ƙasa na Allah ya sa na samu wani zani na tara a ƙasa na kafin na yi wanka. Na yi ta ma Allah kirari ina riƙe da kyautar da Ubangiji ya sake yi mini bayan na fidda rai. Ina ta hailala da kabarbari a cikin zuciyata domin Allah shi kaɗai ne wanda kum fa ya kum ne a lokacin da ya so a lokacin komai yake faruwa.
Ina nan zaune Yallaɓai ya fito wanka, yana ma saka kaya ne Ya Aina ta kira wayata da cewa ga ta nan a bakin get shi ya sa a gurguje Yallaɓai ya shirya ya fita ya je ya buɗe mata suka taho ciki a tare yana gaba tana bin shi a baya har cikin bedroom ɗina sai ga shi ta ganni a zaune gefen gado riƙe da jaririya ai sai ta riƙe haɓa kafin ta ce.
"Ikon Allah da gaske dai kin haihu?
Sai kawai na yi mata dariya ba tare da na yi magana ba.
"Wallahi Ya Aina ni kaina na yi mamakin haihuwar nan, abin da bai gaza mintina goma ba har ta haihu."
"Sannu Dubu. Sannu Dubu na ce barkan mu da arziƙi."
Ta faɗa lokaci ɗaya tana karɓan jaririyar da ke hannuna ni kuma sai na sakar mata ina faɗin" Yauwa Ya Aina."
Na faɗa ina mata mirmishi, gefena ta zauna a kan gadon ta na kallon jaririyar kafin ta ce" Ma sha Allah. Ga ta nan ko kamaanninki ta ɗauko Sadiya"
"Shi ya sa na ce ta gama cin sunan Mama."
"In sha Allahu."
Yallaɓai ya ba ni amsa lokaci ɗaya yana kallona nima shi na kallah ina mai jadadda masa godiyata ta idanuwana. Ya Aina ko sai washe baki take yi cikin hamdala. Yallaɓai ne ya yi maganar tafiyar mu asibiti ya sa ta tashi ta ce bari ta saka ruwan zafi ta fara yi ma jinjirar wanka sai na ce akwai ma ruwan zafi a hiter ta tiolet
Sai ta ce to bari ta yi amfani dashi bam damu ba sanin duk abin da ya kamata za ta yi kamar yadda ta yi mini a haihuwan Baby ita ta yi jinyata a asibiti har muka dawo gida shi ya sa nake ganin ƙimar Yaya Aina ta na yi ma zumunci kara da jikinta da aljihunta.
Nan ta bar ni da Yallaɓai zaune mun ta sa jinjira muna kallo bakin mu ya ƙi rufuwa sai da ta ɗebo ruwan a baho sannan ta karɓe ta. Tas ta yi mata wanka bayan ta yi ta sauya ruwan Yallaɓai na faman kai da kawo, ta saba saboda in dai na haihu kaf dangina da dangin Yallaɓai sun san shi ba mai zama ba ne, da shi za a yi ta shiga da fita in na kamawa ne ya kama sai ya ga jama'a sun taru ne yake haƙura ya fice daga gidan. Na taɓa jin Anty Maimuna na yi masa tsiya a haihuwan Anwar wai yadda suka san shi da hidima a kaina in na haihu amma Gimbiya an mata aiki a asibiti ya bar gida kaca kaca bai iya gyara komai ba. A gabana ne ranar na je giden bayan an sallamota kai tsaye ya ce Sadiya kika ce, ba lalle abin da na ke yi a can na yi shi a nan ba. Sannan bai zama dole shima abin da na ke yi anan na je can na yi ba. Tana jin haka sai ta yi shuru ni ko a fili ma sai da na murmusa ban ji wani mamaki ba saboda sai da a ka yi mini kishiya na fahimci abu kaɗan ma da bai kai ya kawo ba in ba ka kai zuciyarka nesa ba sai kishi ya turniƙe ka.
Shi ya jawo mata akwatin da na haɗa kayan haihuwan ta shirya jaririyan cikin kayan sanyi masu kyau bayan ta shafe mata da man zaitun ta kuma gasa cibiyar sosai ta saka mata mgani saboda ta yi saurin faɗi, ta nannaɗeta cikin towel ta miƙa ma Yallaɓai da yake jira daman. Faɗa mini yake yi yanayin jikinta irin na Baby ne ƙatuwa ce mai kiɓa haka na haifi Baby kuma har gobe ta na nan da ɗan jikinta kuma wannan jikin na su Anty Bahijja ne ko na ce na Nene domin har yanzu da shekaru suka tura akwai jiki a tare da ita. Nan muka bar Yallaɓai Ya Aina ta iza ƙeyata tiolet ta kama mini na gasa jikina kuma sosai na ji daɗi a ciki ta bar ni ta fita zuwa kitchen ashe tea ta haɗo mini mai kauri da ƙwai sannan ta kawo min saban buredi ta bincika ta ga ma ina da garin kunu amma ba shi da yawa sai ta yi ma Yallaɓai maaganar gero sai ya ce in ya fita zai yi magana za a kawo.
Ko da na fito shi yake faɗa mino ya yi ma ta huɗuba da suna Rukayya bayan ya lasa mata dabino a bakinta.
"Allah ya raya mana Ruƙyyaatu Yallaɓai na."
"Na gode. Na gode. Na gode da wannan martabawan na ka. Ubangiji ya yi maka sakamako da wannan karan da ka yi mini."
Kafin ya yi magana Ya Aina ta dawo ɗakin tana tambaya ta omo sai na ce ta duba a dirowan kitchen duk da bai da yawa sai Yallaɓai ya ce in rubuta duk wani abu da ake bukata za a kawo anjuma.
Ta juya da nufin fita sai na kira ta ina faɗa mata Yallaɓai ya yi mata huɗuba da sunan Mama.
"Ma sha Allah. Allah ya raya mai sunan Mama. Allah ya sa ki biyo halin mai sunan."
Dukkanmh muka amsa mata da Amin Amin nan ta fice ta bar mu. Yallaɓai na riƙe da ita na shirya na saka wata doguwar rigana sai gashi ta shige ni, na ɗan ragu amma ciki na nan kamar ban haihu ba sai da Yallaɓai ya ce ko akwai twin ɗin Rukayya ne a ciki ba mu sani ba ina dariya na ce wani twin jini ne a ciki a hankali a hankali zai ta sauka amma zan ɗan riƙa ɗaure shi saboda koyarwa iyayen mu na da kenan ka riƙa ɗaure ciki a cewarsu in ka sake shi haka shi kenan zai bi jikin ka. Pamper na saka na tare ƙasana da shi sannan na zauna ina zaman ƙaryawa na biyu domin sai na ke jin kamar na shekara ne ban saka komai a cikina ba saboda yunwar da na ke ji ina tusa buredi a bakina ina kallon Yallaɓai na yi mata hoto.
"Yallaɓai ba ka sanar da kowa haihuwan nan ba fa."
"Zan sanar yanzu."
Ya faɗa yana ƙara yi mata wani hoton har yana wani karkacewa sai da na yi dariya. Ni dai ai na sha mamakin yadda na iya ta da jug guda da tea na kuma haɗa da ƙaton saban buredi na cinye ga ƙwai manya faifai biyu lalle a gaida Haihuwa domin wani abu sai haihuwa in ba haihuwa ba da cikin jego ba ina ni ina ta da wannan uban ruwan shayin? Haka na faɗa ma Yallaɓai da na ga yana kallona sai ya yi dariya kafin ya ce.
" Ni wallahi hankalina baya kan ki. Ban ma lura da aikin da kika yi ba. Na ce to sannu da aiki Umma Sadiya."
Sai na fashe da dariya yana ta ya ni, a gurguje na shirya muka yi ma Ya Aina sallama muka fita muka barta tana ta wankin kayan haihuwa. Wayata ma a gida na bar ta, muna hanya ne, na ce ma Yallaɓai alkunyar Ruƙayya za mu riƙa kiran ta YUMNA.