Turken Gida Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   41 / 55

120K to 123K   out of 163.1K words

a kaina marasa daɗi.
Wai na ki yadda mu haɗa kai da Gimbiya na koma gefe ina munafutarta wai tun kafin Amaryan ta shigo na ke ta tusa kaina a wajen yar cikina. Mangaganu dai marasa daɗi, ni ko na yi mata rantsuwan duk abin da ta ji ƙarya ne na yi mata cikaken bayanin abin da ya faru  da wanda ke faruwa.

"Sameena na isa na hana Yallaɓai aure? Ni ban isa ba shi ya sa na koma gefe na zama yar kalllo. Itama shawaran da na bata kenan ba ta ɗauka ba, ta biye ma su Anty Bahijja suna faɗa mata cewa ni ina jin daɗin auren da Yallaɓai zai yi sabo da ita. Sun manta nima ɗin mijina ne kuma mace ce ni, ina da kishi sai da na saka haƙuri kuma na roƙi Allah ya cire mini zafin kishi. Kuma ya cire mini shi ya sa na ke zaume lafiya su kuma shi ne ba su so, sun so ne yadda take hauka nima na biye mata duk mu zama mahaukata."

Sameena ta ce "wannan gaskiya ne. To kuma ba a kishiya ke kika bari aka auro ta,? Duk ta manta baya? Wallahi tana ta rigima domin jiya ma mun yi waya da Hajiyar mu take faɗa mini case ɗin gida ma ake yi "

"Gida?

Na furta cikin mamaki domin ni ban ma san da maganar ba
Sai da ta yi mini bayani ashe Gimbiya ta yi tsalle ta ce Amarya ba ta isa ta fara tarewa a gidan ba kafin ita ba.

"Ikon Allah."

Na faɗa ina jinjina kaina.

"Wallahi an ce magana har Baba Tafida ya shiga ciki. "

"To ya ake ciki yanzu?

"Ban sani ba. Amma dai an ce Ya Tafida ya ce in har ta ga ta tarewa a gidan nan to kema kin tare ne amma tun da ta saka tsiya sai ya gani ɗin."

Ni ma kasa magana har muka yi sallama da Sameena. Kenan da gaske Gimbiya take yi? Illau ko kwana biyu da maganar mu da Sameena Yallaɓai ya shigo mini gida da rana kamar kabubuwa ranar a gidan Gimbiya ya kwana ban san kuma me ya faru ba kawai ya ce nima na shirya za mu tare a sabon gida a ƙarshen wata bai ma ba ni damar magana ba ya fita ya shiga mota ya ta fi. Hankalina ya tashi saboda ban shirya komai ba ina ni ina tariya ni da Yallaɓai ya yi ma manyan falo uku da bedroom huɗu na su Gimbiya ne falo Biyu bedroom biyu. Ina na ga kayan da zan yi wannan tariya ai ba tariyan sauri ba ne sai na natsa.

Na rasa yadda zan yi, a yadda Yallaɓai ya zuciya ban isa na kawo wata magana ba. Domin a daran ma da ya dawo ina fara magana ya dakatar da ni.

"In dai maganar tariyan gida ne bana son jin komai. Ki shirya ki tare a ƙarshen wata nan."

Tun da na ji haka na san akwai matsala na rasa wa zan tun kara, na yi niyyar na yi sabbin labulaya. Da Zannuwan gado da ɗan abin da baa rasa ba sauran abubuwan daga baya in Allah ya hore mini sai na yi. Ni kwata kwata ban shirya ba, har ya faɗa ma yara suna ta Murna su Jidda har sun fara parking ɗin kayan su har Yumna tsalle take yi za su koma sabon gida.
Ganin ya ƙi saurarena ya sa na kira Mimisco na sauke murya ina faɗa mata uzirina.

"Ke ma kin yi magana Sadiya. Amma kin sani ki yi shuru kar ki yi masa mgana a yanzu yana cikin tsini ne, ki bari nan da sati ɗaya in ya huce sai na yi masa mgana."

Sai na ce mata to, ban tambayeta ba da kanta ta fara faɗa mini matsalan da aka samu. Gimbiya ta matsa sai ta fara tarewa magana har magabanta ta sun shiga. Hajiyar Tafida ta goyo bayan yarta har tana cewa Tafida bai yi adalci ba ta ya ya wata can za ta fara tarewa ba mu ba, in ni ba zan tare ba amma ya zama dole ita Gimbiya ta fara tarewa. Shi kuma ya ce ba za ta taren ba, ya ɗauka ta gama fahimtarsa ashe ba haka ba ya cije ya yi taurin kai sai da magana ta kai wajen Nene ita ta tursaashi ya amince amma da sharaɗin sai dai mu tare ni da Gimbiya amma ba ita kaɗai ba. Ni dai Gimbiya ce ta kusa ja mini bala'i ina zaman zamana amma tun da Mimiaco ta ce za ta saka baki na san za ta yi mini iya ƙoƙarinta illai kuma ta yi domin sai ga Yallaɓai da kan shi ya zo mini da maganar.

"Me kika ce ma Mimisco?

Sai na gyara zama ina faɗin" Na fada mata ta roƙar mini kai. Ka yi mini alfarman tariyana sai bayan bikin ka sai na tare a tsanake."

Kallona ya yi amma bai yi magana ba ganin haka yasa na gyara zama ina sake faɗa masa hujojina, bai wai ya gamsu ba ne kawai dai ya dakatar dani da cewa" Shike nan tun da kowa abin da ya ga dama ya ke yi. Ni dai Allah na gani ina iya bakin ƙoƙarin sauke nayin da ke kaina. Wacce acikin ku take ganin ina cutar da ita Allah ai yana sama yana kallo."

Sai na ji wani iri a cikin zuciayata da maganaganunsa.

"Ka yi haƙuri. Bari kawai sai na tare tun da haka kafi so."

"Kar ki damu, ki yi na ki tsarin itama can ta tare a lokacin da ta so ba shike nan ba."

Sai na kasa magana saboda a daƙune ya yi maganar kuma tun daga lokacin bai sake ɗaga maganar ba sai na fahimci Gimbiyar ta gama ɓata ma Yallaɓai rai kan mganar gidan nan ba ma ya son maganar kwata-kwata amma ni tun da na samu ya amince shike nan na kama kaina ban shiga abin da ba ruwana ba. Ya faɗa mini ya fara ba ma Rabi'a wasu kuɗi na lefe tun da farkon wata mai kama za ta koma can maiduguri sai an ɗaura aure kamar wasa na ce ya ba ni kwangilan hijabai da iners na Amarya ban ɗauka zai amince mun yi maganar yau washegari ya zo mini da maganar na yi list ɗin komai amma mu yi magana da Rabi'atun na ji size ɗin ta. Jin zan samu nawa a sama ya sa da gudu na amince, na neme ta a wayar Jidda muka yi magana ta tura mini size ɗin bra ɗin ta pant, sai na hijabi adadim yadin da take sawa duk ta tura mini da kalolin da take so.

  Nan take na tura bangaren Hijabai, inears ɗin kuma na shirya da kaina Jidda ta rakani muka shiga kasuwa a rana ɗaya muka siyo komai. Na ci riba domin Yallaɓai bai yi mini ƙauron kuɗi ba isassu ya ba ni. Kuma da ya dawo ya ga kayan shi kan shi ya yaba. Sai da aka kawo hijaban sannan ya kwasa ya kai mata ta haɗa da sauran kayan, abin da aka yi daga ni sai Yallaɓai sai Rabi'atu sai ga magana na yawo a dangin Yallaɓai wai saboda neman gindin zama ni ce na haɗa ma Amarya lefe. Hauwa ta kyanƙyaa mini maganar ta ce a bakin Halima ta ji, sai ga shi na je barka gidan Jamila da ta haihu muka haɗu  da Anty Bahijja ta shaguɓa mini magana da cewa na dai na murna na sani duk abin ka yi shi za a yi maka.

Ni ko na amsa da cewa haƙƙun kuma in ka shuka alheri ka ga alheri in sharri ne ma shi za ka gani. Na kuma ƙara mata da cewa a wannan zamanin ma abin ba ka yi ba shi ake yi maka ballanta ka yi.
Abin da ke ba ni mamaki a ina maganar ta fita? Sannan ma ba za a faɗi gaskiya ba sai an ƙara da sharri. Ni su Hauwa kawai na faɗa ma gaskiyan magana sauran ban damu ba su cigaba da yaɗa duk abin da suka ga dama. Sai da na yi ma Yallaɓai magana na ce ko shi ya yi maganar da wani a can Gwammaja? Sai ya ce ya faɗa ma Nene ina jin haka na ce wata ƙila ita ce ta yi zencen da ya'yanta su kuma da man suna adawa suka ƙara ma labarin gishiri da maggi tun da ba sa son zaman lafiya. Tuni na fita batun su na kama harkan gabana fafutaka na samu yan kudaɗen da zan rage siyayyan tariyan sabon gida. Na samu na labule sauran cafet da zannuwan gado cikin riban siyayyan Amarya Yallaɓai sauran kuɗin da ke hannuna duka zan haɗe su waje ɗaya mu ga abin da Allah zai yi. Shi ya sa duk na faɗa ma su Ya Hamza za mu tare a sabon gida kuma akwai falo ɗaya da bedroom biyu ban san me zan saka ba.

Ya Auwal ya ce na saka karikitai mana, ina laifi Ya Hamza kuma ya ce ni na ma samu duniya tun da har falo  huɗu Yallaɓai ya yi mini. To ya cika ladan shi ya yi kayan ɗakin mana ni dai na yi dariya ban yi magana ba. Na san ba domin hidiman auren da ya ɗauko ba Yallabai zai iya yi mini abin da ma ya fi haka in dai bai fi ƙarfin shi ba. Amma dai yanzu kan bam ma saka rai ba shi ya sa nake ta fafutakana na samu na rufa ma kaina asiri.  Har a raina ban saka rai da samun wasu kuɗi daga Yallaɓai ba, sai ga shi ya ba ni 200k ya ce ba yawa yara kuma 100k  na yi musu siyayyan kayan fitar biki na yi ta godiya domin ban yi tsammani ba. Atamfa kawai na siya mana sai leshi sauran kuɗin na adana, da gayya da Munnira ta yi mini maganar Anko na ce a fitar mana da shi, nan take ta fitar mana da kamfala mai ja da ruwan madara mai kyau, kuma ni na tura ta a group ɗin gidan su Yallaɓai na ce ankon bikin Yallaɓai, kalilan ne suka fito suka yi magana amma su Anty Bahijja gum, na san kuma na sha zagi da man kuma ina kan sha ne.

Ai wannan ankon da na fidda kamar za su saka ni a cikin wuta. Yallaɓai ko da ya ji labari daɗi ya ji nan take ya sake tura mini 50k namu ni da yara har da Gimbiya da aka kawo na aiki Jidda ta kai mata sai ta dawo mini da shi da cewa Allah ya kyauta ita ba ta so, da ya dawo na faɗa masa tsaki kawai ya yi kawai ya ce na yi kyauta da shi. Ho ho ina shan zagi, Mimisco ta ce abin da na yi ya yi dai dai, hankalinta ya ɗauke ba ta yi tunanin haka ba, ba takura wanda ya ga dama ya yi wanda ba zai yi ba, ba takura. Su a cewarsu miye na fidda anko? Ai sai a jira a fidda a bikin Adnan na ce kowa da ranar auran shi saboda haka mu dai mun fidda wanda ya ga dama ya yi, wanda bai ga dama ba ya bar shi.

Su Suwaiba ce kawai suka siya sai su Jawahir, Halima kuma Jamila ta kirani a waya tana faɗa mini irin zagin da ta zo gidanta tana yi mini wai ba na kishi ina ta murna har ina fidda anko. Kamar zan kirata na ja mata kunne sai na fasa na ce bari na jira bikin na ga ni in ta isa ta hana abin da Allah ya tsara. Ni dai da tawagata muna gefe muna shirin mu Ankon Gimbiya kuma Rahila na ba ma ta ɗinka har Amina ta siya za ta zo mini biki. Gimbiya ba ta gayyace ni tariya ba, ban kuma san za ta tare ba sai a bakin Hauwa na ke ji ta tare a sabon gida a ranar 31 ga watan December, na ce Allah ya sa rai ya mora, ba ta gaya mini ba ban kuma je ba shima uban gayyar bai sanar da ni ba.

Hauwa dai ta je amma Munnira ba ta je ba, ita ta zo mini da labarin ina shan zagi wajen su Anty Bahijja na ce sai su yi ta yi, ni kam ba sa gabana. Sun ce wai tarewaar ma saboda ina da mugun nufi na ce sai daga baya to tun da na nuna haka shike nan sai mu zuba su gani. Na rasa me na tare musu suka ɗora mini karan tsana, ga Ɗan uwan su da zai yi aure ba su yi masa haka ba sai ni? Miye nawa saboda nima ban yi haukar da Gimbiya ke yi ba? To in dai haka ne sai dai su yi ta tsana ta amma ni ba zan yi wannan haukar ba a baya ma ban yi ba, ballatana yanzu da girma ya kamani ba ruwana. Su je su yi faɗa da Yallaɓai shi da ya ɗauko auren ni dai ba ruwana shirin auren sa baya gabana, a gefe ɗaya ina ta shirin tariyata da zan yi bayan auren Yallaɓai amma na ce sai ya gama cin amarcinsa sannan zan koma, ba zan iya juran ganin shi yana rawan ƙafa kan wata mace ce. Ita Gimbiya da ba ta gane ba ta kai kanta. Hausawa suka ce ai ƙazantar da baka gani ba sunanta tsabta amma ita kazantar ta je gani Allah kuma ya ba ta sa'a ina nan ina zaman zamana na san za ta yi nadaman abin da ta yi.

*****

Biki ya ƙarato tun da mun shiga sabuwar shekaran 2023. Jidda na shirin komawa makaranta amma za ta je ta biya kuɗin makaranta da na hostel,  sai ta dawo tun da karatu bai kamkama ba sai bayan bikin babanta za ta koma, amma ko a yanzu ba zaman banza take yi ba kullum cikin cin kayan fulawa muke yi a gidan nan Cake kam har kyauta nake yi da shi. Donut kuma sai ya yi sati tun da shi ba ya lalacewa da wuri.

Jidda ta gayyato kawarta Ummu Salma Hamza. Baby ce uwar gayya har da yan haddar su, su ba ruwansu murna kawai suke yi, a na saura sati biyu da wani abu biki Yallaɓai ya ce Rabi'atu a ranar ta koma Maiduguri na ce lalle za ta sha tafiya. Sai ya ke ce mini ai jirgi ta bi amma daga nan gida sati na sama za su tafi da  sauran kayan a mota. Ban ma tambaye shi ba shi da kan shi yake faɗa mini suma a jirgi za su je ɗaurin aure. A raina na ce ai kana da shi ko birnin sin ne za ka biya domin ku je, yana yi mini list ɗin da waɗanda za a je ɗaurin aure Alhajinmu na sahun gaba shi da Tafidan Rano. Sai shi da aminan shi, sai Ya Usman da a can za su haɗu sai Musbahu.

"Kuma duk kai za ka biya kuɗin jirgin?

Yana dariya ya ce" Kawun ki  ya ce zai ɗau nauyi"
Na jinjina kai zai iya tun da shima ya ta da kai. Har anko ya siya ma Marwa kuma da kan shi ya zo ya karɓan mata da ya shigo garin. Tariq ne da man bai kamo su ba amma shima yana da rufin asirin shi.
Yallaɓai bai faɗa mini ya yi kashe kashe kuɗi ba amma ni na san ya yi auran yar maiduguri ba wasa ba, ya faɗa mini an yi masa maganar kuɗin gyaran jiki na ce ai su can kamar al'ada ne.
Amma shi fa bai damu ba murna kawai yake yi ba ya damuwa da kashe kuɗin. Ni ce ma na gaji na tambaye shi gidan da Gimbiya ta tashi ya zai yi da shi? Ya ce mini bai yi tunani ba yanzu an rufe shi in ya yi shawara zuwa gaba zai san yadda zai yi da shi. Wallahi har raina nake son gidana ba na son tashi, amma tunda cigaba ne ya samu ba ni da mafita amma ina son gidan nan kuma ina da tarihi mai ɗimbin yawa a cikin shi.

Yallaɓai ya tsara tun da ban riga na tare ba a gidana za a yi taron biki ba Gwamnaja ko sabon gida ba. Ni da man ban ce kowa ya zo ba iya ni da yan uwana da wanda ya ga zai zo. Gimbiya da man ta ce ita ba biki za ta yi ba gidan matar de za ta zo, saboda haka mukkarabanta can za su sameta a sabon gida. Ni kuma ina gidana da jama'ata.
Tun satin biki Yallaɓai ya fara ƙyallin amarci ni kuma sunan shi ya tashi daga Yallaɓai ya koma Ango da ko na ce Ango zai washe baki yana jin daɗi..komai na buƙata ba abin da Yallaɓai bai kawo ba. Ya ba ni kudin kunshi da gyaran kai ni da yara kuma mun yi, mai kunshi ta zo har gida ta yi mana na yi gayya domin kaf yan gidanmu ban ce na ɗauke ma kowa daga su har yaran su.

Ana jibi biki Amina ta diro daga Kaduna. Faridan Tariq tazo aamma ita sai ana gobe biki. A kuma ranar su Yallaɓai suka daga maiduguri tun da in an ɗaura aure kuma za su juyo da amarya amma akwai sauran kayan da wasu za a kawo su ta mota. Jere kuma a ranar jumma'an da man daga nan Kano dangin su suka zo suka yi, ni ce na yi musu abincin tarba domin Gimbiya ta ce ba za ta yi ba Yallaɓai ya kirani ya ce na dafa na aika akai musu. To ba ma ni na dafa ba su Mubeena ne su kuma suka kai musu abincin can gidan shinkafa da miya da pepe chicken, sai kunin aya da zoɓo. Suka dawo suna faɗa mana irin dukiyar da aka sanya ma Amarya a shashenta da tsaruwan sabon gida.

Da man Mubeena da Marwa ne suka je kai musu. Suka ce Gimbiya na bangarenta ana ta shewa ta shirya rashin mutumci na ce ya ƙare mata can ni ba ruwana da ita. Wannan abin da na yi haka Yallaɓai ya

41 / 55