Turken Gida Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   7 / 55

18K to 21K   out of 163.1K words

farincikine ne a ƙalla dai ina da yaƙinin za ki sake haihuwa zan sake ganin ki ɗauke da cikina Sadiya"
Murnan da ya yi ta ba ni mamaki ban taɓa tunanin zai yi murnan in na ƙara samun ciki ba.

"Na yi kewar laulayin ki. Fushin ki in kina da ciki na yi kewar ganin kumbararun kafafuwanki. Na yi kewar ganin cikin ki ya turo Sadiya. Ina kewar ganin kina shayar da Baby everything da kika sani ina kewar shi a tare da ke"

Hawaye suka cika min ƙwarmin idanuwana.

"A ƙalla yanzu zan ta saka hop. Sannan zan ƙara dakewa ko? 

Ya ƙarishe faɗa yana mai shafa jikina.
Shi murna kawai yake yi.

"Kai ba ka jimamin rashin cikin da muka yi?

Sai sannan ya ɗan sauya fuska kafin ya ce" Na yi jimami sosai amma me ya fitar da shi? Wannan tafiyar da kika yi ranki a ɓace ko?
Ban ba shi amsa ya saka hannuna ya ɗan mari kan shi yana faɗin" Ni ne ko ? Ni ne ko? Sai kuma ya koma ya kwanta a kan cinyata ta wajen cibiyata ya na faɗin" Ni ne na ɓata ma Umma rai, laifina ne da ya sa muka rasa gudan jinnin mu. Sadiya ki yafe mini"

Ya faɗa lokaci ɗaya ya na rungumo cikina zuwa kuguna.
Sai na shafa kan shi cikin tattausan lafazi na ce" Ba laifinka ba ne daman can Allah ya yi ba mai zama ba ne."

"Kuma Allah zai ba mu wani ka ji ko?

Sai ya ɗago ya na kallona kafin na gyaɗa masa ina faɗin" In sha Allahu.  Kar ka damu.'
Sai ya sake komawa ya kwantar da kansa a cinyata yana faɗin" In sha Allahu ma ya bi cikin danshin ya shige.

"Me?

Na tambaya ina kallon shi.

Cikina ya shafa kafin ma ya yi magana na samu amsana sai na samu kaina da amsa wa da Allah ya sa.  Duƙawa na yi da kaina na sumbaci goshin sa.

"Ina ƙaunarki Sadiya ta."

"Nima haka."

"Kema me?

"Ina sonka Yallaɓai na."

Na faɗa ina yi masa murmishi, shima kallona ya ke yi cike da so da ƙauna.
Muna wannan kwanciyar ta soyayya na zayyane masa abin da ya faru a Kaduna da kwanakin da na yi a gadon asibiti.

"Ban ji daɗi da ba ni na wahala da ke ba."

"Haka Allah ya so."

"Allah ya saka ma Amina da mijinta da alheri."

"Amin Amin."

*****

Shike nan faɗa ya ƙare tsakanina da Yallaɓai ni da na ce ko na yafe masa ba zan manta ba sai gashi tuni na manta na kama mijina gam mun fi ma baya ɗinkewa da nuna ma juna soyayya. Jidda kam ta na lura da mun shirya ranar har tsiya ta yi mini  da ta ga na kira mai ƙunshi har gida ta na yi mini buɗe bakin yarinyar sai ce mini ta yi.

"Su Umma manya an gama fushi da Abba kuma yanzu an dawo ana yi masa kwalliya."

Da na balla mata harara sannan na rakata da daƙuwa sai ta shige ɗaki tana mini dariya. Da Yallaɓai ya dawo sai da na faɗa masa shima dariyan ya yi ta yi kafin ya ce" Ahto da gaskiyan uwata an gama min yanga da jan Aji an ga dai ba wani sai ni an dawo mini."
Da ya faɗi haka sai da na maka masa filon da ke hannuna ina kunƙuni ina cewa zan dai yi maneji da shi,  shi ko ya ce ko yanzu ya tashi ƙara aure zai samu budurwa ni kuma in na samu tsoho ma na gode Allah domin duk ya gama suɗe danshin haka na yi ta maka masa filo amma bai yi shuru ba sai da ya ƙarisa ai ko ya daku da filon kujera.

Amina ma sai da ta yi mini shaƙiyanci daga ta kira muna waya ina faɗin Yallaɓai ma ya ce a yi musu godiya ita da Dr.
Sai cewa ta yi" Ya Sadiya wai kin yafe ma Yallaɓan ne da har kika bashi labarin kin samu ɓari?

"To ya na iya Amina. Ya yi ta bani haƙuri sannan ya ce sharrin sheɗan ne shi ya sa na haƙura."

Sai kawai Amina ta fara mini dariya.

"Nan fa kika ce har abada ba za ki manta da abin da ya yi miki ba."

Cikin masifa na ce" Ai ban ce na manta ba na dai ce na yafe masa. Kuma kowa ai yana kuskure ko?
Ganin ta mai da ni mahaukaciya ya sa na kashe wayata ina masifa. Ni kaina ina mamakin yadda duk yadda na kai ga ƙullatan Yallaɓai da ya zo ya lallasheni ya ba ni haƙuri shike nan sai na ji na haƙura sannan na manta da komai mun cigaba da rayuwarmu kamar komai bai faru ba.

Ganin mun shirya ya sa na ce ya dawo mini da ɗana Khalipa. Ya na jin haka washe gari sai ga Gimbiyar ya kwaso mini ita da yaran gabaɗaya. Nan suka yi mini yini, har dare muna tare ranar kuma Yallabai ya na gidana ne daddare muna falon Yallaɓai yaran kuma suna falon su sai ga Baby ta zo kawo min ƙaran Khalipa wai yana mini tsalle saman kujera.

"Ƙyale shi Baby shima gidan su ne ki bar shi ya shaƙata"

Yallabai ya gano mgana na tusa masa ita kums sai ta miƙe tana faɗin don ya na gidan su ai ba za a bar shi ya yi ɓarna ba. Da motar ta  ta zo bayan isha'i ta tuka kanta da yara suka koma gida Khalipa da na ce a bar mini shi ta ce jibi za su tafi Rano ganin kamar ba ta son barin na shi ya sa sai na ƙyaleta Yallaɓai kuma na ji amma bai yi mgana ba.

Sai da muka yi shirin kwanciya sannan Yallabai ya yi maganar akan maganar da na yi ɗazu a kan Khalipa.

"Laa Allah ni ba da wata munafa na yi mganar ba."

"Uhm to shike nan tun da kin ce haka."

Da haka a ka bar maganar amma na ji sanyi a raina tun da ya fahimci in da magana ya dosa. Ni dai ban san ya abin ya ke ba amma ranar da Khalipa ya zo gidana zai kwana da ya yi barcin uban ya kai shi ɗakin su Jidda ya kuma ce ko zai yi kukan jini su bar shi in ya gaji zai kwanta. Sai ga shi ranar barcin mu ka sha, sai da safe Jidda ke faɗin ya tashi yana rigima ya na kiran sunan Abba da ya ga an yi banza da shi ne ya koma ya kwanta. Tun daga lokacin na samu lafiyan Khalipa a raina na ce daman iskanci ne da na yi shuru da yanzu an daɗe ana cuta ta.

Ganin mun samu jituwa da Yallaɓai a wani dare da yana gida na bayan mun gama samun natsuwa sai na ce masa ina so zan koma makaranta.

"Makaranta? Wata makarantar? Islamiya?

Yallaɓai ya tambaya cikin mamaki.

"A'a boko dai. Masters nake so na koma na yi."

Kawai ba sai Yallaɓai ya fara mini dariya ba sai ka ce ya ga mahaukaciya sabon kamu nan da nan na harzuƙa.

"Mene abin dariya a mgana ta?

Sai ya dakata yana faɗin" Ki yi haƙuri amma mganar ce ta ba ni dariya ke yanzu gotai gotai da ke da budurwan ƴ'a ki ce za ki koma makaranta?

"To ana girma da karatu ne?

"A'a kawai dai."

Sai kawai ya cigaba da dariyan shi. Na cika na yi fam ina shirin fashewa.

"Kin ga yi haƙuri."

"Izinin ka na ke nema shekaran da za mu shiga nake so na koma."

"To ai ni ba zan hana ki ba amma da zan ba ki wata shawara."

Sai na kalle shi ta wutsiyar ido duk da akwai duhu a ɗakin amma muna kallon juna ta hasken dake shigowa ta jikin labulan window ɗin bedroom ɗin.

  "Kina so?

"Ina jin ka"

Na faɗa a daƙune.

"Ki haƙura da karatun nan Sadiya. Digree gare ki fa yanzu mata ne nawa ne ke neman kwalin karatun ki ba su samu ba? Komawa makaranta abu ne mai kyau amma wahala kawai za ki ƙara ma kan ki a yanzu. Saboda ƙwaƙwalwar ba za ki haɗa ta da lokacin baya da na yanzu ba?

"Wannan ne shawaran?

Na faɗa ina kallon shi domin so na yi ma na juya masa baya.

"Shawaran ita ce ki bari kawai na ƙara miki jari ki cigaba da kasuwancin sai da hijaban ki kawai "

Ya gama faɗa har yana wata dariya. Raina ya ɓaci na ƙufula.

"Ka ba ni izinin na cigaba da karatun?

"Why not in kina sha'awa? Sai na ce Allah ya ba da sa'a."

"Amin"

Na fada azafafe sannan na juya masa baya sai ya biyo ni ya na faɗin" To jarin fa?
"Ba na buƙata"
"To shike ko kuɗina sun huta"
Ya faɗa yana mini dariya kara shige min ya yi yana tsokanata da Sadiya ta masu mastars ke dole sai kin kamo kwalin karatuna ina jin sa na yi masa banza domin haushi ya ba ni ya ina mganar cigaba na kuma yana mini dariya.

Tun daga lokacin ya samu sara da na yi magan sai ya ce su Sadiyallle masu degree da Masters ni ko na ce da ikon Allah, na gane in ina fushi ma ya fi jin daɗin tsokana ta sai na daina nuna na ji haushin shi,
Maganar jari kuma tun da na ce ba na so bai ƙara mini mgana ba, ni kuma da gasken ba na so shi ya sa ma har su Ya Hamza na faɗa ma zan koma makaranta da na ce Yallabai ya amince fatan alheri kawai suka yi mini.  Na gama shirina tsab saboda muna tunkaran sabuwar shekara da cewa ko Yallaɓai bai taimaka mini da sisin shi ba zan kwashe jarin hijabai na koma makaranta da shi.

****

*2020*

Da gaske na ke yi na nemi gurbin Masters a BUK Kano, kuma har na samu, har na yi cuku cuku, kuma ilai dai bangarena na farko na sake ɗauka na kula da tattalin arziki wato Economics
Sannan Jidda na son ta biya Jamb tun da sai bayan sun rubuta Jam ɗin za su fara jarabawar su ta WAEC.  Ko lokacin da Jidda za ta cike Jamb tare da Musbahu suka je ni ban san ina ta cike ba sai da ta dawo take faɗa minI a first chioce ABU Zariya ta cike.

"Ni dai ba ruwana kin san dai Abban ku ya ce a garin nan za ki yi karatu ba ya son nesa."

"To ni Umma ina son ABU ne kuma ai ba ga Kawu Hamza a zaria ba"

Kallonta na yi kafin na ce" Ya san da shi ɗin ya ce ba za ki je ba"

Za ta fara mini magiya na katse ta faɗin"
Ba ruwana na ma faɗa miki."
Ai ko da ya dawo ta faɗa masa ta sha faɗa ya kuma ce mata ta ma cire rai ba anan za ta yi ba BUK za ta yi domin ba ya so ta yi nesa.
  Jidda na ji ta na gani dole ta cire rai tun da Ya ce ba za ta je ba to mgana ta ƙare.

A she ya je sun yi mgana da Gimbiya itama ta roƙe shi, amma ya ce ya gama mganar sa. Ni daman ban saka baki ba sabo da tun da ya kafe da wahala ya sauya ra'ayi infact nima shirin nawa karatun nake  yi Yallaɓai tun ya na ɗauka wasa ne har dai ya ga na miƙe ga kaina. Wasu abubuwan duk ta online Datti ya yi mini su sauran kuma na shiga cikin makaranta na ƙarisa. Da dai Yallaɓai ya ga tabbas na samu addmission har ya na zuga ni wai na yi part-time.

Ni ko na ce full-time zan yi. Ɗa gare ni ko jika da zan yi part-time sai ya yi shuru. Ina shirin yin rigistration ne Yallaɓai ma ya ba ni kuɗi ya ce na hidimar makaranta ban tambaye shi ba kuma da bai ba ni ba, ba zan tambaya ba.
Kwatsam kawai aka fara cutar corona a Negeria, daman tun december 2019 cutar ta fara ɓulla a na mganar ta a kafafen sada zumunta.
Kafin a motsa ta fara yaɗuwa a Nigeria kafin ka ce me an shiga lockdown wannan hutun na corona shi ya ruguza burina na komawa makaranta Yallaɓai sai ya koma yana mini dariya har wani suna ya saka mini wai mai kwalin masters zaman gida dole.

Sai ga shi da ga ni har yara mun koma mun dafe a gida. Jidda ke ba ni tausayi su da ke da shirin zana jarabawar fita an yi musu tsiya.


*Janafty**TKG0B30D4*

*Littafin TURKEN GIDA 1K ne on Telegram. 09069067488.*

Kina buƙatar kayan kitchens domin ƙawata Kitchen ɗin ki? Ya ke Uwargida kina buƙatar chanza ma megidan sabbin kwanukan cin abinci? Ko kina buƙatar sauya masa kofin shan ruwa? Ko kina so ki burgeshi da farantai masu kyau da yarari? Ko Amarya ce yar ƙwalisa da ke son ƙawata gidanta da kayan alfarma? To ku matso kusaa domin JANAFTY EXLUSIVE AVAILABLE Muna kawo muku ko wani nau'in kayan Kitchen da na kwalliya gida domin farincikin ku, kuma akan farashi mai rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina daga in da muke, ku tuntuɓemu ta wannan lambar domin ƙarin bayani.
09069067488
+234 706 234 9732

Ban ji daɗin ɓullowar cutar corona ba, sannan ban ji daɗin lockdown ɗin da a ka san ya mana ba gabaɗaya ƙasa ta tsaya waje ɗaya cak. Ba makarantu ba zuwa aiki komai ya tsaya, in fita ta kama ka dole sai ka saka takumkumi kamar wani ɓarawo kana tsaka tsan tsan. Shikenan Burina na son komawa makaranta ya tsaya cak shima amma duk da haka ban karaya ba faɗa ma kaina nake yi na san na ɗan lokaci ne kasa za ta daidai ta na cika burina na komawa makaranta.

Kowa na cikin takura da wannan lockdown ɗin amma sai na ga kamar Yallaɓai shi murna ma yake yi, ko don ba aikin gwammati yake yi ba ne wataƙila domin ya ga na shi ayukan ba su tsaya ba ne shi ya sa. Sai daga baya na fahimci har da zama na a gida ban samu tafiya makaranta ba kamar yadda na ci buri saboda ba shi da aiki sai tsokana ta har wani suna ya saka mini yanzu Hajiya Saadiya mai kwalin mastes. In kuma ya tashi tsokana ta da cewa masu masters dai an koma zaman gida tun ina nuna jin haushina shi kuma ya yi ta dariya har wani jin daɗin tsokana ta yake yi ranar dai na gaji na ƙufulu na ƙudirta a raina in ya sake tsokana ta sai na mayar masa da martani kamar ya ko san ina jiran shi sai ga shi ranar ya kwana a gidan Gimbiya sai ya biyo nan gidan da safe mu gaisa sai ya iske ni na ci gayu na cikin riga da wando ina zaune a saman kujeran falon ina danna waya ta lokaci ɗaya kuma ina ɗan kallon talabijin ɗin da Baby ta kunna cartoon a ke yi a MBC3.

Da Surraya Dee mai kyan ɗa'a muke chart na tura mata ciko kuɗin ta domin satin da ya wuce na siya mganin sanyi da haɗin kaza. Tana ta mini tsiya saboda sai da ta ƙara kirana ta ce ta ji shuru ba ta ji ni ba, ni kuma na ce mata lokacin muna ɗan hatsaniya ne da megidan da ya ke ta san yanayin tun da itama matar aure ce. Ta ce Mazan ne sai a hankali su yi tutsu in sun so a yi daɗi ana yi in suka so tsiya ma sun san ta kan shi. Shi ne fa muke ta hira da ita a kan matsalolin rayuwa na yau da gobe.

Jidda na ɗaki tun da suka daina zuwa makaranta in dai ba aiki za ta yi ba tana cikin ɗaki tana karantu Baby ce yar falo mu yi ta hidiman mu, itama ɗin yau ta na can falon Abban na su ta na zane zane a takardu ta bar ni, ni kaɗai ina ta danna waya ta. To tun da an kulle mu a gida sai kafafen sada zumunta suka zama ababen debe mana kewa. Na ji shigowarsa suna mgana da Baby a falo ban tashi daga zaunen da nake ba sai ga shi ya shigo cikin shigar ƙananun kaya ni Yallaɓai har mamaki ya ke ba ni shi bai son ya girma ba ne? Ko don jikinsa ba ya nuna shekarun sa? Ya kama kafar wajen shekaru arba'in da bakwai amma kuma yana jin kansa kamar ɗan shekaru talatin.

"Wannan kallon fa Madam?

Ya faɗa lokaci ɗaya yana jan hancina. Ashe ya ƙariso har gaba na ban sani ba.

"Ko na yi miki kyau ne?

Ya sake faɗa yana mini murmushi har yana kashe mini ido ɗaya.

Sai na yi dariya kafin na ce" Wani kyau? Ina kallon ka ne, a raina ina cewa Yallaɓai na ya fara tsufa"

Yana zama gefena yana faɗin" Ko? Ke dai ce da mganarki amma ni har yanzu ji na, na ke yi kamar ɗan saurayi mai shekaru talatin."
Sai na buge kafaɗansa ina dariya kafin na ce" Jidda fa ƴ'ar ka ce? Ko ka manta ne?
Sai ya jawo kafaɗata saman tashi ya saka hannunsa guda ɗaya ya zagayo ƙuguna da shi.

"To sai me! Ke in ba fa na faɗa ba ɗan Saurayi a ke kallona. Kuma tsab in na tsai da budurwa yar sha za ta tsaya mini"

Hararan sa na yi kafin na ce" Wai ko dai ƙara aure da za ka yi da yarinya ƙarama ne Yallaɓai?

"Me kika gani?

Ya faɗa yana dariya ƙasa ƙasa.

"To na ga da an fara mgana sai ka ce ko yanzu za ka iya auro yarinya yar sha sa'ar Jidda."

"To in ma da gaske ne Haramun ne?

Ai sai na buɗe baki ina kallon Yallaɓai. Ganin na kasa mgana ne ya sa ya rufe mini baki yana mini dariya sai na ture shi gefe ina hararan shi. Shi kuma ya na ƙara naniƙe ni ina ture shi yana minidariya.

"My Sady kishi"

"Ina ruwana ai ba a kaina za ta zauna ba kuma ai ni ka gama mini kishiya. Gimbiya ce a kan layi "

Dariyan nishaɗi ya yi kafin ya ce" Ka ji ta kamar gaske"
Na yi masa banza saboda na ga alamun ya na so maganar ya yi dariya ya na jin nishaɗi. Da gaske nake yi ai ni ya gama mini kishiya ko wata zai aura sai dai Gimbiya ta ji ƙwatan ƙwancin yadda na ji a lokacin da ya auro ta. Kallon

7 / 55