Manar Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Fatima Category :  Romance

Chapter   2 / 66

3K to 6K   out of 196.2K words

kai tace "Allah sawak'e" ba dan ta yarda da abunda yace ba ta nemi guri cikin parlon ta zauna ta d'auki remote tayi powering TV,juyawa yayi ya kalli direction d'in da Manar take tsaye har sannan ya aika mata mugun kallo kafin ya d'auke kai,Amaar da ya kula bata biyoshi ba ya waiwayo,tsaye a k'asa ya hangota ba ta da niyyar tahowa ya girgiza kai yace "Manar! Me kika tsaya kallo?" Saurin juyawa tayi ta bi bayansa,yayi knocking k'ofar bedroom d'in,daga ciki aka basu izinin shiga,tura k'ofar yayi ya shiga da sallama,ta bisa a baya suka shiga tare,y'ar kyakykyawar budurwar dake tsaye wacce baza ta wuce sa'ar Manar ba tana nad'e kayan dake zube saman gado ta waigo ta amsa,tayi masa murmushi tana ci gaba da nad'e kayan tace "Yaa Amaar aunty tana nemanka" yace "where's she?" Tace "tana toilet" Manar ta lek'o daga bayansa tana sakin murmushi tace "Marhaba uktiiy!" Saurin waigowa ta yi jin magana kuma,she thought shi kad'ai ne ya shigo da farkon,dai² lokacin Amaar ya wuce gaban mudubi yana shirin janyo kujera ya zauna,idanunta suka sauka kan Manar dake tsaye tana kallonta sai murmushi take mata,wani ihu ta fasa ta saki kayan hannunta da gudu ta taho suka rungume juna,daga toilet Aunty da ta jiyo ihunta tayi magana "Ameerah! Kin samu tab'in hankali ne kike min ihu?" Cikin farin ciki tana rik'e da hannun Manar tace "Aunty u know what?" Aunty tace "sai kin fad'a" tayi murmushi tace "surprise! Fito kiga" tsaki Aunty tayi saboda sanin shirmen Ameerah,ta gama d'aura alwala ta bud'e k'ofar ta fito,tsaye tayi a door way ta dunga kallon Manar da mamaki tace "daughter! Ke ce da gaske?" Tashi Manar tayi da sauri ta k'arasa ta shige jikinta,Aunty ta rungumeta back tana sakin murmushi tace "saukar yaushe?" Manar tace "yanzu!" Gyad'a kai Aunty tayi ta fara amsa gaisuwar da take mata tana shafa kanta,suka k'arasa bakin gado tana rik'e da hannunta suka zauna,Amaar dake zaune yana danna waya ya d'ago ya kallesu,kafin yayi magana aka turo k'ofar,duka suka juya suka kalli gurin,Dadda ta tsaya gurin fuskarta babu fara'a tana kallon Manar tace "yanzu idan ba iya shege ba,daga zuwa har kin taho gantali,ni kike nufin zan gyara miki gidan?" Tsuke fuska Manar tayi ta d'auke kai tak'i cewa komai,Aunty tayi murmushi tace "sannu da zuwa Hjy" wani kallo Dadda tayi mata kafin tace "yawwa" fuska babu wadataccen fara'a ta ci gaba da mita "ka ga yarinya kamar ba da ita nake magana ba ta manna min hauka.. To kin yiwa uwarki shiru.." Dariya Ameerah ta fara tace "sannu da zuwa Dadda" ko tankata bata yi ba,ta zubawa Manar ido da tak'i kallonta,a fusace tace "wai ba dake nake ba kika k'i kula ni?" Manar ta juyo ta kalleta tace "me zan miki tou?" Dadda tace "da kika taho kika barni ni baiwar uwarki ce ko ta ubanki?" Kicin-kicin Manar tayi ta tsuke fuska itama tana yiwa Dadda wani kallo ta gyad'a kai tak'i cewa komai,a fusace Dadda tace "wallahi tunda kika min haka sai dai ki tafi gurin uwarki dama,baza ki kwanar min a gida ba" murmushi Aunty tayi tace "kiyi hak'uri Hjy bari a tura maids su gyara" saurin washe baki Dadda tayi hakor'in makkan ta suka bayyana tace "to babu laifi,dan dai ni kam dama bazan iya wannan aiki ba daga zuwa na" Aunty tayi murmushi tace "ki shigo ciki Hjy kafin a gyara muku part d'in" saurin girgiza kai tayi tace "a'a a'a! Barni a nan ma tafiya zanyi nasa musu ido,na baro kaya uban dukiyarmu idan ba na gurin ai sai su samu damar sacewa" tagumi Amaar yayi ya zuba mata ido,Aunty tayi murmushi tace "baza su sace ba Hjy ki shigo har su gama" juyawa Dadda tayi fuska a tsuke tace "yau naji jaraba,mutane sai musun bala'i.. Ni dai na tafi bazan zauna ba aje a cuceni" dariya Ameerah ta fashe da,Manar ta tab'e baki ta d'auke kai,Aunty ta tashi da sauri ta fito,a parlon k'asa ta tarar da matar d'azu ta k'araso tana sakin murmushi tace "sannu da hutawa Hjy" wani kallo matar tayi mata kamar ana mata dole ta amsa "yawwa!" Daga haka ta d'auke kai,Aunty tace "kin san Hjy ta dawo?" Bata kalli direction d'in Aunty ba tace "ehh! Da wani abu ne kuma?" Aunty tace "thought ko bayan ta fita kika sakko" ta girgiza kai tace "not at all.." Gyad'a kai Auntyn tayi itama ta wuce hanyar kitchen da take jin motsi,a bakin k'ofa ta tsaya tayi sallama,maids uku dake ciki suna aiki suka amsa suna gaisar da ita,dattijuwa d'aya sai y'an mata biyu,ta amsa fuskarta a sake tace "idan aikin da kuke yi babu yawa Haulatu ke da Ruqayya kuje b'angaren Hjy ku gyara da sauri" amsawa suka yi suka fito,y'ar dattijuwar ta ci gaba da aikin,Aunty ta juya ta bar gurin matar dake zaune parlor ta bita da wani kallo ta tab'e baki,a k'asa Aunty ta tsaya ta rad'oma Ameerah kira,da sauri ta fito tana daga sama tace "ga ni Aunty" Aunty ta mata wani kallo tace "ni kike so na zo na same ki a nan?" Ta fara sakkowa da sassarfa tace "i'm sorry" Aunty tace "ina Manar d'in take?" Tace "tana sama" tace "maza kira min ita kuzo tare" komawa tayi saman,suka dawo tare da Manar,Aunty tace "maza wuce dining kici abinci" satar kallon matar dake zaune tayi,suna had'a ido ta sunkuyar da kanta da sauri ta girgiza kai tace "a'a na k'oshi" wani kallo Aunty tayi mata tace "na fara miki wasa kou?" Murmushi ta d'ago tana yi,aunty ta had'e rai tace "wuce kafin na sab'a miki" girgiza kai ta sake yi kamar za tayi kuka tace "Allah Aunty ba na jin yunwa,ni gida zanje wajen mother" kallonta Aunty ta dunga yi ta fahimci dalilin k'in cin abincin da bata son yi tace "baki je ba dama?" Ta gyad'a mata kai da sauri tace "nan na fara zuwa" Aunty ta gyad'a kai tace "alright Ameerah maza kuje ki rakata" Ameerah dake tsaye har sannan tace "Aunty kayan fa ban gama ba" tace "kuje zan k'arasa" amsawa suka yi suka juya za su tafi,matar dake zaune tun d'azu bata ce musu komai ba ta tab'e baki tace "son a sani.. Wai gaida uwar miji a kasuwa" tsaf Aunty ta fahimci magana ta yar mata,tayi murmushi ta juyo tana kallonta tace "ai ba wani abu bane dan ka gaisheta ko da a taron arfa ne ba a kasuwa kad'ai ba" tab'e baki Mama tayi tace "a'a ke dai kike ganin ba komai bane yin hakan,amma wannan ai dangin shishshigi ne" wani murmushi Aunty tayi tace "haka ne kam.. Sai dai shi kansa shishshigin ma iyawa ne,idan wani yayi an yaba wani idan yayi shegen duka zai ci.."


  
     _#Maa sha Allah! I'm back again by Allah's grace... Hope u guys will love the book. Don't missed it! Yanzun za'a fara._

      #2 be continue 1st/Jan,2021.

   
#Share pls.
#Asli Smasher.
#19/Dec,2020.A.D.
💠💠💠💠💠
©®2020.


                    *♡MANAR¸.•💥*
               

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://t.me/joinchat/VHlmxxheyxG6m9VoUJZbZA 

_Devoted to My Mamma Hjy Maryam Alhassan (Jikar Kulu)._

_Bestowed to Fateema Abdulmajid._

*FROM THE WRITER OF*
-Maktoub
-D'an mace
-Alk'awarin jini
-Wani al'amarin
-Zab'in wa zan bi?
-Bambancin al'adu
-Ina mafita?
-Y'ar garuwa
-Rayuwar wani
-K'azafin kisan kai
-K'addara ko sakaci?

                                02.

#Disliked..
 
   
      Wani shegen kallo Mama ta dunga aikawa Aunty fuskarta a d'aure tace "me kike nufi Bebie?" Dariya Aunty tayi tace "ya za ki tambayeni bayan kinfi kowa sanin abunda nake nufi?" Mama ta dunga gyad'a kai tana kallonta kafin tace "okay! Ta nan kika b'illo?" Aunty tayi dariya ba tare da ta sake cewa komai ba ta wuce za ta koma sama,Mama ta d'aga murya tace "da kin zauna ai munyi.. In banda shishshigi ma har akwai wata uwar mijin da zan dunga ma rawar jiki? In ba neman wurin zama da son a sani ba" juyowa Aunty tayi saurin yi ta kalleta tace "kin ji ai inda aka samu matsalar,da kin san darajar mahaifiya tabbas baza ki k'i nunama uwar mijinki so ba,sannan baza ki k'i yi mata kallon mahaifiya ba" cikin sauri Mama tace "me kike nufi?" Aunty tace "ohoo! Dubawa za kiyi" ta wuce ta barta nan kamar za ta fashe tsabar b'acin rai. Suna fita Manar ta kalli Ameerah tace "wai ina su wad'ancan suke?" Ameerah tace "su wa kike nufi?" Tana squeezing fuskarta tace "ya-ma sunan su?" Dariya Ameerah ta fara yi kafin tace "wai kina nufin kin manta sunan su?" Seriously ta gyad'a mata kai,Ameerah tace "lallai Manar d'an tafiyar nan shekara hud'u har yasa kin fara manta mutanen gidan nan?" Kicin² Manar tayi tace "to ki tuna min mana kuma" Ameerah tace "Deejah da Diyanah" kyab'e baki tayi tana gyad'a kai tace "Mmm!" Daga haka bata sake cewa komai ba suka k'arasa apartment d'in,suna tsaye balcony ta hango fitowarsa daga part d'in da suka baro,ta zuba masa idanu tana kallonsa sanye yake da k'ananun kaya sai sauri yake ya nufi parking space,Ameerah tayi knocking k'ofar tana yiwa Manar tambayar "Sis! Wai kuma za ku sake komawa Saudi?" Manar bata kalleta ba tace "Ehh!" Ameerah tace "when?" Juyowa tayi saurin yi lokacin da taga fitarsa daga gidan tana squeezing fuskarta tace "ni ki min da hausa ban gane ba" Ameerah tayi murmushi tace "sai yaushe?" Hannuwa ta watsa tace "ohoo! Nima ban sani ba,sai lokacin da Dadda tace" Ameerah ta gyad'a kai tace "alright!" Sake knocking tayi ganin ba'a bud'e musu ba har lokacin,daga ciki akace "ana zuwa.." D'an yaro ne k'arami bazai wuce 5yrs ba ya bud'e k'ofar,Manar ta kallesa tayi masa murmushi,tace "marhaba akhul'sagir" wani gwalo ido yaron yayi da gudu ya koma cikin karad'i yana fad'in "Mother ga aunty ta zo" kyakykyawar matar dake fitowa daga bedroom wadda baza ta wuce 47yrs ba d'auke da yarinya a kafad'arta kana kallonta za ka hango kamar da suke da yaranta dake nan a parlon suna faman TV game,tana kallon yaron tace "wace Aunty'n?" Yace "Auntyn mu ta saudiyya ce suka zo" juyawa tayi saurin yi tana amsa sallamarsu,idanunta akan Manar tace "yaushe kuka zo?" K'arasawa tayi ta karb'i baby girl dake hannun mother tace "ba'a dad'e ba" mother ta gyad'a kai tace "sannu ya hanya?" Gaisar da ita Manar ta fara yi,ta amsa sai kallon yadda ta k'ara girma take,Ameerah ma ta gaisheta ta amsa,mother ta juya tana kallon yaran y'an matasa su kusan biyar da suka cika parlon da ihu tace "Mu'awiyah! Maza ku kashe game d'in nan haka" saurin kashewa suka yi suka taso suna yiwa Manar sannu da zuwa,sai murmushi take yi tana kallonsu,mother ta mik'e tayi hanyar kitchen ta barsu a parlor,abinci ta fito musu da shi dining,tana kallon su tace "kuzo kuci abinci" Ameerah tace "ni dai mother i'm full" saurin tashi Manar tayi ta nufi dining d'in bata yi magana ba,Ameerah da ta karb'i baby a hannunta ta bita da kallo baki sake tace "kai Sis! Yanzu fa Aunty tace kici abincin kika k'i" wani kallo ta juyo ta mata tace "to ina ruwanki da ni?" Ameerah tayi dariya tace "Allah baki hak'uri amma dai ki dunga fad'ar gaskiya" b'ata rai Manar tayi tace "to baki ga wancan matar tana gurin ba" Ameerah ta bud'a idanu tace "wace ce matar da take gurin?" Manar ta zumb'uro baki tace "Mamar su Yaya mana" tsawa mother tayi mata tace "iskancin da kika koyo kenan? Hjy Asama'un kike cema haka?" Manar ta d'ago tana kallon mother kamar za tayi kuka ta kasa magana,mother tace "dake nake kika tsare ni da kallo" sunkuyar da kai tayi ta zumb'uro baki,mother ta fara mata fad'an ba ta son rashin kunya,Manar ta fashe da kuka ta tashi da gudu ta fita,Ameerah tana kwalo mata kira bata tsaya ba ta tashi da sauri za ta bita mother tace "d'auki abincin ki kai musu daughter,kice ina gaida Hjy,ina mata barka da zuwa kafin na shigo" Ameerah ta amsa ta d'auki warmers d'in dake cikin wani folded basket ta fita da sauri,a parlor ta tarar da Manar kwance kan kujera tana kuka,ta kalleta ta ajiye basket d'in,Dadda ta fito daga d'aki tana fad'in "waye yake kuka kuma a nan ni Azumi?" Ameerah ta juya tace "Manar ce" saurin k'arasowa Dadda tayi har kamar za ta fad'i tsabar sauri tana sakin salati tace "me aka mata kuma?" Ameerah tace "ita da mother ne" wani kallo Dadda tayi mata tace "wace ce haka kuma?" Ameerah tace "Aunty Mammy" mitsi² Dadda tayi da idanu,bata tsaya sauraren abunda take fad'a ba tayi waje,kamar za ta b'alle k'ofar take bubbugawa,mother dake zaune tana bawa jaririyarta nono ta jiyo bugun ta kwalo ma Mahmoud kira,ya fito daga d'akinsu yace "here i'm mother" tace "je kaga waye yake bugun k'ofa" amsawa yayi ya wuce,yana bud'ewa Dadda ta kalleshi fuskarta a tsuke bata ko amsa gaisuwar da yake mata ba ta fara tambayarsa "Ina ita uwar taku take?" Yace "tana ciki" wucesa tayi ta shigo,mother dake zaune ta d'ago kai tace "sannu da zuwa Hjy" kicin² tayi tace "ba sannu da zuwanki nake buk'ata ba,zuwa nayi naji me yarinya tayi miki daga zuwa za ki sa ta kuka?" Mother ta saki baki tana kallon Dadda tace "wani abu taje tace na yi mata?" Dadda ta tsuke fuska tana mata wani kallo tace "ni ya za'ayi na sani? Zuwa nayi dai naji dalilin kukan nata" a hankali mother ta sauke ajiyar zuciya tace "babu abunda aka mata" wani kallo Dadda ta dunga aika mata tace "ba'a mata komai ba za taje min tana kuka? Wallahi ahir d'inki Maryam,ki fita idanuna na rufe,akan yarinyar nan zan iya sab'awa ko waye,ni ba na son haka daga zuwanmu dan neman rashin son zaman lafiya za ku fara sa yarinya kuka,ni sai na hanata zuwa gurin ki idan abunda za ki na mata kenan,ko nasa ta a gaba mu koma inda muka fito" fad'a sosai Dadda ta dunga yi kamar za ta aro baki,mother ta sauke numfashi tace "kiyi hak'uri Hjy in sha Allah baza'a kuma ba" Dadda ta juya a fusace tace "zai fi miki dai" tana fita mother ta rufe idanunta cike da takaici,tayi shiru tana tunanin anya idan tayi shiru ta zuba ido akan tarbiyyar Manar ta yi dai²? Abun yana damunta ba tun yanzu ba,kawai kara take yi ta zuba musu idanu,ba komai take iya d'aga ido ta kalla ba musamman idan ya shafi Manar. A parlor Dadda ta samesu Amaar ya shigo suna hira,ta kalli Manar dake b'ab'b'aka dariya ta washe baki hakor'in makkan ta suka fito tace "yawwa! Saki ranki takwara,yanzu na je na samu Maryam d'in na mata tatas,baza ta sake miki abunda za kiyi kuka ba har mu koma" sakin baki Manar tayi tana kallonta gabanta sai fad'uwa yake a tsorace tace "me kika je kika ce mata?" Dadda ta fara rattabo mata jawabin duk abunda tace,Manar ta dunga kallonta kamar za tayi kuka,da sauri ta tashi ta fita daga part d'in,karo suka kusa yi da Waleed a balcony yana k'ok'arin shigowa ya rik'eta da sauri yana mata wani kallo yace "ba kya kula idan kina tafiya ne?" Idanunta sunyi rau² ta rik'e masa hannu a tsorace tace "Yaya dan Allah muje ka rakani" kallonta yayi fuskarsa a d'aure yace "ina zan raka ki?" Hawaye suna sakkowa fuskarta tace "zan je na bawa mother hak'uri" wani kallo yayi mata yace "laifin me kika yi?" Tana share hawayen fuskarta a shagwab'e tace "to ba Dadda bace dan ta ga ina kuka taje.." Wani kallo ya dunga mata fuskarsa a d'aure ya mata tsawa "kauce ki ba-ni guri kafin na mareki" wani irin kuka ta fashe da shi da sauri ta fizge hannunta ta wuce da gudu ta nufi part d'in,ya juya yana kallonta sanda ta kusa shigewa ya sauke ajiyar zuciya then ya biyo bayanta,gently kamar mai counting steps d'insa yake tafiya ya bud'e k'ofar ya shiga da sallama,fad'a sosai ya tarar mother tana mata,ya samu guri ya zauna mother ta dakata suka gaisa,a hankali yana kallon Manar dake kuka yace "kiyi hak'uri mother in sha Allah baza ta kuma ba" girgiza kai mother tayi cike da takaici tace "Waleed al'amarin Manar da grandma d'inku ya fara damuna,ban san yaya zanyi ba,duk sanda yarinyar nan za tayi laifi ayi mata fad'a kakar ku tana jin labari za tazo ta maka tatas,akan yarinyar nan wane irin cin mutunci ne bama gani,yarinya sai kace ita kad'ai aka haifa,fisabilillah yanzu shi kenan duk abunda za tayi sai dai a sa mata ido,babu wanda ya isa ya mata gyara idan tayi ba dai² ba?" Waleed yace "kiyi hak'uri in sha Allah za a san yadda za'ayi" mother cikin takaici tana kallon Manar dake matsar idanu tace "itama kuma da yake makira ce kana mata fad'an abunda take yi sai ta b'are baki ta kwasa taje ta fad'a mata.. Gaskiya na gaji da abubuwan da suke faruwa akanta,duk ranar da naga babu haza billah za'a neme ni a rasa cikin gidan nan,bazan iya ci gaba da zaunawa ina kallon b'acin rai ba" hak'uri Waleed ya dunga ba-ta sanda yaga ta d'an sakko kafin ya kalli Manar dake zumb'uro baki a tsawace yace "baki iya bada hak'uri ba ne?" D'agowa tayi tana kallonsa tak'i cewa komai,ya zuba mata ido yana kallonta,ta d'auke kai kamar ba da ita yake ba tana hararan wani guri,bata yi zaton ya ga abunda tayi ba sai ji tayi ya ba-ta rankwashi,ta dafe gurin da sauri a gigice tace "kiyi hak'uri mother" mother ta dunga mata wani kallo cike da takaici ta kasa mata magana,ran Waleed ya b'aci sosai but haka yayi k'ok'ari ya danne ganin a gaban mahaifiyarta ne bai mata komai ba,ya bawa mother hak'uri,sanda ta nuna masa babu komai² ya wuce,yayi mata sallama ya tashi zai fita,a baya Manar ta biyosa,suna fitowa balcony ya tsaya ta d'aga kai tana kallonsa kamar za ta sake sakin wani kukan,fuskarsa a had'e yana mata wani kallo yace "ke! Babu wanda ya isa da ke? Ba ki da wanda za su fad'a miki kiji ko?" Zumb'uro baki tayi tak'i cewa komai,ya mata tsawa yace "ba dake

2 / 66