Manar Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Fatima Category :  Romance

Chapter   9 / 66

24K to 27K   out of 196.2K words

ba" Manar tayi saurin kallonta tace "wa zan fad'awa?" Ameerah tace "shi Yayan" gyad'a mata kai tayi tace "bazan fad'a masa ba" Ameerah tace "promise?" Manar dake kallonta tayi squeezing fuskarta tace "me?" Ameerah tace "kinyi alk'awari?" Da sauri ta gyad'a mata kai tace "ana bu'udak" murmushi Ameerah tayi then ta mik'a mata wayar,da sauri ta karb'a da yake ta haddace number Azaan a kanta nan da nan tayi saurin sakawa ta fara kiransa,lokacin Azaan yana driven kamar bazai d'auka ba da farko ganin da number Nigeria ake kiransa yayi shiru yana tunani kafin yayi parking gefen hanya,ya d'auka yasa wayar hands free,muryar Manar ya ji ta ce "hello! Yaya" da sauri ya katse ya kirata back,hannunta har rawa yake ta d'auka da muryar kuka² tace "Yaa Azaan" tana jinsa yayi ajiyar zuciya yace "na'am baby" kuka ta fashe da shi,a rikice yace "Subhanallah! What happened? Waye ya tab'a min ke?" Toshe bakinta tayi saurin yi,hawaye wani na bin wani,Azaan sai magana yake mata ta kasa amsawa,da sauri ya katse kiran hankalinsa a mugun tashe ya kirata video,tana ganin kiran ta kasa d'auka,shi kuma ya kasa hak'ura sai kiranta yake sake yi,Ameerah dake kwance ta zubawa sarautar Allah ido ganin Manar ba ta da niyyar d'auka ta fizge wayar tayi answering,da wani breaking voice yana ganin an d'auka ko gama tantance fuskar waye akan wayar baiba ya fara tambayar "Baby tell me what happened,me aka miki,ke da waye?" Ameerah tace "Yaa Azaan ita da Yaya ne fa" da sauri Azaan yace "Ameerah! Ita da wane Yayan ne?" Tace "Yaya Waleed" idanu ya zuba mata yana maimaita "Waleed! Me ta masa? Can u explain me ya had'a su?" Ta gyad'a masa kai tace "wayarta ya kwace mata" Azaan yace "ya kwace,for what reason?" Girgiza kai tayi tace "nima ban sani ba,na dawo skul yanzun take fad'a min" gyad'a kai yayi yace "tun yaushe ya karb'a?" Tace "i don't know,amma ina jin tun safe ne" lumshe idanunsa yayi yace "alright! Ba ni ita muyi magana" mik'awa Manar wayar tayi,ta kasa karb'a sai kuka take,Ameerah tace "Yaa Azaan tak'i karb'a fa" da sauri Azaan yace "Baby!" Kina jina?" Ta gyad'a kai bata d'ago ba,yace "kukan ya isa haka,dan ya karb'i wayan kike damuwa?" Tayi sauri ta d'ago kanta wasu hawayen suna sauka cheeks d'inta tace "ni ba a kansa bane" yace "Uhn! Tell me akan mene ne to?" Da muryar kuka tace "kana ta kira ban d'auka ba,na san ka yi fushi" wani beautiful smirk ya sakar mata yace "banyi fushi ba dear,yanzun ba gashi na san dalilin k'in d'aukan kiran ba" saurin karb'ar wayar tayi daga hannun Ameerah tace "da gaske?" Ya gyad'a mata kai yace "absolutely sure dear" tayi murmushi ta share hawayen,ya sake yi mata murmushin da yake k'ara masa kyau,a hankali yace "ki daina kukan haka nan,anjima za'a kawo miki wani kinji?" Gyad'a masa kai tayi,ya sake yin murmushi yace "shi kenan?" Tace "Ehh!" Yace "ina Dadi?" A shagwab'e tace "bata nan" yace "ina ta tafi?" Tace "ta je gidan k'awarta" gyad'a kai yayi yace "sai ku kad'ai ta bari?" Tace "ehh!" Ya gyad'a kai yana lumshe idanunsa yace "alright! Later za muyi waya idan na k'arasa gida ina hanya kika kira" ajiyar zuciya tayi tace "to! Allah tsare hanya" yayi mata murmushi yace "ameen.. Thank u" tace "ina gaisar da Momellah" ya amsa mata,ita ta fara katse kiran,tana d'agowa ta saki ihu,da wani muryar shagwab'a tace "sai yayi ta karb'ewa,ai dai ga shi za'a k'ara kawo min wani" Ameerah tayi dariya tace "Iyeeeee! Y'ar gatan Yaa Azaan" Manar tayi murmushi had'e da yin fari da idanunta tace "ya son ranki?" Ameerah tace "Aahhh! Normal" saurin tashi manar tayi tace "ke ni banyi sallah ba" tayi sauri ta dira daga gadon,bayan ta idar hira sosai suka yi kafin yunwa tasa su tashi suka fita zuwa gidan mother..

#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
©®2021.





*♡MANAR¸.•💥*





*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://t.me/joinchat/VHlmxxheyxG6m9VoUJZbZA


_Devoted to My Mamma Hjy Maryam Alhassan (Jikar Kulu)._

_Bestowed to Fateema Abdulmajid._




08.


#Their origin..

Hjy Asama'u zaune gaban bokansu ita da Hjy Izzatu cikin tsananin tashin hankali bayan ya gama musu bayanin matsalar dake tunkarosu,Hjy Asama'u tace "gaskiya Boka a san yadda za'ayi a juya lamarin nan,idan da hali ina son a cire tunanin yarinyar gaba d'aya daga zuciyarsa a cusa masa tsanarta" Wani k'ak'k'arfan dariya Bokan ya saki sanda yayi iya yinsa da wani irin murya mai ban tsoro yace "wannan ba mai yuwuwa bane,tun farko na fad'a miki,d'anki bazai tab'a jin tsanar yarinyar ba kome za kiyi,soyayyar da yake mata ba abune mai sauk'i da za mu iya rabasa da ita ba" cikin tsananin tashin hankali Hjy Asama'u tace "ni dai Boka kayi wani abu akai,wallahi ko mutuwata ban tsana kamar yadda na tsani yarinyar ba,ni dai idan da taimakon da za ka iya yi kayi ka raba su" directly yace "ki canja wani k'udurin" Hjy Asama'u kamar za ta d'ora hannu aka ta runtuma ihu tace "yanzun boka me kake ganin za ayi?" Wasu irin surutan tsafi ya fara kafin ya kafeta da idanunsa da suka juya,lokaci d'aya yayi shiru idanunsa suka yi wani irin jaa mai ban tsoro gumi duk ya wanke masa jiki,bakinsa yana fitar da bak'in hayak'i yace "akwai hanya d'aya.. Sai dai itama babu tabbas" bakin Hjy Asama'u har b'ari yake ita da Hjy Izzatu wajen tambayarsa "wane hanya ne?" Yace "hanyar shi ne idan har kina son su rabu sai dai idan aure za kisa d'anki yayi,muddin ya bar gidan shi kenan" wani gagarumin ajiyar zuciya tayi tace "idan aka yi haka shi kenan an cire masa ita daga zuciyarsa?" Boka ya kece da dariya yace "ba shi kenan ba" hankalin Mama ida ya kai d'ari ya kai k'ololuwa gurin tashi cike da sarewa tace "sai me kuma?" Yace "Mu nan da bak'ak'en shaid'anu muke aiki,abune mai matuk'ar wahalar gaske mu iya cutar da ita ta ko wane irin fuska,rabasu abune da ya gagari iyawarmu.. Akwai wani sirri tattare da yarinyar,wanda duk k'ok'arin da muke da bincikenmu wajen gano kan al'amarinta abubuwa sun faskara,sun kasa fitowa yadda za mu gane,ko yaushe muka yi bincike haske kad'ai muke gani,sannan wani abu guda yarinyar nan baza ta tab'a fita zuciyar yaron ba,yau ko gobe,yanzu ko anjima tabbas d'anki zai zo da buk'atar yana son aurenta,abune da yake zane cikin zuciyarsa,soyayyar da yakema yarinyar da wuya ya goge daga zuciyarsa,wannan wani k'uduri ne da komai sauyawar zamani wata rana wannan burin zai cika.. Kada ki manta da wannan maganar.." Mummunan fad'uwa gaban Mama ya dunga yi bakinta da jikinta suna b'ari,hawaye suna sauka fuskarta a hargitse cikin gushewar hankali take fad'in "kada ka bari haka ya faru boka,wallahi da kai kad'ai na dogara,ba ni da mafita sai ta ka,ka taimake ni kada su yi nasaran rabani da d'ana.." Zane² yayi cikin iska kafin ya kalli Mama yace "me kike so ayi miki?" Tace "ba na son maganar aurensu nan" yace "idan har ba kya son yazo miki da maganar kiyi gaggawar nema masa mata" cikin sauri ta gyad'a kai tana share hawayen da suka b'ata mata fuska tace "zzzz... Zanyi wallahi,zan nema masa da gaggawa ma" Boka yace "sannan akwai wani abu guda" da sauri Mama tace "mm.. Mene ne shi?" Yace "kun san wanda za ta aura gaba idan an raba ta da d'anki?" Hjy Asama'u tayi sauri tace "duk ma wanda za ta aura Allah gafarta boka taje ta aura mana tunda dai ta rabu da d'ana ai shi kenan,ni d'ana kad'ai ne ba na son ta rab'a,koma waye taita auransa me zai dameni?" Hjy Izzatu ta kara da cewa "koma meye zai faru mu bai dame mu ba,ta auri koma waye" a nan suka bashi kud'ad'e masu ciwo tare da alkawarin idan wata matsala ta taso zai gansu,sanda suka taho a hanya suke sake tattauna maganar cike da sanyin jiki Mama tace "idan har hak'anmu zai cimma ruwa babu matsala,ni zan k'arasa sauran aikin.. Matuk'ar dai ace ina numfashi bazan tab'a bari ahalin Maryam su kusance ni da y'ay'ana ba" Hjy Izzatu ta gyad'a kai tace "ai baima kamata mu bari wannan alamari ya faru ba" har suka k'araso gida maganar da suke yi kenan.


*Flashback...*

Malam Usman Ibrahim Maji dad'i shi ne asalin head na family'n,asalinsa bafulatanin garin Maiduguri ne,da ya fito daga garin Bama,mutum ne shi mai hak'uri da sanin ya kamata,a bangaren sha'anin iyali kuwa mutum ne mai matuk'ar k'ok'ari wajen ganin ya kyautatawa iyalinsa tare da sauke hak'k'ok'in da suka rataya wuyansa,matarsa d'aya Zainab wanda ake kira *AZUMI* tun auren saurayi da budurwa,sai dai ita Azumi ko kad'an ba ta da hak'uri mace ce ita mai mita musamman idan aka tab'a ta,za ta iya wuni sur tana mitar abu,Allah ya azurtasu da yara uku Ibrahim khaleel shi ne babba wanda kunya irin na Fulani yasa Azumi ba ta iya kiran sunansa sai dai ta kira shi da Yaro,sai mai binsa Muh'd,sai autarsu Hafsah wanda daga kanta ne haihuwa ya tsaya musu,tun suna yara sun taso cikin gata da soyayyar iyaye,mahaifinsu Malam Usman ya kasance manomi,dai² gwargwado ubangiji ya arzuta shi ta inda bai bar iyalinsa sunyi kuka ba da rashin wani abu,haka wanda duk Allah ya had'asa zama da su bakin iyawarsa da abunda Allah ya hore yakan taimaka ma wanda suka fishi buk'atar taimako. Duk da Malam Usman baiyi karatun boko ba lokacin da yaransa suke tasowa cikin hukuncin ubangiji sosai ya kwad'aitu da son ganin yaransa sun samu ilimi both ilimin addini da na zamani (boko),da yake shima malami ne bakin gwargwado yana da nasa sanin akan ilimin addini shi yake karantar da su ta wannan b'angaren,a gefe d'aya kuma ya sasu makarantar primary ta nan garin Bama,lokacin ko da Muh'd ya gama secondary,lokacin da sakamako jarabawar SSCE ya fito kai tsaye ya gwada yana son makarantar sojoji,a nam malam Usman yayi duk shige da ficensa ya sama masa makarantar sojoji ta Biu dake cikin garin Maiduguri,nan fa gida ya rage daga Hafsah sai Yaro,tsayin lokaci suna rayuwarsu a garin Bama ba tare da ko wane irin matsala ya gifta musu ba,rana tsaka sai ga rigimar boko haram ya taso a garin Maiduguri,bayan b'arna gami da kashe²,salwantar rayukan al'umma da dukiyoyinsu,Malam Usman ya kasa samun nutsuwa da zamansu a garin,da yake kuma duka iyayensa Allah ya musu rasuwa da jimawa,ganin ba shi da sauran dangi sai y'an uwa na nesa,wannan dalilin yasa shi tattaro kan iyalinsa da dukiyarsa da tayi saura suka yi hijira zuwa garin Kano,a nan ya samawa kansa matsuguni Hafsah da bata gama secondary ba ya nema mata makarantar gwamnati ta ci gaba da zuwa,tun da suka dawo Kano da yake babu wani sana'a da Malam Usman d'in yake yi sai y'ar dukiyarsa da ya k'ullo,a ita suke ci su sha har ma su biyawa kansu buk'atun yau da kullum. Bahaushe kan ce "zara ba ta barin dami" haka ce ta kasance ga Malam Usman da iyalinsa kasancewar babu wanda suka sani a cikin garin Kano kawai dai suna rayuwa ne daga su sai halinsu,bayan wani lokaci ba tare da sun farga ba,y'an kud'ad'e da duk wasu kaya masu sauk'in kud'i da suka zo da shi duk suka k'are,abincin da za suci ya fara gagararsu samuwa,a nan ne hikima ya zowa Malam d'in inda yasa yaransa maza a gabs suka bazama neman abun yi,sune can yau,idan sunga ba'a dace ba gobe su nufi can,duk abunda ya kama idan har za su samu to fa babu girman kai za suyi,hatta sharar rumfunan kasuwa zuwa cikin shaguna idan har aka kira su za suje su yi ko aike,d'an abunda suka samu shi za su tattara su sayi abinci,washe gari idan sun samu kwatankwacin abunda ya faeu jiya haka za su sake yi,sun sha zuwa kasuwa a k'afa su koma a k'afa idan sun gaji su samu guri su huta,malam USMAN yakan ce "suyi hak'uri su jurewa duk wani k'unci,hak'ik'a dukkan tsanani yana tare da sauk'i,dan haka wata rana sai labarimm" sau da yawa idan yana fad'an haka yaran sukan yi dariya suce "da wuya wannan lokacin ya riske mu baba" sai yayi murmushi yace da su "kadaku taba yanke tsammani da samun rahamar Ubangiji, kudai ku ci gaba da hakuri,hak'ik'a nasarar Allah tana nan zuwa a kusa.." Da sun ji ya ce haka sai suce "ko yaushe cikin tsammanin zuwanta muke" sai yace "ku dai kuci gaba da addu'ah,ku mik'a dukkan lamuranku ga Allah,hak'ik'a Allah mai ji ne kuma Mao gani.." Kamar yadda yake fad'a,cikin haka Allah ya had'a Malam Usman da wani mutum da ake kira Alh Yakubu Na Abba,kasancewarsa mutum ne sananne a cikin garin Kano ta b'angaren harkar da ya shafi kasuwanci,kusan duk kasuwannin kano da wahala baka ji an ambaci sunansa cikin wad'anda suka mallaki shaguna ba,Allah ya bashi tarin dukiya da ilimi dai² gwargwado,a b'angare guda kuwa duk wannan d'umbin arziki da Allah ya yiwa wannan bawa nasa,tsayin shekaru tun aurensa na faei Allah baisa an tab'a ko da b'atan wata a gidansa ba,da yawan lokaci bisa shawarar da aka basa ya sha auren zawarawa da yaji labarin sun haihu a wani gidan,ba don komai ba sai don yana sa rai akan ko Allah zai sa a dace ya samu k'aruwa ta b'angarensu,sai dai fa da zaran ya aura d'in idan aka shigo sai dai yaji shiru babu wani labarin da zai sake biyowa baya,wannan dalilin yasa Alh Yakubu yake rik'on y'ay'an y'an uwansa,yakea kyautata musu kamar shi ya haifesu,ana cikin haka ya auro wata matan da ake kira Hjy Ladi,ta zo da yaranta biyu duka mata,Asama'u itace babba sai k'anwarta Rabi,Hjy Ladi ta kasance irin matan nan masu shige² da masifar fad'in rai,lokacin da mijinta mahaifin su Asama'u ya rasu ko da labarinta yaje kunnen Alh Na Abba nan take ya nuna yana ra'ayinta,ba tare da tunanin komai ba ya aika magabatansa gidansu,mahaifinta dattijon arziki ya nemi da su ba shu lokaci ya tabbatar idan babu matsala,bayan tafiyarsu Malam Jauro ya kira y'arsa ya tambayeta ko tana son Alh Na Abba,take a nan ta amsa saboda tun kafin lokacin take jin labarin sa,abu na biyu kuma dukiyarsa wanda ita ce ummul'aba'isin da yasa ta amsa ba tare da jinkiri ba,Malam Jauro ya aikawa wakilan Alh Na Abba a nan aka tsayar da lokacin bikinsu,bayan aure ko da ta shiga gidan ta tarar da mata uku inda ta zo a cikon ta hud'u,yadda Alh Na Abba yake sakar musu dukiya komai a wadace ba kamar gidan tsohon mijinta ba da ta rasu,a nan k'arya ta k'aru,ita da y'ay'anta suka fara jin kansu,har ya zama sun fi asalin y'ay'an y'an uwan Alh Na Abba fank'ama da nuna su wasu ne,gurin shige² da yawon Hjy Ladi ta had'u da wata hatsabibiyar mata a nan mak'otansu mai suna Hjy Zubaida,a hankali Hjy Ladi ta fara shiga jikin Hjy Zubaida har suka d'an fara sabawa,sanda Hjy ladi taga yadda mijin Hjy Zubaida yake mata rawar jiki,duk abunda tace yana b'arin jiki yake yi,wannan abu ya ja hankalin Hjy Ladi ta k'ara k'aimi wajen shiga jikin Hjyr suka zama k'awaye sosai,ta haka suka san da yawa daga sirrin juna,hatta malaman da suke ma Hjy Zubaida aiki sai da ya zama sun san da zaman Hjy Ladi,Hjy Zubaida ta gabatar da ita a gurinsu,y'ar Hjy Zubaida d'aya Izzatu wadda take tsaran Asama'u,bayan had'uwar Hjy Ladi da mahaifiyar Izzatu Hjy Zubaida,da amincin da ya shiga tsakaninsu yasa suma suka zama k'awaye har ta kaisu ga zama aminai kamar iyayensu,lokacin da Hjy Ladi ta k'wace kambun gidan Alh Na Abba komai da kowa ya dawo k'ark'ashinta,ya zama ita kad'ai take sawa ayi kuma ita take hanawa ak'i yi,gaba d'aya y'ay'an y'an uwan Alh Na Abba da suke gidan sai da ta san yadda tayi duk suka koma gidajen iyayensu,dangi gaba d'aya suka daina zuwa,ta nesanta shi da kowa da komai,hatta matansa da ta shiga ta tarar sai da ta fitar da su,gida ya dawo daga ita sai y'ay'anta kad'ai suke rayuwa suke kuma murza zaren su son ransu. Asalin alak'ar Alh Na Abba da malam Usman wata rana cikin irin ranakun da Alh Na Abba yake zuwa kasuwa duba rumfunansa,a lokacin ana tsanain rana da zafi,shigarsa kasuwa ke da wuya yana kan zagayen shagunansa,ya hangi Malam Usman da yaransa suna shara,bayan wani lokaci ya sake zuwa kasuwar da niyyar duba yadda harkoki suke tafiya ya sake ganin Malam Usman sunyi wujiga² suna zaune,a ranar ko karin safe basu yi ba suka fito,a nan yake tambayar wani yaronsa Malam Usman suka sanar masa y'an gudun hijira ne daga garin Maiduguri,tausayi da son taimako irin na Alh Na Abba lokacin da zai barar kasuwa,ya aika aka kira masa Malam Usman,bayan zuwansa suka gaisa Alh Na Abba yace "Malam shin idan na baka aiki za kayi?" Malam Usman yace "sosai kuwa Alh" Alh Na Abba yace "wane irin alk'awari za ka iya yi min da zai gamsar da ni kai mutumin arziki ne,baza ka ha'ince ni ba?" Malam Usman yace "a'a Alh bazan iya yi maka alk'awari ba,amma dai tabbas zan kula maka da dukiyarka tamkar yadda zan kula da nawa" jin abunda Malam usman ya fad'a Alh Na Abba yayi murmushi yace "Yanzu kam na gamsu da yabon da naji ana yi akan ka,daga yau kai da yaranka za kuna zama cikin shagunan da nake da su cikin kasuwar nan" cikin tsananin farin ciki Malam Usman ya yiwa Alh Na Abba godiya har kamar zai durk'usa masa,Alh Na Abba yace "babu komai,daga yanzu ma kuna iya fara aiki" Malam Usman yace "sai dai wani hanzari ba gudu ba" Alh Na Abba yace "akwai wani matsala ne?" Malam Usman yace "idan babu damuwa ni zan fara zuwa,su yaran su ci gaba da zuwa makaranta,ranakun da suke hutunka k'arshen mako

9 / 66