kar ki dake ni."
"Ban isa ba kuma."
"Kin isa ma tun da gashi kin rufe ni da faɗa daga mgana. Na gaji fa wallahi zan daina raga muku daga ke har ita ba daman in yi magana a kan ku da ɗaya daga cikin su sai cibi ya zama kari daga mai cewa ba na yi mata adalci sai yi mini tsaki, sai mai cewa in an cuceta Allah ya isa. Yau dai mai kankat kin ce ni din nan wai Aniyata ta bini, daga magana ko barina ma na ƙarisa maganata ba ki yi ba kin rufe ni da faɗa kamar wani ɗan ki."
Ya faɗa a fusace, jijiyoyin sa na sake miƙewa kamar daman yana jira na ne.
"Kai ba ka ga laifin matarka ba?
"E ban ga laifin ta ba. Na faɗa miki daga yau ba zan ƙara raga muku ba. Ba ta yuyuwa ina mijinku kuna ƙarƙashina amma kuna ƙokarin rika sarrafa ni, saboda kawai ina muku kawaici? Kaina a ka fara auran mata biyu? Na gaji wallahi ku fita hanyata kafin wata rana ku harzuƙa ni na yi muku abin da ba ku yi tunani ba."
Ganin yadda ya fusata ya sa sai na yi shuru, salaf salf na fice zuwa tiolet ina kunshe dariyata ashe itama can rufe shi take yi da faɗa a kaina. Ina ga ita ce ta yi masa Allah ya isa ni dai ba ni ba ce, kama ruwa na yi na fito ina saita kaina ko da na dawo ya ja Yumna ya rumgume yau sai dai na ci kaina kenan mirmishi na yi, na shafa ma hannayena da wuyana turare sannan na kashe fitilar ɗakin na kwanta muka saka Yumna a tsakiya na ja hannun shi ina so na sarke tare da hannuna ya ƙi ya damƙe hannun shi, na tsugule shi a hannun amma ya damƙe sai ma ya rike hannun Yumna cikin na shi na ya jimƙe.
Ni da na ke son rigima sai na taso daga in da na ke na haura tsakiya na raba shi da Yumna na shige jikinsa mamaki ya hana shi magana ina kallon shi ta ɗan hasken dake shigowa ta waje ya ɗan murmusa.
Ya rumgumeni, na kwanta a saman kirjinsa muna kallon Dama ni da shi dukkanmu mun sarƙe hannayen mu waje ɗaya mun rumgumo Yunma ina jin sa ya yi mana addu'an barci ya tofa mana. Ba mu daɗe ba ni da shi barci ya ɗauke mu, Yumna daman ta rigamu komawa tun da ta sha Nono ta koma barcinta.
Asuba ta gari. YUFSAD.
*Janafty**TKGB30L12*
*Littafin TURKEN GIDA 1K ne on Telegram. 09069067488.*
Kina buƙatar kayan kitchens domin ƙawata Kitchen ɗin ki? Ya ke Uwargida kina buƙatar chanza ma megidan sabbin kwanukan cin abinci? Ko kina buƙatar sauya masa kofin shan ruwa? Ko kina so ki burgeshi da farantai masu kyau da yarari? Ko Amarya ce yar ƙwalisa da ke son ƙawata gidanta da kayan alfarma? To ku matso kusaa domin JANAFTY EXLUSIVE AVAILABLE Muna kawo muku ko wani nau'in kayan Kitchen da na kwalliya gida domin farincikin ku, kuma akan farashi mai rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina daga in da muke, ku tuntuɓemu ta wannan lambar domin ƙarin bayani.
09069067488
+234 706 234 9732
Washe-gari haka Yallaɓai ya tashi yana mini cin magani ina masa magana da ƙyar yake amsa ni, sai ya koma ma ya na ba ni dariya. Sai da na sallami yara zuwa makaranta sannan na yi ma Yumna wanka na shiryata na bashi ita ya riƙe ta na koma kitchen ina duba dankalin turawan da na saka amai kar ya ƙone.
Har Jidda yau suna da paper ta tafi daga ni sai Yallaɓai a gida sai Yumna ina daga Kitchen ina jiyo dariyan ta yana yi mata wasa. Mirmishi kawai na yi, in dai Yumna ne yanzu har ta waye da wasannin Yallaɓai ƙiyuwa ta fara yi ma Jidda saboda ita ba ta yi mata wasa amma da Baby ne ko su Khalipa da ba ma ganin su take yi koda yaushe ba har tana zillo in ta gan su. Yallaɓai ko ta riƙa harba ƙafafuwa kenan in ta gan shi in ko tana zaune ne sai ta tsintsira tun ina mamaki har na daina.
Yallaɓai da wuri ya ce mini zai fita, zai fara biyawa ta Gwammaja ya duba Nene kafin ya wuce office. Shi ya sa da wuri ya yi wanka ya shirya nima wankan na yi sannan muka zauna a kan dining muna karyawa sai kiran shi ake yi a waya harkokinsa can dai.
"Yallaɓai ka ce harkokin sun buɗe?
"Alhamdulillah."
Ya faɗa fuskarsa ba walwala lokaci ɗaya yana tusa dankalin a bakin shi sannan ya bi da ruwan tea ɗin dake cikin ƙaramin mug a gaban shi.
"To duk fushin na mene ne mijin Sadiya?
Kallona ya yi sai kawai ya ɗauke kan shi ya cigaba da cin dankalin shi da tea.
"Mene ne uhm? Ni ce? To yi hakuri ka ji Yallaɓai na. Ba na son ina ganin ɓacin ranka"
"A baya ne ba ki san ganin ɓacin raina amma ban da yanzu."
Ya faɗa ba tare da ya kalleni ba, sai na yi mirmishi kafin na ce" To na ji yi haƙuri ka ji?
"Uhn"
Ya faɗa kawai yana cigaba da tura dankali bakin sa.
"To ka ce ka haƙura mana?
"Me kika yi mini? Ba ki yi mini laifin komai ba so ki daina ba ni haƙuri"
"Na yi mana. Maganar jiya ko?
Na faɗa ina kallon sa, ni dai na san ran shi ya ɓaci kuma ya na jin haushina ko don ganin yadda yake magana yana cin magani.
"Ka yi haƙuri ni ba da kai nake ba"
"To da wa kike?
Ya faɗa yana kallona sai na kasa magana saboda ya zura mini idanuwansa cikin wani yanayi yana kallona.
Kai kawai ya girgiza sannan ya mai da kansa ƙasa ya cigaba da shan tea ɗin sa ba tare da ya ƙara wata magana ba ni kuma sai jikina ya yi sanyi sosai nima sai na debo dankali ina mai turawa a bakina cikin sanyin jiki da na zuciya.
Bai wani ci da yawa ba ya share bakin sa da tissue ɗin da ke saman dining sannan ya ɗago yana kallona nima shi na ke kallo.
"Har ka ƙoshi?
"Alhamdulillah"
Ya faɗa yana mai miƙewa sai kuma na ga ya koma ya zauna yana mai duba agogon fatan da ke tsitsiyan hannun shi na hagu, sannan ya sake ɗagowa yana kallona kafin ya kira sunana a kausashe.
"Sadiya"
"Na'am"
Na amsa ina kallonsa cikin natsuwa ganin kamar magana zai yi ganin yadda ya kira sunana.
"Kin yi mini laifi jiya kuma har na ji haushin ki. Amma sai na yafe miki kafin na kwanta saboda ba na so ki kwana da fushin Mala'iku a kan ki."
Sai na kasa mgana na yi jagale ina kallon shi.
"Ba zan hana yin magana ba saboda bakin ki ne. Amma ina so ki sani ni mijin ki ne, ki san irin kalaman da za ki riƙa amfani da su wajen mgana da ni, mijin ki ne ni ba kanin ki ko ɗan ki ba, bai kamata ina fara magana ki rufe ni da faɗa ba kina ta faɗin mganganu son ranki, daga karshe ma har zagina kika yi."
"Zagi kuma? Ni?
Na faɗa ina nuna kaina cikin zaro ido.
"E zagi ko ƙarya zan yi miki?
Ya faɗa yana kallona, sai na kasa magana na dukar da kaina ina fadin" Ni fa ba da kai na ke yi ba. Kawai na"
"Kawai me! Ai ni ne na ke yi miki maganana. Ya kamata ina magana ki ce mini jar uba!?
Ya faɗa yana mai kafe ni da ido sai ya karya lagona. Saboda na san ban kyauta ba amma na kasa magana ba.
"Kar ki sake, ba na so in kuma kina so ki ƙure hakurina ne to shike nan ki ciga ba. "
Ɗagowa na yi ina kallonsa ganin ya mike tsaye alamun zai fita.
"Ka yi haƙuri."
"Na haƙura na faɗa miki ne saboda ki kiyaye."
"In sha Allahu."
Na faɗa cikin sanyin murya kamar ba shi ba sai na ga ya yi mirmishi ya matso ya ɗan ramkwafa ya sumbaci goshinaa.
"Sai na dawo."
Na miƙe ina shirin masa rakiya da sauri ya saka hannuwan shi ya ma yar da ni zaune ya na faɗin" Ki gama ba sai kin yi mini rakiya ba."
"To sai ka dawo. Allah Ya ba da sa'a."
"Amin ki kular mini da kanki. Ke da Yumna."
Sai na gyaɗa masa kai, ina kallonsa har ya fice daga falo ya bar mini ƙamshin turaren shi, ina zaune a wajen na ji tashin motarsa da fitarsa sannan na ji karan jan get an ma yar an rufe, ajiyar zuciya na sauke sannan na cigaba da tura dankalin gabana nima sai na ji cikina ya tushe sai kawai na tattara na rufe ma su Baby in sun dawo makaranta su ci, da yake da safen ma ba su tsaya ci ba amma sun tafi da shi. Khalipa da Anwar amma Jidda tuni ta daina ɗaukan abinci ta ce na yara ne. Baby ce ba ta girma ita wannan uwar acicin ma ranar da ba ta je da abinci makaranta haka za ta dawo kamar ta ci babu.
Bedroom na koma saboda na baro Yumna tana barci, wayata na ɗauka ina latsawa bayan na zauna a gefen gado Data na buɗe na shiga yanar gizo-gizo ina ganin abin da ke faruwa, waɗanda suka yi mini magana duk na amsa su yawancin duk masu oder hijabai ne da yake na kwana biyu ban kawo su amma ina haɗa kan kudaɗen hannuna ne, ko na salla babba ban saro hijabai ba, na dai saro su inners ɗin saboda ba ishashun kudaɗe a hannuna. Daga nan I. G na shiga ina ta kalle-kalle na sai da na gaji jin na fara jin barci sannan na ijiye wayar na kwanta ban tashi ba sai bayan azahar Allah ya taimake ni yau Yunma barci take sha ko tashi ba ta yi ba amma na san za ta taɓa kukan dare tun da ta yi barcin rana sosai haka.
Barcin da na yi duk sai ya sakar mini kasala shi ya sa ko girki ban yi ba. Gidan ma ko sharan shi ban yi ba, yini na yi kwanciya sai danna waya sai da Yumna ta tashi ne na haƙura ma da kwanciyar da suka dawo daga makaranta sauran dankali suka sha tare da Tea, Jidda kuma na ce ta ɗora mana girki har da ni da Babansu tun da yau ba zan iya yin wani girki ba. Shinkafa da miya ta yi sai na kira Musbabu na ce in ba damuwa ina son kayan lambu, sai ya ce mini ba sa nan sun fita shi da Yallaɓai sai na ce to ya bar shi kawai daga karshe Adnan na kira shi ya siyo mana su kabeji da cocumber sai da ya kawo na bashi kudin nan ma ya yi isha'i ya ci abincin yana ta santin har yana ba ma Jidda Tuƙwaicin dubu biyar na girkin da ta yi. Bai jira dawowar Yallaɓai ba ya ta fi saboda Yallabai sai after 10 ya dawo a gajiye ya ce mini na haɗa masa kayan tafiya kala uku Jigawa zai je gobe kuma akwai yuyuwar ya yi kwana uku a can.
Tafiyar Yallaɓai ya sa su Khalipa ba su koma gidan su ba, ni kuma ban ji na duba ta ba na dai kira ta a waya na yi mata sannu ta ce mini ai ta ma samu lafiya, har tana ce mini ya su Khalipa an kawo mini hayaniya na ce ai ba komai. Yallaɓai sai da ya yi kwana shidda sannan ya dawo. Washe gari kuma ko hutawa bai yi ba ya wuce Kaduna daga can ya je Abuja kwangiloli ne yake samu ga su nan akai akai shi ya sa yanzu ba ya samun zama dalilin haka ne ya sa su Khalipa suka share wajen sati uku a gidana ba su koma ba sai a satin da suke da uku ne Yallaɓai ya samu zama a weekend ranar kuma sai ya faɗo yana gidana ne.
Safiyar lahadi, ranar Yallabai zai koma gidan Gimbiya kuma ya ce a shirya kayan su Khalipa za su koma gida tun da Gimbiyar ta samu lafiya. Wankin kayan su daman mai wanki na haɗa mawa sai na kira shi na ce ya kawo sauran kananun kuma tare da Uniform na saka Jidda ta ɗan wanke musu, ni da Baby kuma muka gyara gidan bayan mun gama na ce ta gyara Kitchen ta yi mini wanke-wanke sai Baby ta fara tura baki tana cewa ita kanta ke ciwo.
"Ai ko kan naki zai cire ne sai kin gyara mini Kitchen kin kuma yi mini wanke-wanke yarinya."
Na faɗa ina zare mata ido. Ta san halina tana yi mini wata magana za ta ji dundu shi ya sa bakin ta alaikun ta wuce, Jidda ke yi to yau tana wanki in ta gama ma za ta yi mu su Khalipa wanka. Yumna na goye a baya tun da na yi mata wanka take barci. Yallaɓai na ciki yana ta barci tun bayan da ya dawo sallar asuba ya koma bai tashi ba har muka karya sai ban tashe su ba sanin ya fi sati biyu bai samu lokaci ya huta ba bawan Allah ya na ta fadi tashi duk an kan mu, jiya ma Gwammaja muka yini ni da yara sai dare muka dawo da yake Nene ta ɗan yi zazzabi kwana biyu.
Baby na tura baki da komai ta gama aikin da na saka ta ban bari ta zauna ba na ce ta ɗora musu abinci Jidda tana gama ayyukata ta saka hijabi ƙawayenta sun biyo mata sun tafi tahfez suna ta mura'ju'a domin an kusa yin musu walimar saukar su, jarabawa kuma sauran ta paper ɗaya su gama shi ya sa nake ta tunanin tun da abin ya zo a tare zan ɗan jinkirta na haɗe graduation ɗin ta tare da Walimar saukar su gabaɗaya.
Yallaɓai sai biyu saura ya tashi, ya yi salla sannan ya sha tea ya hau kuma aiki a cikin laptop ɗin sa na wani lokaci ni kuma a lokacin na gaji sai kawai na kwanta Yunma ma a wajensa na bar ta, na daɗe ina barci sai bayan la'sar na tashi shima ɗin hayaniyan yaran ne ya tashe ni, na duba agogon wayata hudu da rabi har ta gota sai ban fita ba, na shiga Tiolet na ɗauro alwala na zo na yi salla sannan na fita falo. Abin da na gani ne ya sa ban san na riƙe kugu daga korido na ƙame ina kallon ikon Allah ba.
An yi mini kaca kaca da falo ba ma wannan ne abin mamakin ba. Illa Yallaɓai da na gani daga shi sai bakin wando sai singlet haka su Khalipa ba riguna sai kananun wanduna har da Baby itama ta ci zanzaro da kayan tekwando ɗin su na makaranta suna wasan doke ni in doke ka su da Yallaɓai gabaɗaya sun haɗa zufa. Jidda ce kaɗai ba ta shiga ba tana zauna ɗauke da Yumna da ke zillo kamar ta je a yi da ita.
Baki na saki da hanci ina kallon ikon Allah. Yallabai na ware hannu yana faɗin su zo su zo, suna zuwa suna kai masa duka yana tarewa suma yana kai musu suna tarewa, Baby ce ta ba ni mamaki yadda na ga ta ware ƙafa ta na kai ma Yallaɓai bugu yana ƙarewa itama yana kai mata tana karewa da sunan wasa. Na ma kasa magana saboda haushi da mamaki Jidda ce ta fara ganina tana dariya ta ce.
" Umma ko zaki shiga a yi chinese din da ke ne?
Hararan da na wurga mata ne ya sa ta rufe bakinta tana dariya ƙarisowa na yi falon ina fadin" Na shige su ni Halima. Yallaɓai me zan gani haka?
Sai a lokacin ya lura da ni ya na wani tsalle na ga kamar zai yo kaina na kwace ina faɗin" Yallaɓai.'"
Na ma kasa magana saboda mamaki Baby ta kalleni tana faɗin" Umma akwai dadi ki shigo mu yi da ke'
"E Umma ki shigo"
In ji Khalipa.
Hararansu na yi kafin na ce" Ni? Ai ba ni da irin ƙarfin ku Allah ya ba da sa'a."
Buɗe bakin Yallaɓai sai cewa ya yi wai na zo ko na rage kitse na ce na ji, amma ni ba zan shiga ba na tuna lokacin ina amarya Yallaɓai ya yi ta ja na da irin wannan wasan tuni na nuna masa bana so saboda shi ya iya kai duka ni kuma ban iya ba daga wasa sai a cuceka.
"Ke me ya sa ba ki shiga ba?
Na faɗa ina zama gefen Jidda. Yumna na ganina ta fara zillo tana miƙo mini hannu sai na karbeta.
"Ban iya ba Umma."
Ta faɗa a hankali ni da man na san ba za ta shiga ba. Ina son Jidda saboda kamewarta da Ajin ta.
"Kin taimaki kanki. Ita wancan da ba ta san ciwon kanta ba ai ga ta can ta na ware kafa kamar wata namiji."
Jidda ta fara dariya ni kuma haushi ya kume ni ganin yaran sun danne Yallaɓai suna kai masa naushin wasa gabaɗaya sun cika mana kunnuwana da iface ifacen su hauahi ya kama ni na yi ma Baby tsawa na ce ta baro wajen nan.
"Me ya sa? Ki ƙyale ta mana."
In ji Yallaɓai ganin ta yi mini wani nakwa nakwa da fuska kamar za ta yi kuka.
"Haba Yallaɓai ita fa mace ce. Ka dai yi can da su Khalipa su da suke maza amma ita bai da ce ba."
"A wajen ba shi ne bai dace ba,
amma ni a wajena Normal ne. Domin ta na mace shikenan ba za ta yi wasa da babanta ba? Ko su mata ba ƴaƴa ba ne?
Sai na yi shuru saboda Yallabai tun da ya tare maganar ba zam iya ja da shi ba, ita ko jin ban yi magana ba sai ta koma cikin murna shi kuma sai ya zo ya ja hannun Jidda yana faɗin" Come on Daughter mana."
Sai ta maƙe kafaɗa tana faɗin" Abba karatu zan yi"
"Ba za ki yi wasa da Abba ba?
Sai ta noke kanta ba ta yi magana sai kawai ya ƙyaleta yana fadin" Kar ki zama raguwa irin mamanki mana Jidda."
Hararan shi na yi kafin na yi magana ya tare ni da fadin" Ƙarya na yi ai ragganta ke hana ki