Turken Gida Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   37 / 55

108K to 111K   out of 163.1K words

zazzau ne na garin zaria itama akwai ƙoƙari kamar Jidda shi ya sa suka fara ƙawance shima ɗin sai da Jidda ta neme shawarata ni kuma na faɗa ma Yallaɓai na ce ya saka a yi masa bincike kan yarinyar kar ya zo ta shiga jikin ɗiyarmu ta cutar damu.

Shi ya bincika kuma ya ce yarinyar ta fito babban gida masu tarbiya. Jin haka ya sa muka ba ma Jidda izini ta saki jiki da ita, to ita ce ta siya hijabai sama da kala ashirin kaloli dabam-dabam. Ni kuma sai na ba ta kyautar ɗaya da dogon wando da sikat da pant saboda kyautatawa mai son ɗiyata. Cikin saƙon Khaleesat na saka musu sakon su can gidan suka je suka karɓa. A lokacin suka fara test ni dai addu'ata ko da yaushe Allah ya tsare mini yarana Jidda kuma ina yi mata fatan sa'a da nasara. Yallabai kuma yaƙini gare shi a kan Jidda da cewa in sha Allahu za ta saka shi alfahari wata rana.

Cikin haka muka shiga watan Ramadana, Jidda sai kusan salla ta dawo gida hutun na su ma na sati ɗaya ne ana fice salla ta koma saboda suna shirye-shiryen fara jarabawar farkon zangon karatu. Mu dai muna gida muna bin su da addu'a sai da suka gama jarabawa suka samu hutu ta dawo gida, duk ra rame sai ɗan wuya da tsawo. Yallabai ya yi ta faɗa wai kar ta saka ma ranta karatu ta mutu saboda naci. Ta riƙa hutawa tana cin abinci, dawowar Jidda na sake saka mata ido ko zan ga wani canji ban ga komai ba sai ma girma da hankali da natsuwa da Jidda ta kara. In ina kallonta sai na cika da alfahari na ce Ubangiji ka gama yi mini komai tun da ka ba ni Jidda. Baby ce dai wannan ko aure ta yi na tabbata sai na rika yi ina kwaɓa mata. Shegen rawan kai ne da surutu gare ta.

Kafin su koma Ummu salma Hamza ta kawo mata ziyara takanas ta zaria. Direba ya kawo ta a ranar kuma suka koma, ni kaina har da ni a masu yi ma Ƙawar Jidda Hidima. Itama na ganta mai kyau da ita age mate ɗin Jidda ce, ita ta fi Jidda haske da kiɓa amma tsawon su ɗaya. Itama a zuwan da ta yi na fahimci tana da natsuwa sosai.  Har Yallabai sai da Jidda ta kira shi ya dawo gida ya ga Ummu Salma suka gaaisa ni kuma ta ba ni mahaifiyarta muka yi waya. Ta ce mini tana shigowa Kano, za ta neme ni wata rana na ce in sha Allahu. Amma ta ce na karɓi lambarta a wajen Ummu sai na kirata na ce in sha Allahu. Ta kawo ma Jidda Atamfa da mayafi, sai Baby ta kawo mata doguwar riga har Yumna an kawo kayan wasa tun da ta san sunansu a baki. Nima da za ta tafi na ba ta hijabai biyu na ce ta kai ma mamanta. Sai turaren wuta da na jiki sauran nawa ne na kwashe na ba ta, Jidda daman ta yi cincin da donut ta kwashe mata aka yi raffing. Yallabai kuma 20k ya ba ta tace karɓa ya zare mata da cewa shi mahaifin Jidda ne. Kuma duk wanda yake aminta da Jidda ya tabbata shi din uba ne gare shi, shi ya sa ta karba ta duka har kasa tana godiya.
Muka rakata har waje, direban daman da ya kawo ta, tafiya ya yi sai da za su tafi ya dawo. Ni da kaina na yi ma Jidda alƙwarin itama za ta je har gida wajen Ummu salma. An ce tuwon girma miyan shi nama.

Kafin babbar salla suka koma makaranta. A lokacin na yaye Yumna, da na biye ma Yallaɓai to ba zan yaye ta ba. A cewarsa wai ba ta gama yin ƙwari ba yarinya bukekiya tana yawon ta ko'ina, tuni na cire ta a nono tana da wattani sha bakwai cikin na sha takwas. Da wajen Ma'u zan kai ta yayen, tun da ita ta yi mini magana. Har Marwa itama ta yi nacin na kai mata Yumna yaye. Ma'un da muke kusa na yi niyyar na kai mata ita ta yayeta kwatsam sai muka wayi gari da rasuwar mijin Baaba. Ma'u na can Kura mu ma mun je mun kwana ɗaya mun dawo har Amina dake Kaduna ta taho. To Allah ya sa dai ita ce uwar yayen Yumna ita tafi da ita Kaduna a can ta yi babbar salla. Tun tana rigiman Umma Abba Baby har ta gaji ta haƙura tun da akwai yara a gida. Yallabai ya gaji da korafi na ɗauki hakkin yarinya ya haƙura shima.

Sai da ta yi wajen wata biyu sannan Amina ta dawo da ita. Yumna ta ɗan rame sannan ta kara girma sun kawo ta da sha tara na arziki ita da mijinta Yallabai na ta fadan wai na tura musu ɗawaniya.  Na ce na ji ba komai ai ƙanwata ce in ta yi mata ba ta faɗi ba.
Rayuwa dai alhamdulillah tana tafiya cikin farinciki. Yallabai yanzu fa na neman ya sha kwana. Kuɗi kawai yake facaka har mota ya sauya wata jeep ce itama mai tsada. Adnan ya faɗa mini da muke hira da shi za ta kai miliyan huɗu daga nan na yi shuru. Sannan ya bude shagunan sai da kayan gini, komai na na'uin gini akwai, kofifi, interlock, simnti, kayan aikin tiolet, kwano, ba abin da babu a wajen ƙasan wajen kuma ya saki shagunan masu aski da wasu yan kasuwan sun kama sannan ginin gidan shi ya yi nisa har an yi linfter an saka kankare tuni yanzu ma rufe yace mini ake yi, an ma kusa gamawa da ya nuna mini a hoto. Sai ina ta mamakin gaggawan da yake yi a kan ginin nan sai da na yi masa mgana.

"Ina so ne ko ba ku tare ƙarshen shekaran nan ba to a farkon shekaran 2023 mu tare a sabon gida in sha Allahu."

"Allah ya amince mai girma Md."

Na faɗa ina dariya har ina jinjina, saboda maganar gaskiya Allah ya buɗa ma Yallabai kwangolili ne wasu na jiran wasu malam. Kuma in dai aka bashi kwangila ya yi shike nan duk wanda ya gani sai ya yaba yace a haɗa shi da shi sillar gasikiya da amana da aiki ba ha'in ci. Mu kan mu mun shaida Mijin mu na da kuɗi yanzu, abinci sai dai mu yi kyautarsa. Duk wani abu na daɗi muna ci, suturu kuwa na kece raini muke sawa mu da yayanmu. Ba mu ba har iyayen shi ma yana yi musu nima ba abinda zan ce masa sai godiya. Ya ba ni kuɗi na kai gida ya kai kayan abinci komai fa sai godiya. Da shi da Kawu sun yi ma Tariq fintikau shi duk cikin su ba shi da ƙarfi tun da aikin Gwammati yake yi. Su kuma yan buga buga ne da man.

****
BAYAN WATTANI HUƊU.

A watan october 2022 Baaba ta gama idda sai ga shi karshen ta dai gidanmu ta dawo da zama ita da sauran ƙannen Ma'u su Zainab. A ɗakin Hajiya Dubu su Ya Hamza suka gyara mata daman tarkace ake sawa a ciki. Baaba duk ta yi laushi kamar ba ita ba, ni ce wai za mu zauna muna hira da ita har muna dariya abin da ban taɓa tunanin fatuwarsa ba. Datti ya samu aiki a NNPC reshen jihar kaduna har an saka masa rana zai yi aure zai auri wata abokiyar karatunsa tun suna KAsu ba ta yi aure ba har ta yi masters tana aiki itama. Duk kuma a kusan lokaci ɗaya aka saka musu ranar aure tare da Adnan, wanda shima ya fara aiki a ma'aikatan Yallabai a matsayin Engeanaring na karatu.

Tuni ginin gidanmu ya yi nisa ko na ce cikin kashi uku an yi biyu saura ɗaya. Tun da ko wancan satin da hanya ta bi da mu ni da Ma'u da su Ya Aina na ɗauko su a motata mun je gaba da in da gidanmu na mu yake, gaisuwa yayar Zaitunan Ya Abubakar ne ta rasu muka je mata gaisuwa. Na bi da su ta gidan har sauka ma muka yi suka gani, Mun shiga ciki ma'aikata ne sama da ashirin suna aiki, wasu sun sanni suna ta faman gaisheni waɗanda ba su sanni ba suna faɗa musu matar injiniya ce.

Mun iske suna ta saka inteelock na tsakar gida. Wasu na ciki ɗakunan suna yin filista, wasu na ma an gama ana saka kofofi daman POP da wearing din wuta ana gama rafta Yallabai ya ce an yi su. Na ga har fulawoyi aka shushuka a gidan har sun girma daman Yallaɓai akwai son shuke-shuke a gida. Ya Aina da Ya Balki suna santin girman gidan da kyan shi, Ma'u ko har da guzarin kasar wajen da yake tana da ƙaramin ciki sha take yi wai ta yi mata daɗi.

Muna tafe a hanyar komawarmu Ɗorayi Ya Murja ta ce"Gidan nan da girma yake. Amma na ga shashi huɗu ko aure Baban Jiddan zai ƙara?
Ya Balki tace" Ni ma abin da zan ce kenan bayan shashin Sadiya da na abokiyar zamanta nata ga biyu nan kusa da juna."

"Nima fa ina ta mamaki."

In ji Ma'u dake gidan Gaba su suna can baya ne.

Ina dariya na ce" To Allah masani. Mu ma dai haka muka gani da na yi magana ya ce ɗaya na shi ne ɗaya na baki. Daga karshe yace ga shi da yara maza ya yi awadace ne."

"Uhm ya dai ce muku ne amma da wahala bai ƙara ko dayan ba ne ballanta yanzu da giyar kudi ke ɗiban shi "

In ji Ya Aina ni ko na saka dariya ina ba su labarin diramasu da Gimbiya.

"In Yau Yallaɓai ya ce zai yi aure ai akwai yaƙin duniya na uku shi da matarsa."

"Ta yi ta gama. In dai ya yi niyya sai ya yi."

In ji Ma'u ita da ta ga zahiri, ga amarya har ta haihu, itama an zama daya da ita.

Ni dai ina ta dariya har muka kariso gida, Rahila ba ta je ba, ba ta da lafiya ta ce sai gobe za ta leko, muna gidan har bayan la'asar muna ta hira da  Baaba da Gwaggo. Har a raina ban kawo ma Yallaɓai aure yanzu ba, ba kuma don ban ji a raina zai ƙara ba amma sai don ina ganin wataƙila akwai sauran lokaci. Sai dai me? Sai na fara ganin canje-canje daga wajen shi, yana yawan kafa-kafa da wayarsa a kwanakin nan. Abin da a baya bai dame shi ba in ba aiki zai yi a ciki ba ko an kira shi ta yini a in da take bai taɓa ba ya fi amfani da laptop ɗinsa a kan wayarsa

Amma a kwaanakin nan Yallaɓai na kan wayarsa har murmishi zan ga yana yi wani lokacin, na rasa me ya ke dubawa ko kuma me ya ke karantawa? Sannan wata rana in yana gidana zai dawo ya yi wanka ya ci uban gayu ya fita in na yi magana sai yace akwai mutanen da zai gani ne. Ni kuma samin shi da jama'a da hulɗodi sai ban damu da fitan na shi ba amma a kwanankin na fara zargin Yallaɓai yana yin wani sabon abun da bai saba yin shi ba, sannan ranar ma Yumna na wasa da wayarsa da ya ijiye a saman kujeran falon sa ya shiga tiolet, sai na karɓa abin mamaki na san code ɗin buɗe wayarsa date ɗin aurenmu ne, amma sai  na gwada ya ƙi buɗewa kenan ya canza. Da ya fito ya ga wayar a hannuna ya ɗan yi wani iri, da sauri kuma ya karɓe wayarsa ni kuma sai na ce masa Yumna ce za ta yi masa wasa da shi na karɓa
Tambayarsa na yi ashe kuma ya sauya code ɗin buɗe wayarsa.

  "E na sauya."

Bai kuma faɗa mini abin da ya sauya da shi ba sai da na tambaye shi.

"Date ɗin ranar da na buɗe ma'aikatana ne."

Haka kawai ya faɗa daga nan kuma ya koma ya zauna ya cigaba da duba wayar tashi. Har yana wani mirmishi na yi kasake kaawai ina bin sa da kallon mamaki amma na kasa magana.

Na ɗauka ni kadai ce na fahimci Yallaɓai na yin wasu baƙin abubuwa. Sai da Gimbiya ta yi mini magana a chart, da man tun bayan faɗan da na yi mata muke yar daɗi da ita in ma wani abu ne ya shige mata duhu akan mijinmu za ta kira ni mu tattauna.

"Maman Jidda."

Na amsa mata lokacin Allah ya sa ina online itama haka.

"Kin fahimci Daddy na yin wani abu a boye wanda ba ya so mu sani!?

Sai na ce mata ban fahimta ba, saboda ko na ce na fahimta ba ni da hujja tun da ban ji ba, kuma ban gani ba.

"Me kika gani? Me ya sa kuma kika ce haka?

Sai na rubuta mata tambayoyin na tura mata sai na ga tana yi mini Vn
Yana shigowa da sauri na buɗe.

"Maman Jidda Daddy na yin wani abu gaskiya. Yanzu fa kafa kafa yake yi da wayar sa kuma a da ba haka yake yi ba. Maman Jidda Daddy fa yanzu sai ya kai 1 na dare yana online sai ka rasa da wa yake yin charting da na yi magana sai ya ce wai da abokan hulɗarsa ne. Sannan sai ya rika yin wanka ya ci gayu ya ɗau mota ya fita sai dare yake dawowa ni fa gaskiya na fara ji a jikina anya anya kina ganin ba wata ce can a waje ta fara ɗauke masa hankali muna nan zaune ba mu sani ba."

"Hmmm."

Kawai na tura mata na ma kasa magana. Ashe dai ba ni kaɗai na lura da wani abu na ɗaukan hankalin Yallabai a kwanakin nan ba.

"Ki yi magana. Ke ma kin fahimci haka,?

"Nima na fahimta amma na kasa gane me ya jawo haka."

Na amsa mata

"Kin ji ko. Wallahi mu tashi tsaye da bincike kar muna zaune wata shegiya ta ɗauke masa hankali.'

Sai kawai na ce mata to zan bincika itama a ɓarayinta ta bi komai a sannu sai ta amsa ni da to, wai har da cewa ta sanni da sanyi wani lokacin wannan karon ba abin yin sanyi ba ne sai kawai na tura mata dariya.

A ranar da muka yi magana yana gidan Gimbiya ne sai washegari da zai dawo gidana ya saba dawowa da wuri, amma yau har goman dare bai shigo ba na gaji da jiran shi kuma na kira shi bai ɗauka ba. Kamar zan kira Gimbiya sai na fasa tun da ni ban saba kiran ta haka ba. Baby ce daman ke jiran shi kan maganar JSSCE ɗin ta na makaranta ta ƙi yin barci daga ƙarshe da ta gaji da jira dole ta kwanta.

Ba Yallabai ya shigo ba sai sha ɗaya saura. A yanayin da ya shigo mini ba na lafiya ba ne. Toilet ya faɗa yana faɗa mini cikinsa ya lalace. Wayarsa da babban rigan sa ni ya bari da su tunda ni ce na tarbe shi.

Na shiga bedroom ɗin mu da niyyar na ijiye masa wayar da key ɗin mota sai rigan shi. Ina shirin ijiye masa wayar a saman gado kira ya shigo. Gabana ya faɗi ras!
Ganin sunan mai kiran RABI'ATU BUK."

Har ta katse na kasa daina kallon wayar. Kaf a tunanina ban tunano wata yar uwan Yallaɓai mai wannan sunan ba. Ban gama mamaki ba gur! Saƙonta ya shigo wayar daga sama na ja na fara ganin abin da ta rubuto.

"Yallaɓai na ka isa gida lafiya? Mun gode...!

Daga nan sai saƙon ya yanke, jiki na rawa na watsar da rigar hannuna ina ƙoƙarin gwada buɗe wayar amma na kasa.
Wata zuciyar ta ce Sadiya ki natsu ki yi aiki da hankali. Sai kawai na ijiye ma sa wayarsa nan saman gadon na zauna a gefe na ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya ina girgizawa.

Mintina biyar sai ga shi ya buɗe kofar bedroom ɗin ya fito yana nishi sama sama.

"Cikina kawai ina hanya ya karta. Ina zuwa sai gudawa kina da ko pulajin ne Sadiya?

Ya faɗa yana dafe cikinsa. Lokaci ɗaya yana ƙarisowa gabana yana kuma ƙoƙarin cire rigar jikinsa.

"An kira wayarka. "

Ya kalleni a ɗan tsume yana cire rigan daga shi sai farar vest.

"Ta kuma turo saƙo."

Sai kawai ya tsaya yana ksllona. Nima ina kallon fuskar shi yanayin shi ya nuna tsoro amma sai ya yi dakiya irin ta maza.

"Rabi'atu ce ko?

Ya faɗa yana kallona.

"E ita ce"

Na faɗa ina kallon shi, shima yana mai kallona sai kawai na ga ya yi murmishi. Mirmishin da na ji ya soke ni a ƙasan zuciyata.


*Janafty**TKGB3017*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX


Assalamu Alaikum Fanmily, mun fara saro muku kayan Kitchen ko wani nau'i, duk abin da kuke bukata na gyaran Kitchen ɗin Amarya da uwargida duk za ku same su a JANAFTY KITCHEN ITEMS, kayan mu masu kyau ne da inganci sannan za ku same su akan rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina a falin Nigerian nan. Domin karin bayani ku tuntuɓe mu ta waɗannan lambobin kamar haka.
09069067488.
+234 706 234 9732

Muna maraba da masu siya ɗaya ko sari🥰

"Da man na san za ta kira."

Ya sake faɗa lokaci ɗaya da ƙwatanƙwacin irin mirmishin da ya yi a farko lokacin da na ce an kira wayarsa.

Gabana ya sake faɗi ras! Ba tunanin komai na kawo ba sai tunanin Yallaɓai ko dai ya fara bin mata ne? To ni dai ban san wannan yarinyar ba sai yau amma shi a yanayin da ya nuna kamar ya jima da sanin ta. Sannan fuskarsa ta bayyana asirin zuciyarsa na yadda take da muhimmaci a wajen shi koda bai furta da fatar baki ba.

"Yallaɓai."

Na faɗa jikina na rawa tare da zuciyata ban san ma na sauke kafafuwana daga harɗe sun da na yi ba sai da na ji suna karkawa, tare da dukan junansu saboda tsoron tunanin da ya shige ni yanzu nan.

"Na'am."

Ya faɗa yana mai kallona fuskarsa ba alamun wani firgici ko nadama.

"Me ya faru?

Ya faɗa yana mai sake kure ni da ido, sai na ga kamar yana neman raina mini wayau bayan ya san abin da ya faru amma kuma yana sake kallona yana tambayata

37 / 55