Ya ce abin da na ke so ai shi za a yi tun da Yallaɓai ya zama ni, nima na zama shi muna ta hiran mu har muka isa asibitin Aminu kano shashen masu awo suma sun yi mamakin haihuwanta da nake faɗa musu yadda lamarin ya faru, suka karɓi Yumna suna ta santi barin ma da suka ganni ras da ni kamar ban haihu ba. Ita dai Yumna an yi mata alluran su na jarirai ne domin rigafi aka ce ranar da ta yi kwana bakwai za mu dawo a yi wasu, ni kuma suka duba ni a tunanina ma na samu ƙari sosai sai suka ce na samu ƙari amma ba sosai ba. Amma dole ne suka rike ni sai sun yi mini ɗinki shi ya sa na kira Yallaɓai na faɗa masa sai ya ce ba damuwa sai ya jira ni daman muna zuwa sai da ya je ya yi sallar azahar da ta suɓuce masa.
Ni ban sani ba ashe Yallaɓai ya ɗora hoton Yumna a status ya yi magana sannan ya tura a family group ɗin su na gida da cewa na sauka lafiya. Ana ta kiran waya ta, mu kuma muna asibiti sai wajen gab da la'asar muka koma gida bayan an yi min ɗinki da dokokin na yi ta shiga ruwan ɗumi,tare da wasu magungunar da likita ya rubuta mini.
Tun muna asibitin ruwan Nono ya fara zuwa har na ma bata ta sha, saboda tana ta rigiman alluran da a ka yi mata. Mu na mota a hanyar komawa gida sai da na ƙara ba ta, tana ta rigima ni kaina azaban nake ji daga ƙasana, saboda ɗinki kana ganina duk na jigata shi kuma Yallaɓai sai kiran shi a ke yi a waya a na masa barka yana amsawa a muryan shi cikin farinciki da Annushuwa.
Ko da muka koma gida, jama'a cike. Rahila ta zo ita da Ma'u da Ya Murja. Ya Balki ce ba ta nan ta je suna a dangin mijinta Jigawa amma ta ce gobe za ta dawo. Nan na iske Hauwa mun dawo ba daɗewa sai ga Munnira da Mubeenan Musbahu sun iso suma, suna ta mamaki wai kamar ban haihu ba, ita kuma Munnira ta kama min masifa wai ace na haihu tun sha biyun rana amma na kasa kiran su sai dai kawai ta ga Mimisco ta poster jaririya a status ina dariya na ce ta yi haƙuri wayar a gida ma na bar ta mun tafi asibiti amma ba ta haƙura ba tana ta mita yadda suka shirya ma haihuwan nan ai kamata ya yi a ji haihuwan daga bakin su da ƙyar na samu ta haƙura amma in dai Munnira ce akwai ta da na cin magana.
Nan na bar musu jaririyan Ya Murja ta saka mini ruwan ɗumi na shiga na gasa ƙasa na sannan na sake yin wanka ina fitowa suka kawo abinci mai rai da lafiya shinkafa da miya da nama suka ce cefane a ka kawo bayan fitan mu na san Yallaɓai ne ya tura kuɗi a ka kawo mana cefane, sai da na natsa sannan na ɗau wayata na ga tarin kira ba adadi. Har Gwaggo ta kira ni sai da na sake dubawa ne sannan na ga har Alhajin mu ya kira ni. Ya Auwal da Ya Hamza dukkansu tare da matayen su sun kira wayata. Sameena ma ta kirani ita da Nafeesa, ina ga lokacin da suka ji labarin haihuwan ne suka yi ta kirana sai dai na riƙa bin su ɗaya bayan ɗaya ina kiran su muna gaisawa da ƙarfin gwiwata na ke faɗin sunan Mamana ta ci Rukayya amma za mu yi mata alkunya da Yumna. Sameena ta ce ai sun sa ni Yallaɓai ya saka a status ɗin shi lamarin ya ba ni mamaki na san ya kan saka hoto wani lokacin amma bai cika yin rubutu a ƙasa ba. Ban da Haihuwan Jidda lokacin a na cikin samartaka wannan ya ɗora ta ya yi ta ma Allah godiya amma Haihuwan Baby bai saka hoto ba ya dai yi rubutun ya samu ƙaruwa. Haka ma na su Anwar da Khalipa amma ita Yumna ta zo a sa a tun da har ya ɗora ta ya yi rubutu nan da nan na buɗe data na shiga na gani. Ta yi kyau ƙwarai a hoton wato wanda ya ɗauke ta ina zaune ne a ɗazu ne. Rubutun da ya yi a ƙasan hoton shi ne.
"Alhamdulillah. Allah na gode maka. Ubangiji ya sake azurtani da samun ƙaruwa daga Sadiyata. Na yi ta jira ban fidda rai ba, na yi ta ji a jikina Ubangiji bai yanke mini samun zuru'a daga tsatson Sadiya ba. Na yi haƙurin jira. Na shekara ɗaya,biyu, uku har zuwa shekaru goma ban cire tsammani ba. Kwatsam sai ga Ruƙayyatu(Yumna) kyautar da Ubangiji ya yi mana ita da misalin ƙarfe 12pm na rana. Ku yi mata addu'ar Allah ya raya mana ita tare da sauran ƴan'uwanta."
Ni kaɗai ina ta faman mirmishi, hoton na ɗauka nima na ɗora a status ɗina.
"It's Baby girl. Name Rukayyatu Yusuf Muhammad(Yumna)"
Nan na ga ruwan comments ana ta Allah ya raya.
Har Hauwa Jamilu sai da ta buga ihu ta yo mini VN tana ce mini ikon Allah ba ta taɓa tunanin zan ƙara haihuwa ba.
Maijidda Bala yar anguwan mu kuwa ta ce mini ita ko in sha Allahu sai ta zo suna sai na ji daɗi na ce mata ina gayyatar duka yan set ɗin mu in sha Allahu gagarumin suna zan haɗa saboda murnan samun Rukayyatu da na yi a lokacin da na fidda tsammani. Nan ta ke Maijidda ta tura mganar haihuwan tawa a cikin group ɗin mu na makaranta sai tagging ɗina a ke yi ana mini barka wanda bai gane ni ba ma su Hauwa na ta yi masu kwatance, a zuciyata sai na ji wani iri lokaci ya yi da zan gyara mu'amalata da ƙawayena ana yi da kai ai ya fi a ce ba a yi da kai.
Ranar yini na yi amsa waya da zirga zirgan mutane. Da yamma su Jidda suka dawo daga makaranta ai sai buga ihun murna da suka ganni da jaririya na haihu, Baby ta haye gadon ta ɗauke ta ta ƙamƙame tana faɗin na bar mata ina ta mata dariya Hauwa ta ce ta ɗauka ai daman na ta ne. Jidda kuma ni take kallo kafin ta ce" Wai da gaske kin haihu ne Umma?
Ina hararanta na ce" A a ban haihu ba jaririyar roba ce."
Munnira da Hauwa na ta mata dariya sai ta ji kunya ta kauda kanta. Baiwar Allah sai ta matso kusa da ni a hankali ta na ce min" Umma amma ba abin da ya same ki ko?
Sai na dafa kafaɗanta ina faɗin.
"Ba abin da ya same ni Hauwa'u. Na gode da kulawa Allah ya yi miki albarka."
Sai ta yi mirmishi ta amsa da Amin a hankali. Da ƙyar Baby ta bari ta ɗauki jaririyar nan sai da Munnira ta zare mata ido tana faɗin" Ke ba fa taki ce ke kaɗai ba." Sai Baby ta kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka Hauwa ta rumgumeta tana lallashinta ni dai ina gefe ina mirmishi su da iyayen su. .Su Rahila da Ma'u da su Ya Aina suna can tare da su Mubeena suna aiki Tuwo suke yi Ya Murja kuma ta koma gida sai da safe za ta dawo da yamma nan sai ga Zabba'un Ya Abubakar fakam fakam da cewa daga gidan Gwaggo take ita ke faɗa mata na haihu sai a lokacin na tuna ban kira su ita da Alhajin mu ba sai na bari sai da a ka idar da sallar mangariba sannan na fara kiran Gwaggo. Ita ce bayan ta min barka na faɗa mata sunan Mama jaririyar ta ci.
"Haka Aina'u ta ce. Allah ya raya mana ita cikin addinin musulunci"
Na amsa mata da Amin Amin sai ta miƙa ma Alhajin wayar ni na fara gaishe shi cikin girmamawa.
"Lafiya lau Dubu an buɗe ido lafiya! Na amsa masa da lafiya lau.
"Kin tabbatar da ba abin da ke damun ki?
Ina mirmishin jin daɗi na amsa masa da cewa ba na jin komai alhamdulillah.
"To Allah ya ba ki lafiya. Gwaggon ku ta faɗa mini sunan jmRukayya kika ma yar ko?
Na ce E Alhajin mu nan take ya fara kwarara mata addu'o'i.
"Allah ya albarkaci rayuwarta Allah ya raya ta. Allah ya tsare ta daga sharrin zamani. Allah ya ba ku ikon yi mata tarbiya. Allah ya yi musu albarka ita da sauran yan'uwanta gabaɗaya. Shi kuma mahaifin su Allah ya yalwata masa arziƙinsa yadda ba zai gajiya ba wajen hidimar ku gabaɗaya."
Na yi ta amsa da Amin Amin ni dai sai da na kashe wayata ina jin tahowar ƙwalla a cikin ƙwarmin idanuwana. Allah sarki iyaye ma su daɗi a fili sai da na ce" Allah ya jiƙan ki Mama "
Na faɗa ina mai kallon jaririyar da ta ci sunan ta, ta na kwance tana sharan barcin ta, duk ba su tafi ba sai bayan isha'i bayan har wanka Ya Aina ta sake yi ma Yumna ni ma na sake yi na shiga ruwan ɗumi sannan na take cikina da tuwo miyar agushi da kuni dukkansu sun tafi da cewa sai gobe za su dawo suka bar sai ni kaɗai sai yara can zuwa ƙarfe tara sai ga Yallaɓai ya dawo gidan ya taho mini da fura da kayan marmari da yawa na ce Jidda ta karɓa ta ɗaurayo ma na sauran kuma bayan sun ɗiba ta saka shi cikin frizer.
Yallaɓai na gidan Mimisco ta kira ni ta yi minI barka bayan ita sai Anty Bahijja ita Anty Maimuna daman tun ɗazu ta kira ni, abin mamaki Gimbiya ba ta kira ni ba sannan ta ga status ɗina amma ba ta mini magana ba. Na so na yi ma Yallaɓai magana sai ban yi ba yana gidan har wajen sha ɗaya saura na dare nan ya ci tuwo ya zauna riƙe da Yumna muna ta hira da ni da shi da yara. Amma Gimbiya da ta kafa kira sai da ya yi mana sallama ya tafi, yau girkinta ne a fargabanta kar ya kwana a wajena tun da na haihu. Dama muna mganar abubuwan da babu ne na ce masa akwai komai sai dai kayan abinci in zai ƙaro sai omo da sabulun wanka da na wanki sai geron da Ya Aina ta yi masa mgana sai ya ce mini na rubuta na aika masa da shi gobe da safe Musbahu zai kawo min. Haka ko a kayi kafin na kwanta na rubuta na tura masa, tare da yara muka kwana Yumna ta tashi da kukan dare bayan na ba ta nono na sakar ma Jidda ita tana lallashinta ban ma san yauahe suka kwanta ba ni dai kamar ƴar maye haka na kwanta ina barci.
Washegari tun safe Ya Murja ta fara dira ko da ta zo ma har Jidda sun yi wanka ta gama ɗumama sauran tuwon jiya. Baby ce har da rigiman ita ba za ta je makaranta ba na ce lalle ta na da aiki ni masifa na fara mata za ta fara mini kuka na ce zan mata bugun tsiya ƙarshen ta dai Ya Murja ta lallaɓata sannan ta amince suka tafi. Yau Ya Murja ta yi ma Yumna wanka nima ta taimaka mini na gasa jikina bayan na shiga ruwan ɗumi saboda ɗinkin dake jikina. Sannan ta fara gyaran gidan ba daɗewa sai ga Gwaggo ita da Balaraba Maman Saude sun zo mini barka kamar haɗin baki sai ga Nene da Hajiya Iya sai Maman farko Adnan ya kawo su sai da na faɗa musu Yunma ta zama mai sa'a kishiyoyinta na ta kara kaina a kanta suna ta dariya. Sun ji daɗin ganin mu tas lafiya lau kamar ban haihu ba. Ba su wani jima ba suka tafi amma Balaraba sai ta tsaya tana kama ma Ya Murja aiki. Bayan fitan su ba daɗewa sai ga jama'ar Gandun albasa ni da kaina na kira Inna Mariya na sanar da ita na haihu, tare ta ke da matan su Kawu Tasi'u dukkansu dai suka yi mini barka ba daɗewa suka tafi.
Da safen Musbahu ya kawo buhun gero sai rabin buhun siga sai kwalin omo guda biyu, tissue sai kayan tea da yawa saboda daman na ce masa sun kusa ƙarewa. Kayan abinci kuma ya ce sai anjuma za a kawo daga kasuwa.
Ranar ma kamar jiya ne, yini gidan ya yi a cike da yan barka Amina ta kira ni a waya tana faɗin tun ana jibi suna za ta taho na ce daman ban ɗauke ma kowa ba har su Ya Hamza na faɗa musu in su na yafe musu to ban yafe ma matan su ba. Tun da na haihu kullun gidana Munnira da Hauwa suke yini da Mubeena , Su Ya Aina ma kullum sai sun leƙo Ma'u da Rahila suma kullun sai sun taho kamar haihuwar farko. Yadda na daɗe ban haihu ba , ba shakka na faɗa ma Yallaɓai taro zan yi ba ni da taro ba domin na yo gayya. Har Tariq da ya kira ni ya yi mini barka sai da na ce ban ɗauke ma Farida ba. Haka ma Kawu da ya kawo Marwa shi da ita na ce to ya sani tun ana gobe suna domin suna zan shirya sunan da ban taɓa yi ba yana dariya ya ce ya amince mini domin ya cancanci na yi taro na gani da za a ba da labari.
Amma Yallaɓai na neman ya kawo minI yawa wai shi ba shi da kuɗi ya faɗa mini an gama ginin kamfamin shi yanzu oder kayan amfani ke gaban shi zuwa farkon shekaran 2021 yake son su fara aiki. A takaice dai yana faɗa mini ba shi da kuɗi na ce na ji ya ba ni iya abin da ya yi niyya.
100k ya tura mini na shgalin suna, 100k kuma ya ce na siya kayan fitar suna ni da yara. Daman ni bai san ina da kala uku a ɗinke ba cikin kuɗin da ya ba ni na hidimar haihuwa na siya ma kaina. Da kuɗin da ya ba ni sai na siya mana wani swiss lece mai kyau blue ni da yara daman suma na yi musu kala ɗaya na Atamfa super kowaccen su na yi mata riga da zani. Nima na ɗinka super wax ɗin amma kalata na dabam ne. Sannan su Munnira sun fitar da ankon suna wata vatik mai kyau da yarari, suka kuma ce ba su ɗauke ma kowa ba. Kaf yayyena sun siya tun da Munnira ce ta saro ankon haka Farida ta ce a ɗaukan mata in kai mata ɗinki ita da Amina Marwa ma an nan kano a ka kai mata ɗinki har Saude da ke dutse ta siya itama za ta zo matan su Ya Hamza a mota a ka sanya musu na su a cewar su ba su yarda a ɗinka musu a nan ba. A dangin Yallaɓai daga Sameena sai Jamila da Suwaiba suka yi, Mimiaco ba ta yi ba amma ta yi ma yaranta ƙananun Mubeena daman yar gidana ce, Munnira duk ta nuna ma su Anty Bahijja amma take faɗa mini Anty Maimuna sai da ta ce wai na cika tsirfa haihuwa ta ukun ne sai na fidda anko ita kuma ta ce su suka fidda. Ba dai wacce ta yi mu ma ba mu damu da su yi ɗin ba domin ba saboda da su muka fidda ba. Na tura su Hauwa Jamilu da su samira duk sun siya an akai musu har gida sun yi mini alƙwarin zuwa mini suna.
Gimbiya ma ba ta siya ba ni da sai da na kwana biyu da haihuwa sannan ta zo mini barka da borin kunya wai ba ta samun zama ne ga aiki ga shago ni dai tak ban ce mata ba. Da Munnira ta nuna mata ankon sai ta ce ba a nuna mata da wuri ba ba lalle ta samu ɗinki ba har tana cewa ai irin wannan in an san za a yi sai a fiddo shi tun kafin in haihun. Munnira na ba ni labarin amsar da ta ba ta sai da na yi dariya wai su yanzu suka ga damar fiddawa kuma ba dole a ka ce sai ta yi ba daman fita haƙƙi ne. Na yi dariya sanin halin Munnira da ba ta barin ta kwana. Har Naja tana ta ya ƙawarta kishi ba ta yi ankon nan ba, ba domin ya gagare ta ba Anty Zabba ba za ta samu zuwa ba amma ta ce mini zan ga saƙo in sha Allahu. Su a tunanin su sunan da zan yi duk na salon na saka ɗan'uwan su kashe kuɗi ne domin Anty Bahijja ma ta furta a can gidan Nene a na jibi suna Suwaiba da ta zo ta ke faɗa mini, ni ko na ce ya ba ni kuɗi da kayan abinci amma sauran hidima tawa ce ba hannun Yallaɓai a cikin shi. Ni Halima ce ma ta ke ƙara ba ni mamaki sau ɗaya ta zo mini barka shima ba ta wani daɗe bs ta yi tafiyarta. Na tuna lokacin da nake zuwa gidanta na ci uwar aiki amma yau ni ce banza a idanuwanta Gimbiya ce gwana. Na yi kyafci a cikin zuciyata domin na saka ma raina akwai ranar da in ta mu ta haɗo mu sai na yi mata wankan tsarki da za ta gane ba ta da wayau.
Tun ranar litini da ya kama ana goben sunan Yumna gidana ya ɗinke da baƙi. Daman tun da na haihu na ce Yallaɓai ya koma wajen Gimbiya ya ce bai ga dama ba sai jiya ne ya tafi can amma ban sanin masa ko zai dawo bayan suna ba amma ni dai na ce masa ya koma gidanta har sai na yi arba'in ya ce ban isa ba. Amina tun safe suka sauka ita da Farida tare suka haɗa tafiyar Marwa ma da azahar ta iso. Rahila da Ma'u da kayan su suka taho tare da yaransu daman na faɗa musu in suka zo