kirani yana ta yi mini godiya sai da na ji wani abu ya motsa a cikin tsokar ƙirjina. Me na yi masa? Komai shi ya kawo kawai nawa na ba da umarni an dafa kuma na aika da shi.
Washegari 30 Jan ranar asabar ƙarfe sha daya na safe aka ɗaura auran Yallabai da Rabi'atu kuma sha sha ɗaya da mintina ni ya fara kira ya sanar mawa.
"Alhamdulillah. Ma sha Allah Allah ya ba mu zaman lafiya ya kaɗe dukkan fitina."
"Amin na gode Sadiyata. Na gode ƙwarai da girmamawan ki."
Ya faɗa cikin farinciki ina jin ta hayaniya ta wayar sai ya kashe. Sai da na ji tahowar ƙwalla amma sai na yi saurin yar da ita. Na yi kwalliya tun da har mai kwalliya na kira na gayyaci su Maijidda da samira duk sun taho mini biki. Waina aka yi da shinkafa sai alele sai zoɓo ga ruwan gora da lemuka sai wanda ka zaɓa. Na diba abincin tun da aka gama na aika da shi Gwammaja. Su Suwaiba ne suka zo mini bioi sai su Jawahir, sai su Hauwa da yan gidanmu duk wanda bai zo ba yana gidan Gimbiya. Na ce duk abin ta dai ga shi ba a fasa ba. Sai ga Ummu Salma da mahaifiyarta sun zo mana biki kuma wallahi na ji daɗi har da su turarenka wuta ta kawo mini da mayukan gyaran jiki ba su kwana ba, bayam la'asar suka juya ta ce sai za mu koma sabon gida za su dawo in sha Allahu. Haka na yi taron biki lafiya aka gama lafiya mun shan ankuna mun sha hotuna kuma duk na tura ma Yallaɓai shima ya turo mini na su da su Kawu sai na shi shi da Amary ta sha lafaya yar maiduguri sak ba ta yi makeup ba fuskarta sak ta bayyana.
Mimisco ta watsa hotunan a can group ɗin su na gida Musbahu ma dake can ya riƙa turowa ma su jin haushi suna gefe suna ji ba su da yadda za su yi. Tun kafin su Yallabai su ta so ya kirani ya faɗa mini, ya ce akwai ma wasu y'an uwa Rabi'atu da tun jiya suka taho. A yi abimci na tarban Amarya na ce ma to. Su Munnira na bar ma aikin,shinkafa suka dafa priderice, sai ferfesun nama da pepe chickenn da kuɗin hannuna na yi amfani ya ce in ya dawo zai ma yar mini. Ba a samu kunin aya ba amma an yi zoɓo sannan ga lemuka da ruwa
Da aikawa na so na yi amma Yallaɓai ya kirani da kan shi ya ce na je gidan na tarban masa Amarya.
"Sai na je? Ba ga Gimbiya da su Anty Bahijja?
"Na san da su na ce ke. In kuma ba za ka yi mini ba ne sai na ji."
Ina jin haka na ce masa ya yi haƙuri zan je, ina ma gidan Mimisco ta biyo ɗaukata ita ta yi tsire ne mai yawa na tarban Amarya nima da su Hauwa da Munnira da Farida muka fara yin gaba sauran kuma na ce su hawo adaidaita. Motata kuma Amina ta tuƙo yan gidanmu zuwa cam. Mun iske bangaren Gimbiya cike da su Halima itama bangaren Amaryam akwai yan uwata a ciki masu jiran tarban ta. Saboda dai a zauna lafiya sai Mimisco ta ce mu fara sauka a bangaren Gimbiya amma na san ita kanta ta yi nadama. Wulakanci suka yi mana, kamar ba su taɓa sanin mu ba, Naja ba ta gaisheni ba amma ta gaishe da uwarta Anty Bahijja ba ta gidan sai Anty Maimuna kamar ta kashe nu in tana da iko. Sai Gimbiyar da ƙawayenta sai yanuwanta daga can Rano. Haka suka yi mana kallon banza wai ni Halima ke yi ma habaicin a yi dai mu gani in tusa za ta hura wuta.
Da Mimisco ta ce in Amarya ta zo a fita gabaɗaya a yi tarba shuru suka yi wallahi da ta iso ƙin fotiwa suka yi, Adnan ne ya ɗauko ta da ita da ƙawarta da kanwar mamanta daga filin jirgi, dagqani sai tawagata sai Mimisco muka yi tarban amarya. Mimisco ta yi tarba da Turaman zannuwa uku da 50k. Nima na yi da 20k da cimgam da su minti kuma wallahi sun ji daɗi, Rabi'atun tana cikin lafaya fara ne a rufe amma tana ganina sai da ta gane ni ta riƙe mini hannu.
."Barka da zuwa Amarya."
Bi sa al'ada bangaren Gimbiya muka fara yi musu jagora. Kanwar mamanta ta tambaya an ce tana da abokan zama guda biyu. Mimisco ta nuna ni ta ce ni ce uwargida ban riga na tare ba ne amma na taho tarban Amarya sai Gimbiya. Wacce ba ta ma fito falon ba duk da ko Mimisco da kanta ta kirata amma wallahi ta kunya ta mu a gaban mutane abin gudun ban takaici. Kanwar maman Rabi,a ta ɗan fahimci wani abu sai ta yi ta cewa a yi haƙuri da juna a zauna lafiya. Rabi'a ƙanwa ce a gare mu mu tsawarta mata in ta yi ba dai dai ba, haka nan muka kwashi sanyin jikin mu muka raka su bangaren Amarya. Ni na ɗauka a gidan Nene za tafara sauka Mimisco ta ce sai gobe za a kaita. Itama ranta ya ɓaci na ga ta kira Naja da Maimuna tana yi musu faɗa ni dai ba mu zauna ba, muna danƙama dangin Amarya abinci muka yi ta kan mu bayan na sanar da ita in tana bukatar wani abu ko ta kirani ko ta kira Yallaɓai za a kawo mata ta ce to.
A daran ma Yallaɓai ba a gida ya kwana shi da su Kawu a hotel suka kwana sai washegari da safe na gan shi da suka shigo gidan. Yallaɓai ana ta baza baban riga yana washe baki da an kira shi Ango ya yi dariya har tana fidda sauti.
*Janafty*
/*TKGB3019*
*EID MUBARAK FANMILY. ALLAH YA MAIMAITA MANA. SON SO.
Da ma Amina ce da Faridan Tariq sai Marwa suka kwana a gidan. Yallaɓai yana ganin Amina ya washe baki yana ce mata ashe ta zo?
Ita ko saboda ta kunna shi sai ta ce ai zuwa bikin nan ya zame mata dole. Ba kunya ya ce ya ji daɗin zuwanta. Megidanta ya tambaya da yara tace suna nan lafiya.
Faridan Tariq kuma tsiya ta fara yi masa wai ya yi biyu ba zai haƙura ba sai ya haura uku.
Yallaɓai na dariyan nishaɗi ya ce" Ta in da za ki gane ni gwarzo ne ba. Ba matsaroci irin mijin ki ba."
Ya faɗa yana nuna Tariq wanda ke gefe yana magana a waya ne tun shigowarsu gidan
Kawu Abba kuma muna gaisawa da shi ne.
Shewa Farida ta yi kafin ta ce" In dai tsoro ne to Allah kar ya cire masa wannan tsoron har abada."
"Muguwa kike Farida?
In ji Yallaɓai yana dariya.
"Sadiya kina jin kawarki ko!
Ya faɗa yana kallona ina dariya na ce" Bar ta sai dai in bai gano wata yar faka faka kamar yadda ka gano ba."
"Wallahi da man na ga a can yana bin yan mata gidan su Rabi'atu da kallo ko ya ga ni yana so ne?
Ya faɗa yana dafa kafaɗan Tariq daidai lokacin da ya gama wayar.
"Nima na lura da munafukin yana ta kallon wata yar fara nan ƙasa ƙasa."
Kawu ya faɗa yana shafa sajen sa, Farida ta ce ba su gani da kyau ba tana kare ma mijinta.
"To ke ina ruwan ki? Ba shi da bakin mgana ne?
Yallaɓai ya faɗa yana dariya.
Kawu ya ce ina zai yi magana ya san gaskiya.
"Ko dai kai ne ka ƙyallo wata kana son ka yi mini kage Kawu?
Tariq ya faɗa yana kallon Kawu shi kuma sai ya buɗe baki amma ya kasa mgana ni da Farida muka fashe da dariya.
"Ina matarsa? Ina marwatun? To ta shirya wata ƙila za mu koma Maiduguri karshen shekara."
"Tariq haka ka zama?
Kawu ya faɗa yana rike baki.
"Ƙarya na yi? Kai Tafida ba ka gan shi a ranar ɗaurin aure da muka je gaisuwan surukai yana tambayan sunan wata budurwa ba?
"Kamar fa na gan shi."
Yallaɓai ya faɗa yana danne dariya.
Kawu ya jinjina kai kafin ya ce" Yaran nan abin tsoro ne. Mu ɗan bangaji juna ne lokacin da za mu shiga za ta fita ita kuma, sai ta ba ni haƙuri na ce ba komai amma saboda ku magulmata ne har kun hango wai ina tambayan sunan ta ba?
"Ashe dai ka yi magana da ita."
"Na yi sai ka hana ni Ubana."
Kawu ya faɗa sannan ya kalleni yana faɗin" Surukata ni fa ban ga matata ba ban ga yayana ba."
Ina dariya na ce suna ciki bari na yi mata mgana.
Sai ya koma ya zauna saman kujeran falon yana faɗin" Yauwa Uwargida ran gida. Ke ce ke da gidan gabaɗaya. A ɓata miki rai mu yi tawaye wallahi "
Ya faɗa yana hararan Yallaɓai kamar ya san da shi ake yi ya ɗaga sannu alaman sarander kafin ya ce" Ba ma mai ɓata mata. Ni kaina in na ɓata mata abin a yi mini hukunci ne "
Kawai ba zato zan wuce na ji Yallaɓai ya rumgumeni ta baya ina ƙoƙarin ƙwace kaina ya sumbace ni a gefen fuska yana faɗin.
"Na gode Abar ƙaunata. Ubangiji ya ruɓanya miki a ranar lahira."
Farida da su Tariq suka amsa da Amin har da Kawu.
"Gaskiya Sadiya tana da kawaici. Wallahi ni ba zan iya abin da ta yi ba har ga Allah. Tun auran Gimbiya na san ita jaruma ce to ga wannam ma. Gaskiya na jinjina mata."
"Gaskiya abin a jinjina mata ne."
In ji Tariq.
"Shi ya sa nake ƙara jadaddaa ma Tafida cewa ya riƙe ta da kyau. Domin kaf cikin matansa ba mata kamar Sadiya. Domin a wannan zamanin ka samu macen da ka yi mata abubuwa da dama ta kauda kai, ta yi maka kara ta mutumta rigarka a idanuwan danginka da danginta ba abar tozartawa ba ce."
"Gaskiya ne."
Tariq ya sake faɗa, ni kunya ma suka kamani na ƙwace kaina ina faɗin" Ka bari mana Yallaɓai.
"Wai ina miki godiya?
Ya faɗa yana kallona da ka gan shi za ka san yana cikin farinciki.
"Ni me na yi? Ai umarnin Allah ne ban isa na ja da hakan ba."
"Duk da haka Na gode miki."
Ya faɗa yana mai kallona tare da yi mini mirmishi.
"Muna godiya Madam"
Tariq ya faɗa sai na amsa shi da cewa" Kai dai kana tsoro ko? Ko ƙawata ta bake ko'ina ne?
Na faɗa ina dariya, ita kuma Faridan tana cewa ita ba ruwanta ya yo mana ai ba kanta za ta zauna ba.
"Ba wani cika baki. Ba ke kika hana shi ya ƙara ba."
In ji Yallabai.
"Kuma wallahi tsoron ta yake ji."
In ji Kawu nan suka haɗe mata kai suna ta caccankanta da cewa kamar fitilar besfa Tariq dai ya ƙi kara aure sai ita kaɗai haba ai gwara dai ya ƙara ko ɗaya ne. Shi dai Tariq na gefe yana dariya.
"To ku ba shi matar ya ƙara mana? Wallahi ko a jikina tun da ba kaina za ta zauna ba amma gaskiyan mgana ba zan iya abin da Sadiya ta yi ba wallahi."
"Ka ji ba "
Kawu ya faɗa yana dariya kafin ya cigaba da faɗin" Za ko mu ba shi mata mu ga karyan cika baki. Kai ka zo Rano na duba maka cikin dangi."
"An gama Kawun mu."
Tariq ya faɗa yana dariya.
"Amma tare da shi za ku ƙara ko?
Yallabai ya tare shi.
"Me?
"Auran mana."
"Ah ni kam ai na tsufa, na fara furfurta matata Marwatu ta ishe ni."
"Kai ma tsoron matar taka kake yi kenan?
Farida ta faɗa, sai ya sosa keya kafin ya ce" Ki fahimta mana "
Tariq ya shuri kafar Kawu yana faɗin"Ka iya addabata da maganar aure kai ma fa? Me ya hana ka ƙarawan?
Ga tafida har ya yi ta uku?
"Na ce muku matata ta isheni kar ku tsananta bincike"
"Sai mun tsananta."
In Tariq.
"Ko ba ka da lafiya ne?
Yallaɓai ya kwaɓo magana ni da Farida muka tafa muna sunne kai.
"Ba shi da lafiya ya haifi su Abdallah munafuki lafiyan sa ƙalau"
Tariq ya faɗa yana dariya da Kawu ya ga sun dame shi kawai sai ya kalle su kafin ya ce" Ba ni da karfin mazukutan da zan tara mata shike nan kuke son ji?
Sai suka yi shuru suna kallon shi, ni da Farida saboda kunya sai muka kama hanyar barin falon saboda kunya.
"Matata ma haƙuri take yi da ni. Ta ina zan jajiɓo wata?
Kawu ya faɗa a maganarsa ba alamun wasa.
"Wallahi ƙarya kake yi munafuki."
Tariq da Yallabai suka haɗa baki wajen faɗa ni da Farida muka bar falon muna dariya in dai su ne in suka fara to sai kowa ya yi shuru ya bar su.
Marwa na ce ma ta je mijinta na kira ta ce to da man ta tsaya yi ma su Abdallah wanka ne.
Jidda na tura da kayan kari falon iyayenta sai ma ta dawo da shi ta ce sun ce a sun yi beakfast daga hotel ɗin da suka kwana, sun jima a gidan sama da awa sannan suka fita. Tariq da Kawu duk a ranar za su koma. Sun ce ma matan su su shirya kafin su dawo. Marwa ke son zuwa gida sai na ce ta yi sauri ta je ta dawo kafin su dawo. Amma ba ta tafi ba sai da suka ta ya ni muka gyara gidan sannan muka yi abincin rana Allah ya sa ba mu dafa da yawa ba tun da sai da na kira Yallaɓai a waya na yi masa maganar bangaren Amarya da danginta ya ce kar na damu Mimisco ta kira shi ta ce za ta yi direba zai kai sai na ce shike nan ta hutattashe ni.
Farida na ta mamaki wai kuma sai na dafa na kai! Na ce me ye a ciki? Ita kam ta ce ba za ta iya ba.
"Ba zan ta yar da hankalina balle na zama abin tattaunawa a dangi ba amma wallahi ba zan yi ba."
Ina ta dariya ita ko tana shan wallahi. Shi ne har muka gangaro maganar Gimbiya ina ba ta labarin duk abubuwan da suka faru kafin auran nan.
"Ba irin shawaran da ban ba ma Gimbiya ba ta ƙi jin maganata. Ni yanzu haka makiyayarta ce. Su Anty Bahijja ne masoyanta su ta rike suna zugata tana yi ma mijinta rashin kunya. Jiya fa a gaban dangin Rabi'a ta kunyata ni da Mimisco abin ba daɗi wallahi."
"Ai ga shi nan ta bar ma kanta abun faɗa. Sai yi da ita ake da cewa mijinta zai ƙara aure tana ta hauka. Gaskiya abin da ta yi ba aji ba ne, ni kaina ba ta wani yi da ni tun ma kafin auranta da Tafida. Bayan auran su kuma ganin muna tare ba ta shigo ni ba."
Ina dariya na ce" Ko yau kika je Allah ya sa ma ta kalle ki. Za ta ce kina murna tun da kika zo biki kika kwana a gidana."
Farida ta ce to sai dai ta ce amma ita ina ruwanta? Tun kafin auran ta da Tafida ya ke aminin mijinta kuma ko shi yayan nata ai ya je ɗaurin auran
"Allah na tuba su maza ina ruwan su?
"Ai shi kan shi ya yi ta faɗa da ya ji labari kin san Tafidan bai sanar da shi ba sai Hajiya ce ta kira shi tana faɗa mai akan na gida ne ma. Kai tsaye ya kira shi ya ce in ta sake yi masa gaddama ya kora ta gida."
Na riƙe baki ina faɗin" Lamarin har ya kai haka? To Allah ya kyauta."
"Ni in na je zan yi mata faɗa ruwanta ne ta ji ko kar ta ji ta gyara "
Ni dai da man ba komawa zan yi ba, zuwa la'asar suka barni ni kaɗai a gida har su Jidda sun tafi Gwammaja. Farida tun wajen biyun na rana ta wuce Gwammaja daga can za ta ƙarisa sabon gida. Amina da Marwa tare suka fita zuwa Ɗorayi, har Yumna da ita Baby suka tafi suka bar ni kaɗai.
Zuwa can Yallaɓai ya kira ni ya ce yan uwan Rabi'a za su kawo ta nan gidana na ce sai sun zo. Na tashi na ɗan ƙara gyara gidan na saka turaren ƙamshi
Ganin ba kowa a gidan har zan kira Munnira na ce ba za su dawo ba ne! Sai ga su ita da Hauwa sun shigo, na ce wayar dake hannuna su nake shirin kira na ce za a kawo mini amarya babu yan tawagata suna ta dariya.
Sai gabda mangariba suka zo. Musbahu ne ya kawo su a motar Yallaɓai, daga Gwamnaja suke an kai ta wajen Nene da su Maman Farko. A can kuma sun fara kai ta shashen Gimbiya. Hauwa ke faɗa mana Mimisco ce ta yi mata fata fata shine da aka kai mata Amaryan ta fito ta karɓa. Ni ma sun kawo min ita suka kuma damƙata amana a hannuna a matsayina na babba na kuma riƙe hannunta na ce na karɓa Allah ya zaunar damu lafiya.
Matar Baffan Rabi'atun na Kano da take zaune a gidan su ce ta kalle ni tana mai faɗin"Rabi'atu ƙarama ce a cikin ku don Allah a kula da ita. In ta kauce a karkato da ita, duk da ba kwa gida ɗaya tun da ke ce babba ki taya mu riƙe wannan Amanar don Allah"
"In sha Allahu. Da yake ba daɗewa nima zan koma can ba matsala Allah ya ba mu zaman lafiya."
Aka amsa da Amin gabaɗaya sannan aka yi addu'o'i sun kawo mini kayan su fulawa har da su dakuwa da nakiya sai tarurukan kamshi na ɗaki da na kaya sai atamfa da kololi sai filantai da kofuna har da kayan kwalliya kaya fa himiɗi ni na ce ma su rage kayan sun yi yawa suka ce ina tuwon girma a miyan shi nama. Sun kai ma surukanta da ɗayar abokiyar zaman nata. Muka karɓa su Munnira suka taya ni godiya nan na tsayar da su suka yi salla sannan suka tafi bayan sun sake yi mini sallama tun da sun ce suna ma yar da ita gida suma za su wuce. Baƙin Maiduguri kuma asuban cin gobe za su ɗau hanya
A bakin Musbahu nake jin suma su Nene haka aka kai musu himilin kayan arziƙin nan ita da su Maman Farko, har da na yayyen miji.
Ina ta mamaki daga baya kuma sai na cire shakku suna da al'adu sannan