ɗayan kuma ya ce" Wannan na ku ne ku da iyayen ku. Wannan kuma na My Sady ne."
Sai Jidda da Baby suka saka dariya.
Gimbiya ta ce" Son kai dai kake nuna mana kamar yadda itama ta nuna mana yau."
"E ɗin an nuna muku son kai ɗin."
Ya faɗa yana zama a gefen Rabi'atu da take zaune a ƙasa tana cin tuwo Afiya na miƙa hannu sai ya ce A kawo masa ita Yumna ta mike ta ɗaukota.
"Yauwa my super women ɗina."
Haka yake kiran Yumma a cewarsa tana da karfi.
Sannu da zuwa muka yi masa gabaɗaya ya amsa yana kallon mu ɗaya bayan ɗaya har yaran yadda suka ba je a falo suna cin tuwo.
"waye ya yo gayyar a cinye mini abinci."
Ina dariya na ce masa Rabi'atu na bashi labarin kwaɗayi ya sa ta jiyo kamshi ta bar fushin ta shigo.
"Ai da man cikin nan nata akwai son daɗi"
"Abba wallahi tuwon ya yi daɗi ka ce Umma ta karo mana "
In ji Rabi'atu
"Ni kuma sai ma ci me?
"Ka sha tea mana."
"Hararanta ya yi kafin ya ce" Ke ki sha tea ɗin mana. Na ki wayau wanda kuka ci sabil ne"
Na ce ƙwarai, dole suka haƙura aka ba je kajin da tsiren da Yallaɓai ya siyo suna ci suna hira, Yallaɓai ya miƙa ma Gimbiya ɗiyar ta ya miƙe yana faɗin.
" Sadiya ta mu je kin ji."
Ya fada har yana miƙo mini hannu na kama yaran nan suka saka mana ihu.
"Kuna fita za mu cinye tuwon nan"
In ji Gimbiya Yallaɓai na jin haka ya ce" To koma ki haɗo komai ki same ni a can"
Ya wuce ya fita bayan ya ba ni ledan hannun shi. Na koma kitchen na hada ƙomai a saman ƙaton faranti na saka lulluɓi na fito ina faɗin" Jama'a mu kwana lafiya."
"Mu kwana lafiya Uwargidan Yallaɓai."
In ji Gimbiya Rabi'atu dai ba ta yi mgana ba ita har gobe ba ta iya boye motsuwar kishinta.
"Umma sai da safe"
In ji Jidda na amsa ina faɗin su rufe kofa in za su kwanta.
Yumna ta biyo ni tana faɗin" Umma nima za ni wajen Abba"
Yarinyar nan shegen wayau ne da ita haka nan na rasa yadda zan yi da ita da na ce Jidda ta kamata ma kuka ta saka haka nan na ta sa ta gaba muka tafi. Ko da na je har Yallaɓai ya shiga wanka sai na kunna mata cartoon ni kuma na shirya mana dining sai da na kira wayar Jidda na ce su kawo min kunin aya da na haɗa yana nan a fridge da Baby ta kawo ne na samu na yi ma Yunma wayau na ce ta ma yar mini da mayafina ganina nan zuwa.
Sai da na gama shirya komai a falo sannan na shiga ciki na samu Yallaɓai ya fito wanka yana ɗaure da babban towel a ƙugunsa.
"Sadiya ta."
"Yallabai na."
Muka kalli juna muna mirmishi.
Ni na taya shi ya shafa mai ya saka jallabiya baka muka fita falo, a kasan cafet ya ce mu zauna nan muka ba je muna cin tuwo muna tuna rayuwar amarcin mu muna dariya.
Ya shayar da ni kunun aya nima na shayar da shi.
Ya zaunar da ni a kan cinyarsa ya ba ni kaza a baki nima na ba shi, bayan mun gama na kwashe komai na kai kitchen na gyara falon muka je tiolet muka wanke baki.
Na cire dankwali na bar masa gashin tunda yana so shima daga shi sai gajeren wando ya cire jallabiyan muka kashe hasken falon sai na tibi muka makale juna muna kallo muna kuma sumbatar juna.
"Sadiya ta."
"Uhm"
Na amsa ina kwance a kirjinsa.
"Na gode'
"Na gode."
"Godiyar ta mene ne?
"Da kika zama ni na zama ke. Da kika yi ta hakuri da duk wani gwagwamaya har tarihin mu ya kawo yau. Na gode da zamowarki TUKEN GIDANA. na tabbata ban yi turken banza ba. Kin kasance mai karfon da duk matar da na auro a kan togacin ki za ta kafa na ta igiyan. Na gode a jiya da shekaranjiya na gode a yau na kuma gode miki a gobe."
"Kai ne turkena Yallaɓai na."
Na amsa masa ina mirmishi sai ya ɗago ni ya fara sumbatata nima sai na tallabe shi.
Na tsawon mintina muka saki juna muna ma yar da numfashi.
"Sadiya ta "
"Uhm"
"Har yanzu dai ruwa na mganin dauda."
Ina mirmishi na ce" Yana yi sosai ma."
Na faɗa ina shafa kirjinsa zuwa kasan maran shi hannuna ya riƙe jikinsa na rawa.
"Sadiya. Ta"
Uhm"
"Yau zan shanye ki ne fa."
"Nima zan shanye ka."
Na faɗa cikin wani yanayi, a wannan daran a saman wannan kujeran Yallaɓai ya biga half time ɗin shi sannan muka ranka ya ciki ya buga roud ɗin shi da kyau. Ba mu muka yi barci ba sai biyun dare da asuba bayan ya dawo sai da ya ƙara saka muka yi facal-facal da ruwa. Ya kwanta barcin safe na fita na je na duba yara da kwana sai na tsaya na yi masa abin karyawa na yi wanka har Sadi direba ya tafi da yara makaranta Yallaɓai saboda gajiya bai fito ba.
Na koma shashen shi domin na tashe shi ina shiga bedroom na ga baya nan na ɗauka ma yana tiolet ne ina jiyowa na gan shi a bayan ƙofa sai ya fara takowa gabana yana yi mini mirmishi.
"Yallaɓai ka sake biya mini Umra ne?
Na faɗa ina mirmishi har hakorin makkan da na sanya yana bayyana.
"Assalamu alaikun farincikina!
gani na zo gun mai haskaka raina !"
Na kwashe da dariya ganin Yallaɓai ya dage yana yi mini waƙa.
"Yallaɓai yau ka zama romie ne?
'"kar ki manta ke ce kaɗai abin faharina."
Ya faɗa yana mai ɗaga hannuna yana juyi da ni ina ta dariya dariyan farinciki da muradi mai girma.
"SADIYA KAR KI SAKE DA NI KO WATA RANA,...!"
Ya faɗa yana mai sumbatar goshina.
Shigewa jikinsa na yi ina mai ƙamƙame shi.
"Ba zan bar ka ba ko wata rana Yallaɓai ko mutuwa ce ta bari sai mun tsufa sai ta ɗauke mu a tare."
"in sha Allahu."
"Ina son ki Halimatuna."
"Ina son ka Yusuf ɗina."
Sai na dago kaina na ɗage kafafuwana na tallaɓo kan shi na fara sumbatar shi, shi kuma sai ya riƙe keyata ya juyar da ni ya haɗa ni da jikin ƙofa ya fara mayar mini da martanin gayyatata da zafi zafi.
"ALHAMDULILLAH*
_ALHAMDULILLAH KARSHEN LABARIN TURKEN GIDA, ABIN DA NA RUBUTA NA DAIDAI ALLAH YA BA NI LADAN TARE DA KU GABAƊAYA. KUSKUREN CIKI ALLAH YA YAFE MINI, KU YI HAƘURI WATAƘILA, NA KARKACE TA WANI BANGAREN. KUN SAN ƊAN ADAM AJIZI NE, TARA NA KE BAN CIKA GOMA BA, NA GODE BISA JIMARIN BIBIYATA, NA GODE BI SA MARTABAWANKU, NA GODE BISA GIRMAMAWANKU, NA GODE BISA YARDA DA AMINCEWARKU GA RUBUTUNA, NA GODE UBANGIJI YA YI MA RAYUWARKU ALBARKA ALLAH YA BIYA KU, YA KUMA HAƊA MU A ALJANNA. NA GODE SOSAI._
*SAI MUN SAKE HAƊUWA A WANI SABON LABARIN IN RAN MU YA KAI. NA GODE*
*Janafty*
20 March 2025.
SUN/09/2025.