su ɗibar ma yaran su da mazajen su a yi komai cikin tsari. Na bangaren mu ragamar na hannun Amina na bangaren su Yallaɓai kuma Munnira ce ni dai na gama jan kunnenta kar ta yi faɗa da kowa a yi suna a tashi lafiya. Ta ce mini ba za ta yi ba amma ni na san sai ta yi mgana ni da na san halin Munnira.
Karfe biyu na rana mai kwalliya ta iso kusan ma lokaci ɗaya suka iso tare da Khaleesat wai mota ta lalace musu a hanya. Itama ta kawo mini turamin atamfa da riga tare da kayan sanyi na karɓa ina ta godiya. Swiss lece na saka cikin wanda na siya na ɗinka sannan a ka tsantsara min kyakyawan kwalliya wanda tun kafin a gama kowa ya shigo sai ya yi santin kyan da na yi kyau ma sai da a ka gama ta yi mini wani irin ɗauri mai kyau da na duba madubi na ɗauka jidda ce tsabar yadda na dawo kamar budurwa. Na yi amfani da takalmi baki mai tudu kaɗan da mayafi baƙi da jaka, Na saka ɗan kunnaye na masu kyau da tsada, ba ni da zinare ko na zobe sai da na yi hawayen takaici na tuna wanda a ka siya mini da Sadaki na, Yallaɓai ya saka na siyar da shi muka cinye kuɗin, da cewa in ya samu zai siya mini wani har yau lokacin bai yi ba ina jin ma ya manta da abin da ya faru. Ni kaina na san na yi wani irin kyau duk kuma in da na gifta Ƙamshi ke tashi, oil ne mai bala'in, wajen wata mai siyar da turaruka a faceebook na san ta Maryam kitty. Tun da na fara siyan turarenta ban taɓa saka shi ba a yi santin kamshin ba Yallaɓai ya daɗe da sanar da ni yana son ƙamshina. Har na ce in na samu kuɗi zan ce ta haɗa masa na maza daga baya da ya ɓata mini rai na fasa.
Yumna ma an sauya mata kaya ta yi kyau daman ta sha kunshi a hannu da kafa da Ya Murja ta sake kun sa mata yau da safe yau ma mun so komawa asibiti amma sai Yallaɓai ya ce mu bari gobe da safe kar mu je a yi mata allura ta dawo da rigima amma dai tun kwana uku da haihuwanta wanzami ya zo ya cire mata belu sannan ya yi mata askin gashin kanta kamar yadda ya zo a cikin sunna. Zuwa biyu da rabi shagalin suna ya kamkama, baki suna ta zuwa ban yi tunanin zan tara mutane haka ba ni da ban damu da zuwa suna ba, duk sun saka ankon su sai suka yi kyau sosai. Maijidda Bala daman ta zo garin lokacin da na haihu da ya ke mijinta ya samu aiki a Dutse sun koma can da zama ita ce ta yo mini gayyar su Samira da Hauwa jamilu sai da na yi ƙwalla da suka kawo min pampers da mayukan jiki da hoda na jarirai sai safa da huluna suka ce kuɗin da a ka haɗa mini ne suka siya mini da shi, duk da ina ba da wa in na gani amma ba kowanne na ke yi ba, amma dai tabbas na ji daɗi na kuma martaba wannan karan da suka yi mini, sun kuma saka ankon su gwanin ban sha'awa.
Muna cikin bedroom ɗina tare da su muna hiran yaushe gamo. A nan Rahila ta kawo musu abinci sinasir da waina sai alale da ruwa da drinks can cikin gida kuma su Munnira na ta ji da baƙi.
Suwaiba da Jamila sun zo mini suna da wuri amma ko Gimbiya sai wajen uku na rana ta zo tare da Halima da Naja. Mimisco daman ta ce mini tana Abuja amma yaranta ƙananun suna nan, Anty Maimuna ba ta zo ba sai can wajen la'asar suka zo ita da Anty Bahijja. Su Nasara da suke kusa duk sun zo mini suna kuma an ba su abinci kamar na kowa ba nuna bambamci ko da suka zo na sauya kaya na saka anko da suka shigo suka ganni sai da mamakinsu ya nuna tun ballantana da suka ga gefen gado na cike da kayan arziƙin da a ke kawo mini. Gimbiya ta ta ba ni saƙo a leda Anty Bahijja ma ta ba ni leda Babba cike ta ce na su ne gabaɗaya daman haka suke yi bai ɗaya suke mini hidima in har na haihu. Naja ce kawai ta ɗauki Yunma amma bayan ita haka suka fita ba su ɗauke ta ba sun fita fuska ba daɗi domin ba haka suka so su ganni ba. Ga shi sun tarar da ɗaki cike da mutane su da ba su yi anko ba sai suka ga su ne ma dabam a wajen domin kowa ya yi ban da su.
Ba abin da zan ce ma mutane sai godiya domin sun yi mini karam kaya sai da na koma jefa su a ƙasa saboda gadon nawa ya cika kowa ba ya zuwa hannu rabbana in ba a bani saƙo a leda ba za a ba ni kuɗi hatta Ya Abubakar da Ya Muntari sun tura mini kuɗi sannan matan su ma sun zo sun kawo mini turame, sai da a ka yi sallar la'asar sannan mai hoto ya zo a haraban gidan shi da yaran shi suka yi decration na ɗaukan hoton. Mamaki kawai na ke ba ma su Anty Bahijja sun kasa magana na fito da tawagata mun sha hotuna zafafa na shiga na fita da kaya sama da kala biyar ni da Yumna, na kuma gayyaci su Anty Bahijja zuwa hoton sun shiga amma a cunkushe Gimbiya ma mun yi ni da ita sannan mun yi da yara. Muna cikin hoton ne sai ga ƴa'ƴan su Anty Bahijja da na Anty Maimuna waɗanda ke gida wasu sun yi aure wasu kuma suna makaranta. Ana gamawa da hoto suka saka kiɗa a speaker suka yi connecting da waya daman Munnira na da home thearter ita ta zo da su daga gida saboda ta ce chasu za su yi ni dai na sulale na koma cikin gida na kira Musbahu na tambaye shi Yallabai ya ce yana office tare da Kawu sai na ce ya zo gida ya karban musu abinci ba daɗewa sai ga shi ya zo na saka Mubeena ta je ta kai mishi har da na shi gabaɗaya.
Sun ta saka kiɗa su suna ruwa ni dai ban shiga ba, ina da ɗinki a ƙasana duk da ya kusa warkewa amma gwara na kiyaye amma da Munnira da Hauwa da Amina suna rawa na shiga na yi musu manni, Yumna ta na hannun Sameena itama ta shiga tana juyawa, har su Suwaiba duk sun shige daman su ai ba ruwan su ana cikin shagali ana ta farinciki suma Gimbiya da tawagarta suna wajen Anty Maimuna dai da Anty Bahijja sun yi mini sallama za su tafi na saka Munnira ta salleme su da ledan su ta ce mini sai da Anty Bahijja ta taɓe baki kafin ta ce"Lalle Tafida ya riƙe ma Sadiya kan macijin har da wani leda ne in mutum zai tafi? Duk abincin da aka ci bai isa ba? Ni dai a yadda ta faɗa mini ta ce ba ta tanka ba amma ni na san ƙarya take yi sai ta ba ta amsa. Sun tafi sun bar su Gimbiya da yaran su ina ga sai daga baya suma za su tafi.
Ana cikin shan wakar ado gwanja na kujeran tsarkar gida, Munnira ta sauya zuwa kirarin uwargida. Kirari ne da wani mawaƙi ya yi ga uwargida je, kuma tabbas kirarin ya yi sosai ni dai ina ta dariya da farinciki su ka ja ni cikin fili suna kuma bin kirarim suna nuna ni.
"Uwar gida ran gida in babu ke gida ya ɓaci. Haka zalika kowa ya zo ke ya tarar. Ke ce Amarya kuma ke ce uwargida, ke kika fara kafa gida saboda haka kowa ya zo ke ya tarar. Ke ɗin dai ce Uwargida haka za su gan ki kuma haka za su bar ki, hassadansu sai dai ta koma kansu. Allah Ya barki da Alhaji Tafida ya kuma kashe ki a ɗakin Tafida.
Takalmin kaza mutu ka raba."
Ina ta dariya saboda duk in da a ka ce Megida sai su sauya suna su kira sunan Yallaɓai. Jin daɗin kirarin ya saka na fiddo kuɗi a jaka ta sabbin yan ɗari bibbiyu da Khaleesat ta ba ni na riƙa manna musu. Daga baya ma Jamila kashe speaker ɗin ta yi ta ɗaga muryanta ta na rausayawa a gabana ta fara faɗin.
"Yau taken naki ne Uwargida a gidan Tafida. Uwar gida ran gida shalele a wajen Tafida. Kowa ya zo ke za ya tarar. A buga a bar ki sai ta Allah ta yi Uwargida sai gaban ki in da kike so. Wallahi ba gaba da gaba ba ko ta baya sai an shirya. Mun sani mun kuma tabbata da tsohuwar zuma ake mgani. In ka ji ana a wasa a wasa ba kaifi, ke ce wakiliyar Tafida kowa ya zo arziƙin ki ya ke ci, kin zama Tafida Tafida ya zama ke, maganarki a ke yi wa ke batun yan karere. A matsa a matsa ga Uwargida Sadiya a gidan Tafida ta hallara na ce a matsa a matsa."
Kaina na ji ya fashe,na ji na yi girim girim nan da nan na zazzage musu kuɗaɗen dake jakata sai shewa da ihu ya ta shi Amina da Munnira suka ɗora da guɗa. Har da Sameena a wajen ni ban ma lura da Gimbiya ba, ballantana na ji cewa ina yi da gayya ne sai bayan mun baro haraba zuwa cikin gida Hauwa ke tsegunta min ga Sameena can naja na yi mata faɗa wai ba ta kishin ƴar'uwanta ta biye mana a na yi ma yaruwanta habaici. Na riƙe haba cikin mamaki ina faɗin habaici kuma? Hauwa ta ce wallahi su haka suka ɗauka sai kawai na ce to Allah ya kyauta ni dai fata na mu rabu da kowa lafiya.
Ai ko na gan su da Sameena a can haraba bayan mangariba lokacin da na fito zan raka su Samira. Su ko salla ma ba su yi ba suna nan suna mganganu har da Halima a wajen, suna ganina suka yi shuru Sameena ko daga gani ranta ya gama ɓaci domin juyawa ta yi ta shige ciki a fusace kamar za ta tashi sama ni dai ban ce komai ba iyaka dai na ce musu ya kuka tsaya a nan? Sai Halima ta ce minI wai tafiya za su yi sai na ce su je su karbi saƙo a wajen Munnira sai ta amsa mini da to.
Ni na dawo cikin gida ban san me ya faru ba Sameena ɗayan ɗakin ta shige nima ban neme ta ba kawai muna cikin ɗaki ni da su Ya Aina suna ta ƙwashe min kayan da na samu nawa da na Yumna sai ga Khaleesat ta shigo tana faɗin wai ga Amina can suna hayaniya da ƙanwar mijina mamaki ya kamani ina tambayan kaina me ya haɗa su? Gabaɗayan mu muka fita can falon Yallaɓai muka iske Amina da Halima suna cacan baki ga su Gimbiya zaune Munnira ce me ke jan Amina da cewa ta yi shuru amma Halima da rashin kunya ina falon ta ce ma Amina.
"An zo an samu banza an tattare, za a kai gida. Saboda babu a house ɗin tsoho sannan a house ɗin miji ma babu."
"Ke Amina me ke faruwa! Me ya haɗa ki da ita?
Na faɗa ina shiga tsakiyar su saboda Amina ta ta so tana faɗin" Wallahi ƙarya kike yi. Kin san ko daga yanayin mu za ki san mun fi ƙarfin wannan abun da kike haƙilo a kan shi. Ni mijina ba mai kuɗi ba ne amma yana da rufin asiri kuma a gidan ubana mun fi ƙarfin abincin shekara. Kaf yayyena suna gidan mazajensu cikin rufin asirin mazan kuma akwai ma'aikacin banki da ma'aikacin bankin kuɗin duniya wato CVN kin ga ko tsakanin ni da ke sai a nemi wanda ke rigima kan tsire. Tsiren da dubu biyat ɗin ki ta gama biya miki bukata amma kin tsaya kina ta da jijiyan wuya. An daɗe ba a gamu ba miyau ya tsinke ƙwadayi ya tashi ba."
"Amina."
Haka na ke kiran sunanta amma ce min take yi" Ya Sadiya don Allah bar ni na ga karshen rashin kunyar yarinyar nan."
"Ni ba mara kunya ba ce. Sannan yarinya na bayan uwarta."
"Ke Halima."
Na daka matsa tsawa domin raina ya gama baci na ga tana shirin zagar mini uwa ne a gaba na kuma a gidana.
"Ni da gidan yayana ke ɗin banza?
"Ƙwarai kin fita iko da shi. Abin da a ka hana ki ma ai yayan na ki ya siya ko?
Naja ta shigar mata, Amina na ja ina mata faɗa.
"Me ya haɗa ki sa'in sa da ita?
"Ya Sadiya ni fa ban shiga harkan ta ba, ba kin ce na riƙe na bakin mu a hannuna ba, kawai ta na ganina da shi ta ce sai na ba ta leda ɗaya ni kuma sai na ga ai ga shi nan a hannunta Munnira ta ba ta, amma matar nan ta na ce sai na sake bata sai na ce ita ta samu wasu ba su samu ba ta bari a sallami waɗanda ba su samu shike nan ta fara zagina ta na gaya mini mangaganu duk yadda na kai ga haƙurina sai da ta ƙure ni."
"Nima na zo ina yi ma Haliman magana tana neman yi mini rashin kunya."
Munnira ta faɗa tana kallona sai na kaɗa kai ina faɗin" Amina dauka ki ba ta. Ko ba yayanta ya siya ba matar yayanta ce ta siya. Ko guda goma take so ki ba ta ai arziƙi ne a zo wajen ka har kana da abin da za ka ba da."
Ina faɗin haka sai Amina ta miƙa mata leda ukun da ke hannunta, su Ya Aina ma suka ce shikenan ko rigima ta ƙare.
Amma sai Halima ta ƙi karɓa sai ma falati da ta yi da ledan daga hannun Amina. Suka watse mini a tsakiyar falon na yi jagale ina kallon Halima na ɗauka iya nan za ta tsaya amma ba ta tsaya ba kamar ta na jirana.
"Ai ni nafi ƙarfin wannan abun. Ke dai ki kara akai gida."
"Kin fi ƙarfin shi kike rigima don an hana ki?
Munnira ta katse Halima. Ya Balki ta saka baki da cewa kowa ya yi hakuri ta duka ta na kwashe wanda Halima ta zubar Hauwa ta amshe ta. Amina za ta sake mgana Ya Aina ta tare ta ni ko daman ina ta danne zuciyata ne amma ba domin haka ba wallahi Halima ba ta isa ba. Gimbiyar ta su na zaune ta haɗa kafafu tana kaɗawa
"Na gode Halima. Tun da masalahan da na nema da ke baki yarda ba, ba na son tashin hankali zo ki fice ki bar mini gidana."
Na faɗa ina nuna mata hanya. Yadda ta kalle ni cikin mamaki ne ya sa na ƙara haɗa rai na.
"E ki fita ki bar mini gidana na gode da sunan da kika zo amma ni ba na son rigima"
"In fita fa ba kika ce?
"E ki fita na ce"
Na ina ƙara jadadda mata sai ta juya tana kallon su Naja suma da mamakina a fuskokinsu.
"Sadiya ƙyaleta kawai. Ai Aminar an shiga da ita ciki maganar ta ƙare."
In ji Ma'u sai na juya ina kallonta kafin na ce" Wallahi sai ta bar mini gida. Ta zo ta fita kawai."
Na faɗa cikin ɓacin rai, ina sake nuna mata hanyar fita.
"To ba zan fita ba."
Ta faɗa tana ƙara cijewa har da riƙe kugu.
"Ba zan fita ba, tun da nan ɗin ai ba gidan ki ba ne."
"Ok to ke gidan ki ne?
Na katsete cikin ina saita kaina domin wallahi in na harzuƙa zan iya jawo ta na yi mata bugun tsiya ba ruwana da aurenta ballanta ya'yan ta.
"Ba gidana ba ne amma gidan yayana ne na fi ki iko da shi. Kuma ai nan ɗin ba gidan ubanki ba ne"
A bazata na ji maganar duk lalacewata a idanuwan Halima ban ɗauka za ta iya zagin ubana ba.
"Ke Halima Sadiya kika zaga?
In ji Suwaiba da ta shigo falon yanzu daman na bar ta a ɗakina tana salla.
"Ita wace ce da ba za a zage ta ba. Na ga za ta nuna mini iko ne da gidan Yayana. Alhalin ba ta isa ba ita ɗin banza abanza k"
"Tas!
Sai ƙaran saukan mari suka ji na sharara ma Halima mari sai ga ta dafe da ƙuunci.
"Ko giwa ta mutu ba ta yi lalacewar da kiyashi zai ja ta ba. Ba ki isa ki zo har gidana ki ci kasuwa a kaina ba ƙaryan ki yarinya gwara tun wuri ki shiga hankalin ki, ki kuma kwashi jikinki ki fice mini a gida kafin raina ya ɓaci wallahi na yi miki dukan tsiya"
"Ni kika mara?
"In ba ki fice mini a gida ba duka zan yi miki wallahi."
Na faɗa ina nuna mata zan iya ya ɗin. Munnira ta kwashe da dariya Suwaiba da Jamila suka ce da kyau.
"Me ya sa kika mare ta a kan gaskiyan ta?
Naja ta miƙe tana challanging ɗina.
"Na mare ta ko za ki rama mata ne?
Na faɗa ina kallonta domin kaɗan na ke jira yanzu sai na saka a yi musu dukan tsiya su bar mini gida amma sai na ga Gimbiyar ba ta yi magana ba.
Kuma ba ta tsawarta ba.
"In nan gidan Yayanta ne ni kuma matar yayanta ne da gidan da shi kan shi yayan nata a ƙarƙashin ikona suke. Kuma ko shi bai isa ya zo yana mini wulaƙanci ba, ballanta ita ɗin banza. Duk wacce ba lafiya ya kawo ta ba, ta zo ta fice mini a gida kafin na haukace muku."
Kawai sai na fara masifa ina faɗin ni da gidana ba shege ko shegiyar da ta isa wallahi. Amma suka ƙi fita na ce zan yi ma Halima duka Ya Murja da su Rahila suka rike ni ashe tun fara faɗan Gimbiya ta kira Yallabai ana cikin haka sai ga su shi da Kawu ashe ma