Turken Gida Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   30 / 55

87K to 90K   out of 163.1K words

su ga wajen ita da Ya Hamza.

Mun yi waya da Jiddan itama can da gabda la'asar da su Ya Hamza suka je, ita ke faɗa mini Yallabai da Antynsu sun tafi gidan kawar Anty ina jin haka na ce gidan wannan ne da Yallaɓai ya yi maganarta ranar. Wani abu ya taso mini daga kasan zuciyata amma dai na daure. Daga baya da muka yi waya da Khaleesat ta ke faɗa mini sai da suka jira su Yallaɓai suka dawo a bakin ta na ke jin sun yi dare nan za su kwana amma yara kawai za su bar musu Yallabai da Amaryansa Hotel za su kama.

Ni fa daman na faɗa, ni na san da wata a ƙasa. Namiji uhm ni Yallaɓai zai yi ma haka? To ai shike nan, shi gogan sai dare ya kira ni ina ga bayan ya sun gama natsawa a hotel ɗin da suka kama sannan ya kirani yana daidaiciyar mgana.

"Sadiya mun yi dare za mu tsaya mu kwana zuwa da safe.'

"Allah ya nuna mana goben lafiya."

Na faɗa a yatsine, na yi kums shuru jin ya yi shuru har ina jiyo maganar Gimbiya amma ban san abin da ta ke faɗa ba.

Ina shirin kashe wayar ne na ji yana faɗin" Yara suna gidan Ya Hamza"
"Anty Khaleesat ta faɗa mini."
Na faɗa da gayya domin ya san na sani.

Jin na ji labarin a in da suke yasa bai ja mganar ba ya yi mini sallama saboda bariki har yana rage murya yana faɗin" Na yi kewar Sadiya ta "
Ashar ne kawai a bakina shi ya sa na yi shuru domin in na yi magana zan zage shi ne shi ya sa na yi kamar ban ji ba.

"Ina Yumna ta? I miss her."

"Ta yi barci."

Na faɗa a gajiye ban bari ya sake magana ba na yi saurin cewa" Zan kwanta sai da safe."
Ban jira cewarsa ba, na kashe wayata ina jan uban tsaki wayar na hannuna ina jin wani abu na taso mini. Ina tuna me na yi ma Yallaɓai da zai shirya mini wulakanci haka.

Shigowar sako daga  waya ta, ya sa na duba Yallaɓai ne.

"Ki yi haƙuri My Sady kin ji?
"I love you."

"Munafuki"

Na faɗa a fili kafin na dankwafar da wayar. Barcina ranar rabi da rabi ne, da na farka sai takaicin Yallaɓai ya taso mini da safe ina ganin kiran shi ba ƙi dagawa. Sai can da muka yi waya da Jidda ta ce sun ta so ba su haɗu ba saboda yau ta fara attending ɗin lactures na yi mata fatan alheri sannan muka yi sallama cike da kewa. Na san za su sauka a gidana shi ya sa ki girki ban yi ba suka dawo ga yunwa ba abinci sai fita Yallaɓai ya yi ya siyo abincin ai yadda ya ganni ina cika ina batsewa ya san in ya yi mini magana to zan fa fashe na fara masifa shi ya sa bakin sa alaikun ya fita ya je ya siyo kuma har ni ɗin ya siyo mawa na karba kuma na ci. Sai da yamma ya tara matarsa da yaran su ya mai da su gida da wuri ya dawo yana mini yar murya da labarin Jidda.
Kallo ni bai ishe ni ba, ya yi ya gama yaga ban tanka shi ba sai ya koma ban haƙuri.

"Kin ga ta ce mini za ta je bai kyautu na ce mataa a'a ba. Ni kuma ganin ba ki ce mini za ki je ba shi ya sa ban kawo da ke ba. Ki yi hakuri na san kina da kara kamar yadda kika ce ke da ita kun zama ɗaya."

Ni kallon shi kawai na ke yi, domin ni ba zan ɓata ma bakina akan shi ba tun da na san duk yaudara ce ta maza. Da na ga zai dame ni sai na ce masa ni ba haushi na ji ba amma da zai ƙyale ni da maganar nan da ya samu zaman lafiya. Shi ya sa sai ya yi shuru da mganar, ranar dai ba mu yi kwanan daɗi ba sai washegari na ɗan saki muka shirya amma na daɗe ina kallon Yallaɓai da wulaƙancin da ya yi mini amma tun da ya karyata kansa sai na ƙyale shi ɓan kara ta yar da mganar ba..
Na  ɗauki girman na yi hakuri na share, Jidda ana can an kwarari sati uku a makaranta ko da yaushe ina kiran ta na ji halin da take ciki. Yallabai ma ko da yaushe satin ma ya shiga Kaduna sai da ya biya ya ganta. Mu dai ta bar mana kewa koda yaushe Baby zencenta kenan Ya Jidda, ni kaina ina kewarta da sanyin halinta gida ya rage daga ni sai Baby sai Yumna.

*****

Cikin Gimbiya ya shiga watan haihuwan shi a bakin Yallaɓai na ji, hankalin shi duk ba a kwance yake ba, ni dai in yana magana ina yi masa fatan Allah ya sa ta sauka lafiya.
EDD dinta ma bai cika domin karshen watan march ya ce mini za ta haihu amma a ba ta kai ba ranar wata laraba yana gidana da safe ta kira shi ba ta da lafiya ya fita. Tun da ya fita bai dawo ba kuma bai kirani ba sai ni ce can na kira shi , a lokacin ya ke faɗamini suna asibiti haihuwa ce amma har lokacin ba ta haihu ba.

"Aikin za a sake yi mata?

"A'a sun ce a dakata a gani za ta iya haihuwa da kanta."

Fatan sauka lafiya na yi masa na kashe wayata. Da a baya ne tsab zan shirya mu je, ni kan ai Gimbiya ta gama yi mini hankali ban ko a raina zan iya zuwa ba. Har dare da Yallaɓai ya dawo ba ta haihu ba, haka muka kwana da shi bai yi barci ba ni dai barcina na sha to ina ruwana, ai ni na gama hana kaina zaman lafiya a kan Gimbiya. Washegari tun safe ya tafi asibitin har yana jirana ko zan je na duba ta na ce ya je zan yi ma Hauwa ko Munnira waya mu je tare nan ko ba zuwa zan yi ba kuma ban kira kowa ba. Ba ta haihu ba sai bayan la'asar kafin ya kirani a status ɗin Anty Bahijja namiji Gimbiya ta sake haifa.

Anty Bahijjan ma a ƙasan hoton ta rubutu mai farar haihuwa ta sake yo wata farar ƙal ma kuwa. Na yi taging na yi Allah ya raya domin ni ba na baƙin ciki.
Sai daga baya angon karnin ya kirani ya faɗa mini ta haihu da kanta. Amma za su riƙe ta zuwa gobe ta zubar da jini sosai."

"Ayya. Allah ya raya ya kuma ba ta lafiya"

Ya amsa da Amin Amin.

"Kin fito ne?

Sai da ya yi magana na tuna da karyan da na yi masa.
Da sauri na ce" Ban fito ba. Na kira su Hauwa sun ce mu bari gobe da safe kawai."
Bai ce komai ba ya ce Allah ya kaimu. Ni ban kira su Hauwa da na yi ƙarya da su ba, washegari da safe da ya bar gidana asibitin ya fara biyawa sai ya iske Hauwa ni ina na sani ba sai da Hauwa ta kirani tana cewa.

"Sadiya me kika faɗa ma Tafida? Mun haɗu a asibiti yana ce mini ya na taho na bar ki alhalin kin ce masa tare zamu zo.'

"To sai kika ce masa me?

"Na kasa mgana. To ni me zan ce?

Na ciji yatsa kafin na ce" Kash! Kin kwafsa mini. Nan na ba ta labarin abin da ya faru.
"Ni fa ban yi niyyar zuwa ba ne"
"Ki tura mata Aniyarta ki zo ko saboda Yallaɓan."
"To bari dai mu gani. Zan je na yi barka amma ba zuwan da na saba yi a da ba."
Da muka gama waya da Hauwa na yi niyyar na je amma sai na kama ciwon ciki sai zawo, zan fita ne ina zawo na yi zama na a gida da daddare da Yallabai ya dawo sai da ya ce mini Hauwa ta je asibiti yau

"E. Ni na ce ta tafi kawai. Ban ji dadi cikina ke ta ciwo sai kuma na fara gudawa."

"Sannu ya bari ko sai mun je asibiti?

Ya faɗa da kulawa sai na ce ya yi sauki, ni bai nuna mini komai ba shi ya sa nima ban damu ba.
Ban kuma samu zuwa ba sai washegari da yamma bayan an sallamo Gimbiyar da safe, Munnira na kira a waya na biya gida na ɗauke ta.
Sanda muka je yan Rano sun zo Mota guda su Naja da Anty Bahijja suna gidan ana ta shewa Anty Bahijja da ba ta gani ta ƙyale sai da ta ce mana.

"Jiya ɗayar ta ku ta zo ku sai yau ake ganin ku?

Wai Hauwa ce ɗayar mu. Munnira ce ta tsaya mata mgana ni gaisheta kawai na yi na wuce ciki wajen  Gimbiya. Mun gaisa da yan uwanta na Rano sannan na karisa gefen gado na zauna muka gaisa na ɗauki Jaririn sak Khalipa yana jariri, na yi masa addu'a na bata shi ba wani jima ba muka tafi, daga nan na mai da Munnira gida da motata na koma gida ban faɗa ma kowa haihuwan Gimbiya hatta su Ya Aina Jidda ta kira ni tana cewa Abban su ya kirata yana murna yana faɗa mata sun yi ƙani na ce ai fa. Ta ce har hotuna ya tura mata. To ba abin mamaki ba ne tun da farar haihuwa ce aka sake yi masa.

Tun da na je barka ban ƙara komawa ba. Ga mamakina ana jibi suna Yallaɓai da zai fita sai ya ce mini na shirya na je na duba mai jego.

"Na je ai na duba ta."

"Na sani. Ya kamata ki sake komawa kafin suna."

Kamar zan yi magana sai ban yi ba, na ce to yana fita ko na ce ba in da zan je. Ranar yini na yi barci ma da ya dawo bai tambayeni amma na san ai ya fara biyawa ta gidan ta. Tun da Baaba Asma'u ta zo wacce ta zauna mata da haihuwan Anwar shi ya sa yake kwana a gidana. Ni ce da kaina na faɗa masa ban je ba ba na jin daɗi.

Na ga ya kalle ni amma ganin bai sauya fuska ba ya san ban damu ba.

"Allah ya sauwaƙe."

Na amsa masa da Amin Amin

Kuma ko washegari ban je ba na yi zamana a gida. Munnira dai da Hauwa sun leka aikin suna ni dai sun kirani na ce musu ba in da zan je.
Ranar suna na yi niyyar lekawa shima ba da safe ba. Danan na cire mata atamfa ɗaya da pampers sai mayukan yara cikin saura na Yumna na saka a leda na ce in na leka goben zan kai mata.




*Janafty**TKGB3N014*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX


Assalamu Alaikum Fanmily, mun fara saro muku kayan Kitchen ko wani nau'i, duk abin da kuke bukata na gyaran Kitchen ɗin Amarya da uwargida duk za ku same su a JANAFTY KITCHEN ITEMS, kayan mu masu kyau ne da inganci sannan za ku same su akan rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina a falin Nigerian nan. Domin karin bayani ku tuntuɓe mu ta waɗannan lambobin kamar haka.
09069067488.
+234 706 234 9732

Muna maraba da masu siya ɗaya ko sari🥰

A daran da Yallaɓai ya dawo yake faɗa mini sunan yaro Muhammad. Na ce Allah ya raya mana Muhammad cikin addinin islama ya ce Amin Amin. Tare muka kwana cikin farinciki, da wuri ya fita saboda ya ce akwai mutanen da ke jiran shi a can office amma ya sha wankan shi ya ci gayu cikin shadda dark blue amma ba mai babban riga ba. Sai ya fito a angon ƙarninsa ina zolayansa kafin ya fita.

Bayan na dawo raka shi na yi ma Yumna wanka na goya ta na fara ayyuka Baby daman ita ta fara fita kafin Yallaɓai. Jiya da daddare na ji ta fara faɗin yau sunan Anty Gimbiya ba za ta je makaranta ba tun kafin Yallaɓai ya ji labari ya ɗaure mata kugu na ja mata kunne shi ya sa yau da safe ba ta yi rigiman ba za ta je ba. Shara na yi sannan na yi mopping gidan duk ya yi ƙura kwana biyu ban yi ba,  da man Jidda ne ta sangartani yanzu kuma tana makaranta Baby kuma ga makaranta ranar weekend kuma tana Tahfez in ma ta dawo wanke-wanke kawai ya isa ta fara tura baki tana faɗin ita duk ta gaji shi ya sa ban ma dogara da ita domin na fahinci ko a zamanin baya Baby ta fi ni lalaci.

Har ga Allah ban yi niyyar zuwa sunan da wuri ba. Wajen sha ɗaya na safe sai ga wayar Hauwa tana faɗa mini na shirya na ce mata ni fa ba yanzu zan je ba sai anjuma.

"Don Allah ki shirya mu taho gidan ki mu wuce tare."

"Ke da wa?

Na faɗa ina tura baki kamar tana ganina.

"Ni da Munnira mana. Mutanen Rano ma suna kan hanya yanzu muka gama waya da Ashen mu."

Cikin mamaki na ce" Ikon Allah suma duk za su taho ne?

"E tare da yan gidan su Gimbiyar ne. Hajiyarsu ta aika ma Mama shi ne ta ce ashe ta shirya ta bi su."

Ni dai sun takura mini ba ni da yadda zan yi sai na ce bari na shirya. Mun gama wayar da ita kenan Marwa ta kirani ashe har da ita a masu tahowa suna kuma a can gidan sunan za su sauka jin haka ya sa sai na ce bari na shirya kawai mu wuce tare da su Munnira. Ni daman yan gidanmu ban faɗan ma kowa ba Ma'u ce kawai ta sani kuma na san ba a bakina ta ji ba, ta yi mini maaganar ashe Gimbiya ta haihu na ce e ta yi fatan alheri ba ta zo ba kuma. Domin gabaɗaya alaqar su da Anty Bahijja ya ja baya. Ni yadda ma Ma'un take faɗa mini Amaryan Alhaji Mustpaha yanzu ita dangin shi suka rike ita da Hajiya Zainab ina jin har Anty Bahijjan ta yi ma Ma'u batulci. Na san ta sarai za ta aikata tun da ita daman ba ta da alkibla.

Kafin na shiga wanka na kira Hauwa a waya na ce na chanza shawara su biyo mun sai na ɗauke su a motata mu tafi tare sai ta ce mini to. Sai da na yi wanka na shirya cikin wani leshina sabo ne yana daga cikin kayan da na samu da sunan Yumna ɗinkin bubu doguwar riga. Leshin mai kalan maroon ne sai na yi amfani da mayafi kalan shi takalmi ma da jaka ina da maroon da su na yi amfani. Yumna kuma na yi mata gayu cikin kaya yan kanti jajaye harta takalmin kafanta da safa ja ne, haka hulan da ke kanta na gyara mata gashin kanta. Ta biyo a sumar kai amma Yallaɓai ba ya bari a yi mata kitso sau ɗaya Maman Nana da ta zo yi mana kitso ni da Baby  na ɗan ce ta yi mata kalaba aka sanya mata band kitson ya yi kyau amma ta yi ta kuka saboda ba ta saba ba.

A daran Yallaɓai da ya dawo ya gani ya ce sai na kwace mata wai an ci zalin yarinya don an ga ba ta mgana tun ballanta da take ta kuka shi a tafau zafin kan ne ya saka ta kuka tun kuma daga ranar ya ce ba za a ƙara mata kitso ba sai ta girma an yaye ko sai kanta ya yi ƙwari. Sanin halin Yallaɓai da naci wani lokacin in har aka sake kuma ya gani ni ce zan sha mgana sai kawai na ƙyaleta ban ƙara yi mata ba, amma kowa ya ganta sai ya ce ga ta da gashi amma ba a yi mata kitso sai na ce babanta ne ba ya so. Daga karshe ma sai na sissiya mata huluna kananun size kamar nata, na ke saka mata in zamu fita yau ma kalan ja mai maroon, na saka mata na rufe mata kan ta da shi, sannan na je ɗakin su Baby na ɗauko mata kaya a cikin dirowanta. Shadda na ɗauko mata doguwar riga da ƙaramin mayafi. Hauwa na tsaya ina ta jira sai wajen azahar ta shigo gidana shi ya sa sai da muka tsaya a gida muka yi salla sannan muka fito na rufe gida na tuƙa mu a mota ta, sai da muka tsaya a kan hanya na sha mai da safe Yallaɓai ya saka mini 5k ya ce na saka mai a mota, wani lokacin ma Adnan zai turo ya ɗau motar ya je ya saka mini wata rana ma da kan shi zai tura ya je ya ciko mini da tankina ya kawo mini. In ba lokaci kuma sai kawai ya ba ni kuɗin amma ba ko yaushe ba wani lokacin ina sakawa da kudina. Ai ya gama yi mini mai wuyar tun da ya siya mini motar. Na man da zan yi zirga-zirga na a cikin gari ba zai gagare ni ba.

  A gidan man kafin layi ya zo kanmu na kira wayar Salisu na sanar da shi in ya ɗauko Baby daga makaranta gidan Maman su Khalipa zai kawo ta. Sai ya ce mini to, a bakin shi na ke jin ashe su Khalipa ba su je makaranta yau ba. Hauwa na ke faɗa mawa ta yi dariya kafin ta ce" To da man ai ba za su je ba. Suna fa ake yi sunan ma na gidan su."

Ban ce komai ba, illa Yumna da nake kallo wacce ke hannun suna ta wasa da yaron Hauwa. Ita har ta yaye shi ma yana neman shekara uku ne ma. Munnira na tuna shi ya sa na kalli Hauwa kafin na ce" Wai kina ganin zuwan Hadiza ba zai hana Munnira zuwa gidan sunan nan ba kuwa?
Na faɗa ina kallon Hauwa. Domin na kira wayar Munnira da niyyar na ce mata mu haɗu a gidana sai mu wuce gabaɗaya. Sai ce mini ta yi mu tafi kawai ƙanwarta Hadiza ta zo daman mun yi ta ɗin da ita tace mini ta zo garin da yake a garin Minna take aure. A yau ɗin ne ta kai ma Munniran ziyara.

"To wa ya sani. Ina jin kamar fa Hadizan

30 / 55