sa nake yi yana tambaya ta Jidda na ce ta na ɗaki sai ya tashi ya shiga dakin na bi shi da kallo. Yallaɓai bai taɓa ce mini yana sha'awan tara mata ba amma ni a ƙasan raina na ke jin giyar kuɗi za ta iya ɗibar sa ya ji mun yi masa kaɗan kuma wannan wargajenjen filin da na ji labarin ya siya ba, ba iya ni da Gimbiya ba ne. Wataƙila shashen mata huɗu ne zai gina a hasashena tun da bai taɓa furta mini haka ba. Ya ce sai an gama ginin kamfanin shi an buɗe shi sannan zai fara ginin gida can kwanaki ma da muka bi ta hanyar na ga Kamfani ya yi nisa kaɗan ya rage a ƙarisa.
In ana misalin maza jajirtattu masu jajircewa da juriya to sunan Yallaɓai zan fara kamawa a shekarun da na san shi sama da shekaru goma sha takwas ya jajirce domin mafarkinsa ya tabbata na gina kamfanin shi, domin ya taimaki matasan da aikin yi to ko a haka ya tsaya wallahi ya cigaba domin matasan da suke aiki a ƙarkashin shi shi kan shi bai san iyakar su ba. Da masu ilimin da ma waɗanda ba su da ilimin duk na shi ne, masu ilimin suna aiki a bangaren ma'aikatan shi mara sa ilimin kuma suna aiki a bangaren kwangilan gine ginen shi. Kuma ya na da tausayi da kyautatawa ga kuma mu yadda ya ke kyautatama mu da iyayen shi, shi ya sa Allah ba zai bar shi ya taɓe ba.
"Ke wai me ke damun ki kike yawan shiga tunani ne?
Na ji yana faɗa lokaci ɗaya ya na mai zama a gefe na. Har ya na wani jawo ni jikinsa yana shafa bayana zuwa kuguna sannan ya cigaba da faɗin.
"Uhm mene ne. Faɗa mini damuwarki yanzu na yi miki mganin ta."
Kamar abun arziƙi na ɗago ina kallon shi kafin na marairai ce ina faɗin" Yallaɓai wai yaushe za a buɗe gari ne? Tsakani ga Allah ba a kyauta mana ba da yanzu fa mun yi nisa da lectures"
Me Yallaɓai zai yi in ba dariya ba, har ya na ƙyaƙyatawa. Ni kuma sai na haɗe rai na koma gefe na yi bakam. Ina jiran ya taɓo ni sauke masa jin haushin shi da nake ji.
"Ai in za ki shirya zaman gida ki shirya. Domin cutar ma ƙara yaɗuwa ta ke yi ba ma maganar a buɗe gari."
Kallona ya ke yi fa yana tsintsira min dariya.
"Hajiyar Masters. Ki yi wannan master ɗin ki a gidan auren ki, taho mu je ciki ni ma ai malamin ne sai na baki karatu"
Ya ma miƙo hannu ya kamani na bige hannun shi ina hararan shi amma bai saka ya daina dariya ba.
"Yallaɓai."
Na kira sunan shi a tsume.
"Na'am My Sady masu kwalin masters"
"Ni dai ko murna kake yi da faruwan wannan abin ne?
Ko daman can da ka ce ka bar ni na koma makaranta ba har zuciyar ka ba ne?
Na ƙarishe ina mai kura masa ido. Ya na danne dariyarsa ya ce" Wallahi har raina na amince miki. Ya za a yi na yi murna da haka?
Ya ƙarishe faɗa yana daga hannu sama amma bai daina mini dariya ba.
"Na ga kamar murna kake yi. Wato gara da a ka yi haka ko?
"Murna kuma! Da girmana Sadiya?
Ya faɗa yana sosa sajensa amma bai daina dariya ba kawai sai na miƙe fuu da wayata ina faɗin"Ohon in ma ka na murnan gwara da a ka yi ne gwara ka daina saboda ba ni kaɗai ba ce a gidan har da ƴaƴan ka"
"Kuma haka ne fa."
Ya faɗa yana kuma cigaba da dariya.
"Kuma in sha Allahu, za a buɗe gari kuma zan shiga makaranta Ehe."
Na faɗa ina mai barin masa falon sai ya biyo ni yana faɗa mini.
"In sha Allahu wa ya isa ya hana ki zama mai kwalin masters"
Gabaɗaya Yallabai ya mai da ni abar nishaɗinsa na so ina shige ɗaki na rufe ne sai ya shammace ni ya biyo ni yana faɗin shi fa ba dariya yake yi mini
"Wallahi in na tuna yadda kika ci burin karatun nan sai na ji duk ba daɗi. Sorry My Sady in sha Allahu zaman gidan ba zai yi tsawo ba."
Wani kallo na yi masa saboda yana faɗa ne amma yana danne dariyan shi kawai sai na fusata na jawo filo na wurga masa ina faɗin.
" Ka fita Yallaɓai"
"Na je ina?
Har tsayawa yake yi yana tambaya ta, sai na ƙara rarumo ɗayan ina ƙokarin jifan sa da shi sai ya mamayeni ya rumgumeni yana mini dariya ni kuma ina fizge fizge sai ya fara min cakulcakuli a dole sai na yi dariya. Yallaɓai akwai mugunta wallahi sai da na yi hawaye, har fa sai da na ce masa zan yi fitsari a wando in bai daina ba sannan ya ƙyaleni. Bai bar gidan ba sai da na dai na fushi na dawo ina dariya ni ce har haraba na raka shi muna soyewar mu.
*****
Tun ina saka ran za a buɗe gari na yi registration ɗin makaranta har na cire rai ganin har mun shiga wata biyu muna kwararan na uku, sai na ce gwara na zauna na yi ma kaina tunanin mafita. Tun da karatu dai ba zai yuyu ba gwara na mai da hankalina kan sana'ar hijabai na da yadda zan ƙara ingata shi, sai na fara tunanin sunan da sanya ma kasuwancina. Da ƙwaƙwalwar ta ƙi sai na nemo Jidda na ce ta sama min suna. Haka muka zauna muna ta zaɓe har sunana ta haɗa ni da Yallaɓai SADYUF na ce ba na so da a baya ne zan iya haɗawa dashi amma tun da ya yo mini kishiya na fahimci Yallaɓai ba nawa ba ne ni kaɗai. Ta haɗa da haruffan sunanta da na Baby na ce ba na so sunan ya yi kama da na ma'aikatan Yallaɓai ne. HM TAFIDA AND SON'S LIMITED. Sai na ce a samu dai wani ganin zai yi wahala na ce kawai ta haɗa min da sunana, mun yi kwanaki ba a samu wanda ya yi min ba sai da na ce mata ina so na saro inears wear sai ta ce to bari a haɗa gabaɗaya. Da ƙyar dai Jidda ta samo min SADY S YASHE HIJABS AND MORE. Sai na ji sunan ya kwanta min arai nan take na ce bari mu tafi da wannan sunan kawai.
Musbahu na nema tun da shi ne ɗan gida ne kuma idon gari ne kusan ya san ko'ina. In da Allah ya taimake ni kuɗin da Yallaɓai ya tura mini na hidimam makaranta da na ce zan mai da masa sai ya ce na riƙe na ƙara jari ya bar mini, da su na yi amfani domin ƙara bunƙasa kasuwancina. Musbahu ya shige mini gaba a ka buga mini ledojin da tambarin logona na SADY S YASHE HIJABS AND MORE. An yi manya da ƙanana sannan an yi na kwali su na manya costumer ne
Sannan an yi min sticker na mannawa a jikin kaya bayan na siya ledoji farare da zan riƙa saka hijaban da kayan in an siya. Tun dai an samu zaman gida bari mu kama sana'a zama bai ganmu ba. Musbahu ya saka cikin masu zanen su na kamfani ya zana min logo mai kyau na saka shi a duka handle ɗina na kafafen sada zumunta.
Kuma kowa ya gani sai ya ce sunan ya yi kyau. Ya Hamza sai da ya ce bai ga sunan Yallaɓai ba ina dariya ban ce komai ba har Ma'u da muka daɗe ba mu yi mgana ba da na ɗora a status a ƙasa na yi caption da cewa.
"SADY HIJABS AND MORE. Muna siyar da nau'in hijaban da kuke so sannan za mu fara kawo muku inners wears, kamar su pants, bra, sikat, mini trouser and more. Please potonorize your Sister. Sadiya Sulaiman Yashe C.E.O"
A nan Yallaɓai ya gani ya yi tagging ya turo mini dariya. Na shaka na auna masa naushin hannu na sticket kawai sai ya yo mini Vn ranar ma ba a gidana ya kwana ba yana gidan Gimbiya amma a daran zai dawo gidana.
"Daman shawaran nan na kawo miki tun farko kiƙa ƙi karɓa. Duk wanda ya tuba don wuya ba lada."
Haka ya ce min fa sannan ya ƙarishe da dariya. Ina masa Typing sai ga shi ya sake turomin mgana.
"Congratulation My Sady. Duk abin da kika saka ma suna ko hannu sunan shi Nasara. I wish you the best"
Kalamansa suka wanke mini zuciya na fasa tura masa abin da na yi niyya.
"Thank you Mijin Sadiya."
Kamar ya ijiye wayar amma dai ya tafi bai kashe data ba. Mutane sai fatan alheri suke yi mini har Anty Maimuna sai da ta ce yana da kyau kam na ƙara da wani abun Anty Zuwaira kuma ta yi tagging da zamu siya in sha Allahu. Daman ita ai ba ta da matsala Anty Bahijja ne ta gani ba ta yi mgana ba. Amma har Gimbiya ta yi mini murna sannan ta ce za ta yi mini talla a status ɗin mutanenta su gani ko za su siya na ce Na gode. Daga nan na kashe data na sauka sai zuwa can an juma Sameena ta kira ta ce ta na son hijabai da na pant da bra shi ne take faɗa min a status ɗin Yallaɓai ta gani ya ɗora sai da muka gama waya sannan na buɗe data na gani.
Ya saka ne amma bai yi wani rubutu ba. Na ga kara domin sun ta sakawa a status suna yi mini tallah. Marwa ma ta saka Hauwa ma da ta yi waya Munnira ma haka yan gidanmu Ya Balki sai Amina har da Datti Ya Auwal dai da Ya Hamza ba a saka su a lissafi su waɗanan ba su damu da saka statua ba irin Yallaɓai ne. Ya Abubakar kuma shi wannan ɗan buga buga ne bai ma cika hawa online ɗin ba. Gidan su Yallabai su Musbahu ne da su Adnan sai Jawahir da su Suwaiba sune daman nawa. Duk kuma wanda ya ga logon zai ce zane ne, ma su abu da abin su kura da kallabin kitse.
Kamar wasa na yi ta samun odar masu siyan hijabai da inners barin ma da azumi ya ke tunkaro mu. Da ya ke a mota kawai ake saka mun ina tura masa bayanan da kololin na Hijabai inners kuma sara na yi da yawa na yara da manya na tura kuɗi a ka kawo minI har na cin kasuwar salla. hijaban dai sai na ƙaro tun da guda 50 na ce a akawo mini. Da suka iso duk wanda ya siya ni da Jidda muka yi zaman saka su. A leda muna manna sticker sai lamarin ya burgeni ni kaina komai da tsari kan ya fi burgewa Jidda ta yi Vadeo muna saka sticker ta kuma ɗora mini a status ta ce kaya sun iso. Nan da nan cikin sati ɗaya kaya suka ƙare sai na sake tura kudi ɓarin ma Inners ɗin sun tafi yadda ma ban yi zato ba daman su Hijabai ana siyan su sosai. Wannan karon sai na ce a sako mini da mayafai da kayan barci suma dai ba laifin ana ta siye da na gida da na waje.
Sana'ata na riƙe gadan gadan. In dai ka ganni da waya to ina can ina marketing. Yallabai har suna ya sauya min wai hajiyar Hijabai ni dai na ce ka ji da iyayin ka tun da karatun dai bai zo hannuna ba gwara na kama abin da ya zo hannuna. Ana cikin haka a ka kawo mana kayan saka ranar Suhailat ɗin Anty Bahijja bayan sallar azumi za a yi bikin kuma Kaduna za a kai Amarya. Ni da kaina na kira ta a waya na yi mata Allah ya sanya alheri. Ni ba na gaba da ita muna gaisawa in mun haɗu amma daga wannan gaisuwan kowa sabgan gaban shi yake yi tun da aka yi mana tsakani ni da ita.
Cikin ikon Ubangiji muka riski watan ramadana cikin lockdow abubuwa duk sai a hankali saboda yanayin zirgan zirgan gari duk da ba kamar lokacin gari na sake ba wannan karon ma Yallaɓai ya siya buhun gero da siga sai wake buhu ɗaya na alale da ƙosai na kai ma Maman Saude yin kunin ita kuma Maman Nana mai yi min kitso a ka ba ta yin ƙosai da alalen. Sannan ya rarraba ma matansa da ke aiki a ƙarkashin sa kayan abinci wasu kuma ya ba su kuɗi, daga can Rano Kawu Abba ya aiko mana da su ƙwai da dankalin turawa. Nima Yallabai ya ba ni kayan abinci har da kuɗi na kai gida duk da na san itama Gimbiya ya ba ta ta kai can Rano amma ni bai gaya mini ba, ban nemi da sai na ji ba kuma
Azumi ashirin da tara muka yi kuma ban sha ko ɗaya ba ko da ban ga period ɗina ban damu ba, ko watan da ya wuce ma bai zo ba saboda an sha yin azumi ni ban sha ba sai ban saka tunanin komai a raina ba. Yallaɓai ya yi mana kayan alfarma ni da yara har salla ta wuce muna saka sabbin kaya sannan ya yi ma iyayena har Inna Mariya ya yi ma turmin atamfa wannan shekaran. Ni kuma na caɓa da cinikin hijabai da inears wannan sallar kaf su Ya Hamza wajena suka yi ma iyalansu siyayya kuma na ji daɗi a dangin Yallaɓai kuma su Musbahu ne da su Anty Zuwaira har Anty Maimuna ta siya ma yara. Gimbiya ma ta siya kuma ta kawo mini costumer kuma na ji daɗi na gode mata. Yallaɓai ma kuɗi ya ba ni na yara sai kawai na cire musu a ciki da ni kaina na saka kuɗin a ciki. Kuma ba abin zan ce ma Allah sai godiya ina samu ina yi ma kaina hidima sannan abu na ƴan uwa ya ta so ina ɗauka na yi ba sai na je ina yi ma Yallaɓai yar murya ba.
An ɗaga bikin ɗiyar Anty Bahijja sai gab da babbar sallah a bakin Munnira nake jin wai uban mijin ne ya biya ma Sulaihait ɗin kujeran makka tare da mijin ana ɗaura auren za su tafi tare na ce Allah ya sa su je lafiya su dawo lafiya.
****
Kamar kar a yi salla sai na fara rashin lafiya. Kuma rashin lafiya irin a tsatsaye haka. Kasala ya riƙa damuna na dai na cin abinci komai ba ya mini daɗi ban da kunin tsamiya mai zafi ba abin da ke shiga cikina. Sannan ba na iya shan kowani ruwa. Ba ni da aiki sai kwanciya tun ina ganin abin wasa har dai na fara tunanin watakila ina da ciki. Tun da in dai na ci abinci sai na yi amai ga Yallaɓai ba ya nan ya je Dutse wajen kwanan su huɗu a can, karyata kaina nake yi da ba ciki gare ni ba saboda ko wancan da na yi ɓarin shi ban ga alamomin shi ba sai kawai na fi amimta da maleria ke damuna na saka a ka siya mini mganin maleria na fara sha. Ai duk ranar da na sha sai na yi amai sannan sai na fara miyau
ba na iya haɗiye miyau. Sannan na yi ta kwana da zazzaɓi gari na wayewa sai na ji sauki. Jidda ta ce za ta rakani asibiti na ce ba zan je ba har waya ta sata ta yi ma Yallaɓai waya ta faɗa mai halin da na ke ciki sai ya ce ta ba ni wayar haka ya riƙa mini faɗa ya kuma ce umarni ne maza maza na tashi na shirya Jidda ta rakani asibiti na ga likita.
Ba yadda na iya haka na shirya. Sai a lokacin na fahimci na rame sannan na ƙara haske, wani asibitin kuɗi muka je muna zuwa suka yi mini tambayoyi na faɗa musu wajen wata uku kenan ban ga al'adata ba sun ɗibi jinina da kuma fitsari muka zauna jiran sakamako Yallaɓai kuma sai kira ya ke yi Jidda ce ke ɗaga kiran ni ina ta kaina sai kwanciya nake yi a kujerun asibiti. Lokacin da sakamako ya fito likita ya ba ni farar takarda sannan ya faɗa mini ina da shigar ciki ɗan kimanin wattani biyu da kwanaki. Duk da alomomin masu ciki sun bayyana a tare da ni ban saka ma kaina yaƙini ba. Hawaye suka zubo minibsai na sharce su a cikin raina na yi ma Allah godiya sannan na yi masa kirari. Jidda na wajen domin ita ta riƙe ni muka shiga da muka fito ina riƙe da takardan muka samu adaidaita da zai mai da mu gida. Amma sai da Jidda ta biya Pharmacy ta siya mini magungunar da ya rubutamin na ƙarin jini da na cin abinci.
Da farko da Yallaɓai ya ce zai kira Salisu ya kai mu tun da motar na hannun shi in fita haka ta kama ina kiran shi ni na ce ya ƙyale shi mu fita mu hau adaidaita sahu. Har a cikin adaidaita kwanciya na yi da leda a hannuna ina tara miyau duk cikina da na yi da ga na Jidda har na Baby ban yi miyau ba, kai ban ma yi wannan laulayin mai wahalar wa ba. Tun kafin mu kai gida Jidda ta kira Yallaɓai tana murna tana faɗa mai likita ya ce Umma na da ciki.
"Jidda da gaske kike yi?
Ina ji saboda wayar an ƙure mata kara. A yanayin muryan Yallaɓai za ka san akwai zaƙuwa da zamuɗi.
"Na rantse da Allah Abba Umma za ta sake haihuwa."
Ta faɗa cikin har sai da mai adaidaitan ya juyo yana kallonta ina ganin shi sai da ya yi murmishi ya juya kai ya na faɗin" Hajiya yanzu daman wannan budurwan ƴar ki ce? Wallahi na dauka ƙanwarki ce ni dai dariya kawai na yi ba tare da na yi magana ba.
"Ma sha Allah. Allah ya inganta.'"
Na ce Amin ita Jidda ba ta ma jin sa ta na can ta na waya, ban yi mamakin kalamansa ba saboda ba shi kaɗai ya taɓa faɗan haka ba sau tari mutanen da ba su sani ba in suka