Turken Gida Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   10 / 55

27K to 30K   out of 163.1K words

za a je."
Sai na ce to Allah ya kai mu Hauwa a ka ce ba za ta je su sai daga baya ba a son a je da yawa ne. Anty Zuwaira ta ce ba da ita ba Anty Maimuna ce da Nasara sai Suwaiba da Halima a yayyen uwa iyaye kenan sai Maman farko da Hajiyar Tafida da ƙanwar baban Sulaihat ɗin a kakkanin Amarya. Sai ƴaƴan yayyen baban ta guda biyu ƙawayenta. Sai a nan aka zaɓo ɗiyar Anty Maimuna sai yar makarantar su guda ɗaya ƙawarta. A Rano kuma an saka yayar Gimbiya amma ita ban ji an saka ta ba sannan har da Faridan Tariq Marwa ma an saka ta ita kaɗai a ce a matan kawun ne. Ana so a yi lamarin da tsari ne kamar da angon ya bukata ba su son cikowa abun ka ga masu kuɗi. An ce matukin jirgin kasa ne Captain akwai kuɗi a hannun shi sannan zuru'an su suna da kuɗi nima duk a bakin Munnira nake ji tsuliyan gari.

Da na koma gida ni kaɗai yara duk suna can na baro su za su kwana. Sai ga Yallaɓai ba a gidana yake ba sai ya ce Gimbiya da yara can za su kwana sai washegari jumma'a ranar walima muna karyawa ya ce.

"Za ki iya zuwa kaduna kuwa?
Ya Zuwaira ta matsa mini sai ke dai kin je."

"Nima haka ta faɗa mini jiya. Ni da Munnira da Anty Zabba."

Yana kurɓa tea ɗin dake hannun shi a mug ya ce" Na ce ga Daughter tun da ita ce ta ce minibza ta je kai Amarya amma sai ta ce a a dole sai ke tun da ke ce Babba."

Ban yi magana ba amma ni kaina na san Gimbiya za ta ce sai ta je kaduna kai amarya yadda ta ke rawan jiki da bikin nan.

"Shike nan tun da za ki iya zuwa sai ki shirya. Amma please ki kular mini da kanki da Baby na."

Ya faɗa ya na mini murmishi.
Nima sai na yi masa murmushi kafin na ce" Da na ce ko ita Gimbiyar ta je?
"A'a gaskiya Ya Zuwaira ta faɗa ke ce Babba kuma ke ɗin ce wakiliyata so ke ɗin ya kamata ki je tun da kin ji sauƙi."
Sai na gyaɗa kaina ban saka aka ba wallahi.
Ranar mun je walima ban san me ya faru ba mun haɗu da Gimbiya a ƙofar shiga falon Anty Bahijja ina washe mata baki ta yi kamar ba ta ganni ba ta ɗauke kanta. Har ta na ture kafaɗanta sai da muka shiga ciki ne Suwaiba ke faɗa mini kan tafiya kaduna ne an ce su bari sau ranar lahadi sai su je tare da wasu kayan ita da Naja shi ne ta ce ita tuni su yi mgana da Tafida kuma ya ce za ta je Kaduna. Ita kuma Anty Zuwaira ta ce ni ce zamu tafi da Amarya gobe shi ne ta fita tana ƙunƙuni

"Topha."

Na faɗa a fili a raina na ce ni ban ga abin ɓacin rai ba.
Munnira ta ce ta raina wayon ta akan kai amarya sai kace zuwa madina?
Ni dai Allah ya kyauta kawai na ce kuma a ranar sai da Anty Zuwaira ta tabbatar mini da na shirya da ni za a je.
Ranar ma ba ta yi mini mgana ba sai fushi take yi tana cika ta na batsewa. Ma'u ta ba ni tausayi da bikin nan kamar ba a santa ba, ita kanta Anty Bahijja ta na fama da mutane ba ta bi ta kanta ba, sai dai tana raɓe wajen dangin mijinta da a ce muna zaman amana ne ni da ita za mu haɗe to da yake ba ta da hali sai ta zama kamar mujiya ga shi Shema ta yi aure da a da ne tare za su zo.

An sha wa'azi malamai uku aka gayyato mata suka yi ma amarya wa'azin zaman aure da zamantakewa sai mangariba a ka tashi. Yallaɓai ya zo ya ɗauke ni wajen taran dare kuma ko gidan bai shiga ba. Bayan mun koma na ga ya na ta waya abin da ya sa na fahimci da Gimbiya yake mgana saboda maganar da ya yi mata.

"Me ya sa kike da taurin kai ne Saudatu? Na ce miki ba za ki je ba Sadiya ce babba ita za ta je kuma hakan ne ya kamata."

"Ok to ki yi yadda kike so"

Ya faɗa a fusace ya kashe wayar. Ban taɓa jin ya kira sunanta ba sai ranar, ta kwaɓe musu saboda zuwana Kaduna ni ko da karambani bayan mun kwanta na ga har lokacin bai huce ba sai na ce masa na hakura ya bar ta ta je kawai.

"Wallahi ba za ta je ba. Ke ma in ba za ki je ba fine amma na riga na rantse ba za ta je ba kuma kin san ba macen da isa ta saka ni na yi kaffaran kan aikin banza da wofi."

Ai ina jin haka sai na koma na lafe a kan filo na ji shuru. Shi da kan shi da ya hucen ya matso ni jikinsa lokacin na ma ɗan fara barci ina ƙoƙarin motsawa na ji yana mini raɗa
a kunni.

"Sai da safe"

Ban amsa mishi ba saboda barcin ya fara fizgata. Na dai ƙara shiga jikinsa sosai na lafe shi kuma ina jin sa yana rufe mana jiki da bargo.






*Janafty**TKGB30E05*

Washegari asabar muka tashi da shagalin biki. Sha ɗaya na safe a ka ɗaura aure kuma sun ce a lokacin za su tafi da amarya. Shi ya sa duk nuƙu nuƙun da a ka tsaya yi ɗaya da rabi motacin ɗaukan Amarya suka miƙa hanya. Ni mota ɗaya muka shiga da Munnira da Anty Zabba sai Marwa. Faridan Tariq tana motar Amarya a gidan gaba.

  Da yake motocin sabbi ne sannan kuma masu lafiya ne a na gudu ma sai ka ji kamar ma ba a yi. Zuwa huɗu da rabi biyar saura mun sauka a gidan Amarya. Mun iske matar Jafar Nauwara, sai ƙawayen Anty Bahijja ina ga su ƴan Kaduna nan ne da wasu dangin angon su suka tarbe mu. Ma sha Allah gida ya yi kyau ƙwarai. kuma iyayenta sun kashe mata kuɗi kayan ta kaf ba na Nigeria ba ne a ƙasar waje a ka siyo su kuma ba a sauke su ko'ina ba sai Kaduna. Kuma da ya ke akwai ma'aikata maza su suka gyara komai, mu kan mu kayan kitchen ne muka zo da shi sai su cafet da labulanya sai ɗan abin da ba a rasa ba. A nan muka yi sallar la'asar muka ci abinci sannan muka kama a ka ƙarisa gyaran daƙun nan. Muna gidan har dare dangin mijin na ta zuwa a nan ne ma mu ke jin jibi jibin nan za su bi jirgin yawo zuwa Madina, mai son ganin ɗakin Amarya sai dai ya jira bayan salla kuma in sun dawo daga Hajji.

Ba a gidan Amarya muka kwana ba. Ni da Munnira da Anty Zabba har da Marwa gidan Faridan Tariq muka kwana. Ita ma Nauwaran Jafar ta diɓi wasu ƴan'uwa. Daga ƙawayenta sai kakkaninta a ka bar Amarya da su ta kwana. Kuma bayan mun kwana can muka hantse sai wajen sha ɗaya muka dawo gidan Amarya da ke anguwan malali.
Da yake abin na yan gayu ne ba wani cikowa sannan an gyara ko'ina tsab. Muna komawa ba daɗewa sai ga Naja ta zo ita da Suwaiba da Halima sai Anty Maimuna jiya ba su samu tafiya ba. Ni dai ban ga Gimbiya ba, ban kuma Tambaya ba amma Munnira sai da ta tambayi Suwaiba ita kuma ta ce Gimbiyar ce ta mata musu lokacin a na ta jiran ta daga baya ta ce su ta fi ba za ta je ba. Zuwa kai Amarya kamar wani kayan gabas ni Sadiya?
Sai da muka yi azahar muka ci abinci sannan a ka kawo mota muka ɗau Amarya da su turamen atamfa da shadda sai kayan abinci da su cincin ɗin da su Naja suka taho da shi.

Gidan Iyayen mijin muka je da ke NDA.  Muka kai musu Amarya sannan da kayan da muka ta ho da shi. Amarya ta samu tarba da kuɗaɗe sosai. Da ya ke suna da kumbar susa ko su gidan iyayen na shi ma a abin kallo ne. Sai a lokacin suke  faɗa mana tafiyar su Madina  jibi in sha Allahu a ka yi ta fatan alheri. Muna gidan har wajen uku saura sannan muka yi shirin tafiya daman kowacce da shirin ta tun da sun faɗa mana daga nan Kano za a wuce da mu. Nan muka bar Nauwaran Jafar da Farida sai Hajiyar Tafida da Tariq ya riƙe ta wai ta jira shi zuwa gobe zai saka a mai da ita gida. Mu kan mu an ba mu turamen Atamfa kowaccen mu sannan da kuɗi cash 10k sannan a ka ɗauke mu zuwa Kano cikin motocin alfarma kamar yadda a ka ɗauko mu.

Ba mu isa gida ba sai bayan Mangariba kuma suna ijiye mu suka juya zuwa Kaduna. A gidan Anty Bahijja muka sauka tun da ita ce uwar biki ya kamata ta ga dawowar mu, amma ba domin haka ba gidana zan wuce na gaji sannan kasala duk ya rufe ni, tun da muka je ban ci wani abincin kirki ba. Na yi amai duk na galabaita barin ma yau ɗin amma ban ƙi sauka ba. A na ta yi ma na maraba da dawowa muna zaune dukkan mu a falon Anty Bahijja a na ta mai da yadda a ka yi a can Kaduna. Maman Farko na ta faɗin Sulaihait ta yi dacen surukai masu dattako sai fatan zaman lafiya sannan ga labarin kyautar ban girman da a ka yi ma na Anty Bahijja sai faman washe baki take yi. A raina na ce wato kowa na son na shi ya je ya ji daɗi. Amma ta na takura ma wasu in ta ga suna jin daɗi lalle wanzami daman a ka ce ba ya son jarfa.

Tun da muka sauka kowa na ta zuwa mana sannu da zuwa. Tun da akwai sauran jama'a a gidan har Hauwa a gidan muka same ta. Ni ban ma san Gimbiya tana gidan ba sai da na fara ganin Khalipa. Ban ga Jidda ba sai Baby ita ke faɗa mini Jidda na gidan Gwaggon su Zuwaira. Bedroom ɗin da ke falon Anty Bahijja na shiga domin na kama ruwa na yi salla ina shiga na ga Gimbiya ta fito daga cikin tiolet ɗin cikin ɗakin ɗauke da Anwar kamar ta wanke masa kashi ne tun da na gan shi ba pampers. Ina ganinta na washe mata baki ina faɗin.

"Maman Khalipa ashe kina gidan?

Amma sai matar nan ta yi kamar ba ta ji ni ba, gani ni da ita a cikin ɗaki ban dandara ba na sake faɗin.

"Mun dawo yanzu ba daɗewa a na ta hira a falo ban gan ki ba."

Na saki baki kawai ina bin ta da kallo domin zuwa ta yi ta raɓa ta gefe na ta fice daga ɗakin kamar ba ta san Allah ya yi ni a tsaye a wajen ba. Har ta na banko ƙofar a saman fuskata  bam! Jikina ya yi sanyi ban san adadin sakannin da bakina ya yi a buɗe kafin na rufe shi ba. Jikina a sanyaye na shiga tiolet na yo alwala na zo na yi salla da hijabin da na samu a cikin wardrope ɗin ɗakin ina jin na Suhailait ne domin ɗakin nata ne kafin aure ya tashe ta.

Ina idarwa na fito da niyar na ce ma su Munnira ni zan ta fi gida. Sai kawai na ga Gimbiya suna mgana da Naja. Kamar zan wuce na ƙyaleta sai kuma wata zuciyar ta ce na yi mata mgana na ji ko na yi mata wani abu ne da zan yi ta mata mgana tana mini wulaƙanci.

"Anty Sadiya ba dai tafiya ba?

Naja ta faɗa ganin na taho in da suke tsaye a gefen falon suna mgaana. Tana ganina ta wani haɗe rai kamar ta ga mutuwarta.

"E yanzu na ke son tafiya ba na jin daɗin jikina ne."

"Gaskiya sannu. "

Ta faɗa sai kuma ta juya tana ce ma Gimbiya."Amai ta yi ta yi a can wallahi."
Ban san ko maganar ta suɓuce mata ba ne, ko kuma daman da niyya ta faɗa ban sani ba sai ji kawai muka ji ta ja wani ubn tsaki kafin ta ce.

" Mtswww to ina ruwana ni dai mu cigaba da zencen mu. "

Ba ni kaɗai ba hatta Naja sai da ta ji wani iri ina kallonta ta na ma Gimbiyar mgana da ido. Ni ko da farkon da na zo wajen har na sauya shawara na wuce kawai ba tare da na yi mata mgana ba tun da na ga da ta ƙara ganina ta haɗe rai amma kalamanta na yanzu su suka ɓata mini rai ya sa na ce sai na yi mata mgana.

"Amma ko dai ba ruwan ki ai mgana mai daɗi ma Sadaka ne in ji Annabi(SAW)"

Na ma yar mata da martani ina kallonta sai ta wani ɗauke kanta sama jikinta na jijjiga irin ƙiris take jira ɗin.

"Don Allah ki yi haƙuri Anty Sadiya."
Naja ta faɗa ta na kallona na so na danne zuciyata na yi haƙurin amma sai Gimbiya ta ɓata komai.

"Mi ye na wani ba ta haƙuri an yi mata wani laifi ne?

Ta faɗa tana mini yatsina. Na ga rainin hankali a lamarin Gimbiya fa ya fara yawa tun ina hakuri tana ƙure ni daman kuma tun da na samu cikin nan a wuya na ke abu kaɗan ke ɓata mini rai ina kiyaye mata sabo ni ba sa'ar yin ta ba ce wanda ya ijiye mu ni shi ne daidai da ni tun abun na mu na mu uku ta ja sai da mutane su ka far ga da abin da ke faruwa domin ni dai ba zan yi shuru ina kallonta ta na so ta ci kasuwa a kaina ba.

"Ba ko a yi mini laifi ba. Amma ina tunanin wata ƙila ni na yi miki laifi tun da tun shekaranjiya in muka haɗu a gidan nan in na yi miki magana sai ki yi kamar ba ki jini ba yau ma ban dandara ba ina ganin ki na yi miki mgana kika yi banza da ni. Ni ko Gimbiya me na yi miki da zafi haka? Me na yi miki da ya sa kike jin haushina?

Kawai sai matar nan ta fara ɗaga murya tana faɗin" A a malama ɗan dakata ba na son sharri ni yaushe kika yi mini mgana ban amsa ki ba? Ai ko sai dai in ban ji ki ba. Ni dai ki tsaya da mganar nan a nan ahto domin kar ta je gaba. Yanzu sai  ki ji magana a gaba ana ƙokarin ɗora min jarkar tsaba."

Naja na yi mata mgana amma tana mini rashin kunya har ta na wani ƙara yarfa hannu tana cigaba da faɗin" To Naja haka kurum ina cikin zaman lafiyana ta jawo mini wani masifan. Yanzu nan sai ki ji mgana ta kai kunnen Daddy shi kuma da yake ba ta laifi a wajensa ya hau ni da faɗa. To ba na so mganar ta tsaya iya nan, maganar kin yi maganar na yi banza da ke ban san an yi haka ba wataƙila lokacin da kika yi mini maganar ban ji ba ne."

Ai sai na ma kasa mgana sabida mamaki lokacin har su Munnira sun zagaye mu suna tambayan ba'asi ita kuma Gimbiya Naja na janye ta tana ba ni haƙuri tana ce ma su Suwaiba ba wani abin faɗa ba ne na ce ne na yi ma Gimbiya mgana ta yi banza da ni sai ita kuma Gimbiyar ta ce ba ta ji ba ne. Amma ba faɗa ba ne.

"Ba faɗa ba ne ta ke faɗa minI kar na kai mganar gaba? Wato ga munafuka ko me? Kin taɓa jin wani abu ya faru Yallaɓai ya ce daga bakina ya ji? Ina ruwana da sha'aninki da za ki tsaya a gaba na balle na riƙa hirar ki da miji? Kina gidan ki ina gidana me ye haɗina da ke! Ni ma sha'anin gabana ya isheni ba ni da lokacin wannan sannan ban gane kin ce wai ni daman ba na laifi a wajen shi ba? Me kike nufi? Sannan kina nufin ni zan yi miki ƙarya ne Gimbiya? Na ci riban me? Ke ma kan ki kin san ba ki isa na yi miki ƙarya ba domin isar ki ba ta kai har haka a wajena ba"

"Sadiya me ya faru?

Maman farko da tambayeni lokacin da ta ƙariso wajen ina ƙoƙarin magana kawai sai Gimbiya ta buga shewa tana faɗin" Ahayye. Shi ya sa na ga kin yi ƙutun ƙutun kin tafi Kaduna. To ina fatan kin je kin ciwo abin da ba ki taɓa ci ba ko?

"Ke Gimbiya me ye haka?

Anty Maimuna ta faɗa tana shiga tsakanin mu.

"Ba dai rashin kunya za ki yi ma Sadiyar ba ko?

Anty Zabba ta faɗa. Hauwa ko rike ni ta yi tana cewa kar na ce komai Munnira ko faɗi take yi" Jaruba wallahi kika ce za ki yi ma Sadiya rashin za ki daku a falon nan wallahi."

Wata shewar ta buga kafin ta ce" Ko ita ba zan da kun mata ba. Ballatana ku yan koren ta."

"Haba Saudatu"

Maman Farko ta faɗa kamar ranta ya ƙara ɓaci Anty Bahijja ba ta wajen daga baya a ka kirata ta zo dai dai lokacin da Munnira ke sa'in sa da Gimbiya.

"Ni kaina ba kai isar da zan yi sa'in sa dake ba. Ballanata Sadiya ta fi ƙarfin ki. Kuma Kaduna ta je ke ma ya sa ba ki je ba? Kin ga kenan isar ki ce ba ta kai ba ita kuma da na ta isar ya kai miji ya sahale mata ta je duk shi ne haushin na ki? Sorry ki yarinya mijin wata kika aura dole ki zamo ta baya ko kina so ko bakya so. Kuma na san duk wannan kumfar bakin da kike yi ba a kan tafiyar mu Kaduna ba ce, haushi ne baƙin ciki kin ji labarin Sadiya na da ciki sannan Tafida na ririta ta shike nan sai

10 / 55