Turken Gida Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   21 / 55

60K to 63K   out of 163.1K words

suna hanyar zuwa ne ta kira shi wai gani nan na kori Halima har ina marinta. Lokacin da suka shigo na gama harzuƙa yana tambayan ba'asi ni ban bi ta kan shi ba Suwaiba ce da su Munnira ke ma yar musu da zence.

"Wallahi sai Halima ta bar minI gida in kuma ba ta fita ba ni zan fita na bar mata gidan."

Na faɗa ina numfarfashi Kawu ne ke ba ni haƙuri har yana cewa" Gwara da kika mare ta. Kuma kina dai-dai da ki kore ta tun da, ba ta da kunya."
Yallabai da suka yi tunanin zai goyi bayan su sai ya kware musu faɗa ya yi mata kaca kaca ya kuma ce ta fita ta bar gidan tun da ba alheri ya kawo ta ba.

"Amma Uncle."

Naja ta tare shi za ta kare ma Halima.

"Rufe min baki kawun me? Me ya sa ba ki tsawarta mata ba?

Ta yi shuru ta kasa mgana Gimbiya ma tas ya yi mata ya ce ta iya kiran shi ta faɗa masa na mari Halima amma a gabanta Haliman na yi mini rashin kunya ba ta iya mata mgana ba.

"Ni miye nawa a ciki? Na saka baki sai a ce kishi ne. Ba ruwana kar ka sakani a ciki "

Ta faɗa tana wani tura baki ni saboda haushi ciki na koma ban san yadda suka ƙare ba amma na so wallahi na yi mata dukan tsiya. Kuma ta ƙara dawo mini gida ta gani sai ta raina kanta. Sameena ke faɗa mini daman suna jirana ne sunq ta zagina wai na yi albuzurranci da kuɗin Tafida na ce bakomai na isa ne. A nan ta ke faɗa mini yadda suka yi mata wai ta shige mini saboda munafunci ita kuma ta ce tana tare da ni tuntuni saboda Gimbiya ba za ta ja baya da ni ba.

Ranar raina ɓace na kwana da safe a hanyar mu ta zuwa asibiti ya ke sake ba ni haƙuri na ce bakomai. Mun je an duba ɗinkina suka ce ya kusa warkewa sannan an sake yi ma Yumna allura. Mun dawo gida na iske suna ta suyan ragunan da aka kawo su a yanke yau da safe. Daman na san magana za ta je ta dawo sai da Anty Bahijja ta kirani wai me Halima ta yi mini na mare ta? Na ce rashin kunya ta yi mini buɗe bakin ta sai ce mini ta yi ashe ba daɗi ni ba na yin rashin kunyar ne? Ni kuma na ce ni ban bi kowa gidan shi na yi masa rashin kunya ba itama gidana ta zo kuma ko yau ta dawo wallahi ta ƙara mini rashin kunya duka zan mata ba ma mari ba. Ai sai ta ce to kar na fasa mu ka kashe waya zukata na ƙuna.

Ranar yini na yi zuciyata ba daɗi da wuri suka gama suya suka ɗibar mini nawa. Sai na su na can Gwammaja. Na saka su Ya Aina suka ɗiba na su har da y'an can gandun albasa. Nima na ɗibar ma su Hauwa a ka raba da yaji kafin yamma gida ya watse har su Laila suna koma Ɗorayi za su kwana washegari su ɗau hanya. Ina ta musu godiya na su Samira Rahila na ba mawa na ce ta aika ma Maijidda za ta kai ma su Samira. An yi taron suna an ta shi lafiya gyaran gidan washegari Saude da Marwa da Mubeena suka gyara mini tun da sai ranar da Yamma Kawu ya zo ya ɗauke ta suka koma rano.

Tun da a ka yi suna a ka gama na mai da hankalina wajen renon Yumna. Ta tsiri rigiman dare ba ta barina na yi barci ɗan kumarin da na yi duk na fara sakewa. Ga shi Yallaɓai can gidan Gimbiya yake kwana nan ya gama cika mini baki shi bai amince ya koma can ba amma sai ga shi an gama taron suna gida ya watse amma bai dawo ba ni kuma ban yi masa magana ba daman na san can munafumcin ne irin na su na maza. Sai dai ya zo duba mu safe da yamma.
Daga ni sai yara suma suna zuwa makaranta sai yamma asabar da lahadi kuma Tahfez Jidda har ta kusa sauka izifinta hamsin da biyar Baby kuma ta na cikin izifinta na ashirin. Ni kaɗai a gida ga fama da aiki ga fama da Yumna wacce ta cika rigima ga tsotso mintina kaɗan ta fara rigiman nono shi ya sa ta zama wata burkuta da ita.

Muna da kwana goma sha biyar da haihuwa na ga Yallaɓai ya dawo kwana a gida na kamar zan yi masa magana sai dai ban yi ba. Kwana biyu tsakani kuma sai ya ɗauke kafa ya koma can ni sai na koma kawai na zura masa ido saboda na ga jeka ka dawon da ya ke yi, na kasa gane nufin sa.

Sai a tsakanin Munnira ta sake leko ni a bakinta nake jin rigima ce suka yi shi da Gimbiyar ta sa har sai da Nene ta shiga ciki. A kan dai maganar kuɗin da ta ce ya ara mata na shipping ɗin kayanta ya ce ba shi da kuɗi amma ni ya ba ni kuɗi na yi suna har ina kiran mai hoto. Ita ko abin ya tsaya mata a rai ta ce mini ranar ta na gidan a ka yi har da su Maman farko a shigar maganar shi kuma ya rantse ba shi ya ba ni kuɗin wasu abubuwan ba da kuɗina na yi, amma ba ta yarda ba ita a dole ya yi rashin adalci. Wato dalilin dawowan shi gidana kenan sannan kuma ya koma bayan sun shirya. Ni dai na ce ma Munnira Allah ya kyauta can su ƙarata.

Sai da ma muka yi maganar hotuna da Munnira sannan na tuna na tura ma mai hoto ragowan kuɗin sa ya turo mini hotuna. Washegari ko carbi na yi a status ɗina hotuna ne ba adadi na saka.
Na farko nawa da Yallaɓai na saka da yara wanda Amina ta ɗauke mu ranar suna da safe.
Na yi caption da cewa" Shekaru ashirin da albarka ƴaƴa uku. Alhamdulillah."
Sai na saka wanda muke mu uku ni da shi da Yumna. Shi ke riƙe da ita ni kuma sai na shafa sajen sa. A ƙasan hoton na saka sticker ɗaga hannu na za a saman kai sannan na ce" Jama'a na ba ni Yallaɓai na ne na ga ya fara furfura"
Ai ko na sha comments har Ya Hamza sai da ya yi mini mgana da cewa. Ke kina nufin ya dauwama a saurayin da kika aura ne? Sorry yarinya."

Maijidda Bala ta yi dariya ta ce" Sadiya rayuwar auranki da Yallaɓai a bar sha'awa ce Allah ya bar ku tare."
Na amsa mata da Amin ba ta san tarin ƙalubalen da na fuskanta ba ne. Ba su san ma an yi mini kishiya ba sai a sunan Yumna na faɗa musu suna ta mamaki ai ni yanzu na yi hankali na kama jama'a. Ni dai ban ɗora hoton Gimbiya ba amma ma tura mata wanda ta ke ciki haka ma su Anty Bahijjs. Yan gidanmu duk na tura musu sun ɗora mu. A gidan su Yallaɓai da ga Mimisco sai su Suwaiba su Munnira daman nawa ne, mazan kuma daman Musbahu da Adnan suka yi ta ɗora mu suna addu'a. Yallaɓai ma turamai na yi wajen guda hamsin sai turo mini emojin mamaki ya yi ni kuma na ce masa miye? Da alaman tambaya sai ce mini ya yi wai wa ya ba ni kuɗin waɗanan hotunan? Na ce tun da bai bai ba ina ruwan shi sai ya turamin na emojin baki da zip kuma ina tunanin bai buɗe hotunan ba, shi ya sa ko a status bai saka ba. Ban damu ba sanin halin Yallaɓai wani lokacin ba ya yin abin da a ke zaton shi da shi sai saɓanin haka

Har Shemau Ma'un ta kirani ta mini barka saboda ma yafe ma Ma'u shi ya sa itama na ji na yafe mata. Ta ce mini in ta shigo garin za ta shigo ta ga Baby na ce sai ta zo so. Kara an yi mini shi sosai kuma na gode ni ce na tara turamen atamfa kaɗan ne babu a hamsin bayan kayan jarirai da sabulai da sauran su da masu tura mini kuɗi. Da na nuna ma Yallaɓai sai da ya jinjina kai kafin ya ce wai ni da kaya sai nan da shekaru biyar na ce bai isa ba. Ya saka albarka yana dariya a ciki na nemi shawaran shi na ce zan ba ma Gwaggo ɗaya Nene ɗaya sabulai kuma na ba su Maman farko da su Inna Mariya ya ce duk yadda na yi dai-dai ne tun da kayana ne. Ban damu ba sanin halin shi, shi ya sa na yi gaban kaina na ware musu da niyyar in na yi arba'in in na je gaishe su na kai musu.

Mun shigo watan december ƙarshen shekara. Ina ta jego na ina kula da kaina gefe ɗaya bikin Alhaji Mustapha na ta ƙaratowa. Ma'u duk ta damu ni ce ma ƙarfin gwiwanta. Sai ma Allah ya sa a ka ɗaga bikin sai Jan ƙarshe.
27 ga watan december na yi arba'In a ranar da na yi arba'in Gwammaja na yini na kai ma su Nene saƙon su suna ta godiya tun da na je Yumna na tsakanin ɗakunan su Maman farko da Hajiya iya sai da zamu fita. Washegari kuma na yini a ɗorayi na kai ma Alhajinmu matarsa nan da nan ya ce shi kan ya saki jidda ya samu sabuwa Gwaggo na dariya ta ce da tsohuwar zuma dai a ke mgani. Ranar ma a wajen Alhajinmu ta yini kuma ikon Allah ba ta yi rigima ba, a jere na haɗa fitan na je gidajen su Ya Aina na je har can gandun albasa wajen su Inna Mariya. Na je gidan Munnira da Hauwa na yi musu yini da ban gajiya wajen kwana goma har Yallaɓai ya ce ba zan sake fita ba duk gari an gama gani na kullum sai na fita sannan na samu natsuwa a gida na fara gyara kaina.

Surayya dee ce mai kayan ɗa'a ta gyara ni da haɗin kazar sababi na masu jego. Daman kuma bayan haihuwata na dage da cin kayan marmari da ganye da kuma kifi domin ƙarin ni'ima. Sannan Amina ma ta aiko mini da Gumba na sha da madara Yallaɓai na ta rara gefe na hana shi sai da na ji na yi tsab sannan na gayyace shi. Ranar na sha sambatu amma na gane ba ni da wayau, domin Yallaɓai kaca kaca ya yi wajen ɓarnan ruwa sai da ya famshe kwanakinsa har yana haɗa wanka ma.



*Janafty**TKGB3J010*

Washegari ma bai bar ni na huta ba, ko falo bai bar ni na fita ba sai wajen sha ɗaya na safe su Jidda ma shi dai ya fita suka gan shi suka gaishe shi. Daman ba sa jira na yanzu sun girma komai na buƙatunsu, su suke yi ma kan su. Sai alokacin na samu damar yi ma Yumna wanka sannan nima na shiga wankan kuma na bar mishi Yunma kwance a gefen shi shi kuma yana duba abu a cikin laptop ɗin shi.

Ina fitowa ɗaure da Towel a ƙuguna na iske sa har ya gama abin da yake yi ya ture laptop ɗin gefe. Tambayarsa nake yi Yumna ta yi barci ne? Sai ya leƙata yana faɗin ta soma barci.

"Ai gwara ta yi barcin nan kowa ya huta."

Na faɗa ina mai zama saman stool ɗin madubin dake bedroom ɗin namu.
Ban san tahowar shi ba sai kawai jin sa na yi yana shafa min wuya a lokacin ne na ci karo da fuskarsa ta jikin madubin dake gabana.

"Me ya faru Yallaɓai?

Na faɗa ina mai kallon shi ta madubin, bai amsa ba sai ma sunkuyowa da ya yi ya na mai sumbatar wuyana. Tun da na ga haka na sha jikin jikina da sauri na ture shi ina faɗin" Na yi wanka fa Yallaɓai."
"Me ya sa kika yi wankan?
Mamaki ya sa sai da na ɗago ina kallon shi.
"E. Ai ban sallameki ba hajiya."
Ya faɗa har yana wani ƙara tsumewa irin shi fa da gaske yake yi.

"Yallaɓai tun daran jiya kake abu ɗaya. Yau da safe ma don Allah kai baka gajiya ne?

Na faɗa ina cigaba da shafa ma jikina man shafawar da na lakuto a hannuna.

"To ni ban gaji ba."

"Ba ka gaji ba?

"E"

Ya amsa mini har yana wani haɗe rai sai na kalle shi kafin na ce" To ai sai dai ka yi haƙuri zuwa anjuma ka ga na riga na yi wanka."
Amma Yallaɓai ya ce bai san wannan ba sai ma jikina da ya matso da ƙarfi ya ta da ni tsaye ya rumgumeni yana faɗin.
"Ke ce kin ƙara sugar. Wato ta bakin ki haihuwan Yumna na dabam ne."
Ya faɗa ya na shafa cikina, hannunsa na bige sai ya kai shi saman ƙirjina yana matsawa da ɗan ƙarfi har sai da na yi yar ƙara yadda na haɗe rai ne ya sa ya fara mini dariya yana faɗin" Ki gama shan kunun ki sai na ƙara horan ki kenan. Me ya sa kika yi wanka ni ban ba ki izini ba?

Kasa magana na yi, kuma abin da ya faɗa sai da ya cika shi. Lalata mini wanka ya yi kuma bayan mun gama ina shirin sauka daga gadon ya riƙo ni wai bai ba ni izini tashi ba haka nan na koma na kwanta ya cigaba da jagwalgwala ni son ran shi sai da ya nishaɗi don kansa ya ce mu je mu yi wanka sai tura mishi baki na ke yi amma ko a jikinsa. Ban samu lafiya ba sai da ya fita sallar azahar ma ta suɓuce masa sai dai ya yi ta a gidaa bayan mun karya a lokacin sannan ya yi mini sallama ya fita.

Yana fita nima bayan na yi sallar na koma barci. Daman Yumna tun da ta ji ruwan zafi take barci. Ba mu muka tashi ba sai gab da la'asar shima ɗin kukan Yumna ne ya tashe ni. Sai da na ba ta Nono sannan na tashi na ɗauro alwala na yi salla sanin Yumna ba za ta kwanta ita kaɗai a ɗaki ba ya sa na goyata sannan na shiga kitchen domin neman abin da zan dafa ma su Jidda kafin su dawo daga makaranta.
Da yake Yallaɓai ya yo mana cefane cikin satin nan sai kawai na yi mana cous-cous mai kayan lambu. Da yake ba shi da wahala nan da nan na kamalla shi. Ko da suka dawo ina falon su ina cin nawa Yunma na hannuna tana ƙiriniyar su na yara. Suna dawowa Baby ta fara damuƙarta daman in dai tana gida ba ni da haufin yar reno tun tana kuka in ta ɗauke ta har ta saba in ma ta ganta ta dinga kallonta alamun tana nuna mata sani. Sai da na karɓe ta sannan Baby ta samu daman cin abinci. Bayan sun gama na goya mata ita, Jidda kuma ta je ɗaureye musu kayan makaranta.

Ranar da wuri Yallaɓai ya dawo gidan ko kafin tara mun shige ciki ni da shi da Yumna Baby ta yi barci Jidda ce ke karatu tun da mun shiga sabuwar shekaran 2021 akawai jarabawowi a gabanta. Ni dai kwana biyun da Yallaɓai ya yi a gidana da wayyo Allah na ƙarishe shi duk cinyoyina ciwo suke yi da gaɓɓaina saboda bai sarara mini ba, in na yi ƙorafi sai ya ce wai ai ya yi ƙoƙari wajen kwana hamsin sai na ce ba yana da wata matar ba sai ya harare ni ya ce ita sunanta Saudatu ke kuma Sadiya kin ga kowacce na da nata tarim bambamcin da ya bambamta ta da ƴa'ruwata tun da na ji haka ban ƙara yi masa magana ba.

Da ba ya gidana barci na yi ta sha ina hutawa ina zan iya. Haka dai rayuwar ta cigaba da tafiya. Shekaran 2021 ta zo ma da Yallaɓai da babban buɗi na alheri domin ya dace da samun wani babban kwangilan gina jami'ar kuɗi a nan garin Abuja. Yadda Yallaɓai ke murna ne ya sa na san cewa ba ƙaramin alheri zai samu ba abin farincikin ma sun bashi 70% na kuɗin aikin shi satin kaf yini ya yi cikin farinciki shi ya sa ba tare da sanya ba ya saka Khalipa a makarantar su Jidda. Amma shi Gimbiya ke kai shi da kanta su Jidda kuma Salisu ne.
Samuwar kuɗin hannun shi ya sa ya tsayar da lokacin buɗe kamfanin shi ƙarshen watan Feb. Tun da ya ce yana tunanin kayan da ya yi oder su sauka a tsakiyar wata mai kamawa.

A cikin haka ne aka fara shagalin bikin mijin Ma'u. Mu ne gaba gaba masu dannen ƙirji, na ba ma Ma'u gudummuwa sosai a wajen auren nan, a ka yi taro lafiya aka tashi lafiya ba tare da na bari an ga gazawarta ba. Ta ji daɗi ta kirani tana ta yi mini godiya har shi Alhajin ya yi ma Yallaɓai maaganar daidaitarwar mu ba ƙaramin canji yake gani a tattare da Ma'u. Ni daman haƙuri na ce ta yi gashi da ta yi haƙurin har an yi auren komai ya wuce. Har Baaba da ke adawa da ni yanzu ta ɗan sakar mini,nima sama sama tunda daman can ni da ita jininmu bai haɗu ba.

Jidda ta sake sabunta rigister ɗin ta na Jamb. Da ƙyar da saka bakin Kawu Abba Yallaɓai ya bari ta cike ABU zaria a first chioce ɗin ta. Shi dai wai baya so ta yi nesa da gida ni kuma na ce ai duk in da take addu'armu na tare da ita kuma ai zaria gida ce. Hmm kawai ya ce shi fa daman ya amince ne domin an fi ƙarfin shi ba domin yana ra'ayin haka ba. Ita dai Jidda tun da ya amince sai murna ta ke yi sai bayan salla za su yi jamb ɗin da sun zana ta, za su fara rubuta jarabawar fita babban sakandiri. Shi ya sa ba ta zama yanzu ita ce jamb class da lesson har asabar da lahadi yanzu ba ta zama

21 / 55