Turken Gida Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   34 / 55

99K to 102K   out of 163.1K words

ne sai da na dago kaina na ga kallona yake yi na wani lokaci sannan ya gyaɗa kai ya yi wani mirmishin su na manya kafin ya ce.

"Dubu ba dai kina so ki faɗa mini rashin kunya kika yi ma mijin naki ba?

"A'a. Kawai dai raina ne ya baci nima na ma yar masa da martani Alhajimmu."

Sai ya yi dariya wannan karon mai sauti kafin ya ce" Hohoho hausawa suka ce ko shekara ɗari ka yi baka haɗu da mutum ba. In ka fara ganin shi tambayi halin shi, domin hali zanen dutse ko zai iya sauya komai to ba zai iya sauya wannan halin na shi ba."
Na yi kasaƙe saboda ina so na fahinci in da maganar Alhajinmu ta dosa.

"Dubu na san ki sarai bakin ki ba ya iya shuru. Kina da saurin hasala da faɗa. Kina so na ce kinyi daidai da abin da kika yi ne? To ba zan ce kin yi daidai ba sai ma na kira sunan ki ki amsa na sanar da ke da kaushin murya da cewa ba ki kyauta ba."

Baki na buɗe ina kallon Alhajinmu. Duk da na san halin shi amma ban tsammaci zai iya cewa wai ban kyauta ba? Me na yi na rashin kyautawar?

"Na san a cikin zuciyarki kina ta tamtaman me kika yi na rashin kyautawa ko? Duk buɗe kunnuwanki da kyau Dubu. Kin yi rashin kyautawa da yawa a cikin duka abin da ya faru. Kuma hukuncin da Yusuf ya so yankewa yana kan daidai ne shima. Tun da ba a gaban shi komai ya faru ba shima faɗa masa aka yi, kuma da bakin ki kika ce daga can gidan abokiyar zaman taki an faɗa masa ƙarya da gaskiya. To ke me ya sa da ya zo gare ki, ba ki zaunar da shi kin faɗa masa gaskiyan abin da ya faru ba?

"Alhajinmu bai ba ni da mar haka ba faɗa kawai yake yi ta in da yake shiga ba ta nan yake fita ba."

"Shi ne kuma yana faɗa kina fada. Har kika yi masa rashin ɗaa da gatsen ko yanzu ya ce ki bar masa gida za ki ta fi ko? To menene abin kuka don ya yi miki abin da kika bukata Dubu?

Ai sai na kasa mgana na dukar da kaina kasa. In Alhajinmu ya saka a ɗaki tun kana jin kana da gaskiya sai ka sare ka fahimci kai ne ba ka da gaskiya saboda irin kalaman da yake amfani da su wajen jawo hankalin mutum

"Ni da ke nan da Yusufa zai ƙara aure na kira ki, a wannan falon kika zauma kamar haka na yi miki nasiha? A cikin duka nasihin da na yi miki wata kalma na yi ta jadadda miki da in kika rike ta zaki rabauta?

"Haƙuri. Ka ce na je na yi ta hakuri wata rana ni ce zan zama mai riba."

"To ashe ba ki manta ba? To me ya sa yanzu kika kasa haƙurin kika kuma kasa rabauta da sakamakon masu hakuri?

Sai kawai na sake fashewa da kuka ina fadin" Alhajinmu na yi ta haƙru wallahi ba ka san hakurin da na ke yi ba ne. Ko wani abu ne suka yi mini da na tuna da nasiharka na ke ma yar da komai ba komai ba. Yau ma ɗin ya ƙure ni ne shi ya sa na tanka masa."
Na gama faɗa ina ta jan hanci saboda kuka.

"Du ka na ji kin yi haƙurin a baya amma abin da kika aikata yau duk ya kore wancan haƙurin na ki na baya "

Na ma kasa mgana na buɗe baki zan yi sai na ma yar na rufe. Ni fa na manta ne in dai Alhajinmu ne ba zai taɓa bani goyon baya ba da gaskiyan Gwaggo Alhajinmu na ganin ƙimar Yallaɓai a duk cikin surukansa ya sha faɗa ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba.

"Kina maganar ke ma da kika haihu ba ta zo ba kaza da kaza ina ruwan ki da wannan? Ke dai ba ki yi don Allah ba ai bai kamata,ki duba ita abin da ta yi miki ba. Ke kin yi mata domin Allah da zaman tare. Ruwanta ne ta ma yar miki da martanin Alheri ko sharri. Ke dai Ubangiji ya yi amfani da zuciyarki kuma ladan ki na wajen Allah. Ba hujja ba ce mijinki ya ba ki umarnin ki je asibiti ki dubata ki yi zaman ki, ki ƙi zuwa kin ga kenan kin saba umarninsa kuma mala'iku sun yi fushi dake matuƙar ba ki nemi gafaran shi ba. Sannan kuma abin da ya faru yau sanadin ki ne, ko da ruwan zam zam ba za ki iya wamke kanki ba tun da kin je wajen sannan waɗanda ke tare da ke ne suka yi hatsiyani ni da ke mun san ke ba ki saka su ba amma ba za mu ƙi gaskiyan cewa a sanadinki suka yi komai."

"Wallahi ni Alhajinmu ban ce kowa ya yi faɗa saboda ni ba."

Na fada ina ƙara rantse masa da Allah.

"Na ce miki ni da ke mun san ba ki saka su ba. Amma shi da sauran mutane in suka ji labarin za su yarda ba bakin ki a ciki! Ki yi tunani ki gani. A wannan gabar Yusufa ba shi da laifi abin da ya ji da shi zai yi amfani."

Ina sharan ƙwallah na ce" Amma me ya sa ba zai yi bincike ba sai ya rufe ni da faɗa har yana ce mini ina da mugun nufi a raina?

Dariya na ga Alhajinmu ya yi kafin ya ce" Dubu ke kika jawo duk zargin da ya yi miki. Me ya sa kika bashi kofar ya fahimci kamar kina jin haushi da haihuwar da aka yi mass? Ki tuna  shi ma fa ɗan adam ne yana da zuciya kamar yadda kike da ita. Sheɗan ne ya kawata masa a zuciyarsa amma ina da tabbacin ba haka yake nufi da gaske ba. Ai in da kima da mugun nufi akan matarsa da tun a farkon auran shi zai fahinci haka."
Ni sai na ga kamar kawai ina zaune Alhajinmu na ta faman boye laifukan Yallaɓai yana bayyana nawa.

"Har fa ce mini ya yi wai ina kishi da tana haihuwan Maza ni kuma Allah bai ba ni ba "

Na faɗa hawaye na kece mini saboda takaicin kalamansa.

"Haka zai yi tunani haka ma kowa zai yi tunani. Haihuwa kuma na Ubangiji ne daman Allah ya faɗa mana wasu zai ba su maza da mata, wasu mata kaɗai wasu mazan kaɗai wasu ma har su koma ga Allah ba zai ba su haihuwan ba ki godema Allah kina cikin zabaɓɓun Ubangiji. Maganar ita tana yin farar haihuwa ki bar ta da tunaninta, tun da ai shi mijin na ku bai ce ba ya son matan ba duka yana so kuma duka ƴaƴan shi ne. Sai ki roƙi Ubangiji ya baki mai albarka daga Mazan ko daga matan."

Kawai sai na cigaba da sharan ƙwalla domin ni dai Alhajinmu ya gama ƙure duka mganganuna.

"Ki yi haƙuri ki daina kuka ba wai ina goyon bayan shi ba ne a'a ina faɗa miki gaskiya ne a matsayina na adalin Uba. Ba wai don kina ƴ'ata na goyo bayan ki ba, a'a ni ke da shi duka ƴaƴana ne zan yi miki adalci kamar yadda zan yi masa. Ki daina kuka ya isa haka nan ba wani abu ba ne. Kawai sheɗan ne ya shiga tsakani ganin kun kasa samun fahimtar juna."

"Alhajinmu ta ya ya zai fahimce ni?

"Ta hanyar amfani  da kalamai na kwantar da hankali kar ki ɗaga sautin ki sama da na shi, na tabbata da kin yi haka da kun fahimci juna.'

"Uhm"

Na sha numfashi saboda na fahimci Alhajinmu ba zai gane karatun kurma ba.

Murmishi ya yi ganin na yi shuru yana kaɗa kai ya ce" Kukan ya isa kin ji share hawayen ki."
Ban yi musu ba share hawayena.
"Yau kike so ki koma gidanki ko sai gobe da safe?
Na kalli Alhajinmu baki buɗe kafin na ce" To kore ni fa ya yi me ya sa zan koma?

"Ashe ba yanzu na gama yi miki nasiha na ganar da ke kuskuran ki ba? To za ki koma gidan auran ki in sha Allahu. Shima ai na san yana can cikin damuwa in bai zo a daran nan zai da safe ina da tabbacin haka"

Kallon Alhajimmu na ke yi na kasa mgana yadda kawai yake da confident a kan Yallaɓai ke ba ni mamaki. Don ba warware masa komai ba! Ai wallahi da ya san wani abu da tuni zai daina wani cika baki a kan shi.

"Har gobe ina ganin sa da ƙima. Tun bayan shekaru ashirin da doriya na ba shi amanarki dai dai da rana ɗaya bai taɓa kawo mini ƙaran ki ba. Ko da yaushe ya zo gaisheni godiya yake yi mini yana yaba miki. Duk da na san kina saɓa masa shina haka amma bai taba fada mini saɓanin alherin ki ba. Ya zauna dake cikin daɗi da rashin sa. Kema ai ba ki taba kawo mini ƙaran sa ba sai yau. To na yau ɗin ma duk kishi ne shi ya sa ban ɗauke sa wani abu mai girma ba. Ki koma gidanki ki daidaita da mijinki domin yana yi miki kara ba domin komai sai domin yana son ki. Ki je ki ba shi haƙuri ki kara haƙuri  Mai hakuri in ya yi ta shan haƙuri ba ya kiɓa lokaci ɗaya amma watan wata rana zai zama giwa in har ya koshi da hakuri"

"Ki yi hakurin kin ji ko?
Ki koma ki cigaba da Biyayya aure. Domin Aljannarki tana a karƙashin diga digin mijin ki ne Dubu. In kin yi masa biyayya ki rabauta. In kin saɓa masa ki taɓe. Ni ba ruwana na riga na sauke haƙƙin Ubangiji na in kin bauɗe na faɗa miki gaskiya."

Na yi shuru ban yi magana ba kaina na ƙasa amma na daina kuka.

"Kin ji ko?

Ya sake faɗa yana kallona sai na gyaɗakaina kafin na ce" In sha Allahu Alhajinmu na gode Allah ya ƙara girma."
Ya amsa da Amin kafin ya cigaba da faɗin" Da dake da Rahila ne na ke yawan kafa misali da ku. Na kan ce tun da na aurar da ku ba ku taɓa tada mini hankali da korafin mzajen ku ba. Sannan suma ba su taɓa kawo mini maganar sharrin ku ba sai alheri. Amma sai ga shi a wancan satin nan in da kike zaune Muntari ya zauna yana karanta mini wani abu daga cikin na ƙuntata da Rahila ta ke yi masa ya kasa haƙuri ya kasa tanƙwasata sai da ya karya kaurin nan ya zo gabana yana faɗa mini na kira ta na yi mata faɗa. To kema ko sati ba a yi ga ki nan zaune kina kawo mini suka akan mijin ki, ke da Rahila kuna so ku ba ma misalina kunya ne?

Da sauri na ce" Ba za mu ba ka kunya ba in sha Allahu Alhajinmu."

"To na ji daɗin haka. Allah ya sa. Allah ya yi muku albarka addu'ata a koda yaushe ya zaunar da ku lafiya sannan ya yalwata ma mazajen ku samun su yadda za su riƙe ku bisa gaskiya da amana."
.
Na amsa da Amin kafin na yi tambayar da ke sosa mini rai.

"Alhaji me Rahilan ta yi ma Ya Muntari?

"Ina ruwan ki? Wannan tsakanina da ɗana ne. Ya faɗa mini kuma na sauke haƙƙi na kirata a wannan falon na yi mata faɗa ta yi mini kuma alƙawarin ta daina. Kamar yadda kema ba zan yi taɗin nan da kowa ba itama ba zan zo ina faɗin rashin kyautatarwarta ba. Ni kamar alƙali ne shi kuma alƙali ana son shi da gaskiya da rike sirri "

"Ai ni za ta faɗa mini Alhaji"

Na faɗa ina mirmishi shima mirmishin ya yi kafin ya ce" Wannan shima dai duk tsakanimku ne. In ta faɗa miki ba ta yi laifi ba. Domin tare kuka tashi kuka girma, akwai sirrukan masu yawan da zaku tattauna a tsakaninku na yan uwa."

"Haka ne Alhaji."

"To kin gani. Allah ya yi muku albarka gabaɗaya. Tashi ki je ki samu wani abu ki ci sannan ki kwanta da safe ki koma ɗakin mijinki ki tallafi yayanki. Ke da kika kusa kai ga suruki Dubu amaryata da na saka ana can jami'a ana ta karatu ko?

Ina dariya na amsa masa" E Alhaji amma ai ta ce ba ta ssku ba auranku na zoɓe ne."

"Manta da ita, ga matata ta gaskiya me zan yi da ta roba?
Amma dai ina nan ina jiran ta a falon nan ta kawo mini suruki na ga ko na fishi dogon hanci."

Me zan yi in ba dariya ba, da man shi Alhaji dariyan ya ke so na yi.  Ya sallame bayan ya ce na ce Marwanatu ta zo su gaisa ita da wannan yarinyar na ta mai kukan tsiya duk ta cika masa kunni.
Na fita ina dariya na koma ɗakin Gwaggo na iske su suna ta hira na faɗa mata saƙon Alhaji sai ta sunkunci yarta ta fuce tana faɗin" Shi ta ke jira ya lallasheta."
Bayan fttan ta Gwaggo ba ta matsa mini sai ta ji yadda muka yi da Alhaji ba amma dai na faɗa mata zan koma saboda Yumna.

"E gaskiya ya kamata baiwar Allah na san za ta sha kuka."

"Wallahi  Gwaggo Nonuwana har sun fara tasawa."

"Wayyo sannu. Ko za ki sha panadol ne in kin ci abinci."

"To Gwaggio"

Ita ta kawo mini abincin Tuwo ne miyar kubewa bushasshiya. Na ci da yawa muna hira ban gama ba Marwa ta dawo ta ce ma Gwaggo ta je ta ba ma Alhaji Tuwo kafin ya suma saboda Yunwa.

"Ai  da man ke ce kika tsayar da shi, amma shi uwarhaka ai ya koshi ya kwanta."

Muna ta dariya ta fice ta bar mu, Marwa ta zauna muka ƙarishe cin tuwo da ita ta fita da kwamukan ta ɗibo mana ruwa na sha mgani da shi.
Akwai katifa a ɗakin Gwaggo ita Marwa ta shimfiɗa za ta kwanta ni kuma na ce ina gado
Na yi mata sai da safe ganin waya a hannunta sai na yi tunanin mijinta za ta kira.
Har na juya ta kirani.

"Umma."

Na juyo ina kallonta.

"Za ki koma ko?

Sai da na yatsina fuska kafin na ce" Alhaji ya matsa. Zan koma gobe in sha Allahu."
Sai ta kama murna. Na yi shigewata na bar ta. Kayan jikina na cire, na samu wata rigar Gwaggo ta makka ce Ma'u ta kawo mata ita da daɗewa lokacin da mijinta ya koma. Gwaggo a lokacin ta ce ba ta so wai na yara ne muka matsa mata ta karba. Ashe za ta yi mini amfani ita na zuba mai taushi har kasa na ɗaure kaina dakallabi na haye gadon Gwaggo. Na daɗe ban yi barci ba kewan gidana kewar 'ƴayana da mijina. Su suka taru suka yi mini rufdugu na yi ta juye juye sai can barci ya kwashe ni har ina makara sai da na ji Gwaggo na kiran sunana.

Sannan na iya tashi na je na ɗauro alwala na yi salla nonuwana sun yi mini nauyi sun kwana a ba tsotsa ina jin kamar zazzaɓi zai kama ni amma haka na fita na share tsakar gidan nan tas na haɗa wamke-wanke Marwa ta karba sannan na je na gaida Alhajinmu ƙara jadadda mini yake yi da na ƙarya na shirya na koma gidana. Ni dai ba ni da ta cewa daman ai dole na koma ko domin Yumna amma a kasan zuciya ina cewa ba don halin Yallaɓai ba shima.

Ɗumamamman tuwon jiya muka ci da safe, na ƙara shan panadol na kwanta da niyar na dan runtsa barci ya sarkeni, tun wajen tara na kwanta ni ce sai wajen sha ɗaya na tashi. Shima ɗin tada ni Marwa ta yi wai tana faɗa mini ga su Kawu nan.

"Wani kawun?

Na faɗa ina mitsike idanuwana masu cike da barci

Kafin ta samu zarafin magana na ji kukan Yumna ai da sauri da diro daga saman gadon Gwaggo a ƙofar falo muka ci karo da Baby ɗauke da Yumna tana ganina ta rumgumeni tare da Yumma tana faɗin" Umma mun yi kewarki jiya. Yumna ta kwana kuka Abba ne ya yi ta lallashinta yana ta ba ta tea"
A zuciyata na ce da kyau na ji daɗi da ya ɗanɗana.
Ture Baby na yi baya kaɗan ina karɓan Yumna wacce ke ta miƙo mini hannu tana faɗin Uma.

Da sauri na karɓeta na rumgumeta ni da ita muka sauke ajiyar zuciya kamar mun shekara ba mu ga juna ba..zama na yi a saman kujera na fara ba ta nono. Allah sarki baiwar Allah ta karɓe da sauri tana sauke numfashi. Ina shafa kanta ina mai jin tausayinta. Sai na ga an yi mata wanka itama Baby ta yi wankanta.

"Ba ki je makaranta ba?

"Umma mun fa makara. Abba bai yi barci da wuri ba sai 7:30am muka tashi fa."

Ta faɗa tana kirga mini da hannunta.

"Uhm wa ya yi ma Yumna wanka?

"Abba mana. Ni kuma na yi da kai na shi ya soya mana doya da kwai Umma."

"Ya kyauta."

Na faɗa ina jinjina kai Marwa na kalla ganin tana ta shiri alamun kamar ta yi wanka ne.

"Gida za ki leƙa?

"A'a tafiya za mu yi"

"Ke da wa?

"Ni da Kawu mana. "

Sai ta ga na yi shuru ina kallonta sai ta yi dariya kafin ta ce" Umma ni da Baban Abadallah."

Sai na ware ido kafin na ce" Ya zo ne?

"Ya zo tun dazu tare muka zo da shi da Abba."

Baby ta fanshe ta sai na fara tunanin ko wa ya faɗa ma Kawu ko kuma dai ya zo ɗaukan Marwa ne bai san abin da ya faru ba sai yau.

"Ni ba ruwana. Nima da safen nan ya ce mini zai zo Abban Jidda ya yi masa waya akan kum samu matsala."

"Uhm"

Kawai na ce na cigaba da ba ma Baby Nono Jidda na ta yi mini surutu na yi kamar ban jiba. Wayata na gida ban san adadin waɗanda suka kira ni ba. Ba daɗewa muka ji muryan su a tsakar gida sai ga Gwaggo ta shigo da hijabinta tana faɗin"

"Ki ta so ta..'"

Ganina a zaune sai ta ce" Au ashe kin tashi? To maza ki shirya ga mijinki can na jiran ki."
Baki na tura kafin na ce" To ban yi wanka ba zan tafi Gwaggo

34 / 55