Turken Gida Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   6 / 55

15K to 18K   out of 163.1K words

na ɗora ma su Jidda girki da man macaronin guda ɗaya na dafa.

Cous-cous na dafa mai kayan lambu daman kuma Yallaɓai na so shi ya sa na yi. Sai zoɓon da na haɗa daman tun safe na riga na dafa genyen zoɓon haɗawan kawai na yi. Sai sauran kayan marmarin da suka rage mana na yanka na yi mana fruit salad ni da Yallaɓai.
Shidda saura su Jidda suka dawo makaranta ajaran majaran saboda yunwa ko uniform ba su cire ba suka fara cin abinci. Baby na faɗa min Umma cikina kamar an kwashe min kayan cikina ina gefe ina ta yi mata dariya ganin tana cin abinci hannu baka hannu ƙwarya.

"Baby ki ci a sannu kar ki shaƙe.'

"Umma ba ki san yunwan da na ke ji ba ne"

Ina ta mata dariya ni na je na kawo musu da zoɓon ya yi sanyi na saka a firiza.

"Ya Jidda ke ma duk yunwar ba baka sai kunne?

Sunne kai ta yi ta na faɗin.

"Umma ni kin ji na yi magana ne?

"Ba ki ce komai ba. Ke dai ci abinci kawai."

Na faɗa ina yar dariya. Yarinya na jin yunwa tana noƙewa.

Bayan sun gama cin abincin sun ƙoshi, suka sauya kaya zuwa na gida lokacin an kira salla sai muka yi alwala muka yi salla yau ba mu yi karatu ba saboda wankin uniform muka fita  ta baya muka wanke su tare da yan riganunan barcin Baby da ƙananun wandunan ta daman Jidda ke wanke musu tare da na ta. Muna gamawa ana kiran sallar isha'i muka sake ɗauro alwala muka yi sallar isha'i. Muna idarwa ni kuma na faɗa wanka bayan na fito na yi gayu na cikin riga da zani na wata atamfata hollond ta na cikin kayan da na siya lokacin auran Yallaɓai da Gimbiya.

Na kashe ɗauri na ture ka ga tsiya na ba za gashina ya sauko har kafaɗuna. Har da su jan baki na saka na kuma zirara gazal a girana, na fita falo wajen yara da dai na ga shuru Yallaɓai bai shigo ba sai na diɓi abincina na ci na kora da zoɓo da fruit salat. Bai kuma shigo ba sai goma har ta ma gota. Tuni har na kaɗa su Jidda ɗakin su na ce su yi shirin kwanciya so ni kaɗai ya iske zaune a falon ina kallo duk da hankalina ba akan kallon yake ba.

Miƙewa na yi ina kallon shi, nufar sa na yi ganinsa da ledoji a hannunsa.

"Sannu da zuwa."

Na faɗa ina karɓan ledojin hannunasa.

"Yauwa Madam ya gidan?

Ya faɗa lokaci ɗaya yana sakar min ledojin a hannuna.
Na amsa da lafiya lau lokacin da na nufi kitchen na duba ledojin tsire ne sai fura mai sanyi an dama ta a leda. Na san ni ya siyo mawa da yake ya san ina son fura duk da cikina ya cika amma ta ba ni sha'awa zan sha zuwa anjuma in cikina ya sassaɓe.
Naman dai a firiza na saka shi  da safe sai mu ci na san na mu ne Yallaɓai ba ya son tsire ya fi son gashi na naman rago. Sai ya ce wai tsire duk ƙuli ne ba nama ba.

Ko da na fito ba shi a falon ya na ciki sai na koma kitchen ɗin na hada masa abinci na kai dining sai da na gama shirya masa duk abin da zai buƙata sannan na koma bedroom ɗin na iske Yallaɓai ya fito daga wanka ya na saka sauƙaƙƙun kayan zama cikin gida riga da wata ƙaramar riga mara hannu. Sai ma yau na ƙare ma Yallaɓai kallo da gaske kam Yallaɓai ya fara ijiye tumbi da na ƙura ma gashin kansa ido har na hango ƙyali ƙyalin furfura a saman kan shi har ma da sajen shi. A raina na ce su Yallaɓai tafiya ta fara miƙawa.

"Tunanin me Sadiya ta take yi ne ahalin ga ni a kusa?

Ya faɗa ya na mai sagalo hannun shi a kafaɗana sai na tattaro murmushi na kalle shi na yi masa.

"Abinci.?

Na faɗa ina kallon shi sai ya shafa cikin sa yana faɗin daman yunwar yake ji. Ya ƙi sakina ya na dafe da ni muka fita can falo sai da zai zauna saman kujeran dinning ne ya sake ni.
Nima gefen sa na zauna na zuba masa cous-cous ɗin da zoɓo sai fruit salaf ɗin sai ya ce na zuba masa leda ɗaya na fura yana so zai sha sai na koma kitchen na juyo masa a wani ƙaramin mug. Ina gefen shi har ya gama cin abinci kuma daga yanayin sa na fahimci ya ji daɗin haka. Barin ma yadda na ga ya ci abincin sosai da alamu dai yau Yallaɓai ya yi ta su Baby ta babuwa ta addabi cikin sa.

"Girki ya yi daɗi. Haka ma mai girkin ta yi kyau."

Ya faɗa ya na kallona sai na yi murmushi k amma ban ce komai ba.

Bayan na tattara abubuwan da ya ɓata na mai da kitchen ina dawowa ya ce wai kallo za mu yi, kujera mai zaman mutum biyu na samu na zauna amma Yallaɓai sai da ya biyo ni ya nane minI, ina basarwa ina komai karshenta dai sai gani a saman jikinsa kamar yadda muke yi a baya in muna kallo. Ɗankwalin kaina ya zame min yama ta wasa da gashin kaina shi ke kallon ni kuma na kwantar da kaina kawai a saman ƙirjinsa ina tunanin rayuwa juyi juyi. Yanzu fa yadda nake yi da Yallabai haka itama Gimbiya take yi da shi gabaɗaya sai na ji ƙuncin zuciyata ya dawo. Har wani gishiri gishiri na ji miyan bakina na yi saboda takaici ina jin sa yana ta ɓabatun magana amma ban biye masa ba.

"Ƙitson nan ya yi kyau. Yaushe a ka yi shi?

"Yau."

Na bashi amsa kai tsaye.

"Lalle ko za ki karɓi tuƙwaici domin kitson ya yi kyau sosai."

Ya gama faɗa sannan ya sumbaci kaina.
Ni ko mgana ban yi ba ganin haka ya sa ya leƙo fuskata yana faɗin" Kin yi shuru?
"Me zan ce?
"Komai ma ki ce Sadiya ta."
Sai kawai na yi masa shuru saboda ni ai ya gama shanye ruwan kaina ba wani sauran abin da zai yi mini da zai kankare mganganunsa a wajena suna nan damfare a ƙasan zuciyata sun yi min tsataa.

Ganin kamar ba ya jin barci ya sa na fara yi masa hamman ƙarya na ce ina jin barci dole ya kashe kallon muka koma bedroon ɗin mu amma ni na fara yin gaba shi kuma ya tsaya duba yara sannan ya kashe wutar duka ɗakunan kafin ya shigo har na yi shirin kwanciya amma ban kwanta ba. Na saka wata doguwar rigar barcina mai taushi.
Ina shafa humra a wuyana da hannayena ya shigo. Shima dai tiolet ya shiga ya kama ruwa ya wanke baki sannan ya dawo ya tuɓe riga ya kuma tuɓe wando da ga shi sai gajerun wando ya hau gadon a gefena maimakon ya yi nashi ɓarayin sai ya mirgino har kan filona ya tsoma na shi kan

Muka yi shuru ni da shi, muna kallon rufin dakin da hasken wutar tun da bai riga ya kashe ba.
Juyowa ya yi ya na kallona ni kuma da sauri na ce" Ka rage mana hasken wutar mana."
"Ba yanzu ba."
Sai na ƙura masa ido kafin na samu sararin magana ya cigaba da faɗin.
"Sai mun yi maganar mu."
Na kalle shi amma ban yi magana ba sai na ga ya miƙe zaune nima ya umarce ni da na tashi ba ni da mafita dole na mike zaune a saman gadon muna kallon juna.

"Sadiya"

"Na'am."

Na amsa mishi kamar yadda ya kira sunana.

Sai kawai na ga ya kama duka hannuwana ya jimƙe cikin tafukan hannayen shi.

"Ki faɗa mini duka abin da na yi miki da ya ɓata miki rai ni kuma na yi miki alƙwarin zan ba ki haƙuri."

Ya faɗa yana murza hannayena sannan kuma yana mai tsareni da ido.

"Ni fa ba komai. Komai ya wuce."

"Bai wuce ba."

"Allah na ce maka ba komai ba sai ka ba ni haƙuri ba.'"

"Me ya sa kike haka ne?

Ya faɗa ya na tsareni da idanuwansa a kaushashe ya cigaba da faɗin.

"Fahimtar juna nake so mu yi Sadiya. Ni dake ba shekaranjiya muka faro rayuwar nan ba, ba kuma jiya ba ne, ba kuma yau ba ne. Sabo da haka maganar komai ya wuce ni dake mun san ba haka ba ne ko?

Ya gama faɗa ya na mai tsare ni da idanuwansa kuma ya kama hannayena ya riƙe ba halin na ƙwaci kaina.

"Haka ne"

"To ki yi magana domin mu fahimci juna."

"Na ce ba komai fa"

Na faɗa ina kauda kaina sai ga shi ya saka hannu ya dawo da fuskata zuwa in da yake.

"Ni na san akwai komai fa"

"To mene ne? Komai ya wuce tun da na haƙura ga shi ni da kai muna zaune a waje ɗaya."

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Komai bai wuce ba. Saboda na yi miki mganganu ranar marasa daɗi kuma na san har ga Allah ke ma ranki ba zai yi miki daɗi ba.'

Ashe ya san abin da ya yi? Shima ya san bai kyauta ba! A lokacin ya sani ko sai yanzu daga baya."

"Raina ne ya ɓaci a ranar har na kasa fahimtar ki sai daga baya da na zauna na yi tunani sai na fahimci ni ne ban kyauta ba sannan na yi miki rashin adalci."

Ƙura masa ido na yi, hawaye suna taruwa a ƙwarmin idanuwana. Maganganunsa na baya suna mini amsa kuwwa kamar a lokacin yake faɗa mini.

"Na yi kuskure. Kuma na gane kuskure na don Allah ki yi haƙuri ki manta komai."

"In manta komai fa ka ce?

Na katse shi cikin rawan murya.

"E ki manta na ce. Ki ɗauka na faɗa ne a fatar baki amma ba har cikin zuciya ta ba."

"Har gorin haihuwan da ka yi mini Yusuf? Har cewan da ka yi ina baƙin ciki da Gimbiya da ƴaƴanta? Har goran ta mini da ka yi na cewa ba kai ka ce na je na yi planning ba ni na saka kai na? Har shi na manta har shi kake so na manta kamar komai bai faru ba?

Sai ya kasa mgana na ƙura masa ido, amma ya dukar da kaina ya na faɗin

"Ki yi haƙuri ɓacin rai ne."

"Sai ɓacin rai ya sa ka yi mini gorin gida Yallaɓai?

Na faɗa ina mai kecewa da kuka. Kukan da ke taso mini daga ƙasan zuciyata. Kukan sanadin rasa gudan jinina kukan ɓacin rai da baƙin ciki da mganganun Yallaɓai suka dasa min a cikin zuciyata.

"Ka rufe idanuwan ka. Ka manta da ko planning ɗin da na yi da amincewar ka na yi. Kuma in da na tara sanin haka zai faru da ni zan yi har jawo mini matsala ne? Kuma ka sani ko ban yi ba in Allah ya ce Jidda da Baby kaɗai ne rabona na ƴaƴana a nan duniya ba ni da yadda zan yi kokawa da kaddara ta. Kuma ka ce ina baƙin ciki da Gimbiya da ƴaƴan ka, wannan kam sai na ce ba ka yi mini adalci ba ban taɓa zama da matarka da wata zuciyar ba sai zuciyar musulunci su Khalipa kuwa ɗaya suke da su Jidda a wajena. Amma rana ɗaya kuskure kaɗan da kai ne ka yi amma ka rufe idanuwanka ka ce ba na son jininka. Sannan daga ƙarshe ka yi mini gori. Gorin nan gidan uban su khalipa ne ni kuma ba gidan ubana ba ne.'"

Na dakata ina shessheƙan kuka ina ji ya na damƙe hannayena da ke cikin na shi alamun rarrashi amma bai hana ni kuka ba.

Na nuna saitin zuciyata ina cigaba da faɗin.

"A nan mganganun ka suka yi min illa. Ban taɓa tunanin irin ta ka martabawan ba kenan Yusuf. Na ɗauka ni ina da ƙima da karamcin da za ka guji faɗa mini kalaman da za su sosa mini rai in har kana yi min karan shekarun da muka shafe ni da kai muna zaman aure. Ni da kai mun wuce karnin soyyayya mun koma abu ɗaya. Abu ɗaya Yallaɓai."

Na ƙarishe ina mai cigaba da kukana sai na ji kamar lokacin ne ma lamarin yake faruwa.

"Ki yi haƙuri. Sharrin sheɗan ne."

  Ina jin sa amma ban yi magana ba ina cigaba da kukana, sai ga shi ya matso kusa da ni ya rumgumeni ya na faman lallashina.

"Am sorry."

"Ki yi haƙuri don Allah ki yafe mini Sadiya ta."

Sai kawai na ƙara karfin kukana ina ƙokarin ƙwace kaina daga riƙon sa amma shi bai sake ni ba.

"Wallahi ni kaina na azabtu da kalaman da na faɗa miki. Sharrin zuciya ne."

Hannayena na saka duka biyu ina dukan shi a ƙirji lokaci ɗaya ina kuka har da sheshesheƙa.

"Sharrin zuciya ne ya sa ka yi min goron haihuwa? Ƴaƴana biyu fa, ko a haka Allah ya bar ni na gode masa kuma ko garke Gimbiya za ta haifa maka wallahi ni mai farinciki da haka, ban taɓa jin zan yi baƙin ciki saboda ka samu ƙaruwa da wata matar ba ni ba. Illa ni mai farinciki be ina cewa jinin ka jinina ne, duk ɗaya na ɗauke su da su Jidda. Amma kai zuciyarka ta saka maka bambamci Yusuf."

Na faɗa ina ta dukansa ta ko'ina kuma bai hana ni ba sai da na gaji don kaina sannan na lafe a jikinsa na yi laushi.

"Ki yi haƙuri ina mai neman afuwarki."

Ya yi ta nanata na yi haƙuri har sai da muryansa ta dishashe nima nawa ya daɗe da disashewa saboda kuka.

Ɗago kaina ya yi ya na share mini hawaye.

"Ba zan ƙara ba. Kin ji ko?

Ya faɗa ya na matse mini fuska sannan ya sumbaci goshina.
Sai kuma ya gangaro wajen laɓbana ya na sumbatata. Ban buɗe masa bakin ba sai na datse shi kuma sai ya kalleni ya na faɗin" Ba ki maraba da ni ne? Ko ba ki haƙura ba ne?

Ina kallon shi saboda akwai hasken a ɗakin shima ni yake kallo na tsawon wani lokaci.

"Na tsufa Yallaɓai me za ka ji in ka maraban ce ni?

Ya buɗe baki da sauri zai yi magana na yi saurin rufe masa baki da hannuna guda ɗaya.

"Yaushe rabon da ka neme ni mu yi ɓarnan ruwa? Na tsufa ko? Ko na ƙafe ne yanzu babu danshin ruwa?

Na faɗa ina zubar ƙwalla da sauri ya fizge bakin shi, yana kallona na buɗe baki na yi magana ya damƙe bakina ya shiga sumbata na da karfi da karfi lokaci ɗaya yana sabule min rigar barcin da ke jikina.
Sumbatata yake yi da zafi zafi tun ina tamke bakina har dai na saki na ba da kai bori ya hau. Bai saki bakina ba sai da ya kai ni kwance bayan ya raba ni da rigar jikina.
Ina haki ya na haki, ya dakata ya na kallona. Ya yi wurgi da gajeren wandon da ya cire daga jikinsa. Ni da shi naked muna kallon duka jikin mu abin da ba mu taɓa yi ba in za mu ribaci juna sai a cikin duhu ba mu taɓa kaɗaicewa da juna cikin haske irin na yau ba.

"Ni za ki faɗa ma kin tsufa Sadiya? Ni na ɓare ki a leda kina  ƴ'ar yarinyar ki. Ni ma ke kika ɓare ni a leda ina saurayina. Sadiya ko wajen babu danshin ruwa ni Yusuf zan da dasasa shi har sai na ɓulɓulo da wannan danshin"

Ina shirin mgana ya saka nauyin ƙirjinsa ya danne ni. Lokaci ɗaya ya na haɗe nipples ɗin sa da nonuwana. Har tsakiyar kaina na ji abin ban dawo hayyacina ba na ji ya ƙara kama bakina, komai da zafi zafi yake yi mini alamun yau in na shiga hannu sai na gane ba ni da wayau. Ai ko na gane domin da gaske ya ke ko ba danshi sai da ya ɓulɓulo da wannan danshi na yi ta zubar ruwa. Ranar ba in da Yallabai ba lashe a jikina ba hauka ne kawai ban yi ba amma har ihu sai da ya sakani, kusan fa famshe duk kwanakin sa ya yi, da ya sauka muna gama sauke numfashi sai ya sake damƙo ni da na fara masa magiya sai ya ce ai na ce wajen babu danshi to danshi ya ke so ya ɓulɓulo mini da shi.

Da hasken wutar lantarki muka yi komai yana kallona ina kallon shi ni da na ji nauyi sai na runtse idanuwana muka daina haɗa ido da shi bai ƙyale ni ba sai da ya ce na yarda ban tsufa ba? Na yarda ko mun tsufa za mu iya samo wannan danshin ruwan na ce masa na amince sannan ya sarara mini sai da na yi gashi. Dukkan mu sai da muka tsarkake jikinmu muka saka wasu kayan barcin muka koma muka kwanta maƙale da juna. Zuciya ta yi sanyi duk haushin da nake ji a kan Yallabai ya tafi ban ma san in da fushin na wa ya je ba, amma na danganta haka da yadda ya fahimci ya yi laifi kuma ya ba ni dama na yi magana ya ba ni haƙuri.
Barci muka yi cikin salama makale da juna wanda mun daɗe rabon mu da wannan yanayin.

Ko bayan sallar asuba sai da Yallaɓai ya sake biyo danshin nan ta bakin shi, bayan mun gama ne muna sauke numfashi ba mu ma tsarkake jikin mu ba a lokacin kaina na saman hannunsa na hagu da ya rumgumo ni da shi.

"Yallaɓai."

"Uhm"

"Ranar da na je kaduna."

"Uhm"

Ya sake faɗa kamar mai jin barci.

"Na samu miscarriage"

"Uhm"

Sai kuma na ga da sauri ya mike zaune har ya na wancalar da kaina sai kuma ya saka hannu ya ta da ni zaune ina mai danne kafaɗuna da duka hannayen shi guda biyu.

"Me kika ce"?

Ina murmushi na ce" Na ce na samu ɓari a kaduna. Cikin wata ɗaya ne ni kaina ban san dashi ba sai da ya fita."

Ƙura minI ido ya yi kafin ya ce" Da gaske kike yi Sadiya?
Ya faɗa da wani irin murna a muryansa.
Sai na gyaɗa masa kai alamun haka ne sai kawai ya rumgumeni ƙamƙam yana faɗin.
"Alhamdulillah."
"Ka ji abin da na ce da kyau Yallabai?
Na faɗa ina tantama in ya fahimci na ce ɓari na yi.

Sai da ya saki rumgumar da ya yi mini ya na kallona sannan ya riƙe hannayena yana dariya ya ce" Na ji da kyau. Kin yi barin ciki ko Sadiya?
Sai na gyaɗa masa kai sai kawai ya ce" Ina

6 / 55