Manar Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Fatima Category :  Romance

Chapter   31 / 66

90K to 93K   out of 196.2K words

kallo tana share hawayen dake zubowa daga idanunta,a hankali ta koma ta zauna a bakin gado tana sauke ajiyar zuciya,ko minti biyar ba'ayi ba da fitar Waleed daga gidan Dadda ta dawo d'akin tace "tashi muje Yaro yana son ganinki yaji laifin da kika yiwa mutumin can,yau dai in sha Allahu in munyi sa'a ya yi mana iyaka da shi,ina murna ya yi aure,zan rabu da saka ni maganar da yake zuwa yi,ya ce shegiyar tukuna ma da duk ban sa ki magana ba" kallonta Manar tayi saurin yi tace "ni dai wallahi babu inda zanje,haka kawai ke kamar an saka ki daga abu ya faru sai kice za ki kaiwa Abba k'ara,naga dai bai min komai ba,ni ce ma na masa laifi d'azun shi sa,kuma na ma basa hak'uri" sakin baki Dadda tayi tana kallonta,Manar ta mik'e ta nufi k'ofa tana cewa "ke komai akayi sai ki d'auka kije ki sanarwa Abba,baza ki jira kiji abunda ya faru ba" daga haka ta fice daga d'akin tana zumb'uro baki ta bar Dadda a tsaye sororo ta fice ta bar mata gidan ma gaba d'aya because she knew idan ta zauna yau mitar da Dadda za ta mata kan abunda tayi ko bacci ba lallai ta barta tayi ba..



#Kuyi addu'ah zuwa dare na sake muku posting...😉



#Asli Smasher.
[2/6, 6:05 PM] My number 1: 28...





*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*


*Subscribe and read happily without feeling any guilt.. It's ₦200 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman,Access Bank or MTN recharge card/VTU and then show ur evidence of payment through my whatsapp account 08165726609 to be added in the paid group.*


_Jinjina gareku team Waleed,comments d'inku yana ba ni nishad'i,a ci gaba dai da gashi,da sannu za kuyi farin ciki,kuna comments ina baku update,Dadda ma ta ce a gaishe ku all,tana maku fatan alkhairi,saboda k'aunar da kukewa Mamman d'inta.🤗🤩_


A hankali ta bud'e k'ofar parlon su ta shiga gabanta yana fad'uwa,sanda ta tuna abunda Waleed yace wai zai sanar ma Daddy,gaba d'aya ta tashi hankalinta ta hana ma kanta nutsuwa,though ta san ma bazai tab'a fad'a ba kawai dan ya tsorata ta ne ya fad'a mata hakan ta sauke wani ajiyar zuciya a hankali,Mother kad'ai ta tarar a parlon tana zaune da Hafsat a hannunta tana bacci,ta tsuguna a hankali ta gaisheta,Mother tana kallonta tace "how are u feeling?" A hankali tace "I'm feeling better" mother tace "Allah ya k'ara lafiya,have u taken ur drugs?" Kai ta gyad'a mata a hankali tace "ehh" ta gyad'a kai tace "alright! But me ya fito dake yanzu da daren nan?" A sanyaye kwalla tana kawowa idanunta tace "a nan zan kwana" daga haka ta mik'e ta nufi d'akinta,mother bata ce komai ba ta bita da kallo,tana shiga d'akinta ta cire hijab d'inta ta haye kan gadon gabanta har lokacin bai daina fad'uwa ba,ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta kunna wayarta za ta cire daga flight mode,taga already ma ba'a kai yake ba kawai dai wayar yana silent,tana kallon screen d'in taga turutun missed calls da message guda kusan biyar,call log ta fara shiga taga kiran Azaan ne mafi yawa daga ciki sai wasu na Waleed,tayi wani ajiyar zuciya har ranta taji sanyi dan ko fuskarta ma sai da ya nuna tace "yau Yaya ya cire ni daga blacklist" ganin few minutes ago ya kirata,na Azaan ne dai tun yamma,ta bud'e text d'in tana dubawa taga duk sak'on nuna damuwa ne da rashin jinta daga Azaan,sai wani guda d'aya da ta gani daga Waleed,sanda ta bud'e kamar idanuwanta za su fad'o tsabar mamakin kalaman da ta gani ya rubuta mata,ta maimaita text d'in ya fi a k'irga,can kamar za tayi kuka ta ajiye wayar tana hararta,almost ten minutes tana zaune ta yi shiru tana tunani sai kuma ta d'auko wayar ta masa reply tana tura masa ta kashe wayar gaba d'aya tana sakin murmushi,ta mik'e ta shiga bathroom tayi wanka ta canja pad d'in jikinta ta d'auro alwala ta fito bayan ta gama shirin bacci ta kashe wutar d'akin ta haye gadon taja bargo ta rufe half d'in jikinta. Washe gari ya kasance Monday sosai ta ji sauk'i hakan yasa tayi shirin zuwa school da safe,tana cikin k'arasa assignment da bata samu ta yi ba sai lokacin,taga wayarta dake saman study table d'inta ya yi haske,k'arasawa tayi ta d'auki wayar taga text d'in friend d'inta Nusy ne ya shigo tana requesting tayi online yanzu za su yi magana,tayi mata reply da cewa su had'u skul kawai yanzu za ta shigo,ta ajiye wayar ta d'auki backpack d'inta na makaranta ta fita daga d'akin,ta yiwa mother sallama ta fita gidan,a hankali take tafiya kamar tana counting steps d'inta,ta k'arasa parking space lokacin duk sauran yaran gidan sun fito suka shiga motarsu driver yaja suka wuce skul,suna kan hanya Ameerah take tambayarta "sis ya jikinki?" Tace "da sauk'i" Ameerah tace "Allah k'ara lafiya,kin yi assignment kuwa?" Ta gyad'a mata kai tace "sure" suna ta hira tsakaninsu har driver ya sauke su get d'in makaranta ya juya,tun shigarsu premises d'in makarantar ta hango Nusy tsaye a jikin window ta zubawa hanya ido,tayi d'an murmurshi suka k'arasa class lokacin few mutane ne suka zo,can k'arshen class suka koma da Nusy wanda idanunta suka nuna damuwa k'arara,tace "sis kin san me ya faru?" Manar ta girgirza mata kai tace "nope!" Nusy tace "i want an advice from u" Manar ta zaro ido tace "ni kuma?" Nusy ta gyad'a mata kai idanunta sunyi rau²,a hankali tace "okay! Allah sa zan iya,what happened?" Nusy tace "wani cousin d'ina ke sona ni kuma banji ina sonsa ba gaskiya,yanzu ga shi ya fad'awa Daddy na,har ya basa damar zuwa wai mu had'a kanmu" zaro ido Manar tayi kamar eye ball d'inta za su fad'o tace "nima fa ban gaya maku bane kawai amma abunda yake shirin faruwa da ni kenan" here ta sanar musu kaf alak'arta da Waleed da kuma tsakaninta da Azaan,kallonta Nusy ta dunga yi kafin tace "to ke wa kike so a cikin su?" Manar tace "ni dai Yaya Azaan nake so" Nusy tace "shi kuma Yaya Waleed fa?" Manar tace "shima ai ina sonsa,amma Yaya yana auren k'anwarsa ne?" Kafin Nusy tayi magana,kawai sai ji suka yi Ameerah dake zaune tare da su ta fashe da wani dariya,suka kalleta tare Manar tace "mene abun dariya ke kuma?" Tana had'e rai,Ameerah tayi mai isarta kafin ta tsaya tace "kun san me ya faru?" Suka ce "a'a" suna had'a baki,Ameerah ta kalli Nusy tace "kefa na ki duk mai sauk'i ne,tunda ba ki da wanda kike so,why not baza ki amshi cousin d'in naki ba? Yana da wani aibu ne da baki so?" Nusy ta girgiza mata kai tace "nope! Ba shi fa da wani matsala nice dai kawai banji ina sonsa ba" itama ta sanar musu irin shak'uwar da suka yi da Abdoul d'in,Ameerah ta dunga b'ab'b'aka musu dariya,sai da taga duk sunji haushinta kafin tace "ba fa sonsa ne ba kya yi ba kema,kawai dai dan bai tab'a zuwa miki da irin maganar nan bane shisa kike ganin kamar ba kya sonsa" ta kalli Manar tana sakin wani murmurshi tace "sis nifa na jima ina zargin Yaya yana sonki kawai bai tab'a fad'a miki bane" kallonta Manar ta yi da sauri tace "wa yace maki haka?" Tace "i just sit and think" wani murmurshi Manar tayi tace "to ni dai Allah ina da wanda nake so" Ameerah ta fara dariya tace "shi kuma Yayan fa?" Manar ta d'aure fuskarta tace "shi ai Yaya na ne,besides kuma yana da mata,nima aure na zanyi" ta k'are maganar tana murgud'a baki,wani dariya Ameerah ta sake fashewa da shi tace "wait please.. Kina nufin ba kya sonsa wai?" Manar ta gyad'a mata kai tana b'ata rai,Ameerah tace "but idan ba kya sonsa me yasa ranar da kika ce ya yi kissing d'inki baki ji haushi ba? And me yasa kike zuwa jikinsa? Kina tunanin zuciyarki ba ta sonsa ne?" Manar ta sake gyad'a mata kai,wani kallo Ameerah ta mata tace "Wallahi k'arya kike yi kice ba kya sonsa na yarda,kawai dai akwai wani abu tsakaninki da shi da yasa kika kasa fahimtarsa,but billah Yaya yana sonki,so ba na wasa ba.." Wani kallo Manar ta dunga yi ma Ameerah idanunta sun cicciko da hawaye a fusace tace "ni dai ba shi nake so ba,kuma ai kema kin sani" Ameerah tace "ai ke na jima da raina tunaninki,har yanzun baki san meye kalmar so ya k'unsa ba,ki samu lokaci kiyi tunanin maganata maybe ki iya fahimtar wanda zuciyarki take so.." Dai² nan teacher su na physics ya shigo,suka koma seat d'insu. K'arfe hud'u sun fito school tare da Nusy suna sake tattaunawa kan maganar da suka fara da safen,Nusy ta hango cousin d'inta da take bawa su Manar labarinsa tsaye jikin motarsa ya rungume hannu idanunsa sanye da glasses,sosai gabanta ya fad'i ta bud'a idanunta tana kallonsa,a hankali ta tab'a Manar tace "friend kin ga Yaah Abdoul can tsaye,wanda nake baku labari" Manar ta d'an waiga suka had'a ido da shi yana sakin lallausan murmurshi,a hankali tace "kai friend yanzu meye laifin wannan guy d'in ke kuwa?" Ameerah tace "barta dai tayi wasa,tana zaune za taga wata ta kawo masa tallan kanta" wani kallo Nusy tayi ma Aneerah mai kama da harara,Ameerah ta fashe da dariya tace "ai gaskiya na fad'a kike hararata" d'an murmurshi Nusy tayi tace "muje ku gaisa" suka k'arasa inda yake tsaye,Manar tace "ina wuni" ya gyad'a kai yace "lafiya lau k'awarmu ya skul?" Tace "alhamdulillah" suka gaisa a mutunce,Nusy ta gabatar masa da su as manyan friends d'inta da ba ta da kamarsu,sai murmurshi yake musu har da basu sak'on su kular masa da ita ya basu amana,and su tayasa campaign,suka yi dariya then suka yi musu sallama saboda driver da yazo d'aukan su,daga haka ya zaga ya bud'e mata ta shiga ya rufe,then ya zagaya mazaunin driver ya shiga ya tada motar suka wuce. Manar tana dawowa skul that same day taga miss call d'in Azaan,kasa kiransa tayi da farko don bata san me zata ce masa ba,can dai tayi dialing number a hankali ta kai kunne,wayar yana fara ring ya katse ya kirata,tayi gathering courage tayi picking,murya can k'asa² tayi masa sallama ya amsa yace "why are u ignoring my calls?" Zaro idanunta tayi a shagwab'e tace "nooo! Yaya ba fa ina sane nayi haka ba,ba na kusa da wayar ne,na bama Hjy ajiya tun ranar Saturday" yace "okay! I thought u where ignoring it shi sa ma ban zo ba da daren munyi hira,ya jikin?" Ta langwab'ar da kai a shagwab'e tace "na ji sauk'i" yace "maa sha Allah" shiru ya biyo baya can tace "me yasa to baka zo ba da ban picking call d'in ba?" Yace "me yasa zan zo?" Turo baki tayi tak'i cewa komai,yayi murmushi dan ya fahimci me tayi yace "i'll call u idan na sauka flight d'inmu zai tashi" wani zaro idanu tayi cikin damuwa tace "tafiya kayi baka bari na dawo ba?" Yayi murmushi yace "yeah! There's something important da ya sa ni tafiya ban miki sallama ba,but zan dawo soon saboda qur'anic grad d'inki" fuskarta a d'aure ta amsa masa ba don ta so ba,da ya fahimci ta ji haushi yace "I'm sorry Guddi na ce fa zan dawo" kuka ta fashe da shi ta katse wayar,ya dunga kiranta tana kallo ta k'i d'auka,ya tura mata text shima dai bata yi masa reply ba. Tun daga ranar da ya tafi bata k'ara kiransa ba,sai dai shi ya kirata,ko chat ma kafin tayi masa magana sai shi ya fara mata,tsakaninta da Waleed kuwa tun ranar da ya mareta bata k'ara saka shi a idanunta ba,gaba d'aya ya yiwa gidan yaji. Ranan thursday da yamma sun taso islamiyya lokacin saura 2 day's saukarsu,suna zaune parlon Dadda suna ta shirin sauka Waleed ya shigo,ta d'aga kai ta kallesa ta b'ata rai,ya zauna kan kujera suka gaisa da Dadda dake ba su sak'o gurin aminiyarta Tasallah,bayan sun gama karb'an aiken Manar ta kalli Dadda tayi k'asa da muryarta tace "Hjy ko za kice Yaya ya kaimu please,driver ba ya nan wai" wani kallo Waleed ya mata saboda ya ji me take cewa yace "i'm not a driver of anyone,kuje ku samu napep ya kaiku" Dadda ta kallesa ta marairaice murya tace "hava kai kuwa Mamman,ka taimaka ka kai min su mana,sa fi dawowa da wuri ma akan idan motar kasuwa suka shiga" mik'ewa yayi saurin yi ya d'auki keys d'insa zai fita fuskarsa a d'aure yace "sai su jira driver ya dawo ya kaisu,ni ba hanyar zanyi ba bare ki sani na rage musu hanya" yayi ficewarsa ya bar Dadda da bud'ad'd'en baki,cikin jin haushi kamar jira take yana barin parlon ta fara mita "jeka d'an kwal uba,idan ka kaisu baka haifu cikin Asama'u ba.. Da wasu shegun mitsil² d'in leb'unansa da suka zurma ciki,tsabar tsotson masifa,tun kana k'wailiyinka dama ba mutunci kake da shi ba.. Ni ce dai za ka dawo ka tarar da ni ai.." Dariya Ameerah da Manar suka kwashe da shi har da kwanciya,can Manar tayi saurin tashi tace "ina zuwa bari naje naga idan Yaa Amaar yana nan ya kaimu" ta fita da sauri,ta sauka k'asan balcony taji an fizgota,ta waiga a tsorace taga Waleed ne,tayi ajiyar zuciya fuskarta a d'aure tace "Yaya ka sake ni aike na Hjy tayi fa" kallonta ya dunga yi ganin yadda tayi ya lumshe idanunsa a hankali yace "ke me yasa idan kina son abu baza ki iya fad'a ba sai dai kice Hjy ta fad'a min?" Da sauri ta kallesa,ya d'aga mata girorinsa,ta d'auke kanta tace "to ba dai ka ce baza ka kaimu ba kuma" yana kallon lips d'inta da suka sha red chapstick hancinta da ring shaped d'inta,nan da nan ya d'aure fuskarsa yace "ban hanaki saka abubuwan nan kina fita da su ba?" Rau² idnunta suka yi da ta gane akan abunda yake magana tace "Yaya.." A fusace yace keep quite.. Ban ce kada na sake ganinki da su ba?" Hawaye suna saukowa fuskarta tace "bazan sake ba" ya saketa yace "oyah! Ku fito muje" da sauri ta juya tana goge hawayenta,ya bita da kallo har ta shige part d'in,yayi ajiyar zuciya,bata jima ba sosai suka fito da Ameerah,can parking space ta hangoshi yana zaune cikin motarsa,suka k'arasa ta bud'e front seat ta shiga Ameerah ta shiga back,ya tada motar suka bar gidan,suna tafiya a hanya motar ya yi shiru,Waleed ya kalleta yace "u two should tell me abunda kuke buk'ata na saukan ku,though ba'asa ni ba na tambaya yanzun" Dariya Ameerah tayi tace "ehheeenn! Yaya muna komawa gida dama zan maka list" ya kallota ta mirror yace "alright!" Hakimar kam ko tari bata yi ba har suka je gidan Tasallah suka kai mata sak'on Dadda,suna fitowa gidan Ameerah ta klleta tace "sis ko za kice Yaya ya kaimu gidan su Nusy mu kai mata card?" Manar tace "tabb' d'i kina kallon yanzu ma fa abunda yayi kafin ya kawo mu" Ameerah tace "please ki gwada kiji ko zai yarda" suna zuwa Manar ta shiga motar ya kalleta yace "gulmar me kuke yi?" Manar ta kalli Ameerah itama ta kalleta da sauri Ameerah tace "babu komai" yace "really?" Ta gyad'a masa kai,ya tab'e baki yace "kada kiyi zaton ban jiku ba" ta zaro ido tace "Yaya ba fa wani abu muka ce ba" yace "ko?" Ta gyad'a masa kai,strictly yace "a ina ne gidan da za ku yake?" Wani zaro ido tayi tace "Yaya dama ka ji?" Ya kalleta ta mirror yace "a'a kin san ai ni kurma ne" tayi murmushi ta fad'a masa,ya gyad'a kai ya tada motar suka bar unguwar su Baba Tasallah. Sanda ya kaisu GRA da gidansu Nusy yake,kafin su fita motar ya musu warning kada su b'ata masa lokaci,suka fita suna amsawa,they spent about 30 minutes a ciki,Waleed yaga ba su da niyyar fitowa,ya fito motar ya jingina yana kiran line Manar,tana ganin kiransa ta kalli Ameerah ta mik'e tsaye tace "Yaya ne yake kira kizo mu wuce kafin ya fara fad'a" Ameerah ta mik'e tana kallon Nusy dake sakin wani murmushi tace "wane Yayan ne?" Ameerah tace "Yaya Waleed" Nusy ta kalli Manar tace "is he our love?" Kafin Manar ta bata amsa ya sake kira,gabanta har fad'uwa yayi,Nusy tace "ki d'auka mana kuma kike kallon wayar" a sanyaye ta d'auka kafin tayi magana yace "It's past six now sai yaushe za ku fito?" Wani sanyayan ajiyar zuciya tayi jin ba da fad'a ya tambayeta ba tace "yanzu za mu fito" bai sake magana ba ya katse wayar,ta kalli Ameerah tana sauke ajiyar zuciya tace "thought fa zai balbale ni da fad'a,muje kada ya k'ara kira ma" suka fita d'akin Nusy,after sun yiwa Mummy'nta sallama ta musu murnan saukar da za suyi tace "it's better ku yiwa friend d'inku fad'a ta k'i shiga islamiyya ku ga shi har za kuyi sauka" Manar tayi dariya tace "in sha Allah Mom za muyi mata" after then suka fita Nusy ta rakasu har gurin mota suka gaisa da Waleed,then suka yi sallama da su tana d'aga musu hannu tace "sai mun had'u skul gobe" Waleed ya ja motar suka tafi,suna kan hanyarsu na komawa gida kira ya shigo wayar Manar,ta kalli screen d'in ganin Azaan ne yake kiranta,ta Dd'an kalli Waleed kafin ta d'auka ta kai wayar kunnenta,a hankali tayi sallama,wani kallon gefen idanu Waleed ya mata bata kula ba kawai sai ji tayi ya k'ure kid'an dake tashi a motar,tayi saurin kallonsa za tayi magana taga ya d'aure fuskarsa,a hankali ta kai wayar dai² bakinta tace "Yaya zan kira ka idan na sauka" ta katse wayar,suna isa line ya tsaya few houses away,Manar ta kallesa tace "Yaya.." wani kallo ya mata yace "get down" ransa a b'ace,Ameerah tana ganin haka ta bud'e motar ta sauka,Manar kam k'in fita tayi,sai kallonsa take tana mamakin abunda ya b'ata masa rai cikin few minutes,ya kwantar da kansa a hankali jikin seat d'in ya kulle idanunsa yana jin wani irin damuwa yana lullub'esa

31 / 66