Manar Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Fatima Category :  Romance

Chapter   48 / 66

141K to 144K   out of 196.2K words

da sauri za ta koma sama,a tare Mama da Afiyah suka bita,sanda ta haura saman da sauri tana k'ok'arin saka k'afarta cikin d'akinta Afiyah ta rik'ota ta fizgota tace "zo nan munafuka algunguma,ai yau sai munci uwarki dake da shegen cikin da kike d'auke da shi" a tsorace Manar ta dunga girgiza musu kai hawaye cike a idonta tace "dan Allah kar ku tab'a min baby,me ya muku ni za kuma idan ma wani abu na muku" bakinta Mama ta gwab'e tace "rufewa mutane baki shegiya makira" da sauri ta dafe bakinta hawaye suna sakkowa fuskarta,tace "me na muku wai?" Afiyah tace "tambaya ma kike?" Kafin kace me sun rufeta da duka kamar wanda aka aiko su,banda kuka babu abunda take ta kasa magana sai kare cikinta da suke kaiwa naushi take tana cewa "karku kashemin babyna,me mukai muku?" Mama sai haki take tace "dan uwarki ba baby ba har kema sai mun kusa kashewa" tun suna dukanta a wajen bedroom d'inta sanda ta nufi hanyar staircase tana k'ok'arin guduwa ta kwaci kanta,Afiyah ta d'aga hannu Mama ma ta d'aga hannu kafin su sauke a kanta Waleed ya bud'e k'ofa ya shigo,maganar Manar cikin kuka tana cewa "ku rabu da ni,me nayi muku kuke dukana" yasa shi kallo saman da sauri,ya kallo inda yake jiyo kukanta,idanunsa suka sauka kan Mama da Afiyah sai kilarta suke,wani kururuwa yayi yana kiran sunan Manar,a firgice Afiyah tayi baya,cikin tsautsayi ta tad'o k'afar Manar,k'afafunta suka lankwashe Mama dake rik'e da ita tana sakinta ta fara gangarowa tayo k'asan kamar wanda aka cillo da gayya,a gaban Waleed ta fad'o a kife akan cikinta,tunda tayi wani firgitaccen k'ara sau d'aya ta daina motsi...




#Asli Smasher.
[3/3, 9:40 PM] My number 1: 46...





*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*


*Subscribe and read happily without feeling any guilt.. It's ₦200 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman,Access Bank or MTN recharge card/VTU and then show ur evidence of payment through my whatsapp account 08165726609 to be added in the paid group.*




Cikin tsananin tashin hankali Waleed ya durk'usa gabanta hawaye suna zubowa idanunsa,kamar mai jin tsoron tab'ata ya kai hannu ya d'an tab'ata yace "hhhh.. Hey! Llll.. Lil.. Lilac!" Jin shiru kamar ba ta motsi ya sake cewa "Hey! Wake up.. Wake up pleaseee" kamar wanda akace ya kallo k'asanta yaga jini ya fara biyowa yana ma kansa hanya kamar wani watersheds,zaro idanunsa yayi cikin k'araji ya kira sunanta at the same time ya kai hannuwansa ya d'auketa yayi hanyar fita,Afiyah ta kalli Mama cikinta har wani juyawa yake yana bada sounds sanda ta gano jini kwance a inda Waleed ya d'auke Manar tace "na shiga uku" jikin Mama ya d'auki wani rawa ganin aika²r da suka yi,a fili tace kada dai ace sun kashe har Manar d'in,ita dai bata zo da niyyar su kashesu duka ba,cikin jikinta kawai suka zo su rabata da shi,Waleed da har ya saka k'afarsa waje hawaye sai sauka fuskarsa suke uncontrollable ya waiga yana kallon inda suke da wani kakkausan murya yace ma Afiyah "Before i get back,ki tabbatar kin bar min gidana,na sake ki saki uku.. If something happens to my wife or my kid na rantse da k'udirar ubangiji bazan bar duk wani mai hannu a ciki ba.. And then i would advise u to hide urself whenever u heard my name mentioned,saboda dole na karb'an mata hakkinta.." Yana gama fad'a bai k'ara kallonsu ba ya fice a gaggauce,ya sata a mota ya shiga ya tada motar jikinsa duk jini haka hanyar da ya biyo jini yayi layi,wani uban horn da ya dunga dannawa tun bai rufe motar ba,sanda ya firgita mai gadin gidan,yana bud'e masa yayi zooming off ya fice da mugun gudu,yana driving yana share hawaye kamar mace,even though Waleed yana cikin mutanen da Allah ya yisu masu dauriya da juriya,but ko yaya abu ya had'a da Manar sai kaga ya zama wani rago,abu kad'an yake sa shi kuka akanta,ikon Allah ya kaishi hospital d'insu,kafin ma ya k'arasa tuni ya yi waya da wani friend d'insa ya fad'a masa yana nan zuwa da patient,Dr Mahfouz ya bada umarnin a tanadar masa kayan aiki yana da emergency case,sanda Waleed yayi parking ya samu gado yana jiransa,bai ko tsaya gyara parking ba ya fito yana kokawar bud'e back seat nurses d'in da suka fito tarbarsa suma suna kici²n bud'ewa,ya samu dai ya bud'e ya d'aukota ya d'ora kan gadon,a gurguje suka wuce da ita ICU (intensive care unit),Waleed zai shiga Dr Mahfouz ya hanasa dan yanda ya gansa a birkice ya san babu abunda zai tsinana,yace yaje gida ya canja kayan jikinsa kafin su fito da ita,daga asibiti kai tsaye gidansu ya wuce,yayi parking ya fito ya nufi b'angaren Dadda,ko sallama baiba saboda wani karyewan da zuciyarsa ya sake yi,Dadda ta fito d'aki tana gyara d'aurin d'ankwalinta ta ga mutum tsaye tayi mitsi² da ido tace "wa nake gani kuma haka?" Waleed ya kasa tanka mata ya juya da sauri zai fita tace "tou ai dama idan ba kai d'in ba wa zanwa magana ya min banza" ko kula da yanayinsa bata yi ba,yana fitowa ya nufi b'angaren iyayensa,ya haura sama ya bud'e bedroom d'in Aunty,samunta yayi suna waya da Ameerah akan maganar bikin Amaar da ake shirye²,bai iya yin sallama ba sai hawayen da yake sake gogewa ya zauna kan kujeran gaban mirror,kallo d'aya Aunty tayi masa taji gabanta ya fad'i,da sauri suka yi sallama da Ameerah tace za su k'arasa maganar later,tana sauke wayar daga kunnenta tace "Waleed lafiya?" Ya d'ago a hankali ya bud'e bakinsa zai mata magana wasu hawayen da suka gangaro fuskarsa suka hanasa fad'an maganar,Aunty cikin tashin hankali tace "subhanallahi! Waleed me aka maka? Ina Manar? Kai da waye please ka sanar da ni?" Kuka sosai ya fashe da shi ya rufe fuskarsa da both palms d'insa,Aunty ta taso da sauri ta rik'o hannunsa ta sauke daga fuskar ita kam tana ganin tashin hankali,wai kamar Waleed shi ne ya shigo mata babu ko sallama kuma yake kuka haka,ta d'ago fuskarsa da wani irin rauni a maganarta tace "wani abu ne ya samu Manar d'in?" Kai kawai ya iya gyad'a mata da sauri kuma sai ya mik'e zai fita,Aunty tayi sauri ta rik'osa tace "tou taya zan san me yake faruwa baka fad'a min ba kuma?" Da kyar ya daure ya iya mata bayanin abunda ke faruwa "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.." Was the first word da ya zo bakinta tana tafe hannu da jinjina girman maganar,a gaggauce ta juya ta d'auki hijab da wayarta tace masa "muje da sauri" suka fito tare lokacin tana yiwa Abba waya tana fad'a masa za taje hospital Manar babu lafiya,Abba yace babu matsala ta dubata kafin ya baro office ya shigo,da suka fito tace yaje yayi wanka ya canja kayan jikinsa kafin ta yima Hjy Dadda bayani,idan ya gama ya jirasu a mota,da kyar ya yarda ya shiga d'akinsa na gidan,Aunty ta fita ta wuce b'angaren Dadda da sauri,tunda ya fito wanka ya d'auki wasu kayan yasa ya fito ya bud'e motarsa ya rasa me yake masa dad'i,yana zaune cikin motar ya had'a kansa da steering wheel yana sauke ajiyar zuciya da tunanin ko a wane hali take yanzun? Ya jiyo hayaniyar Dadda tana kururuwan "idan na yarda na kyalesu Allah ya d'au raina,shi kenan sun kashe min jika,Manar d'in ta mutu ko? Ku fad'a min gaskiya.." Sai kuma ta rushe da matsanancin kuka,Mother dai tunda Aunty ta fad'a mata maganar ta kasa magana sai Aunty ke bata baki tana cewa "kiyi hak'uri Hjy har muje muga halin da take ciki" sanda suka shiga ya d'ago idanuwansa da suka yi ja ya gaisar da mother,jikinta duk ya yi sanyi ta amsa tace "ya mai jiki?" Kasa amsawa yayi sai hawayen da ya goge dan gani ma yake kamar idan yace da sauk'i ya zalunci Manar d'in,sanda suka baro gidan motar ta yi shiru babu mai magana Dadda kad'ai take mita,idan tayi² sai kuma ta fara share hawaye tana rantsuwan duk abunda ya samu Manar baza ta yafe ba sai ta you k'aran mutum,shigar su hospital d'in bayan yayi parking sun fito suna shiga ward d'in ya yi dai² da lokacin da Dr Mahfouz ya fito neman Waleed,yana hangosa ya rik'o hannunsa da sauri yace "dama kai na fito nema,yi sauri muje" yace ma su Aunty yana zuwa yabi Dr Mahfouz office d'insa,a can Dr Mahfouz ya masa bayanin komai har miscarriage d'in da ta samu,and then due to koma wane irin matsala ne ya faru da yayi sanadiyyar zubewar cikin shi ya janyo mata dogon suma,but sun shawo kan matsalar sun wanko abunda bai k'arasa fita ba,sanda ya gama yi masa bayanin komai,wasu irin sababbin hawaye suka sake saukowa fuskar Waleed,tunaninsa ya tafi akan yanzu shi kenan sun masa asarar cikinsa? Ya fita kenan? Tunda Dr Mahfouz ya gama masa bayanin yake zaune ya kasa kwakwkwaran motsi,kawai ya rufe fuskarsa yana kuka mara sauti,Dr Mahfouz yana bashi hak'uri,sanda yayi mai isarsa kafin ya yiwa Dr Mahfouz godiya ya fita,bai ce da su Aunty komai ba ya wuce d'akin da take special room ne ita kad'ai,ya sameta kwance a kan gado kamar mataciyya hannunta ansa mata k'arin ruwa,sanda ya kalli k'irjinta yaga tana sauke numfashi kad'an² yayi wani ajiyar zuciya ya k'arasa bakin gadon ya zauna yana kallonta cike da tausayi,ya jima sosai a d'akin dan baima san adadin lokacin da ya shafe ba kafin aka bud'e k'ofar aka shigo,bai juya ya kallesu ba suka k'arasa shigowa tare da Dr Mahfouz ya mik'a masa takardan da yayi prescribing magungunanta,ya karb'a yana kallo a hankali,Dr Mahfouz ya masa Allah k'ara lafiya,shi kuma ya masa godiya tare da su Aunty then ya fita,d'akin yayi remaining silence saboda Dr Mahfouz ya fad'a musu ba'a son hayaniya a inda take,amma Dadda sai girgiza kai take fuskarta a d'aure. In less than an hour labari ya gama zagaya family,Ameerah da Azaan sun kira sun masa jajen abunda ya faru kafin su zo,dan tunda Aunty ta sanar da Ameerah take kuka,gani take kamar ita aka b'ararma da ciki,dole sai da Azaan ya lallasheta kafin tayi shiru,haka ko Raj Jarood da Rani Naheed sun kirasa,Rania kuwa dama cewa tayi k'afarsu k'afarta sai ta je Nigeria duba Manar,Mommella ma dai tana hanya tace da suka yi waya,dan ta san dole ayi zama na musamman akan case d'in,guraren maghreb Abba ya k'araso hospital d'in tare da Amaar,Dadda dai tana d'agowa ta kalli Abba sanda suke shigowa d'akin ta fashe da wani kuka tana fad'in "billahillaziiy yau mai rabani da Asama'u sai dai Allah'n da ya halliceni,amma wallahi bazan yarda a b'arar ma da jikata ciki a sata dogon suma ya tafi a banza ba,idan na yafe musu Allah tsine min albarka" Abba ya kasa hak'uri yace "wai me yake faruwa?" Saboda har lokacin Aunty bata yarda ya san asalin abunda ke faruwa ba,it was there ta bud'a baki za tayi magana Dadda tayi zaraf tace "kana jina kou Yaro?" Abba ya kalli Dadda ya gyad'a kai yace "ina ji Hjy" Dadda ta daddage kamar a gabanta akayi ta fara rattabowa Abba bayanin kaf abunda ya faru,Abba yayi shiru ya kasa magana sai kallon Manar dake kwance bata ma san inda kanta yake ba,ya gyad'a kai yana sauke ajiyar zuciya yace "Allah ya kyauta" wani kallo Dadda ta masa baki sake tace "ban gane hausan Allah ya kyauta ba? Me kake nufi Yaro?" Abba yace "tou Hjy idan ban ce haka ba me zance?" Tace "ai kawai ka sawwak'ewa wancan matar,Allah na tuba dama idan banda mutuncin Alh Na Abba me za'ayi da surukuwa irin Asama'u? Tou yanzu kuwa tunda Allah ya sa baya raye bare muji kunya ai shi kenan maganar kunya kuma ya k'are" Aunty dai kallon Dadda kawai take,lokacin Waleed ya bud'e k'ofa ya shigo jikinsa a sanyaye yana d'auke da wani basket guda biyu,sai trolley d'in kaya ya k'arasa ya ajiye ya gaisar da Dadda da su Aunty,suka gaisa da Amaar ya masa ya mai jiki,d'an ajiyar zuciya yayi idanuwansa akan Manar da har lokacin bata farfad'o ba yace "alhamdulillah!" Abba dai sai kallon Waleed yake sympathetically ganin yanda ya rame kamar shi ne a kwance a hospital d'in ba Manar ba,ya masa Allah ya kiyaye gaba,har guraren 9pm su Abba suna hospital d'in kafin suka fara shirin tafiya,nan fa Dadda tace ai sai su tafi su barta ta kwana da ita tunda dai bata farko ba har lokacin bare su san a want hali take,Abba yace "Hjy ai su nan hospital d'in masu jinya basa kwanar musu sai dai ka wuni ka tafi da safe ka sake dawowa" Dadda ta dage ita wallahi sai a tafi a barta ko ba'a kwana ita dai yau sai ta kwana gurin jikarta har da kukanta,da kyar dai Aunty da Amaar suka lallab'ata ta yarda za ta tafi bayan ta gama mitar wannan dai ba tsari bane ace za'a bar mutumin da yake jinya shi kad'ai kamar ya rasa dangi,Waleed yace zai zauna tare da ita babu matsala suje sai da safen,haka suka fito suka wuce a motar ma sai mita take har dai suka k'arasa gida. A b'angaren Mama kuwa sanda Waleed ya bar gidan hannu biyu ta d'ora a ka kukan ma ta rasa ta inda zai zo mata saboda tsananin tashin hankali da rud'anin data tsinci kanta a ciki,abu na farko dake sawa zuciyarta rauni shi ne furucin Waleed,na biyu kuma dai ta san duk bala'i tunda Waleed ya ganta red-handed dole ma ko ya rufa mata asiri idan Manar ta farfad'o ta tona,tou wai ita yanzu ta ma fara bin hanyar gidan? Idan taje tace musu me? Ta kalli Afiyah dake kuka wiwi tana sak'e² a zuciyarta dan dole ma ya zamar mata ta koma gidan ta san matsayin aurenta duk da dai ta san zai wahala Abba bai rabu da ita ba a lokacin,bata iya cewa Afiyah komai ba ta zare jikinta ta lallab'a ta bar gidan ko noticing Afiyah bata yi ba,sai da ta gama koke²n ta d'ago da niyyar mata magana taga wayam,duk inda take tsammanin ganinta sanda ta duba bata ganta ba ta gyad'a kai ta kirata a waya,Mama tana ganin kiran lokacin ta gama waya da wani cikin malamanta yace kada ta damu zai mata aiki ya rufe bakin su ko tambayarsu akayi baza su fad'i gaskiya ba,ta masa godiya kafin ta hau napep ko ta kan kiran driver bata bi ba ta nufo gidan da kwarin guiwarta,sanda taga kiran Afiyah kasa d'auka tayi saboda bata san me za tace mata ba tunda dai ita shaida ce akan Waleed ya saketa saki uku,ba ta da damar sake tursasa sa sai ya mayar da ita gidansa kuma,ko ba ma wannan ba ita kanta ta kanta take yi da igiyar aurenta biyu da suka yi saura a yanzun,saboda haka sanda wayar ya katse ta turama Afiyah sak'on ban hak'uri sai kuma kalmar ta na k'arshe wanda ya masifar k'onawa Afiyan rai shi ne da Mama tace "kowa yayi ta kansa" Afiyah ta share hawaye tana k'ara jinjina kalmar kowa yayi ta kansa a ranta,tace "za ki san ni kika cewa kowa yayi ta kansa" ta wuce bedroom d'inta fuskarta ya yi jaa ya kumbura ta d'auka mayafinta ta had'a kayanta cikin trolley ta fita daga gidan tana waiwayensa tana sake share fuskarta. Around 2:00am Manar ta farka da matsanancin ciwon ciki,kukan da take k'asa² tana rik'e cikinta ya dawo da Waleed daga duniyar tunanin da ya tafi,da sauri ya matsa kusa da ita ya kamo hannunta yana mata sannu,yana kallonta yake tambayarta ina yake mata ciwo,ta kasa magana sai nuna masa cikinta take,da kyar ya lallab'ata ta kwanta ya matsa inda ya ajiye magungunanta da ya siyo a pharmacy d'azun sanda ya fita,ya had'a mata tea sai dai bai cika sugar ba a ciki ya bata,shi kad'ai ta iya sha kafin ya had'a allurai ya mata ya zauna gefenta ya rungumeta yana shafa bayanta yana hura mata iska a kunne,tun tana kukan kad'an² sanda ciwon ya fara mata sauk'i tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya,wani wahalallen bacci ya sake d'aukarta,kusan a haka suka zauna sai da aka fara kiran assalat kafin ya gyara mata kwanciya ya fita ya nufi masallaci,after ya fito guraren 6am ya dawo d'akin ya zauna yana gadinta,idanunsa tar a kanta yanda yaga rana haka darenma ya gansa,sai guraren 7am ta sake farkawa,but wannan karon alhamdulillah jikin da sauk'i sosai sai d'an abunda baza'a rasa ba,ya tambayeta or did she feels pain anywhere kuma? Tace a'a ba ta ji,yace idan ta ji canji ko ya ya ne ta sanar masa ta amsa shi,shi ya mata wanka saboda yanda jikinta yake ba wani kwari ya shiryata,da yake tun a jiyan ya taho mata da kayanta daga can ya biya gida ya karb'an musu abinci gurin Mother,sanda ya kwantar da ita kan gado yace "ki huta kafin su Hjy su k'araso" zai bar kusa da ita ta rik'o hannunsa tana kallonsa da pale idanunta tace "Yaya ina za kaje kai?" Ya d'an girgiza mata kai da wani cool voice yace "i'm not going anywhere Lilac,ina tare dake" d'an gyad'a masa kai tayi ta matsa masa kusa da ita tace "tou kazo mu kwanta tare,kaima ai baka huta ba" da sauri yace "no kiyi baccin ki,ba na son takura miki" b'ata rai tayi tana kallonsa hawaye cike a idonta tace "ni dai sai ka zo mun kwanta a nan" yaga rigima take nema dole ya rab'a ya kwanta kan gadon though ya musu kad'an ta wani shige jikinsa tana sauke ajiyar zuciya suka yi shiru,can da aka jima he thought ko ta yi bacci,sai ji yayi ta kira sunansa da muryar kuka,ya lumshe idanuwansa a hankali yana jin damuwa duk ta masa yawa,bai iya amsawa ba sai da yaji tana shafo fuskarsa tace "Yaya!" Ya daure duk da hawayen da suke neman zubo masa yace "uhn!" Bud'ar bakinta tace "Yaya mun yi asaran baby'nmu kou?" Kasa magana yayi saboda zuciyarsa yayi mugun karyewa,idan yace zai yi magana kuma kuka zai iya kwace masa a ko wane irin lokaci,but the way ya sake k'ank'ameta a cikin jikinsa har tsoro ya bata,nan

48 / 66