Manar Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Fatima Category :  Romance

Chapter   3 / 66

6K to 9K   out of 196.2K words

nake ba?" Shiru tayi ta k'i cewa komai sai zumb'ura masa bakin da tayi tana k'unk'uni k'asa² ba'a ji,a fusace ya kawo mata mari tayi saurin matsawa gefe tana saake zumb'ura masa baki tace "kayi hak'uri" ransa ya mugun b'aci da abunda tayi ya dunga kallonta ya kasa magana sai can da aka jima yace "surely zan gyara miki zama a gidan nan,y'ar k'arama dake baza'a fad'a miki kiji ba,wa kika haifa a nan? Waye sa'anki?" Tace "Babu kowa" yace "babu wanda kika haifa,dole ne a fad'a miki kiji,duk ranan da na sake ganin an miki fad'a kin kwasa kinje kin fad'a mata wallahi sai na sab'a miki,za ki sha mamakina ranan,ki bar ganin kina zuwa kusa da ni zane ki zanyi sai na fasa miki jiki.." Wani kuka ta kece da shi,ya mata tsawa "hey! Hey!! Be quite before i slap u" tsit tayi ya matso inda take fuskarsa babu alamun dariya yace "idan kika kuskura kika je kika fad'a mata na yi miki wani abu,billah kika bari muka had'u sai na zaneki,kin ji me nace?" Gyad'a masa kai tayi saurin yi tana zumb'ura baki,ya maka mata harara kafin ya juya ya bar gurin,k'asa² sanda ta tabbatar ya tafi tace "Allah ya isa na" then ta nufi apartment d'in tana cika,a parlor ta tarar da su yana zaune kan kujera yana danna waya,ta harari inda yake tana zumb'ura baki ta wuce hanyar bedroom,Dadda dake bawa Ameerah labarin zamansu a Saudiyya ta bita da kallo sanda taga wucewarta kamar za ta tashi sama ta kyab'e baki tace "ita kuma wannan matar ko ita da wa take k'unci ohoo?" Bai d'ago ba yace "ni ne na mata fad'a ko ban isa ba?" Kallonsa Dadda tayi saurin yi tace "akan me? Wani gagarumin laifin tayi?" Yana ci gaba da danna wayarsa yace "sai tayi laifi za'a mata fad'a?" Tsuke fuska Dadda tayi saurin yi tace "ka ga Mamman ba na son haka,ba na son sa ido,ina ruwanka da ita da za ka saka ta gaba eh?" D'ago idanunsa yayi ya mata wani kallo yace "wai me yasa kike haka ne? Shi kenan duk abunda yarinyar nan za tayi shi ne dai² baza tayi mara kyau a tsawatar mata ba? Abunda kike yi kin kyauta kenan ko shi ne dai² a na-ki ganin?" Sororo Dadda tayi ta zuba masa idanuta ta kasa masa magana,Waleed yace "Tambayarki nake abunda ya kamata ki koya mata kenan? Haka kike so taje gidan mutane tana yi?" Wani tsuke fuska tayi tace "wane gidan mutanen za taje?" Yace "kina nufin baza tayi aure bane? Ko wani ya fad'a miki za ku dawwama tare?" Washe hakor'in makkanta tayi tace "Aihooo! Ashe gidan aure kake magana.. Sha kuruminka k'afata k'afar jikata bazan tab'a yarda ta tafi ita kad'ai ba,haka kawai ina nan zaune aje a cutar min da ita na shiga uku" kallonta Waleed ya dunga yi yace "shi wanda zai auretan mahaukaci ne amma?" Da sauri ta maka masa wani kallo tace "A'uzhubillahi! Kuji min wani magana gurin wannan mutumi.. Aniya bil'aniya,aniyarka ta bika,in sha Allahu ba dai jikata ba,bakinka ya sari d'anyen kashi.. Sai dai ka auri mahaukaciya amma ba dai *ZAINAB* d'ita ba.. Sha Allahu mijin da takwarata za ta aura kaf zuri'ar mu ma babu wanda za ta samu kamarsa.." Kallonta kawai ya tsayi ba tare da ya sake cewa komai ba ya mik'e ya kama hanyar fita,ta rakasa da mugun harara tace "Allah raka taki gona,ni dama ban nemeka ba,kai ka kawo kanka ehee! Mutumi babu abunda ya iya sai fatan tsiya!" Tsayawa yayi gurin ya juyo ya kalleta yace "haka kika ce kou?" A fusace tace "na fad'a ubana sai a san yadda za'ayi da ni" gyad'a kai yayi ya juya yace "za ki neme ni da kanki" a fusace tace "ni wallahi babu abunda zaisa na nemeka,dama magana kake zuwa ka sa ni,dan ka daina zuwa dubunka za su zo" fita yayi da sauri fuskar nan a d'aure ya wuce zai nufi apartment d'insu,tun bai k'arasa barin part d'in ba ya hangota tsaye jikin window daga ita sai wani gantalallen singlet na mata fari kar da ya kama jikinta,bisa tsautsayi idanunsa suka sauka kan k'irjinta da suka d'an tasa nipples d'inta da suke nan erected sun fito sunyi rad'a² a jikin rigar babu alamun akwai wani rigar a ciki,saurin kawar da kansa yayi zai wuce ta kwalo masa kira "Yaya!" Cak ya tsayawa a gurin ba tare da ya sake kallon direction d'inta ba yace "what happened?" Zumb'uro masa baki tayi ta rungume hannuwanta a k'irji tace "kayi hak'uri!" Bai ce mata komai ba ya ci gaba da tafiya,a shagwab'e ta d'aga murya tace "to ai dai na ce ka yi hak'uri" wani mugun kallo ya waiga ya mata,idanunta suka yi rau² da gudu ta juya ta bar gurin,yana jiyo sautin kukanta ya tab'e baki ya wuce ya bar gurin da sauri. Da dare lokacin ya shigo gidan,yayi parking ya fito ya rufe motar ya wuce apartment d'insu,yana shirin shiga part d'in ya jiyo sautin kukan mahaifiyarsa da sauri ya k'arasa shiga,ganin da yayi ba ita kad'ai bace a parlon yayi sallama,mutumin dake zaune wanda a shekaru zai kai 65 years ya d'ago ya amsa masa,ganin mahaifinsa a gurin yasa shi sauke ajiyar zuciya ya k'arasa a hankali ya zauna ya gaisar da shi,cikin kuka Mama dake zaune gaban mutumin tace "ni dai gaskiya Alh ka yima matarka magana,babu ruwanta da ni a gidan nan,tayi harkarta nayi tawa,dama ba shiga shirginsu nake ba" numfashi ya sauke yace "na tambayeki abunda ya had'a ku kink'i fad'a,me kike so nayi miki kuma?" Matsar hawaye ta ci gaba da yi tace "ai ba sai na fad'a maka abunda ya had'a mu za kayi hukunci ba,ni dai kawai ka raba ni da ita" idanunsa akanta bai bar kallonta ba yace "alright! Sai a bar maganar tunda ba kya so na san abunda ya had'a ku ko?" Da sauri tace "kamar ya abarshi? Baza ka mata magana ba kenan kake nufi?" Yace "haka nake tunani" ranta a mugun b'ace tana kallonsa da idanunta da suka yi ja tace "ai dama na san haka za kace,duk abunda zai faru a gidan nan ba ka tab'a goyon baya na,kullum akayi abu ni ce mara gaskiya,kamar wata jaka ni ake laftawa laifi ko da ba ni nayi ba" wani murmushi mutumin yayi kafin ya kallo gefen da Waleed yake zaune kansa a k'asa yace "Waleed je ka kira min Aunty'n ku" amsawa yayi ya tashi ya nufi sama,yayi knocking bedroom d'in Aunty ta bud'e k'ofar,tana ganinsa tace "Waleed! Shigo mana" d'an murmushi yayi yace "dama.. Abba ne yace na kira ki" kallonsa tayi with suspicion tace "ni kuma?" Ya gyad'a kai yace "sure" gyad'a kai tayi tace "alright! I'm coming" ta koma ciki shi kuma ya sauka k'asa,ba'a jima ba sosai ta sakko tun kafin ta k'arasa inda suke take kallon Mama dake matsar idanu,ta d'auke kai ta zauna tace "ga ni Alhaji" Abba ya kalleta yace "me ya had'a ki da Hjy Asama'u?" Murmushi Aunty tayi tana kallon Abba tace "wani abu tace maka ya had'a mu?" Abba ya girgiza kai yace "i'm jist asking me ya had'a ku?" wani murmushi Aunty tayi tace "ni kam babu abunda ya had'a ni da ita,sai dai ban sani ba ko ita ka tambayeta kaji" saurin kallonta Mama tayi tace "wallahi k'arya take Alhaji" d'aga mata hannu Abba yayi saurin yi yace "ban zo kanki ba" tayi shiru tana kallonsa ranta a mugun b'ace,Abba dake kallon Aunty yace "Hjy Fatima!" Aunty tace "na'am!" Yace "i want to know me ya had'a ki da Hjy Asama'u" jimm Aunty tayi kamar baza ta ce komai ba then tace "Alhaji ni dai da ka bar maganar nan,gaba d'aya banga amfanin taso da abunda aka riga aka yisa ya wuce ba" Abba yace "ko me yasa kike so a bar maganar?" Kafin Aunty tayi magana,Mama tayi zaraf tace "saboda ta san itace mara gaskiya mana" wani kallo Abba ya juyo yana mata yace "ban ce kimin shiru ba?" Mama tayi kicin-kicin cikin jin haushi tace "amma Alhaji wannan ai ba adalci bane,kace za ka hana ni magana" Abba yace "alright! Ci gaba" ya nad'e hannunsa ya zuba mata idanu,tace "maganar gaskiya bai kamata kace za ka hana ni fad'ar abunda yazo baki na ba" Abba dake saurarenta yace "shi ne ai na baki dama ki ci gaba kou?" Tace "haka kawai ina zaune parlor ta zo ta dunga gaya min magana,ni dai ka ja mata kunne ta bar shiga harkata" kallonta Aunty ta dunga yi tsabar mamaki ma ya hanata cewa komai,sai da Abba ya kalleta yace "ke nake sauraro" numfashi ta sauke har lokacin bata yi niyyar fad'awa Abba abunda ya faru ba tace "dan Allah Alhaji kayi hak'uri ka bar maganar nan,ni wallahi ban san maganar da yasa kace nazo ba kenan" Abba yace "da kin sani baza ki zo ba?" Ta girgiza kai tace "a'a! Ya ya ma za'ayi nace bazan zo ba?" Abba yace "ke nake sauraro ki sanar min abunda ya faru" kan babu yadda za tayi ganin Abba ya dage ta fara rattabo masa jawabin kaf abunda ya faru,ran Abba ya b'aci sosai ya dunga yiwa Mama wani kallo cike da takaici yace "wato rashin zaman lafiya kike son haifar min a cikin gidana kenan? Shi yasa sai kika ga bari ki fara tara na da maganar,ina tambayarki kuma da kika san ba ki da gaskiya kika k'i fad'a" Mama tayi kicin-kicin tak'i cewa komai,ran Abba a b'ace ya dunga mata fad'a ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba sanda yayi mata tass kafin yace ta tashi ta bashi guri,b'ata rai tayi tace "ai sai dai kace matarka ta tashi kuma tunda ka san ranar girki nane yau" ajiyar numfashi Abba yayi ya lumshe idanunsa yana kiran sunayen Allah lamarinta damunsa yake yi sosai hak'uri kawai yake yi da ita musamman cikin y'an kwanakin,wani murmushi Aunty tayi ta mik'e tun Abba baiyi magana ba tace "Allah ba mu alkhairi.. Mu tashi lafiya Alhaji" tayi sama abunta zuciyarta fes,Mama ta bita da mugun kallon zan yi maganin ki mai cike da zallar tsana..


#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
©®2020.



                    *♡MANAR¸.•💥*
               


*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://t.me/joinchat/VHlmxxheyxG6m9VoUJZbZA

_Devoted to My Mamma Hjy Maryam Alhassan (Jikar Kulu)._

_Bestowed to Fateema Abdulmajid._



                                03.

#Bitterness

       
      Washe gari Friday gaba d'aya yaran gidan basa nan sun tafi skul sai Manar kad'ai dake kwance a parlor kan kujera,sanye take da wani sleeveless mai net ta wajen boobs d'inta red colour,rigan ya zauna a jikinta sosai sai short d'in wando da iyakar tsayinsa k'asan buttock d'inta kanta ko d'ankwali babu ta kafe TV da kallo,a nutse ya tura k'ofar ya shiga sanye cikin k'ananun kaya black trouser da polo t-shirt yellow,a ciki² yayi sallama ganinta ita kad'ai ya k'arasa yana d'aure fuskarsa,ta d'ago ta amsa tana sakin masa murmushi tace "Yaya! Sabahal khair" had'e rai yayi bai amsa ba yana jifanta da wani dirty look yace "wane irin iskanci ne wannan?" Kallonsa ta dunga yi bata gane me yake nufi ba ta dai zuba masa idanunta,wani tsawa ya mata yace "ba dake nake ba kike kallona?" Zumb'uro masa baki tayi cike da shagwab'a tace "to ni me nayi kuma?" Ya fara takowa inda take yace "ni kike tambaya?" K'unk'uni ta fara masa "to ai ban san me nayi ba,daga zuwanka ka fara min fad'a" hannu ya kai zai kamota tayi saurin gocewa,bisa tsautsayi ta fad'o daga kan kujeran ta buge k'afarta,uban azabar da ya ratsa kwakwalwarta yasa ta fasa wani gigitaccen k'aran da yayi calling attention Dadda dake cikin d'aki tana gyaran kaya,ganinta kawai suka yi ta fito kamar an cillota a rikice ta k'arasa ta d'agota tana tambayarta "me ya faru?" Wani kallo Waleed ya dunga mata yana jira yaji me za tace,cikin kuka bata yarda ta kalleshi ba tace "to ba Yaya bane" da sauri Dadda ta katseta tace "me ya had'a ki da shi?" Tace "ni ban masa komai ba kawai zuwa yayi zai doke ni" tsuke fuska Dadda tayi ta kalli Waleed dake tsaye yana kallonsu cike da takaici tace "dan Allah Mamman zo ka fita kafin raina ya gama b'aci" yace "na je ina?" A fusace tace "duk ma inda za ka kaje mana,ko da ni kake tambaya idan za ka fita?" Tab'e baki yayi ya wuce zai zauna,tayi maza ta sha gabansa da sauri ta fara kakkare kujerunta,cikin masifa tace "idan ba sai ka fita ba kafura uwata ta haife ni,ni dai da girmanka ba za ka zo kana sani magana ba,ko yara basa zuwa su sani magana kamar haka,sai kai gaskiya bazai yiwu ba,maza ga hanya can fita ka ba-ni guri,ko yanzu nasa a kira min Yaro" had'e rai yayi yace "matsa na wuce" a fusace tace "ka wuce kaje ina?" Yace "ki matsa na wuce nace,babu inda zanje sai na gama uzurin da ya kawo ni" wani kallo ta dunga masa tace "idan na k'i na matsa fa?" Yace "zan janyeki na wuce" mitsi² tayi da ido ta kama waistband d'inta ta rik'e tace "to janye nin muga" bata gama rufe bakinta ba ya kama hannayenta duka kamar wata y'ar tsakuwa ya matsar da ita gefe ya nemi saman kujera ya zauna yana had'e rai,wani kallo ta dunga masa tana tsaye inda ya matsar da ita ta kasa magana,bai kalli inda Manar take ba fuskarsa babu fara'a yace "ke! Je ki had'a min breakfast" zare idanu ta fara yi da sauri ta kalli Dadda tana jira taji me za tace,Dadda tayi mitsi² da idanu a fusace tace "a ina za'a maka girkin?" Yace "a nan" wani kallo ta aika masa tace "ka kawo min kayan abinci dama da idan kaji yunwa za ka kwaso k'afafunka kazo a dafa maka?" Bai kalli inda take ba yace "sai na kawo za'a dafa min,think Abba yake siya ko?" Cikin fad'a tace "da Yaron ya siya ya aiko min yace ni da kai ya siyawa ne? Naga dai bai ce saboda kai ya aiko ba da za ka kwaso jiki kazo min,kuma dai tunda ka san baka tab'a kawo min ko k'wallin shinkafar ka ba,maza ka tattara tsumman rayuwarka ka tafi gurin uwarka da kake kaima albashinka kaci a can" wani kallo ya d'ago ya dunga mata fuskarsa a d'aure,for about 3 minutes ya kasa cewa komai,sai kuma ya mik'e da sauri ya nufi k'ofa,ta rakasa da mugun harara tace "Allah raka taki gona" yana jinta ya k'i tankata ya fita dan taji haushi sai ya bar mata k'ofar a bud'e ya san ta tsani a fita ak'i rufe mata k'ofa,ta saki baki cikin takaici tayi k'wafa tace "ke! Je ki rufe mana k'ofa maza kada k'ura ya cika mana gida" tashi Manar tayi ta nufi k'ofa ta rufe ta dawo ta kwanta ta ci gaba da kallonta. Around 12pm ta fito part d'in za ta je gurin Aunty,a hankali take tafiya kamar mai counting steps d'inta,har ta kusa k'ofar part d'in ta jiyo muryar Ameerah tana kwalo mata kira,tsayawa tayi a balcony tana kallon su har suka gama fitowa daga motan,Ameerah ce da wasu y'an mata biyu da baza su wuce sa'anninsu ba,suna mugun kama da Waleed kana kallonsu za kasan they're from one mother,har suka k'araso inda take Ameerah ta fara mik'a mata hannu tana sakin murmushi suka yi musabaha,Manar tace "har kun dawo?" Ameerah tayi murmushi tace "kai sis mun dad'e fa a skul d'in tun 7am muka fita,na san time d'in ma ko juyin farko baki yi ba" murmushi Manar tayi kafin tayi magana d'aya daga cikin y'an matan da suka zo tare da Ameerah ta tab'e baki tana musu wani kallo tace "ya ma za'ayi ta sani tunda babu fuss!" D'ayar dake gefe tayi saurin karb'an zancen "dama tunda an fi ganewa a tafi wani duniyar karuwanci a b'ige da karb'ar sabil ai baza'a san komai ba,haka za azo a koma cikin duhun jahilci" dariya suka fashe da shi d'ayar da ta fara magana tace "ai ko yanzu ma sis Diyanah kada ki fitar da tsammanin kamosu aka yi aka dawo da su,basu yi niyyar zuwa ba" wacce aka kira Diyanah ta fashe da wani dariya tana rik'e ciki tace "kina nufin dai sun zama *TAKARI* kenan?" Dariya suka sake sakawa suka tafa,Ameerah dake kallonsu ranta ya mugun b'aci da maganganunsu tace "haba guys wannan ai ba yi bane,me yasa za kuna fad'an irin maganganun nan?" Diyanah tana mata wani kallo a tsiwace tace "an fad'a d'in ko akwai abunda za kiiya yi?" Ameerah ta girgiza kai tace "babu abunda zanyi but zan fad'awa Abba muddin baku daina ba" Manar dai sai cika take kamar za ta fashe ta kasa magana tsabar yadda taji maganar ya daki zuciyarta sai hawaye take ta k'ok'arin mayarwa,d'ayar budurwar ta watsoma Ameerah wani mugun kallo tace "ai dama dole ki tare mata,tunda an tab'a k'anwar uwarki.." Saurin dakatar da ita ameerah tayi "A'a Deejah kada mu kai nan,duk abunda za ku fad'a ya tsaya iya kanmu,amma kada ki kuskura ki k'ara saka iyayen mu" a tsiwace Deejah tace "idan an tab'a me za ki iya yi?" Ameerah tace "sai kin gwada zan nuna miki abunda zanyi" dariya suka sa su biyun Diyanah dake jifansu da mugun kallo tace "kin ji fa sis kamar za ta iya mana wani abu,duk fa kwad'ayi ne yasa ta shiga maganar ma" Deejah tace "ke rabu da su kwad'iyi ai mabud'in wahala,idan ma za ku hak'ura da abunda kuke da shi ku zauna ku rungumi rayuwarku zai fi muku,amma kuna biyewa waccan tsohuwar tana d'ora ku turba mara kyau,duk sai kun yi dana sani a lokacin da bazai muku amfani b.." Bata k'arasa fad'an abunda yazo bakinta ba Manar da zuciya ta zo mata iya wuya ta cakumota a masife tace "wa kike kira waccan tsohuwar?" Diyanah tana k'ok'arin matsowa ta rik'e Manar da suka fara kokawa da Deejah Ameerah ta tareta da sauri tace "dakata malama baza ku mata

3 / 66