Turken Gida Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   33 / 55

96K to 99K   out of 163.1K words

don Allah ka dauki mataki in ka isa."

Na faɗa ina isa gaban shi na tsaya ina riƙe kuguna.

"Da gaske banza ce tun da ba ta iya ramin kanta sai dai na wani. Kuma wallahi tallahi ba ta isa na amsa laifin da ban aikata ba. Rashin kunya ba irin wacce ƙanwarta ba ta yi mini ba shi ba a faɗa maka ba sai gulma da munafunci?

Na faɗa ina zare masa ido.

"Ki matsa daga gabana kafin raina ya ɓaci na yi miki abin da ba ki yi tunani ba Sadiya."

Ya ɗan fara saukowa tun da ya daina ɗaga murya ko saboda yara ne oho. Marwa ta ja su sun koma ciki amma har lokacin ana jiyo kukan su.

"Me zaka yi! Na ce Yusuf me za ka yi?

Na faɗa ina ƙara ɗaga murya ni fa tun da ya jawo wannan faɗan to gwara a yi shi kawai kowa ya san matsayin shi.

"Ƙina so ki ga abin da zan yi ne ?

"E. Ina so na gani. "

Sai ya wani nuna kanshi kafin ya ce" Ni kike tsarewa cikin gadara kina faɗin na ɗau mataki akan sadiya?

"E sai me? Tsoron me zan ji? Ƙarshen mataki kenan ka ce ka sake ni ko Yusuf? To ai ba ƙarewar rayuwata ba ce ta zo in na rabu dakai ba sai me.'

Kawai sai ya tsaya yana kallona nima ko ina kallon shi ido cikin ido.

"Yau yanzu ka ce na fice maka a gida zan fita. Tun da daman ka ce ba gidan Ubana ba ne."

"To ki tafin ma who stop you? Na hana ki tafiya? The door is open Sadiya. A sauka lafiya."

Ya faɗa yana nuna mini ƙofar falo. Na razana da kalamansa amma ina zuciyata ta ƙekashi ban nuna masa na razana ba, kawai sai na yi mirmishi kafin na ce" Da a ce yau Sulaiman Yashe bai da gida da na sha wulaƙanci."

  Ba ni da kuɗi a jikina daga ni sai hijabin salla na amma ina ganin in na koma ciki zai ga kamar na gaza ne. Sai kawai na wuce har na isa kofa falon sai na juya ina kallonsa dafe da kai a kausshe na ce.

"Ni Sadiya ni yau Yusuf ka kora a gidan ka ko?

"Kin ce za ki tafi kina tunanin zan tsayar da ke ne? Ki sauka lafiya na ce Halimaaa.!

Ya ja sunan shima a kausaahe yana kallona ina kallon shi. Idanuwanshi sun kala nima nawa ya kala ya yi jajir sai kawai na buɗe kofar falon na fice ina jin Marwa ta biyo ni tana Umma Umma.
Sai a lokacin na tuna da ita a fusace na waiga ina faɗin" Ki dauki mayafinki mu bar masa gidan shi Marwa."

"Umma..amm"

"Wallahi zan mare ki za ki taho mu tafi ne ko na yi tafiyata."

"Zan zo."

Ta fada tana zakuɗa goyon ta dake bayanta har ta fara hawaye.
Baby ta fito ita da Yumna ina jin Yallabai ya rike su yana mgana da su kasa kasa.
Marwa ta dauko mayafi ta fito na ji ta tsaya tana mgana da Yallaɓai a fusace na ce" Wai ke ubanki ne da za ki tsaya kina masa mgana?
Ki jira har sai ya kai ga haɗa ki da jami'an tsaro sannan sai ki bar masa gidan sa."

Na ga ya buɗe kofar falon ya fito Yumna na hannun shi tana ganina ta fara Uma tana miƙan hannuna na juya zan fita Marwa dake bayana ta ce" Umma ko Yumna ba za ki tsaya ki karba ba!

"Ba da ita na zo ba. Saboda haka ba da ita zan koma ba."

Baby ta rigo tana Umma Umma cikin kuka na tsayar da ita da hannu ina faɗin" Kar ma ki ƙariso ki koma nan ne gidan Ubanki nima gidan nawa Uban zan koma ya tattaraku ya kai ma Matar so ta haɗa da farar haihuwa duk ta riƙe "

"Sadiya."

Ya kira ni a tsawa ce, ko kallon shi ban yi ba na fice daga falon ina jin kukan Baby da yadda Yumna ta yanka ihu. Ni kaina duk dauriyata sai da na ji hawaye sun kece mini. Wani abu ya tsaya mini kahon zuciya, wai ni ce yau Yallabai ya kora daga gidan shi. Lalle duniya juyi juyi na gaba ya koma baya.

*Janafty**TKBB3N15*

Lokacin da na fito daga gida na san ba ni da kuɗi a tare da ni amma hankalina bai tashi ba
sai da muka kai titi. Sannan na fahimci daga ni sai kayan jikina da hijabi na fito. Takalmin kafata na silafas ɗin cikin gida ne, tsabar a yanayin da na fito ba mai daɗi ba ne. Marwa na kalla da ke biye da ni, ga Afra sai ƙananun kuka take yi tana faman jijjigata.

"Marwa kin fito da ƙudi?

Na tambaya ina jan majina. Saboda tun fitowarmu har bakin titi hawayena bai  tsagaita ba.

"E na ɗauko ƙaramar jaka ta"

Ta faɗa tana nuna mini jakar sai na sake jan hanci irin na masu kukan nan, mun ɗan jima kafin mu samu Adaidaita muka shiga na ce Ɗorayi zai kai mu.

Muna tafe shuru sai kukan Afra ni dai ina ta goge hawaye lokaci bayan lokaci ina jin nono na yana zuba kenan har yanzu Yumna ba ta daina kuka ba. Sai na ji tausayinta kamar in koma in ɗaukota amma kuma gwara da na barta shima ya ji in da daɗi.

"Umma."

Marwa ta kira sunana tana kallona, nima da rinanun idanuwana na kalleta.

"Me ya faru?

Ganin ta ƙura mini ido amma ta kasa mgana.

"Umma me ya sa kika taho?
Da kin tsaya kun fahimci juna da Kawu "

Wata uwar harara na jefa mata sai ta yi saurin kama bakinta ta yi shuru.

"Kika sake yi mini maganar shi zan kwasa miki mari Marwa."

Na faɗa ina huci ni kaɗai har ya yi mini wannan tozarcin kuma take tunanin na zauna mu fahimci juna? Mutumin da ya ce na bar masa gida ai ya gama magana.

"Ke ko a ranki ba ki ji haushin tozarcin da ya yi mini ba. Amma kina maganar wai da ban taho ba na zauna mu fahimci juna. Tun da ke a yanayin da kika gan shi kin ga alama yana buƙatar hakan."

"Ki yi haƙuri Umma "

Ta faɗa a sanyaye amma ni sai na ji kamar ana hura ma ɓaçin raina wuta ma na cigaba da faɗa ta in da nake shiga ba ta nan nake fita ba, saboda ni gani nake yi goyon bayan Yallaɓai take yi ni kuma tana ganin laifina domin na bar masa gidan sa kamar yadda ya buƙata.

"Umma da kin taho da ko Yumna ne?

"Ba zan taho da ita ba ɗin. Lokacin da ya auro ni ai ba da ita Alhajinmu ya haɗo masa ba. Su zauna gidan ubansu nima gidan nawa uban za koma."

"Umma tana ta kuka fa"

"Ke zan ci ubanki fa Marwa in ba ki ƙyale ni da waɗanan mganganun naki ba. Kina ƙara tunzarani."

"Allah Ya ba ki haƙuri"

Ta faɗa tana sunkuyar da kai kamar munafukar tsabar yadda ta ba ni haushi kamar na kai mata duka.

"Namiji ya yi maka irin wannan wulakancin kuma don ba ka da zuciya sai ka cigaba da zama? To ko ke Kawu ya yi ma haka ni uwarki na ba ki Umarnin ki baro mishi gidan shi ki dawo gida domin ya san ubanki na da gida ba a daji ya auro ki ba."

Ba ita kaɗai har mai Adaidaitan sai da ya juyo yana kallona na haɗe rai ina harare harare.

"Hajiya a dai yi haƙuri. Rayuwar auran yanzu duk ɗan hakuri ne."

Hararan bayan shi na yi, domin ni yanzu duk wani namiji na gama sallama shi wallahi. Duka halin su ɗaya ba su da adalci sannan butulai ne. In za ka yanki naman jikinka kana ba su suna ci wata rana sai sun nuna ma duniya kai ne mara amfani a wajen su. Ni yau Yallaɓai ya kalla ido cikin ido ya ce ina da mugun nufi a kan matarsa wai har yana faɗin an targaɗa masa mata a sanadina. Ai na ɗauka yadda ya zo yana cika yana batsewa zai rama mata ne, sai wataƙila ya ji huce daga raɗaɗin taba matar so da aka yi. Ban ga laifin su ba duk mganganun da suka shirya masa in har ya yi amfani da hankalin shi da tunanin shi bai kamata ya fara da haka ba, da sai ya fara yin bincike kafin ya zartar da wata mgana.

Har muka sauka a Dorayi ni kadai na ke cika ina batsewa ina karkaɗa kafa. A bakin titi muka sauka Marwa ta biya shi kuɗin shi da taka da kafarmu muka ta ka zuwa gida. Lokacin ana ta kiraye kirayen sallar isha'i a wasu masallatan anguwan. Ai ban ji wani kukan baƙin ciki ya taho mini ba sai da na ji kafafuwana sun taka zauren gidanmu. Bayan shekaru ashirin da wani abu yau Yallaɓai ya bar mini tarihi. Tarihin ma mai nauyin da na ke jin sa har a cikin zuciyata.

Ni ce a gaba Marwa na bin bayana. Ba wutar nepa amma akwai hasken tocila a tsakar gida sai da muka ƙariso tsakar gida sannan na ga Alhajinmu duke yana alwala. Gwaggo ce ke tsaye tana haskamai da fitila. Ni na yi sallama amma muryata ta shaƙe da farko, sai da na sake yi kamar a tare ni da Marwa.

Gwaggo ta amsa lokaci ɗaya ta nai mai hasko fitila cikin mamaki.

"Sadiya.';

Gwaggo ta faɗa cikin mamaki da har ya bayyana a muryanta
Alhajinmu kuma sai da ya idar da alwala sannan ya miƙe yana mai kiran sunana.
"Dubu"
Kamar yana tantama ɗin ce ko ba ni ɗin ba ce.

"Na'am Alhaji."

Na faɗa cikin karyewan sauti kafin lokaci ɗaya na fashe da kuka.
Gwaggo ta ce" Subhanallah ke da waye haka?
Alhajinmu kuma duk ya ruɗe faɗi yake yi.
"Maimuna kama ta ku shiga ciki. Ba lafiya"
Kamar haɗin baki sai ga nepa sun kawo wuta tsakar gidan ya yi haske ɗau.

"Marwanatu."

Alhaji da Gwaggo suka haɗa baki wajem ambaton sunan ta.

"Na'am."

Ta amsa itama a sanyaye. Ai sai Alhajimmu ya kalli Gwaggo itama ta kalle shi Allah kaɗai ya san mai suke sakawa a zuciyarsu amma in zan iya karantar fuskokin su, sun bayyana damuwa tare da mamakin ganin mu a tare a wannan daren.

"Dubu lafiya? Me ke faruwa ne? Me Marwanatu ke yi tare da ke?

"Alhaji ƙafafuwana sun fara rawa. Allah ya sa dai lafiya.'

Gwaggo ta faɗa cikin damuwa.

"Ina fa lafiya. Ba lafiya Maimuna "

Alhajinmu ya faɗa shima a muryansa har ta bayyana damuwa.
Muna tsaye ni da Marwa mun kasa mgana, gwara ita ba kuka take yi ba ni kuka na ke yi har yana ba da sauti.

"Shin ba ku faɗa mana abin da ke faruwa ko sai kun sarƙe mana Numfashi da zullumi?

Gwaggo ta faɗa tana ɗan karisowa in da muke tsaye.

"Ke Sadiya bar kuka. Taho mu je abin da ke faruwa.'

Ta faɗa tana riko ni, ina jin ta taba ni sai na faɗa jikinta na ƙara fashewa da kuka ina faɗin" Gwaggo Yallaɓai ne ya ce wai na bar masa gidan sa"

"Innalillahi wa'inna ilaihirraju"un.

Gwaggo ta yi salati.

"La'ilahaillalahu."

Alhajinmu ya karɓa.

"Muhamadan rasulillahi."

Gwaggo ta ƙarishe cikin wani yanayi

"Da kika yi masa me zai kore ki da girman ki da kuma daren nan?

Gwaggo ta tambaya daga jin muryan ta za ka san hankalinta ya tashi.

"Ban yi masa komai Gwaggo a kan matar shi ne ya ke son ya wulaƙanta ni."
.

Na fada ina shessheƙa. Gwaggo ta na bubbuga bayana alamun lallashi ta ce"Kai jama'a. Me ya sa Yusuf zai haka? Da girmansa?
To ita Marwanatu ba  na gan ku tare a wannan daren?

"Suna ta zo. Gimbiya ce ta haihu yau suna suka taho daga Rano ɗazu da rana"

Ina jin Gwaggo ta sauke numfashi kafin ta ce" To da sauƙi ai na ɗauka itama wata matsalar ce."

"Umma ce ta ce na taho mu tafi. Mun baro Baby da Yumna na ta kuka."

Marwa ta faɗa kafin Gwaggo ta yi magana Alhajinmu ya ɗan murmusa yana so ya yi magana sai kuma ya yi shuru.

"Alhaji ya ka murmusa? Ka na ji surukin naka da ɗazun nan ka gama yabon sa ya baka kunya ya koro maka y'a kusan shekaru ashirin da aure cikin dare."

"Ho Mata kenan ku dai ba a rabaku da son kai. Ni daman na san ai ta tsuniyar gizo ai ba ta wuce ta ƙoƙi ko?

"Ban ga ne ba Alhaji. Kuka fa Sadiya ke yi?

"Duk na ji. Kamata ku shiga ciki bari na je masallaci na dawo sai mu zauna mu yi magana. Allah ya rufa mana asiri.".

Ta amsa da amin ya fice ni kuma Gwaggo ta rike ni zuwa falon Alhaji Marwa ta bi bayan mu. Zama muka yi a saman kujera mai zaman mutum biyu ni da Gwaggo.

"Wai shi Yusuf din ya ce ki bar masa gidan shi!

"Wallahi shi ya ce Gwaggo "

Na faɗa ina jan hanci irin na masu kuka.

"Me kika yi masa da zafi haka? Gaskiya ya ba ni mamaki ai ko mai kika yi masa bai kamata ya yi miki haka ba "

Ina goge hanci ina zayyana ma Gwaggo abin da ya faru ina hawaye ina faɗin" Abin takaici Gwaggo wai ni Yallabai ke kallona ya ce ina da mugun nufi a kan matarsa saboda tana haihuwan yaya maza ni kuma mata shine ina bakin kishi da ita na kasa hakuri na saka an dakar masa mata shi ne ya zo yana ta faɗa mini mganganu son ran shi daga ƙarshe ya ce na bar masa gidan shi"

Gwaggo ta yi salati ta dire kafin ta ce"oH ni Maimuna. Ashe yarinyar makira ce? Ina ganinta shuru shuru kamar ta Allah. Su suka shirya masa komai, shi kuma laifin sa ɗaya rashin bincike sannan na ga ɓakin sa da ya iya buɗe baki ya ce ki bar masa gida Haba. Ai ba ki cancanci wannan tozarcin ba.'

Uhm"

Kawai na iya cewa saboda zuciyata suya take yi. In ina tuna abin da ya faru.

"Umma ba cewa fa ya yi ki tafi ba. Ke kika ce mai za ki tafi ya ce shi ba zai hana ki ba "

Marwa na ƙura ma ido cikin takaicinta da bakin ciki. Na ma kasa mgana saboda na rasa abin da zan ce mata. Ina tunanin ba ni ce ƙanwar uwarta ba Yusuf Muhammad Inuwa ne.

"Af to me ya rage? Ai duk ɗaya. Mata ai mu haka Allah ya hallice mu, wata ƙila ta fadi haka ne ta gwada zurfin matsayinta shi kuma sai bai ba ta kunya ba, ya nuna mata iya na shi tattalin a kanta ya ce ta tafi ba zai hana ta ba. To ai shike nan bari Alhaji ya dawo sai ya ji shi ne da an tashi hira sai ya ce mijin Dubu  dabam ne ina ganin ƙimarsa. To ai yau ga ƙarshen ƙima nan ya kore masa ƴ'a gabanin mangariba da isha'a da girmanta da komai, bai yi miki haka kina da kuruciya ba sai da shekaru suka fara gangarawa."

Gwaggo sai faɗa take yi ni sai na ga ma ta fini ɗaukan zafi. Har a ƙasan raina ban ji daɗin da ma zo gida na buɗe cikina ba amma kuma ai shi ya ja. Da bai yi abin magana ba da ba a yi magana ba. Alwala muka yi ni da Marwa muka yi salla muna cikin sallar Alhajinmu ya dawo shi ya sa muna idarwa Gwaggo ta zo ta kira ni, da man a ɗakin Mama muka yi sallar.

falon Alhajinmu na koma yana zaune ga kwamukan abinci Gwaggo ta jera masa amma bai taɓa komai ba. Duk da ya nuna kamar bai damu ba amma na san ya damu ya kasa yin wani abu ba tare da ya ji damuwata ba. Allah sarki Alhajinmu ina son shi saboda in dai matsala ta tunkaro iylanshi shi baya samun natsuwa sai ya ga ya yi maganin matsalan nan. Dattijo ne mai juriya da jajircewa. Sai a lokacin na ji nadama da tunanin me ya sa na taho gida na ɗaga musu hankali? Da man ban zo ba, ssi wata zuciya ta ce gwara da kika zo a karon farko yau dai Yusuf zai fahimci ba da gidan shi kaɗai kika dogara ba.

"Dubu."

Alhaji ya kira ni kamar yadda ya saba. Ina mai zama gaban shi na tankwashe kafa na amsa masa.

"Na'am ina yini Alhajinmu."

"Lafiya lau. Sai kika baro mini mata can tana kuka?

Kaina na kasa na kasa mgana.

"Bai kamata laifin wani ya shafi wani ba Dubu. Rukayyatu nawa take da za ta fara karban hukuncin da ba na ta ba? Ba mama take sha ba har yanzu?

"E Alhajinmu."

"Kin ji ko? Me ya sa kika yi haka Dubu? Koda na sanki da fushi ai ban san ki da rashin tausayi ba ko?

"Ka yi hakuri Alhaji na yi kuskure."

"Kin yi kuskure babba. Domin kin ɗauki alhakin ran da bai ji ba, sannan bai gani ba, kar ki ƙara irin haka komai zai faru kar ki yi hukunci a in da bai dace ba. Ina ruwanta? Ta sam ne babanta ya yi miki? To ko domin wata rana ki yi aikin hankali kin ji ko?

"Na ji. In sha Allahu ba za a sake ba."

Na faɗa ina wasa da gefen hijabina.

"Yauwa. In kin baro ita Mai sunan Gwaggon ta ku ita babba ce. Amma Rukayyatu kin ɗauki haƙƙin ta."

Ni dai na yi shuru, saboda sai a yanzu da Alhaji ya sake jadadda mini sannan na sake fahintar ban kyauta ba. Ina jin nonuwana suna cika na san tana can tana rigima.

"Allah ya kyauta na gaba."

Na amsa da Amin shuru na wani lokaci kafin Alhajinmu ya sske kiran sunana.

"Halima."

Tun da na ji haka na san mganar mai girma ce.

"Na'am"

"Me ya haɗa ki da Yusufa har ya ce ki taho gida a daran nan?

Nan da nan na gyara zama cikin natsuwa na warware ma Alhajinmu komai tun daga farko na haihuwan da ta yi ban je barka da wuri da abin da ya faru yau. Har mganganun da muka yaba ma juna na fada masa, ni fa duk a tunanina Alhajinmu zai goya mini baya in ji ɗibar albarkar da Yallabai ya yi mini saboda matarsa.

"An faɗa masa ƙarya da gaskiya daga can Alhajinmu kawai yana zuwa gida ba bincike bai ji ta bakina ba kawai ya fara mini masifa da faɗa kamar zai dage ni."

Na ƙarishe faɗa ina goge ƙwalla da gefen hijabina. Domin ina mai da yadda aka yi hawaye suka kece mini.

Alhajinmu ya yi shuru ni na ma ɗauka ko wani abu

33 / 55