Manar Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Fatima Category :  Romance

Chapter   60 / 66

177K to 180K   out of 196.2K words

jin haushinsa,even though k'amshinsa ya mugun cikata,but haka ta danne ta ki basa space d'in da zai san idonta biyu,abunda bata sani ba kuma tun shigowarsa d'akin ya san ba bacci take ba,hatta juyawan da tayi ta kalleshi tsaf ya gani,da yaga ba ta da niyyar motsawa kawai ya d'agota yayi waje da ita kaman ya d'auki jaririya ya wuce bedroom d'insa da ita,yana shiga ya ajiyeta kan gadon ya zauna kusa da ita yana kallonta da wani murya yace "I knew u aren't getting any of what u are doing.. Ki bud'a idanunki ki min magana,me na miki ne kike jin haushi? Tun d'azun na kula dake da irin kallon da kike min" kamar dama jira take ya tsokano maganar,ta bud'a idanunta da sauri tana jan numfashi ta fesar a hankali,cikin muryanta mai sanyi tace "I don't know what really happened to u,me isa kan y'ar maganan da Hjy tayi maimakon ka mata a sannu har ta fahimta za ka nuna mata kai tsaye kaman bata isa ba? Don't u look shekarunta sunyi nauyin da sai muna binta a sannu? I think bai kamata ace kai da za kaga munyi ka hanamu ba kaine kake mata magana this way ba.. Me yasa haka ne Yaya?" Wani irin sanyayyan kallo yake binta da shi tunda ta fara maganar har tayi shiru ta zuba masa na ta idanuwan tana jiran taji ya yi magana,a nutse ya sauke numfashi,idanuwansa har sannan a kanta yace "ohhh! Akan wannan kike fushi kenan?" Da d'an k'arfi like ranta har sannan a b'ace tace "ya bazan ji haushi ba tsakani da Allah? Matar nan fa saboda mu tazo nan,me isa kuma za mu b'ata mata rai fisabilillah?" Tab'e baki yayi because shi dai ya san duk abunda yayi baiyi da niyyan ya b'ata mata ba,he just said that saboda bai son ma ta fara kawo maganar raba musu gida,shi dai bai ce baza'a mata wanka ba,kawai maganar tafiya da su side d'in Rani Naheed ne bai so yayi nisan da za su sa ya amsa ba da son ransa ba,so sai kuma akayi rashin sa'a duk sun fahimcesa a bai²,da wani sanyayyan voice ya kai hannu ya janyota jikinsa while saying "ke a tunaninki na yi haka saboda na b'ata mata rai?" Da sauri ta gyad'a masa kai,ya gyad'a kai shima yana sauke numfashi yace "lallai idan haka ne duk kun fahimci al'amarin ba dai² ba" saurin d'ago kanta tayi tana kallonsa tace "kamar ya?" Ya lumshe idanuwansa yace "kamar yanda kika ji" wara masa idanuwa tayi tace "i didn't get u" a hankali ya bud'e idanunsa ya sauke su a kanta,kamar bazai ce mata komai ba then kuma sai ya fara mata bayanin dalilinsa har ta fahimta,a nutse suka sauke ajiyar zuciya tare ta k'ara yin luf a jikinsa tana shak'ar k'amshinsa dake k'ara mata nutsuwar zuciya,lokaci d'aya wani irin bacci ya fara kawo mata ziyara,a hankali take sakin hamma,har sanda baccin yayi gaba da ita yana rungume da ita yana shafa ta. Da safe sanda yaje gaisar da Dadda k'in kulasa tayi saboda har lokacin bata bar jin haushinsa ba,sai da ya ba ta hak'uri da dabara ya mata bayanin dalilinsa na k'in amincewa su tafi b'angaren Rani,a cewarsa ai bai kamata suje can sun takurasu ba suyi zamansu a nan kawai ai zai fi,da ya gama mata bayanin ya samu ta sauka daga mugun fushin da ta fara yi da shi,here ya zauna suka d'anyi hira ma,can ta kallesa tace ita ya nuna mata mad'bak,da sauri Waleed dake satan kallon Manar tun shigowarsa tana bacci ya kalleta yace "me za kiyi a mad'bak kuma Hjy?" Tace "iiiihh! Yo girki zan ma Manar mana" yayi murmushi yace "kiyi zamanki ki huta komai kike so akwai masu yi a nan" baki sake ta kallesa tace "me suke yi?" Yace "everything!" Wani kallo ta masa tace "meye hakan kuma?" Manar da farkawanta a bacci kenan tana jinsu bata san sanda ta fashe da dariya ba,Dadda ta d'aure fuska tana jiran amsansa,yayi murmushi yace "na fad'a maki komai suna yi" sanda ta karkace kai tace "sun iya tuwo?" Da sauri ya kalleta sai kuma ya girgiza mata kai yana tab'e baki,ta tab'e baki itama tace "aikin banza dama me suka iya in ba jagwalgwalon turawa ba? Allah na tuba wannan har abincin da ya kamata mai jego taci ne?" Yanda take magana yasa suka fashe da dariya,Manar har da hawaye,Dadda ta tsuke fuska tace "ka ga tashi muje ka gwada min inda mad'bak yake yanzu na shirya mata abinci mai rai da lafiya,wanda zai gina mata jiki" Manar dai couldn't help it dariya kawai take musu yanda taga Dadda ta dage,Waleed ya tab'e baki yace "muje to in ba rakaki nayi ba na ga alama baza ki hak'ura ba" tace "na ji dai muje" tasa shi gaba suka fita,Manar ta sauko daga gadon tana goge hawaye ta shiga bathroom,sanda ya rakata suka dawo tare yana cewa "tou ke yanzu in banda rigimanki ma Hjy ina za ki samu wani abun da za kiyi tuwo da shi a nan tunda ba Nigeria kike ba?" Bata kallesa ba tace "ka tsaya kai kallo Malam,ni nan da ka ganni da komai na nake tafe.. Yo Allah na tuba mu da mukayi zaman saudiyya ina ne za mu shiga mu kasa rayuwa?" Ya jinjina kai yace "babu kam" tace "aatooh! Ai shi isa nake fad'a maka dama" suka shigo d'akin tare,Manar dake fitowa bathroom sai murmushi take musu,ya bita da wani adorable kallo sanda ta koma kan gado ta zauna tana k'ara jan bargo ta rufa,Dadda dai bata kalle su ba ta wuce gurin jakunkunanta ta janyo wani ta ajiye,sanda ta zuge ta fara fito da kaya,su man shanu soyayye da aka d'urasa a gallon,yajin daddawa da su kukarta mai kyau da kub'ewa busashshe,Waleed ya bud'a idanu yana kallonta yace "Hjy wannan fa daga ina?" Tace "yo ban fad'a maka ba ne? Ai mu dama da guzirinmu muke tafiya.." Ya gyad'a kai bai sake mata magana ba ya juya gurin Manar yana mata magana a hankali yanda ita kad'ai take fahimtar me yake cewa,Dadda dai da ta gama had'a kayanta ta kallesu taga idanun Manar a kulle she thought ko bacci ta koma,ta kalli Waleed da yake ma Al'hussain Addu'o'i seeing that tun d'azu yake firgita,ta wuce ta nufi hanyan fita tana cewa "to idan ka gama ka fito dai ka barsu su huta tunda bacci suke" ya bita da wani kallo bai kulata ba har tayi waje,da sauri ya rufe yaron ya matsa kusa ita ya rankwafo yana mata rad'an "get up Lily ta tafi,tashi kiji maza fita zan yi" kwab'e fuska tayi bata d'ago ba tace "dan Allah.." Bata k'arasa ba yace "wallahi kada ma ki fara had'ani da Allah ki cuce ni,da baki min alk'awari ba zan iya hak'uri,but na gama saka rai da abun.. Tashi muje d'aki na nan Hjy za ta dawo yanzu.." Babu yanda za tayi haka ta tashi tana kumburi ta bisa,suna fita su Azaan suna shigowa gidan lokacin za suje kiran da Raj Jarood yake musu suka shigo su masa magana,tunda ya gansu ya d'aure fuska kamar wanda aka aikoma sakon mutuwa,ba d'on ya so ba dole ya hak'ura,suka fita yana mata alaman za su had'u idan ya dawo,tayi murmushi mai had'e da ajiyar zuciya nan suka zauna hira da su Ameerah suka cika gidan da surutunsu,Dadda kuwa tana kitchen tana girkinta. Cikin haka kwanaki sukaita zuwa suna wucewa,kullum Dadda ke mata wanka tun ba ta so har dai ta sauka dan babu yanda za tayi,musamman da Mommella da Rani suka sa baki,ko shi Waleed Allah ya sani ba a son ransa ake wannan wankan ba,kullum suka zo wankan yana jin rigiman da suke da ihunta,abun ba k'aramin tab'asa yake ba haka yake lek'ensu ba ya zuwa inda suke,tun ranan da ya shiga da yaji ihunta Dadda ta had'a da shi a wankan,azaban ruwan zafin yasa bai k'ara marmarin kai mata agaji ba,because fatarsa ba mai jure irin wannan azaban bane,ranan da suka cika kwana biyar da dare family d'insu suka sauka k'asar,wanda ya had'a da Mother,Daddy,Aunty,Abba,Deejah da sauran yaran gidan,Hafsat Autar Mother ma yanzun ta yi wayo sosai ta fara zama y'an mata,sosai idan yarinyar tana surutu idan ba ganinta kayi ba za kayi zaton babbace,da yake kuma ba ta da wuyan sabo,shisa yarinyar take da mugun shiga rai,d'an zama kad'an ya had'a ku idan bata nan sai kaji kewanta,yara dai tuni suka amsa sunansu babu wani canjin da aka musu,though Waleed ya k'udurce wani abu a ransa da kamar ace yaro d'aya suka samu,but yanzunma ba wai ya fasa abunda yayi niyya bane,ya bari zuwa next haihuwan da Manar d'in za ta kuma yi. Tunda suka zo Deejah taga yanda su Manar suke rayuwa da su Ameerah basa b'oyewa junansu komai,da yanayin canjin da suka yi,taji tana sha'awar son tayi aure itama,sai dai ta san al'amarin isn't that easy but tana addu'ah sosai kan Allah ya mata zab'i na gari,ranar kam a nan b'angaren Manar suka kwana suna hira,Manar na tambayarta Mama dan suna waya yanzun sosai,since ta haihu Mama ta kan kirata taji lafiyarsu da yaran,a nan nema Manar ta fahimci lallai Mama ta sauko,ba wadda ta sani bace da can,haka kou da ta tambayeta Diyanah ma,tace ai bata je gidan ba har yanzu,saboda Abba bai barin tana fita,Manar tayi murmushi ganin damuwa a fuskar Deejah tace "ayyahh! Allah sarki idan muka koma naija za muje tare in sha Allah,ni ranar Master yake sanar min ma ashe k'anin Dr Mahfouz ne mijin Diyanah?" Deejah tace "ohh! Yaya dama ya san y'an gidansu?" Manar tayi murmushi tace "sosai ma tare suke aiki a can fa" Deejah ta jinjina kai tana maimaita sunan da Manar ta kira Waleed da shi a ranta tana murmushi sai dai bata san ma'anarsa a gurin Manar ba. Washe gari da safe kam tare Deejah da Dadda suka shiga kitchen suka shirya breakfast,haka kou lunch ma tare suka yi har su Ameerah da Rania da suke gidan suka had'u a kitchen,dan nan ne dandalinsu tun da akayi haihuwar,Dadda dai tun zuwanta ta k'i yarda a k'ara bata abincin turawa,Mother da Aunty kam suna b'angaren Rani kowa d'akinta daban da mijinta,yaransu maza ma haka sai Hafsat dake gurin Ameerah,saboda surutunta yasa Azaan yake mugun son yarinyar,sak tasowarta irin na Manar,komansu babu bambanci,shisa yake mugun jinta a ransa,yake tunanin idan su Mother za su tafi zai rok'i alfarma gurin Daddy ya bar musu ita,kafin Allah ya azurta su da haihuwa,because har yanzun ko b'atan wata Ameerah bata yi ba,a ranar da dare Deejah ta kawo akwatin kayan yara da Mama ta bayar ta kawo,Dadda ta kawo manyan zannuwanta biyar masu tsada,da rigunan yaran suma guda biyar²,duk wanda ya kawo kaya a ranan ya fito da su,ba k'aramin kaya suka samu ba,nan akai tafi da su b'angaren Rani a can akaita d'aga kayan ana fad'an wanda ya bayar,ana sa musu albarka. Ranar suna da safe bayan an gama shirya yaran cikin shiga na alfarma,kayansu da abun d'aukansu duk iri d'aya,aka wuce da su bangaren Rani Naheed inda iyaye da kakanninsu suke,kowa yayi adonsa cikin shiga na alfarma,shima dai ranar kaya kusan iri d'aya suka sa kamar lokacin aurensu,da dare sanda suke shirin dinner mazan suka sa dark green d'in riga ta sama,ta cikin da wandon kuma farare,su kuma matan rigunansu ne farere da nad'in sari d'insu green,Dadda kam Pakistan ne riga da wando green sai mayafinta fari,sosai suka yi masifar kyau,Manar da Waleed kan su komai na su a ranar iri d'aya suka dunga shiga suna cirewa,sanda za suyi dinner suka sa white color sai suka fita daban,duk inda suka shiga sai an gano su,haka yaran ma lokacin da suka taru babban parlon gidan da aka k'awata an tsara tables da ko wani event center albarka,saboda manyan mutanen da Raj Jarood da Dad mijin Mommella,haka kou Rani Naheed ma da Mommella ba kad'an ba suka yi gayyata sunan jikokin nasu,lokacin Deejah za ta shiga gurin Diyanah ta kirata,hakan yasa sai ya fasa shiga ta d'an tsaya balcony ta amsa kiran,bayan sun gaisa tace "ya taron suna?" Deejah tace "alhamdulillah! Dan baki ga abunda ake ba sis,i wish u were here wallahi,sai nake jina alone na kasa sakewa sosai cikinsu duk yanda suke ja na a jiki,saboda abubuwan da muka ma Manar,ina jin inama ina da damar mayar da abunda suka faru baya,da na goge su kaf mun yi rayuwa irin ta y'an uwa masu son junansu,ke sai kinga yanda suke da Ameerah,abun gwanin burgewa wallahi.." Diyanah da jikinta yayi sanyi da furucin Deejah cikin sanyin magana tace "nima ina jin babu dad'i,musamman idan na tuna abunda muka dunga musu da maganganun da muka dunga fad'a akan Manar wanda Mama ke kitsa mana,har cewa muka yi Dadda ta d'auki Manar ta tafi da ita saudiyya ta kaita karuwanci.." Muryar Diyanah da ya fara rawa sakamakon tunawa da abunda ya faru da ita yasa ta yin shiru tana share hawaye,jikin Deejah ya k'ara yin sanyi sakamakon furucin y'ar uwarta,hawaye suna kawowa idonta tunawa da abunda Diyanah ke son fad'a,tace "haka ne sister,but duk abunda ya faru sakayya ne akan maganganun mahaifiyarmu da mu kanmu,sannan kuma Allah ya tsara dama haka zai faru cikin rayuwarmu,sai muyi fatan Allah yasa haka ya zama darasi gare mu da sauran al'ummah baki d'aya.." Manar dake tsaye bayanta da Ameerah tun d'azun suna sauraron wayar da take a tare suka had'a baki gurin cewa "Ameen ya Allah.." Saurin juyawa Deejah tayi ganinsu tsaye yasa jiki a sanyaye tace ma Diyanah "sai an jima sis,idan mun sake magana" Diyanah tace "Dan Allah ki d'an tura min video na taron ku na gani kinji? Ko na kiraki video ki nuna min fuskar kowa please!" Deejah tace "alright! Babu matsala" suna yin sallama ta sauke wayar daga kunnenta,Manar ta matso ta kama hannunta tana mata murmushi tace "zo muje sai nemanki muke a ciki" suna shiga parlon inda duka family da manyan bak'in da suka fara zuwa suke Diyanah ta kirata video,ta d'auka da sauri tayi mata murmushi tace "hi!" Tana d'aga mata yatsunta,Diyanah na kallon Deejah cikin sari Green ta sha kwalliya kamar ba ita ba,ta zaro idanu tace "woah! My sis kece da gaske?" Deejah tayi murmushi ta mata fari da ido tace "me idonki ya nuna miki?" Diyanah ta girgiza kai tace "can't believe kece kika dawo haka,kin ganki yanda kika koma kamar jinin indiyawa" Deejah tayi wani dariya tace "gama zagina dai" Diyanah tace "wallahi ba da wasa nake maki ba" Deejah ta tab'e baki tace "ke dai ki fad'i gaskiya,ban yi kyau ba kou?" Diyanah tace "a'a wallahi kin yi kyau sosai ma,bari ma kiji" ta kalli Hjy Aisha da sauri dake saukowa tana nuna mata Deejah tace "Mom kinga wai bata yi kyau ba take cewa?" Hjy Aisha dake d'auke da jaririnsu mai sunan Alh Baffanyo ta kalli Deejah tayi murmushi tace "maa sha Allah! Kinyi kyau abunki daughter sosai" cikin jin kunya Deejah tace "na gode Mom,ina wuni?" Hjy Aisha ta amsa tana mata murmushi,dai² nan Dr Mahfouz suka shigo tare da Farhan suna dariya,Diyanah ta karb'i wayar tace "sis ina Manar da Ameerah,ya kids d'inmu da waye suke kama,Yaya kou Manar?" Manar dake jinta cikin zolaya tace "dake suke kama" Diyanah tace "tabb' d'i ai da Yaya suka biyo dai ko ke,sa yi kyau na gaban kwatance amma ni ai sai an had'a musu da suratul yusuf za su samu mata" dariya suka yi duka har su Dr Mahfouz da suke zaune suna magana da Hjy Aisha,d'aya bayan d'aya babu fuskar wanda Deejah bata haskawa Diyanah ba kafin suka yi sallama tana ta murnan ganinsu bayan tsayin lokaci dan tsoron zuwa gidan take saboda Abba,itama Deejah sai murmushi take saki da tayi magana da y'ar uwarta taji lafiyarta,sosai aka ci aka sha a gurin walimar sunan,kud'i kam kamar yayi aka narkar da su,ranan sunyi kuka ba na wasa ba,an d'auki hotuna saboda tarihi,a nan Raj ya dunga gabatar da su Waleed,Manar,Azaan,Ameerah,Amaar,Rania matsayin Yayansa,da na k'aninsa (ina nufin Dad mijin Mommella) gurin manyan sarakunan da suka zo masa Allah raya,yara da iyayensu kam sun samu kyaututtuka fiye da tunani,sai da dare ya fara nisa kafin aka watse,bayan duk bak'in da suka zo sun tafi suma iyalin gidan kowa ya nufi makwancinsa..


#Afuwaan habibties,wallahi ban san meke damuna ba nake kasa yin rubutun,gaba d'aya ba na jin typing d'in cikin kwanakin nan,but kuyi hak'uri in sha Allah nan da few days zan k'arasa muku,kafin mu shiga ramadhan..


#Asli Smasher.
[4/3, 9:53 PM] My number 1: 58...





*WATTPAD:REAL-SMASHER.*


*Subscribe and read happily without feeling any guilt.. It's ₦200 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman,Access Bank or MTN recharge card/VTU and then show ur evidence of payment through my whatsapp account 08165726609 to be added in the paid group.*


*_Allahumma ballighna ramadhana bil iimaan.._*🤲



Sanda su Manar suka yi shirin kwanciya bacci,duk irin gajiyan da suka yi bai hana su mayar da labarin yanda taron ya kasance ba,a haka har bacci ya d'aukesu cike da gajiya,da safe bayan sun shirya sunyi breakfast suka wuce b'angaren Rani Naheed saboda duk kyautan da suka samu can suka barosa,a nan suka sake bajewa suna duba gifts,daga nan aka koma hira kuma,su Daddy da sauran mutanen gidansu duk sai ranar suma suka ba da na su,Dad (mijin Mommella) ya yima Manar kyautar sabon mota fil,bayan kayan da ya mata set guda na akwati ita da yaran,Daddynta ma ya sake siya mata mota though ya san ba hawa take ba,duk inda za ta Waleed yake kaita,a nan ya shaida mata already motar ma yana gidansu na Nigeria,su Mother kuwa kyautarsu na musamman ne ita da Aunty,bayan kayan barka suka had'o mata da kayan gyara,sai dai shi a sirri suka ba ta tare da bayanin yanda za tayi da su,Rani Naheed da Raj Jarood ma kayan da suka mata ba'a magana,kowanne da dank'areran gold,earrings,bangles,ring da chain na wuya da

60 / 66