Turken Gida Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   40 / 55

117K to 120K   out of 163.1K words

ci riba."

Ni dai ban furta ba, domin har a cikin zuciyata ban ji daɗin tafiyarta ba ba ni da yadda zan yi ne. Maganar auren Yallaɓai ta fasu a gari tun da duk an sanar a groups ɗin su na gida,nima sai na faɗa ana gidanmu. Ya Aina ta ce af ita ai ta san za a rina Ma'u ta yi ta masifa wai Yallaɓai ya cika haɗa ma har Ya Auwal ya fito ya ce ba ma son gaskiya. Shima yana da niyyar sai ya yi huɗu in sha Allahu muna ta dariya.
Hauwa da Munnira sun yi ta ƙorafin me ya sa na amince amarya ta fara tarewa a sabon gida?

"To miye a ciki? Mijin ma gabaɗaya za ta mu raba shi tare miye abin damuwa a gida. Ta tare can ya gama mararinta daga baya mu sai mu koma."

Daga haka na kashe bakin su, Gimbiya sama da sati biyu sannan ta dawo, shi kuma da kan shi ya faɗa mini har yana faharin shi bai je ba, su Anty Bahijja ne suke je suka dawo da ita Bayan Tafidan Rano ya yi mata faɗa sosai. Har kuma ta dawo su Khalipa na gida ba su koma ba, shi bai ma yar da su ba nima ban ce su koma ba na bar su ko itama za ta samu kwanciyar hankali. In da ta ji shawarata wallahi da duk haka bai faru da ita ba.

Kwana ɗaya tsakanin faɗa mini da ya yi ta dawo. Ranar ma a gidan ta ya kwana da safe da ya ke ranar laraba ne su Khalipa na makaranta suna Jarabawa ne ina cikin bedroon su Jidda ke da gidan yanzu tun da suna nan daga ita har Baby ba na yin aikin komai sai dai na kwanta na tashi na ci kawai. Haihuwa mai rana
Ina cikin ɗakin Baby ta zo ta ce mini ga Gwaggo Bahijja da Anty Gimbiya nan sun zo, na yi ta mamakin zuwan su. Ban ɓata lokaci ba na saka ɗankwali na fita falon Yallaɓai in da suke zaune

Wallahi na tsausayama Gimbiya duk ta faɗa ta yi zuru zuru ba gayu yau. Na yi mamakin da muka gaisa da Anty Bahijja faram faram kamar ba mu taɓa samun matsala ba ashe alfarma aka zo ci dole a yi mimi haba haba.
Wai Anty Bahijja ke faɗa mini mu haɗa kai da Gimbiya domin mu rusa wannan auren tun da Yallaɓai na jin maganata.

"In ma auren ba zai fasu ba. To ku tabbata bayan an yi aurwn yarinyar nan ba ta ji daɗin zama da shi ba. Ku haɗe kan ku ke da ita domin ku tsira tare."

In ji Anty Bahijja.

"Kuma ma har da maganar gida. Ke sai ki amince yarinyae can ta fara tarewa? Wallahi ba zan yarda da."

In ji Gimbiya.

"Yauwa har maganan gidan ku haɗe kai ku ce ba ku yarda ba. Ko ya gyara ku fara tarewa kafin auren ko itama ya nena mata wajen zama ta jira ku tare gabaɗaya ko ba gaskiys ba."

Anty Bahijja ta faɗa tana kallona.

"Gaskiya ne."

Na faɗa ina ƴar dariya ina mai kallon su a ɗage ɗaya bayan ɗaya..
Sai yanzu ne suka san ina da amfani? Wato na haɗa kai da Gimbiya saboda su mafitarsu suke nema. Ni kuma wallahi ba wacce ta isa ta saka ni na zubar da girmana. Yallaɓai ya nuna ma yarinyar nan ina da daraja a rayuwarsa shima ya nuna ma duniya ina da ƙima a wajen sa saboda kishiyar da ba ta ɗauke ni a bakin komai ba ba zan yi wasa da mutumcima ba.

"Ku yi hakuri zencen gaskiya ki cire ni a wannan lissafin ba zan iya aikata ko ɗaya a ciki ba '

Na faɗa ina kallon su, suma ni suke kallo cikin mamaki.

"Aurn da zai yi umarnin Allah ne. Maganar gida kuma gidan shi, don ya ce ga yadda za a yi ni ban isa na ce ba haka ba. Allah na tuba mijin ma aka yi sharing ɗin sa da ita sai gida ne zama abin damuwa ? Ni a ganina wannan ba hanyar ɓulllewa ba ce, hakuri shi ne kawai. Amma ba abin da za a fasa."

"Da man na faɗa miki ba za ta yadda ba. Ita fa jin dadi take yi Saboda ni za a yi mawa ba ita ba tana bashi goyon baya."

Gimbiya ta faɗa ma Anty Bahijja.

"Naga alama."

Sai kawai na miƙe ina faɗin" Duk yadda kuka ɗauka dai dai ne. Ni dai Allah na gani ba zan yi hauka saboda Yallabai zai ƙara aure ba, in ke za ki yi haushi to ki yi shi kaɗai amma ba tare da ni ba. Sannan sai yau da zai ƙara aure na ke da amfani a wajen ku? Ai ba ki taba kawo ta ko ce mu haɗa kai ba sai yau. Saboda amfanin ku ne, to ba zan yi ba kowa tashi ta fishshe shi."

Ina gama faɗin haka na bar musu falon na san sun yi suman zaune da mamakina.



*Janafty**TKGB3018*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Gkzmhd0zmnFChYrdONLFYp

Bedroom ɗina na koma na yi zama na ban san lokacin da suka tafi ba, har ga Allah ba ina murna da ƙarin auren Yallaɓai ba ne saboda kishiya ai sunan ta kishiya nima a zaman matar mijina take. Na so Gimbiya ta ji maganata ta kwantar da hankalinta saboda ta tsira da sauran mutumcinta amma taƙi jin maganata tana biye ma su Anty Bahijja. Wanda na tabbata in aka juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe, dole akwai bangaren da za ta nuna mata Yallaɓai ne jininta na kusa ba ita ba.

Abin da nake yi ita a ganinta ina bin bayan auran Yallaɓai ne saboda ita, abin da ba ta sani ba da na bi baya da ban bi baya ba ban ga dalilin da zai saka Yallaɓai ya fasa wannan auran ba, yau ko Nene ce ta hana shi na tabbata zai yini yana yi mata karatun da za ta gane har ta amince domin bai ɗauko maganar auran nan don ya fasa ba. Shi ya sa gwara ta kwantar da hankalinta domin ba abin da za a fasa.
Rasa wanda zan kira na tseguminta masa zuwan Gimbiya da Anty Bahijja sai Munnira ina faɗa mata ta yi dariya da shewa kafin ta ce.

"Sai yanzu suka san ana haɗa kai? Wato sai yanzu da suke neman mafitar su."

"Wallahi, ni kaina zuwan su ya ba ni mamaki. Har Anty Bahijja na faɗin wai mu haɗa kai ko ba mu rusa auran ba mu hana su zaman lafiya har sai ya gaji ya sake ta"

Na faɗa, ina riƙe baki domin sai a lokacin na ke jin ma ƙarin mamakin zuwan su da magangansu.

"Lalle. Ni ban yi mamaki da man na san za a zo wajen. To ke me kika faɗa musu?

"Na ce ni ba zan haɗa kai domin a yi tashin hankali da ni ba itama ina na faɗa mata gaskiyan ta bar ma komai ta kwantar da hankalinta. Amma ba ta ji ba ita a ganinta ina goyon bayan Yallaɓai saboda ita ne, ni kuma wallahi ba haka ba ne Munnira. Kin sanni ba ni da wanman muguntar, ina tausaya mata ne domin a irin rawan kafan da Yallaɓai ya ke yi a kan auran nan ni ko ita wallahi ba mu da darajan da za mu iya dakatar da shi, shi ya sa na koma gefe na zama yar kallo na shafa ma kaina lafiya."

"Haba na sani wallahi. Kin huta da man a irin wannan lokacin in baku sauke
a kai ba sai a samu matsala. Kuma su Anty Bahijja ne za su ɗora ta akan keken ɓera su kaita su baro ta."

Na amsa da wallahi, domin in ta kwaɓe su kan su ba za su iya ba. Wai maimakon su ce ta yi haƙuri ta ma yar da lamarin ta ga Allah, amma suna zugata ta yi tashin hankali da miji. Har muka gama waya da Munnira ita kanta ta ce da Gimbiya ta kwantar da hankalinta da zai fi mata alherin akan wannan haukan kishin da ta ke yi, nima abin da na hango mata kenan. Bayan Munnira ban faɗa ma kowa zuwan su Gimbiya ko Hauwa ba mu yi taɗin da ita ba, a satin na je Ɗorayi gai da su Alhajinmu ina faɗa masa ƙarin auran Yallaɓai, sai ga magana tiryan tiryan a bakin Alhaji.

"Har nan falona in da kike zaune nan megidanki ya zauna ya sanar da ni zai ƙara aure, ya kuma dawo ya roƙeni na shirya aje nema masa aure da ni sai kuma aka yi rashin sa'a ranar zan je Yashe shi ya sa ban samu zuwa ba amma na yi masa alƙawarin zuwa masa ɗaurin aure."

"Maidugurin Alhajinmu.?

Na faɗa ina zare ido saboda mamaki.

Sai kawai Alhajinmu ya yi dariyar su na manya kafin ya ce" In sha Allahu in dai muna raye zan je. Ai ya girmama ni matuƙa nima zan ma yar masa da girmamawan sa."
Uhm kawai na ce na ma kasa magana saboda mamakin Alhajinmu wai zai je har Maiduguri ɗaurin auran Yallaɓai, ni bai ma taɓa nuna mini ya zo ba ashe ya zagayo sai da na koma gida da Yallaɓai ya zo yi mana sallama a daran nake masa mganar aahe ya wanke kafafunsa ya je ya faɗa ma Alhajinmu maganar aurensa.

"Ya ba zan faɗa masa ba! Me kike nufi? Alhaji ai uba ne dole na je na same shi na faɗa masa komai dangane da aurena. Bai ma samu zuwa maganar auren ba amma ya yi mini alƙawarin zuwa ɗaurin aure har can maiduguri "

Kallon Yallaɓai kawai na ke yi, a fatar baki na ce Allah ya kaimu da rai da lafiya. Tun da Alhaji ya yi niyya wa ya isa ya hana shi, ni ma kafin na fito sai da ya sake yi mini nasiha sosai akan haƙuri na zauna kuma da kowa tsakani ga Allah, ina jin daɗin manganganun Alhajinmu shi dai har na zama mai ɗaga ma mijina hankali. Na zama mace mai samar masa da zaman lafiya a cikin gidan shi, haƙurin da na yi a farko yanzu na ninka shi, nan gaba kaɗan zan ga riban haƙurina ko ya ce zan ƙara gani domin ribar haƙuri na gan shi tun da har gobe  mijina ya yaba mini da hallaya masu kyau.

Tun da aka sanya lokaci Yallaɓai bai zauna ba shiri kawai yake yi kamar zai yi auran farko. Ko da yake budurwa zai ɗauka dole ya yi rawan jiki, ranar sati na zuwa Yallaɓai ya ce na shirya yara za su je su gaida Gimbiya. Shi ya sa ya ƙi ma yar da su Khalipa gida, ni na ma manta da zencen amma shi yana sane bai manta ba faɗa mini yake yi ai ta riga ta gama shirin tarɓansu tun da ya faɗa mata za su zo, Jidda na saka ta shirya yaran suma na ce su shirya sun ci gayun su ni dai ba ni da komai Hijabi da mayafi na ba ma Jidda na ce ta kai ma Antyn na su. Yallaɓai kamar bakin shi zai yage saboda farinciki shima ya ci gayu yana rawan jiki har sai da na yi masa magana.

"Yallaɓai wai ba can za ka bar yaran ka wuce office ba?

"E ina tunanin haka akwai baƙin da zan gani."

Sai na yi shuru domin na ga yana rawan kafa ne har ya wuce misali, har yana yi mini godiyan saƙon da na ba da akaikace na ce bakomai yiwa kai ne.
Shi ya ɗauke su a motar shi, tun wajem sha ɗaya na safe, ina jira na ga Yallaɓai ya dawo mini da yara amma shru har la'asar shi kuma na kira wayarsa bai ɗauka ba sai na kira Jidda ina mata faɗan zaman me suke yi ne har yanzu ba su dawo ba.

"Umma Abba ya ce mu jira shi zai dawo ya ɗauke mu."

"Kenan shi kuke jira?

Na faɗa ina mai kama baki, kafin ta yi magana sai na ji an yi mini sallama cikin sanyin murya ina jin murya na gane na Rabi'atu ne
Gaishe ni ta yi na amsa nima cikin sakewa kafin na ce" Yau an kawo miki gidan gabaɗaya hayaniya ya dame ki ko?
Tana mirmishi ta ce" A'a ni da man su kwana Anty"
Sai nima na yi dariya kafin na ce"Haba dai. Ba yanzu ba ki jira saura ƙiris wata rana ma sai kin kore su saboda gajiya."

"Ni ba zan kore su ba. "

Ta faɗa tana yar dariya, godiya ta yi mini na saƙo na ce mata haba yi wa kai ne. Na ce su kira Yallaɓai in ba zai samu komawa ya ɗauke su ba Jidda ta  yi jagoranci su samu a daidaita su dawo gida yamma ta yi.

"Ya ce zai dawo ya ɗauke su. Na san yana hanya."

Ai ni sai na kasa magana tun da ga abin da ya ce. Ni dai ban ga yara ba sai bayan sallar isha'i, Yallaɓai bai isa can ba sai bayan mangariba can suka ci abinci sannan ya tarkato yara suka taho. Baby ke faɗa mini a mota suka jima Abban su na cikin falo da Antyn na su. Ni fa tsoron rawan jikin Yallaɓai na ke yi a kan yarinyar nan har ta haukata shi, sun dawo da kayan zaki kaya guda kamar za a buɗe shago su bickit ne da su katan ɗin boo na yara. Yallaɓai yana faɗa mini ya ce ta bar shi amma ta fara fushin yana nuna mata su Jidda ba ya'yanta ba ne, ni dai ban yi magana ba saboda ba ni da ta cewa
Godiya ma shi ya yi mini na ci sai na kirata na yi mata godiya kamar wani laifi ne in ban yi mata ba haka nan na ce Jidda ta kira ta a wayarta tun da sun karɓi lambar wayar juna. Shi ne na samu na yi mata godiya tana ta jin kunya da man iyayin Yallaɓai ne amma ni na san har tsaraban ma duk shi ya siya ba wai ita ba, in ita ta siya ma da kuɗin shi ne.

Washegari Lahadi Gimbiya ta aiko aka tafi da su Khalipa. Da man ko ba ta aiko ba ina shirin na roƙi Yallaɓai ya ma yar da su to sai ga shi bayan fitan shi, ta aiko Salisu ya zo ya tafi da su. Da ya  dawo a daran da man yana gida ne, ya ga bai gan su ba ya tambaya na ce sun koma gida.
Sai ya fara faɗan wai ba na jin maganarsa me ya sa zan ma yar da su ba tare da izinin shi ba.

"Ah ni fa ba ni na ma yar da su ba kana fita mamansu ta aiko Salisu ya tafi da su."

Sai ya yi shuru bai yi magana ba amma ya yi ƙyafci alamun ran shi ya ɓaci ni ko a raina na ce can ku ƙarata ba ruwana. Sai da muka zauna ne Baby ke ba ni labarin da suka je gidan su Antyn ta su haka ake ta zuwa ganin su, a raina na ce dole a zo a gan ku Jidda ba ta magana ita da man Baby ce da man yar surutu amma faɗa mini take yi Antynsu na da kirki gidan ta za ta koma na ce Allah ya ba da sa'a.

Jidda ce mini kawai ta yi She is young Umma, ko ba ta faɗa ba na san ƙaramar yarinya ce Yallaɓai zai aura. Kuma yadda yake rawan kafa wannan in aka yi auran sai Allah kawai kar Yallaɓai ya lalace a gindin yarinya ƙarama. Ni ban san a in da Gimbiya ta ji labarin su Khalipa sun je wajen Antyn ta su ba amma na fi tunanin a bakin Khalipa ta ji tun da yana da magana shima. Kawai bugo mini waya ta yi da man tun zuwan su gidana na ce ba na tare da su ba mu ƙara magana ba.

Ni wai Gimbiya ta buga ma warning akan me ya sa zan yanke hukunci kan ya'yanta? Me ya sa na tura su gidan wata banza ba tare da sanin ta ba.
Ni ko cikin mamaki na ce' Umarnin megidan ne amma ba ni na tura su ba "
Sai ta fara masifa tana faɗar manganganu wai da sanina aka yi komai da ban ba da goyon baya da ba a tura mata yara gaida wata banza ba tare da sanin ta ba.

"To ki yi haƙuri."

Haka kawai na ce mata ganin kamar ni ce take jin haushi yanzu ba mijinta da zai ƙara aure ba.

"Ahto ni dai a kiyayeni. Ya'yan dai nawa ne ba wani ya haifa mini ba, in kina son neman sunan ki aika na ki ƴa'ƴan amma ban da nawa."

"To in sha Allahu hakan ba za ta ƙara faruwa ba'

Kawai sai ta yi mini tsaki mai girma har ina jin sa a cikin kunnuwana sannan ta kashe wayarta ta bar ni sake da baki. Ni zan fita? Ina ruwana a wannan maganar da abun zai dawo kaina? Raina ya ɓaci amma sai na danne zuciyata na ɗau girma na yi haƙuri shi ya sa ko zencen ban yi ma Yallaɓai ba. Nima bai  yi mini ba. Mun shiga tsakiyar watan December, Yallaɓai na ta shirin shi na gida ina ga ma an gama gyara bangaren da Rabi'ar za ta zauna sai maganar lefe ya fara yi mini. Da cewa ya yi magana da Mimisco ta ba shi shawaran kawai ya ba ma ita Rabi'an kuɗi ta siya komai da kanta. Nima da ya faɗa mini na ce hakan ya yi, tun da Mimisco ita ce kaɗai ke supporting ɗin sa sai su Suwaiba amma su Anty Bahijja sun ja tunga shi ko ya ce uwarsa ba ta hana shi ba ba wacce ta isa ba.

A bakin Suwaiba na ke jin wasu mangaganun, sun ce ni ce ke zuga shi saboda na ga ba ni za a yi ma kishiya ba ni in suna faɗar haka har mamakinsu nake yi mijina ne fa zai ƙara aure? Ni ba mace ba ce ba zan yi kishi ba? Ba dangin Yallaɓai kaɗai na ke shan zagi ba hadda na su Giimbiya a can Rano. Sameena ta kira ni a waya tana faɗa mini mganganun da ta ji

40 / 55