wanka da sallah. Yallaɓai ba ya gidana ya na can gidan Gimbiya sai na kira shi a waya amma bai ɗauka ba a na farko sai da na sake kiran shi Gimbiya ta ɗauka ba gaisuwa ba komai ta ce mini wai yana wanka. Duk da na ji wani motsi a cikin zuciya ta ban nuna mata ba sai na ce in ya fito ta faɗa masa yaron Ya Abubakar ya rasu za mu tafi Ɗorayi ni da yara sai ta ce to za ta faɗa masa sai a lokacin ta ce Allah ya jiƙan sa na ce Amin.
Bayan na kashe wayar sai da na duba lokaci shidda na safe ta gota da mintina ashirin. Na san kuma dalili ɗaya ke saka Yallaɓai wankan safe. Wani abu ya ƙara sukan raina daman da gayya ta ɗaga wayar domin ta faɗa minI ta yi sunna da Yallaɓai. Ganin ni da a ka yi ma rashi tuna kishiya ba nawa ba ne sai na watsar da maganar Gimbiya na fita na je ba yi ma su Jidda mgana na ce su shirya mu je ɗorayi. Hamzan Ya Abubakar ya rasu Baby sai ta fara kuka Allah sarki abokin wasanta ne in dai suka haɗu Jidda ma ta yi shuru jikinta duk ya yi sanyi.
Ba mu tsaya wanka ba muka saka hijabai na kulle gida muka samu adaidaita zuwa can Ɗorayi. Gida cike da mutane har Ma'u a can na ganta. Sai dai ina zuwa Rahila na zuwa har Zaitunan da ƴan'uwanta suna gidan Allah Sarki ta na ta kuka gwanin ban tausayi. Gwaggo ce ta yi ma yaron wanka su Ya Abubakar da Alhajinmu da su Ya Muntari duk suna waje a ƙofar gida. Bayan Gwaggo ta gama yi masa wanka a ce iyayen shi suje su gan shi su yi masa addu'a. Shi dai Ya Abubakar ya yi dakiya amman Zaituna sai da a ka riƙe tana ta kuka kamar za ta shiɗe. A ƙofar gida a ka yi masa salla sannan a ka tafi kai shi gidan sa na gaskiya. Allah ya ba mu sa'a. Su Jidda duk sun yi tsuru tsuru jikin su ya yi sanyi. Rayuwa kenan Allah ka kyautata ta mu bayan ta su Amin.
Sai da a ka dawo daga kai shi can wajen sha biyu Zaituna da ƴan'uwanta suka koma can gidan ta saboda masu zuwa mata gaisuwa mu kuma sai muka zauna a nan saboda makota. Amma Ya Balki ta bi su can gidan, su Amina duk sun kira sun yi gaisuwa Ya Hamza da Ya Auwal sun kira kuma matan su sun kira. Sun ce za su shigo gaisuwa weekend saboda yanayin aikin su. Sai can rana Yallaɓai ya kira ni ya ce mini gashi ya zo ya ba ni mamaki tun safe sai yanzu? Sai da ya shigo cikin gida muka keɓe muna mgana ne ya ce mini Gimbiya ba ta faɗa masa ba har sai da ya tashi barci. Kasa mgana na yi kawai na tsaya ina kallonta.
"Lalle."
Kawai na iya furtawa saboda mamaki ya hana ni ma mgana.
"Sai da na yi mata faɗa. Wai ta manta ne ba ta faɗa mini ba lokacin da ta tuna kuma na kwanta. Na ce da tashe ni ai mutuwa ta wuce komai."
Ni dai kawai na kalle shi amma ban yi magana ba. To me zan ce? Ai da yaron yayanta be ya rasu ba barci ba ko me yake yi za ta tashe shi ta faɗa masa amma tun da bai shafe ta ba ba za ta damu da ta faɗa masa a kan lokaci ba.
"Ki yi haƙuri. Allah ya jiƙan sa."
"Amin"
Na amsa masa kafin na ce" Ka zo kuma Zaitunan ta koma gidan ta ɗazu."
"Ayya to mu je ki rakani na yi mata gaisuwa daga can sai na wuce office."
Sai na ce masa to daman muna korido ne a tsaye muna mgana cikin gida na koma na ɗauko Hijabi ina faɗa ma Gwaggo zan raka Baban su Jidda gidan su Zaituna. Rahila na zaune ta miƙe ta ce za ta je. Ma'u na kalla tana zaune ta yi tagumi tun da safe na lura da ita ba ta da kuzari ta yi firgai firgai kuma ni dai a yadda na san Ma'u ba haka ta ke ba. In ma idanuwana sun gano min dai-dai ta rame ta yi baki sannan ba gayun nan ba surutu. Kuma ba za a ce mutuwar da a ka yi ba ce ta mai da ita haka ba ai Baaba na raye ban ga abin da zai saka Ma'u ta susuce haka ba. Ko a lokacin suna zaune kugu da kugu ita da Ya Murja. Wataƙila koma me ke damunta ita za ta fi kowa sani tun da suna tare.
Ni dai ban samu na furta ma kowa yanayin da na ga Ma'u ba har muka kai Yallabai gidan Zaintuna ya yi mata gaisuwa mu can ya bar mu ya wuce.
Da ya ke ba nisa. Ya Abubakar ya siya wani ƙaramin gida a can ƙasan layin gidanmu shi ya sa sai suka dawo kusa.
Mu na gidan sai bayan la'asar muka koma gidanmu. Nan ma ana ta shigowa maƙota da abokan arzuka duk wanda ya zo sai a yi masa kwatancen gidan Zaituna. Ya Murja da Ya Aina su suka yi abincin rana tun da akwai mutane.
Muna gidan har dare ni dai da wuri na tafi bayan mangariba Yallaɓai ba gidana yake ba, sai da muka koma ya kira ni ya ce zai zo ya ɗauke mu na ce mu kan muna gida.
Washegari ma ban jira shi ba. Tun safe na ta da Jidda ta taya ni muka dafa abinci shinkafa da wake muka saka a babban kula ƙarama da babba. Babban a ɗakin Gwaggo karamar kuma na ba ma su Jidda su ka kai gidan Zaituna. Ƴan'uwan Yallaɓai duk sun kira sun yi mini gaisuwa da ya ke Yallabai in wani abu ya faru na jaje ko na murna ya kan saka a group ɗin su. Ranar biyu Hauwa da Munnira suka zo mini gaisuwa. Sai ranar da a ka yi uku Gimbiya ta zo lokacin ma ta iske su Suwaiba da Jamila sun leƙo mun gaisuwa. Shi ya sa ba ta wani daɗe ba daga ita sai Anwar Suwaiba ce ma ta tambayi Khalipa sai ta ce ta baro shi a can Rano. Ni dai ban ko tambaye shi ba tun da ba ta ma wani daɗe ba ta ce za ta tafi na yi mata rakiya har waje. Ta zo da mota har ta rage ma su Suwaiba hanya zuwa Gwamnaja. Na ko ga sabuwar motar ta a fili ma ɗaukan ido take yi.
Bayan an yi uku ne ban sake komawa ba sai ranar da biyar. Ranar lahadi kenan da su Ya Hamza suka zo ba su kwana ba a ranar suka koma. Shi daman Ya Auwal ya ɗan zo yin wani abu ne a reshen su na nan Kano kuma ba shi kaɗai ya zo ba shi ya sa bai jima ba ya tafi da cewa daga can kawai za su koma Abuja ne. Kuma tun daga ranar ban koma ba sai ranar bakwai a gidan Zaituna, muka zauna a ranar su Inna Mariya suka zo gaisuwa an manta da su sai da Amina da ke kaduna ta kira wayar Inna ta faɗa mata. Da suka zo tana ta faɗa ni dai na ba ta haƙuri na ce wallahi an sha'afa ne. Matar Kawu Tasi'u ta zo da fanke da yawa na sadaka sai bayan la'asar suka tafi. Dukkan mu muna gidan har Ma'u da ranar ba da wuri ta zo ba ashe ba ni kaɗai na fahimci Ma'u ta susuce ba sai da Rahila ta yi mini mgana.
"Sadiya wai Ma'u ciwo ta yi ne?
Ta ke tambayata sai na kalleta kafin na ce" Ni ko ta ina zan sani? Nima dai haka na ganta duk a firgice tun ranar da a ka yi rasuwar na."
Rahila ta jinjina kai kafin ta ce" Nima wallahi na tun ranar na lura. Kamar wacce ta yi jinya duk ta firgice."
Sai na jinjina kai ina ƙara kallon Ma'u. Wallahi har idanuwanta sun zumar ma. Sannan na daina ganin Zainab ƙanwarta da ke wajenta ko ta koma gida ne oho? Sannan ba ta ma zo da yara ba tun da a ka yi rasuwar ita kaɗai take zuwa ba. Kuma ban ga Alhaji Mustapha ba na ji dai a bakin Ya Aina ranar da a ka yi rasuwar da shi a ka yi jana'iza.
Duk da ba na shiri da Ma'u na ji na damu da ganin yanayin ta. Na tuna a shekaran da ta wuce na taɓa zuwa gida Alhajinmu ya kirani yana mai tambaya ta.
"Kina zumunci da ƴar'uwan ki Asma'u kuwa Dubu?
A lokacin ban ɓoye ma Alhajimmu komai ba gaskiya ta na faɗa masa.
"Ina dai yi maka kara Alhajimmu. Ina gaisheta in mun haɗu sannan in abu ya kama na jaje ko na murna ina yi mata."
"Kin kyauta Dubu. Kin yi mini kara sannan kin yi ma zumunci kara."
Daga lokacin bai ƙara matsa mini ba. Tun da dai ya samu tabbacin ba ma gaba da juna. Nima hakan ya fi mini tun da yanzu na samu sauƙin ta. Sai yanzu da na gan ta sai na fahimci itama ta na can tana fama da kanta ne. Ko da ga ganin yanayin ta wani al'amari ne mai girma ya gigita tunaninta Ma'u fa macen da ba komai yake razanata ba. Ba a cika ganin gazarta ba amma yau na ga kasawa a yanayinta da idanuwanta.
Ashe ba ni da Rahila duk muka fahimci Ma'u ba ta hayyacinta ba har da Ya Aina da Ya Balki. Ita dai Ya Balki Zainab ta fara tambaya da yara sai Ya Murja ta amsa da cewa Zainab ta je ganin gida. Su Alhaji ƙarami kuma suna gidan iyayen Alhaji mustpha sun je hutu.
"Oh shi ne na ga Ma'un duk ta yi wani sanyi haka? Kewar yaran ce?
Ya Aina ta faɗa cikin zolaya. Ma'u yaƙe kawai ta yi ta kasa mgana.
Ina lura da Ya Murja ta na son mgana amma kuma sai ta fasa yi shuru.
"Wai ni kam ina labarin Shema'u? Na daɗe ban ganta ba ina jin tun auren ta."
Sai Ma'u ta rausayar da kai kafin ta ce" Tana can Gombe. Mijinta kulle yake yi mata."
"Kuma ba ta da ciki?
In ji Rahila.
"Ba ta da ciki gaskiya."
Ta faɗa a sanyaye ni dai kallonta kawai nake yi. Maganar Allah Ma'u ta rame ko ni kaɗai ke ganin ramar na ta? Na faɗa a cikin raina.
"Shi ya sa ba ta yawan zuwa kenan." To Allah ya zaunar da ita lafiya da man wasu mazan akwai kulle. Kuma itama Shema'u sai da haka in da ya bar ta da duk sati za ta iya zuwa Kano a shirmen ta."
Sun cigaba da tattauna mganar Shema'u. Ma'u na gefe ta yi tagumi ta yi shuru da ga gani ta shiga zurfin tunani kamar ba zan yi mgana ba sai na muskuta da cikina a gaba. Wata doguwar riga ce a jikina da na saka a ka ɗinka min su bubu tun da duka kayana sun yi mini kaɗan. Sai na siya yaduka da ƙananun atamfofi na ba da a ka mini ɗunkunan masu ciki su na ke sawa ina jin daɗin su.
"Wai ni kaɗai na lura da Ma'u duk ta rame?
Na faɗa ina kallon su Ya Aina sai suma suka kalle ni sannan suka koma suna kallonta duk sai ta tsargu.
"Nima wallahi na lura. Ba har na yi magana ba ranar."
Rahila ta faɗa, Ya Aina ko sai ta yi shuru kafin ta ce" Ni kaina na ga haka tun kwanaki da na ganta. To na yanzu ma abin ya ƙara lalacewa idanuwanta duk sun zurma"
"To ko ciki ne da ke Ma'u?
In ji Ya Balki. Sai Ma'u ta kasa mgana ta dukar da kai tana wasa da kwalliyar material ɗin rigar da ke jikinta.
"Ma'u me ke faruwa da ke ne? Mu ƴan'uwan ki ne. Kina ganin bai kamata mu san matsalar ki ba?
Kawai sai Ma'u ta saka kuka. Ni fa har ina buɗe baki saboda mamaki. Na daɗe ban ga kukan Ma'u na haƙika ba sai ranar. Duk sauran kukan da na saba gani na makirci ne amma na yau na gaske ne fitowa yake da sauti daga ƙarkashin zuciyanta.
"Subhanallah me ya faru Ma'u?
Ya Balki ta faɗa. Ni da Rahila ma mun kasa magana. Ganin yanayin Ya Murja ya sa na san ta san abin da ke faruwa.
"Ya Murja fa ina ganin ta san wani abu."
Na faɗa ina kallon su Ya Aina duk suka mai da kallon su kan Ya Murja.
"Murja me ke faruwa?
Sai ta kalli Ma'u kafin ta ce"Uhm aure Alhaji Mustapha zai ƙara. An kusa karshen shekaran nan."
Yadda na zaro ido kamar na ga wani abun tsoro
Kowa sai jikin sa ya yi sanyi. Duk da ba na son Ma'u itama ba ta so na amma jini ya yi aiki a kaina wallahi na tausaya mata matuka. Kishi bala'i ne ba wanda ke gane yanayin sai wanda ya faru a kan shi. Ni da ya ke Victim ce ai na san irin yanayin da take ciki.
Na ji na ƙara tausayinta da Ya Murja ke faɗin karamar yarinya ce yar sha takwas zai aura kuma sai da a ka saka ranar ta ke ji bakin Uwargidan shi. Matsaloli da dama yanzu ya daina ma rawan jiki a kanta da ta yi masa mgana bai faɗa mata sai da suka yi tsiya har ya ce in ba za ta iya zama ba ta tafi shi bai hana ta ba ashe gurmu a ka yi har sai da Baaba ta zo garin nan amma Alhajinmu bai sani ba. Itama Ya Murja ta ce faɗan su na biyu ne Ma'un ta zo gidan ta, ta na kuka shi ne ta san abin da ke faruwa ita da mijinta suka mai da ita. Yadda ta ke faɗa yadda Alhaji Mustapha ya ɗauko auren nan to uwarsa ce kawai za ta ce kar a yi ya saduda. Amma ba Ma'u ba ya ce ko za ta mutu sai ya yi auren ita ba a aure ya aure ta. Yadda Ya Murja ta ce Ma'un ta faɗa mata ita uwargidan sai daɗi ta ke ji tana ƙara zunguran Alhajin da maganar auren.
"To daman me zai dame ta tun da ba ita za a yo ma wa ba?
Na faɗa ina jin wani motsa daga ƙasan zuciyata. ta ba ni tausayi kishi ai masifa ce.
"Haka ne. Amma ita ma Ma'u ta kwazzaɓi kanta tun da ta san ba zai fasa wannan auren ba, me ya sa ba za ta kwantar da hankalin ta ba?
"Ya Aina Alhaji ba ya sona yanzu. Magana kaɗan sai ya rufe ni da faɗa. Hajiya Zainab ce ke juya shi ta na gaba gaba wajen zuga shi ya yi auren kuma yarinya ƙarama fa zai auro."
Ta faɗa ta na ƙara rushewa da kuka. Da gaskiyanta haka a ke ji fa in za a yi ma mutum kishiya. Balle ita da ta haɗu da kai din kishiya ita ai daman za ta so a yi mana amma kuma ba ta kyauta bai kamata in ba ya kamata in ba za ta iya hana shi ba to kar ta ingiza shi.
"Duk da haka Ma'u da kin kwantar da hankalin ki. Kin ta rama ki kashe kan ki a banza shi fa ba fasawa zai yi ba"
"Wallahi kuwa. Ki yi hakuri ki kauda kan ki. Ki yi koyi da Sadiya mana. Lokacin auran Baban su Jidda jarumtar da ta nuna wallahi sai da ta burge kowa."
In ji Ya Balki.
"Gaskiya. Haƙuri a ke yi tun da su Maza in suka yunƙuri da maganar aure ba mai iya hana su. In ka matsa ma sai su ce ka yi gaba."
Cewar Rahila.
"Wallahi nima haka na yi ta faɗa mata ta yi haƙuri da kwantar da hankali ta ki jin mgana ta."
Ya Murja ta faɗa, duk suka haɗu suna ta mata faɗa ta kwantar da hankalinta ta yi hakuri da na so na yi shuru tun da ai kamar alhakina ne yakama ta, lokacin da za a yi mini kishiya ta biye ma su Anty Bahijja ana mini dariya ta manta ita mace ce zai iya faɗowa kanta. Ita ai kishiya yanzu ta zama ruwan dare in ba a yi miki ita a kusa ba. A gaba kaɗan za a iya miki ita.
"Ma'u kalle ni nan in ba ki wata shawara in har zaki iya ɗauka."
Na faɗa ina kallonta itama sai ta bar goge hawayen tana kallona.
"Kukan ki da wani fushin ki da ramar da kike yi duk a banza ne a wajen namiji. In dai suka tashi ƙara aure in ke ta gida ba ki haƙuri ba wallahi sunan ki sorry. A gari a kalle ki a wacce za a yi ma kishiya ta ki kwantar da hankali. Shi kuma yana miki kallon mai son kanta. Dangin sa suna yi miki kallon ba a aure a ka aure ki? Mafita ɗaya ce a gare ki, ki kwantar da hankali ki dogara ga Allah. Ki kaima Allah kukan ki shi Ubangijin kowa ne mai share ma kowa kukan shi. Ki roƙe sa ya cire miki damuwa ya ba ki dangana. Ya ba ki juriya da haƙurin ɗauka. Sannan ki sani dole sai kin toshe kunnuwan ki, abin da kika ji ki nuna baki ji ba, wanda kika gani to ki nuna ba ki ji ba. Ki tsaya a matsayin ki magana in ba ta shafe ki ba ki zare kan ki ciki. Magana in dai ba ta tsallake hurumin da kika ga za a tozarki ba kar ki sake ki tanka. Yanzu gazawar ki a ke nema domin a samu damar ya ƙar ki, in ki ka yi sakaci kaɗan in ya auro ta za ki zama a bar takawarta amma in kika rumgumi haƙuri wallahi za ki ci riba. Ki zauna da ita saboda Allah sai ki ga ubangiji ya yi miki nasibin da har shi mijin na ki zai dawo yana daraja ki. Ki yi duba da ni ba irin abin da ban gani ba. Amma na yi hakuri na jure, Gimbiya kishi ta ke da ni muraran amma ban nuna