Turken Gida Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Janafty Category :  Love

Chapter   16 / 55

45K to 48K   out of 163.1K words

ya ga na kira to ba lafiya.

"Kai kaɗai ne a in da kake?

Na tambaye shi sai ya ce shi kaɗai Gimbiya ta can ɗakin yara.

"Me ya faru ne?

Ya sake tambaya kamar bai yarda da cewa wani abu bai faru ba."

"Jiya ne bayan fitan ka sai ga Ma'u ta zo mini cikin kuka Alhaji Mustapha ya sake ta."

"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un wani irin saki kuma?

"To ai har da marin ta ma ya yi Yallaɓai"

"Mari?

Ya maimaita cikin sigan tambaya.

"Ƙwarai kuma ya ce ta bar masa gidan sa a daran"

"Subhanallah me ya faru a tsakanin su haka?

"Ka taho gida in ba damuwa yanzu sai mu yi mganar."

Nan da nan ya ce min gashi nan zuwa. Bayan mun kashe wayar na zauna kawai ina tunani rayuwa kenan
Yau wai ni ce Ma'u ta zo mini da matsalanta, yau ina su Ya Murja ina su Anty Bahijjan ina su Shema'u? Yau duk ba za su yi mata amfani ba dole dolenta dai jininta ne zai yi mata wani anfanin da a da take ganin ni ban isa ba, kuma yadda ta zo ta faɗa mini wallahi sai Alhaji Mustapha ya roƙi gafaran Ma'u a kan wannan cin zarafin da ya yi mata. Zuciya ta sai ta fara zafi ina cin wani raɗadi daga ƙasan zuciyata kamar ni a ka yi mawa, na yadda akwai jinin Ma'u a jinina shi ya sa yake motsawa a kan ta in wani abu ya same ta.

Ina nan zaune a falon su Jidda sama da mintina arba'in har Yallaɓai ya shigo gidan. Shima dai ya nuna damuwarsa a saman fuskarsa na zauna na zayyana masa duk abin da ya faru na ƙarishe da faɗin" Tun jiya da ta zo ta ke kuka. Ta ce ba za ta koma ba tun da ya tozarta ta, ba ta yi barci sai da safen nan ba ka ganta ba gwanin ban tausayi."

"Gaskiya bai kyauta ba. Haba da hankalin shi me ya sa zai yi haka?

Yallaɓai ya faɗa kai tsaye, shi ma ai ya san gaskiya kowa kuma ya ji wannan mganar sai ya ce bai kyauta ba.

"Kuma a kan gaskiyanta ta yi mgana. A kan gadon ta fa ya je yana yin waya shi ne ta yi mgana ya yi mata wannan wulaƙanci."

Na faɗa cikin bayyana jin haushina.

"Shi ya sa na ce miki bai kyauta ba. Ya kuma nuna ko auren ya yi ba zai yi adalci ba. In ba wawanci ba me ya sa za ka zo cikin gida kan gadon ku na sunna kana waya da wata macen da ba ka riga ka aura ba, kenan itama ka nuna mata matar ka ba ta da daraja a wajen ka in ta shigo gidan za ta iya taka ta yadda ta ga dama tun da kai ka ba ta damar haka.'

"Gaskiyan mgana kenan"

Na faɗa ina kallon Yallaɓai ina mirmishi. Shi ya sa na ke son Yallaɓai ta wanni fanni akwai shi da faɗin gaskiya komai ɗacin ta.

"Ita kuma rashin kyautawarta ɗaya ne me ya sa ta fasa masa waya? Da ta yi masa magana bai ji ba da ta ƙyale shi ta bar masa ɗaki in ta yi haƙuri zai wuce har kuma wata rana ya dawo ya na jin kunya. "

Duk abin da Yallaɓai ya faɗa gaskiya ne, nan na zauna ina faɗa masa wasu abubuwan da suka faru a baya ya jinjina kai yana faɗin" Duk laifin shi ne a matsayin shi na magidanci bai zama adali ba, ai ba a ce in za ka ƙara aure ka tozarta matarka ta gida ba. Ita kuma in ta nuna damuwarta ba ta yi laifi ba mijinta ne zai ƙara aure kuma tana dai-dai da ta nuna kishinta afili sai dai kuskurenta ɗaya me ya sa ba ta yi kishin cikin ilimi ba? Ta yi kishin da ta ta yar ma da mijinta hankalinshi kuma ganin tana kishin ne ya sa ya ke yi duk abin da ya yi, in da a ce ta yi masa kamar ba ta san yana yi ba da tuni ba ta kai su ga haka ba. Ta yi koyi da ke mana? Na san kina kishi na amma kishin mummuƙe kika yi mini sai da na dawo ina jin kuyar ki cikin ruwan sanyi kika saka na gane ba ni da wayau"

Ya ƙarishe faɗa yana kallona yadda na ga bai yi dariya ba ne na ga ne ba wasa yake yi ba. Sai da na harare shi sannan ya yi mini mirmishi yana faɗin ai gaskiya ne kishin mata masu Aji kenan a gasa namiji ta ruwan sanyi da zai zo ya na ba da haƙuri da kan shi, shuru na yi ban yi magana ba domin ni kaina ai ya gasa min aya a hannu kawai dai ana kauda kai ne a zamantakewa.
Mun tattauna dashi sosai daga karshe ya ce mu karya sai mu tafi tare da shi har da Ma'un nan kuma take ya kira Alhajin Mutspha ya ce za mu taho gidan Ma'u nan ba daɗewa ba ko kunya ya na faɗa ma Yallabai sun samu matsala jiya ba ta kwana a gidan ba Yallaɓai ya ce ya sani gidan sa ta kwana tare ma za mu taho ya ce yana gidan Hajiya Zainab amma zai taho nan gidan Ma'u yanzu.

"Ka ji min munafuki wato saboda ita Hajiyar ta san Ma'u ba ta nan shi ya sa ya je can ya kwana."

Na fada cikin jin haushi tun da duk na ji wayar na su a speaker ya saka wayar lokacin da ya kira shi.

"To mi ye laifin shi? Matan ahi biyu bai kamata ya yi kwanan gauro ba."

Wata uwar harara na jefi Yallaɓai dashi sai ya fara mini dariya ya na faɗin" Daga magana? Yi hakuri ba ni na kai zomin ba rataya kawai a ka ba ni."
Saboda haushi ban tanka shi ba yanzu yanzu ya na maganar kamar zai yi gaskiya a lamarin shin amma kuma yanzu ya na so ya yi son kai a lamarin shi.

Tare da shi muka dafa ruwan zafi shi ya ma soya ƙwai, ba buredi sai ya fita ya siyo, kafin ya dawo Ma'u ta tashi na saka ma ruwan a hiter ya yi zafi na ce ta yi wanka mu karya Yallaɓai ya zo za mu tafi can gidan na ta gabaɗaya.
Sai da ta yi wanka nima na yi, kaya na bata ta saka nima na zurma doguwar rigata mai kama da buhu ta bakin Yallaɓai bujun bujun ga cikina gaba ina tafiya a tale, Yallaɓai na falo can na je na same shi muka karya ita Ma'u ciki na kai mata na ta saboda ta samu sakewa. Sai da za mu tafi na ta da su Jidda suna ta barci na ce mata za mu fita ta yi musu wani abu su karya dashi ita da Baby in kuma za su sha Tea ne dai ga su ga gidan nan mu mun fita zuwa gidan Umman su Ma'u.

Yallaɓai ya ɗauke mu a motar shi, sai da muka ɗau hanya ne suka ƙara gaisawa da Ma'u ya na ba ta haƙuri sai ta fashe da kuka ta na faɗin" Baban su Jidda sakina fa ya yi a kan wata macen?

"Ki yi haƙuri ya yi kuskure kuma zan faɗa masa."

"Kuma wallahi sai ya biya ta marin ta da ya yi."

Na faɗa a fusace, sai Yallabai ya kalleni kafin ya ce"To ya biya ta, ko rama marin na ta za ta yi?

"In ta kama ba"

Sai Yallaɓai ya girgiza kai hankalin shi na wajen tuƙi ya ce" Ma'u kar ki biye ma wannan ƴar'uwan ta ki, a kusa ta ke kin dai gane"
"Ba wani a kusa na ke sai gaskiya ai ba zai mari banza ba."
"To na ji bai mari banza ba, daman ai ya san bai kyauta ba kuma ina da tabbacin yanzu haka ya yi nadama."

"Daga baya kenan an yi sadaka da bazawara."

Har Ma'u sai da ta yi dariya shi ko Yallaɓai kallona kawai ya ke yi yaa girgiza kai ganin yadda na haƙiƙance.

"To ni dai ki yi haƙuri kar mu je sulhu ki ɓata ma lamarin."

Na harari Yallaɓai ina faɗin" In dai har ina wajen sai na yi magana in kuma ba ka son hakan ta faru sai dai ka sauke ni na koma gida tun da ba ka son na faɗi gaskiya."
Na faɗa ina murguɗa masa baki ai sai ya yi shuru bai ƙara mgana ba, ko da muka isa gidan Alhajin na Ma'u bai iso ba sai da muka shiga muka jira shi.

Lokacin da ya zo har ya yi wanka ya ba za shadda na maiƙo har da babban riga a raina na ce kuɗi masu gidan rana duk su suke saka shi wani jin kai da ganin zai iya yin komai. Da ƙyar na gaishe shi saboda ina jin haushin shi a nan falon Ma'u muka zauna shi Yallaɓai ya fara ba ma dama ya maimaita magana sai kame kame yake yi, wai ta raina shi tun da ya ce zai ƙara aure taƙi kwantar da hankalinta ta sauya ta na abubuwa waɗanda ba halinta ba har ya na cewa wai haƙuri ya ke yi da ita sai jiya ta ƙure shi, shi kuma ran shi ya ɓaci har ya mare ta kuma ya furta sakin amma a jiyan bayan ta fita har bayan ta ya bi bai ganta ba kuma a jiyan ya janye sakin ya mai da ɗakin ta

Kallonsa nake yi a ƙasa ƙasa ina taɓe baki, ita ma Ma'u ta faɗi na ta a zencen gaskiya duka laifin shi ne. Duk shi ya rikita Ma'u ta koma haka a zaman nan ya ya bi Hajiya Zainab ban san sau adadin nawa ba ne, yana alfahari da cewa ita ba ruwanta ba ta ɗaga masa hankali lokacin da zai auri Ma'u ba yanzu ma ba ta ɗaga masa ba, sai yanzu ne ita za ta ɗaga masa hankali. Ya yi ta maganganu Yallaɓai ya ba ni haushi bai wani nuna masa kuskurensa ba yana wani lallaɓa sa, ni yadda ya nuna mini a gida ban ɗauka zai yi masa wannan lakwa lakwan ba. Daga ƙarshe an samu masalaha ya ba ta haƙuri itama ta bashi, kuma ya yi alƙwarin ba zai sake yin waya a gidanta ba in ma zai yi to ya kauce ma jin ta da ganinta. Ni ko ganin ba a yi maganar mari ba na gyara zama da cikina tulale a gaba na ce.

"To marin da ka yi mata fa? Tsakani ga Allah ba ka kyauta me ya sa za ka mare ta a kan wata?

Na faɗa ina kauda kaina cikin jin hauahi. Yallaɓai na yi mini abin da ba na so mutumin nan ya wani tattare wai an gama mgana ina dawo da su baya.
"To ka gama mgana ba ka yi maganar mari ba?
Na faɗa ina kure sa da ido, kawai ya wani bi ya tattare ni ai gwara a nuna masa bai mari banza ba.

"Ahto ka sani cewa Ma'u tana da gata duk abin da zai shiga tsakanin ku kar ka sake kai hannunka jikinta. In kuma ka sake to za mu kai mganar gaba, tun da Alhajin mu mata ya ba ka ba jaka ba"

Yadda na fiffitike ne ya sa har shi Alhaji Mustapha sai da ya yi dariya.

"Alhaji ka rabu da ita. Kasan masu ciki suna da saurin harzuƙa."

Na ma kasa mgana saboda Yallaɓai ya kai ni bango.

"Haba ba komai gaskiya ta faɗa na yi nadama kuma ni da ita zan rarrasheta. A yi mini afuwa Ya Sadiya."

Ya ce mini yana kallona Yallaɓai ma yana dariya dukkansu a ɗage nake kallon su a cikin zuciyata na ce ai duk kanwar ja ce.

"Yau na sake yadda da maganan nan ta hausawa da suke cewa jini jini ne. Ga shi yau Sadiya na mini faɗa saboda na taɓa mata Ma'u."

Sai da ya yi maganar sai na ji kunya na tashi ina mirmishi na ja Ma'u muka shiga ciki muka bar su nan a falo.
A ciki ba shawaran da ban ba ma Ma'u ba, ganin tana cikin damuwa ya sa na ce ta je ko Kura wajen Baaba ta bar Kano za ta samu natsuwa na kwana biyu sai ta dawo.

"Ina zan je Sadiya? Baaba fa cikin kishiyoyi take ba na so na je na bar mata abin faɗe"

"Ai ba dawo mata kika yi ba. Zuwa za ki yi da niyar za ki yi sati ɗaya daga nan in kika huta zuciyarki ta yi sanyi sai ki dawo ba tare da ita ko ita Baaban ta san wani abu ya faru ba."

Sai ta kalleni kafin ta jinjina kai ni kuma sai na ƙara da cewa" Saboda zuciyarki ta yi sanyi. Kuma Baaba uwa ce in kina ganinta hankalin ki zai kwanta ga su Zainab za ki samu yar natsuwa. In ma za ki dawo sai ku dawo tare saboda ta ɗebe miki kewa. Yara kuma kar ki yi mgana lokacin da ya ga dama ya dawo da su duk ɗaya ne da can da nan ɗin. Kar ki sake ki sake yi masa mgana kin ji ko?

Sai ta gyaɗa min kai alamun ta ji, hannuna ta riƙe tana faɗin" Na gode Sadiya. Allah ya bar ki da Yallaɓai har abada ya ba ku zaman lafiya."
Na amsa da amin amin nima ina mata ƙwatanƙwacin addu'ar da ta yi mini.
Ba mu baro gidan ba sai da muka sulhuta komai sai gashi tare suka rakomu har haraban gida muna fita bayan mun ɗau hanya Yallaɓai ya kalleni yana faɗin.

"Kin ga ni ko? Shi ya sa na ce miki kar ki zaƙe mata da miji sai Allah."

"Uhm"

Kawai na ce ina kallon Yallaɓai da na so kar na yi magana amma na ga dai ba zan iya haƙuri ba.

"Yallaɓai ni dai ka daina mini irin haka. Kawai ina so na ƙwatar ma y'ar uwata yancin ta kana dakatar da ni"

Ya kalleni ya sake kallona kafin ya ce" Me na yi kuma? Daga mgana. To ai na bar miki kin karɓan mata Umma Sadiya"
Ya faɗa yana mini dariya na yi kamar na kai masa duka saboda haushi amma ban yi ba saboda dai ya wuce duka in dai a wajena ne. Yallaɓai ai sha kumdum ne maƙura ne.
Muna hanya wayar sa na tsakiyar mu Gimbiya na ta kiran shi ya ɗauka ban ji dai me ta ce ba amma na ji shi ya na ce mata gashi nan zuwa. Ina zaune a gefe ko kala ban ce ba, ita wai nan ya fita da safe ranar girkinta shi ne take ta jaraban kiran shi.

Kafin mu isa gida na sake masa maganar koyon mota kawai sai Yallaɓai ya ce" Ke da wannan abin a gaban ki ne za ki je koyon mota? Kya bari dai ki haihu."

"Za ka koya mini in na haihun! In ba za ka koya mini ba na nemo ko Adnan ko Musbahu"

Sai ya fara dariya kafin ya ce" Ba za a yi haka ba Uwargida sarautar mata. Ke ce Alhaji Alhaji ya zama ke. Dole na ijiye duka harkokina na cika umarnnin ki."
Ko gatse dai ya yi na biye mishi na ce ƙwarai kuwa.
Yana kawo ni gida ko shiga bai yi ba Amarya na ta kira kai Gimbiya ba ta da haƙuri a rayuwarta ni dai na sauka na shige gida shi kuma ya wuce ban san yadda suka ƙare ba domin ni ban sake ganin shi ba sai washegari da yamma da zai dawo gidana.

Labarin abin da ya faru da Ma'u da mijinta daga ni sai Yallaɓai ko su Ya Aina ban taɓa faɗa mata ba duk ko yadda muke da ita. Na aminta da wani abu ɗaya ka riƙe sirrin wanda ya aminta dakai. Ba daɗi ta ji wannan mganar a bakin su sai ta ji ta raina ni, yadda nima ban faɗa ba itama kuma ba ta fidda mganar ba. Haba ai ba abin faɗe ba ne tun da ba abin daɗi ba ne muka rufe maganar a tsakanin mu tun da dai an samu sulhu. Kuma ko sati ba a yi ba mun haɗu a gida mun je duba Gwaggo da take zazzaɓi har ƙarin ruwa a ka yi mata a gida. Ta ga har mun zo mun taru gabaɗaya mun kuma rabu ba ta ji na yi maganar ba tana komawa gida sai da ta kira ni tana mini godiya har tana cewa na nuna mata na fita. Da ita ne ko domin a yi mini dariya za ta faɗa amma ni na nuna mata na yi ma zumumci kara kamar Yadda Alhajinmu ya roƙe ni.

"Ai ba mganar daɗi ba ne Ma'u. Sirrin ki kuma ai sirrina ne in na je na faɗa to ni za a yi ma dariya."

Ko Ya Aina sai da ta yi mini mgana. Ta ga ni da Ma'u gwanin sha'awa har Rahila ma sai da ta yi magana na yi dariya kawai na ce duniyar ma nawa take? Ya Aina ta ce haka ne kuma na burgeta. Rahila kuma har tana mini shaƙiyancin da cewa ko na kusa mutuwa ne na zama saliha, na ce mata ai ba yanzu zan mutu sai ta rigani mutuwa muna ta dariya ni da ita. Ba su san irin masifan da Yallaɓai da su Jidda ke karɓa ba, sun ga masifa da cikin nan kala kala.

A ƙarshen watan aktober a ka ba da sanarwa lafawar cutar corona. Farkon watan November kuma a ka buɗe gari har da makarantu gabaɗaya. Su Jidda a na ta murna an koma makaranta ta ɗauka da sun koma za su fara jarabawa ne amma sai a ka ce sai sabuwar shekara saboda calander ya birkice Jamb sai sun sake rigister. Wato abubuwa da dama a hutun nan na corona ya dagula shi, komai ya koma baya sai dai kuma a hankali komai zai dai- dai ta ni dai ban yi maganar komawa makaranta ba, in ma na yi Yallaɓai dariya kawai zai yi mini na ji ma kamar ba ni da rabon karatun ne daman haka Yallaɓai yake so. Ko da na koma bayan na haihu renon fa ai aiki ne mai zaman kan shi kafin sai kawai na cire karatun a raina na ce wata ƙila ba alheri ba ne. Na mai da hankalina kan sana'ata na hijabai

16 / 55