duk dare daga shi har Manar haka suka sabar musu,ko sunyi bacci kuma ya shigo zai shiga ya gansu ya musu addu'o'i ya musu kiss sannan ya ja musu k'ofar,sanda ya nufi k'ofar fita da sauri yana cewa "bari na duba Mummy,tun safe na kula da yanayinta.." Little dake kan gadonsa gefe da gadon Alhussain yace "Daddy baka ce muzo muje tare ba" da sauri Waleed dake wani tunani a ransa yace "noo! Kuyi mata addu'ah daga nan zai isa gareta" Little yace "tou Daddy za muyi mata,Allah ba ta lafiya" Waleed ya amsa da "ameen" ya fita ya kulle musu k'ofar,a hankali ya tura k'ofar bedroom d'inta yayi sallama,Manar dake durk'ushe k'asa ta rirrik'e beddings zufa duk ya wanke mata fuska da jiki ta d'ago kai cikin wahala da azabar ciwo ta sauke idanunta a kansa,da sauri ya k'arasa kusa da ita yana mata wani kallo ya rik'ota yace "sannu Lily" kai kawai ta iya gyad'a masa,yace "za ki haihu yanzu in sha Allah" ita dai addu'o'i kawai take ja,ba ta k'arasawa zai kufce ta kama wani,sanda ya duba yaga haihuwan a kusa ya d'auketa ya wuce bathroom da ita,ya sakata cikin tube,ya durk'usa kusa da ita ya rik'e mata hannu,d'aya hannun kuma yana shafa fuskarta yana mata sannu da k'warar mata guiwa,cikin hukuncin Allah babu jimawa faya da babyn suka taho tare,k'atuwar baby girl jajir da ita tana fitowa ta tsanyara kuka,sai ga mabiyyan ma ya biyota,da sauri ya auna ya yanke cibiyan yasa clip ya mak'ale ya d'ora mata babyn a k'irjinta,ita kam nunfashi take sauke na samun salama tana jero kalmomin godiya ga Allah,ya cire mabiyyan yasa a leda da hand gloves ya nad'esu then ya juyo ya d'auki Babyn ya gogeta da Olive oil,ya had'a ruwa mai d'umi ya mata wanka sannan ya dawo ya gyara uwar y'ar itama,sanda ya gama gyarasu ya d'auko y'arsa yana rik'e da hannun Manar suka fito ya zaunar da ita bak'in gado yana mata sannu ya fita zuwa kitchen,da kansa ya had'o mata lafiyayyen abinci,yana shiga bedroom d'in ya tarar da ita rungume da sai kallonta take tana murmushi,ya zauna gefenta yana kallonsu cike da so da k'auna,da kansa ya dunga bata tana ci,sai da ya tabbatar ta k'oshi ya kyaleta,yace tayi feeding Babyn,babu wanda ya sanarma haihuwar sai da safe,nan su Ameerah suka shigo suka iske ana drama da Waleed da su Alhussain da suke son Manar ta ba su Baby yana cewa kada ta soma,haka kawai su jefar masa da y'a,Ameerah tace "haba Pappy ai kuwa ko dai kowa bai d'auketa ba ya kamata abari 3 brothers su d'auketa" nan duk yaran gidan suka fara murna suna cewa suma a basu,Waleed yace "ai kunji inda matsalar yake,ban amince a bama kowa yarinyata ba.." Ba'a son ran yaran ba,amma babu yanda za suyi dole suka d'auki hak'uri. Ranar suna yarinya ta ci sunan Zainab itama amma za suna kiranta da (Mahasin),bayan anyi hidimar suna,y'an uwa da suka zo suna duk sun koma,aka bar Manar da Baby'nta Mahasin (meanin-Beauty). Bayan wasu watanni da haihuwar,tana zaune tana feeding Mahasin da tayi wayo Waleed ya shigo d'akin da sallama,sanda ta d'aga kai ta kallesa ta amsa tana masa murmushi,ya k'araso yana sauke wani numfashi da k'ureta da kallo,ya zauna gefenta yana kallonsu cike da burgewa har ta gama feeding Mahasin da zuwa lokacin tayi bacci,tana k'ok'arin mayar breast d'inta cikin riga yayi saurin rik'e hannunta yana narke fuskarsa yace "Mummy ki barmin abuna kada ki b'oye min cikin riga,ina so nayi ta sha ina tab'a abuna" zaro idanu tayi a shagwab'e itama tace "ni dai please.." Bai bari ta kai k'arshe ba da sauri ya karb'e Mahasin ya kwantar da ita kan gadonta,sanda ya juyo ya nufo gadonsu,fuskarsa tana bayyanar da wani k'ayataccen murmushi ya k'araso inda take a hankali yace "hey girl.." Tace "hi Man" yayi murmushi yace "What's ur name?" Cikin wani irin kallo da salo tana juya masa idanu tace "my name is Zainab Muh'd Maji Dad'i" want k'ayataccen murmushi ya k'ara yi yana sakin mik'a yace "aaahhh! Lallai yau za ki tabbatar min da sunan maji dad'i.." Dariya ta kyalkyale da shi,sai kuma ta sunkuyo ta d'ora goshinta saman nasa,hancinsu yana gogan na juna tace "zan saka kuka fa" da sauri ya juyata ta koma samansa yana sauke numfashi a hankali yace "abunda nake buk'ata kenan.." Tana masa murmushi tace "ka tara ka samu.." Daga haka tayi saurin had'e bakinsu,tun daga nan har k'arshe ita tai riding d'insa,cike da nishad'i sanda suka samu nutsuwa yana rungume da ita yace "thank u Lilac.." Ta d'aga masa gira tace "alaa shuu?" Yace "for everything.." Nan ya fara lissafo mata,irin jin dad'i da farin cikin da ya samu ta sanadinta,tayi murmushi tace "Pleasing u is my only purpose in life.." Yayi murmushi mai yalwa cike da jin dad'i ya k'ara rungumeta,a haka bacci ya d'auketa,Waleed dake jin zuciyarsa cike taf da k'aunar y'ar uwarsa,jininsa,matarsa kuma uwar y'ay'ansa,it was there ya zuba mata idanu yana kallonta da tunanin lokacin baya sanda suka sha fama da Mama akan soyayyar Manar da ta addabesa,har zuwa lokacin da take fad'a masa bazai auri Manar ba in har tana numfashi,duk irin rigimar da suka yi sai da ya tuno har bakin da ta kusa yi masa,yau gashi komai ya zama tarihi,har da rabon Yara hud'u da suka haifa,wanda gaba kuma bai san nawa za su k'ara samu ba,cikin sanyi da godiya ga Allah abisa ni'imar da yayi agareshi ya sauka daga gadon ya shiga bathroom ya d'aurai alwala,bayan ya fito ya shirya banda k'amshi babu abunda yake ya shimfid'a pray mat,sanda yayi nafila ya k'ara godema Allah,kafin ya haura saman bed d'in ya sake rungumeta yana tuna maganar sayyadina Aliyu (R.A) da yake cewa "Ahbib habibaka haunan maa asaa anyakuna baghidaka yauman maa,wa'abghid baghidaka yauman maa asaa anyakuna habibaka haunan maa..." Cike da jin dad'in yadda al'amura suka daidaita ta kowane b'angare ya lumshe idanunsa yana tasbihi ga Allah da yake da ikon canja dukkan lamura,a haka shina wani irin bacci mai cike da nutsuwa,sukuni da godiyar Allah ya d'aukesa yana kwak'ume da ita a jikinsa...
*_#KARSHE..._*
#Alhamdulillahillazii bii ni'imatihi tatimmus'salihaat.. On this occasion i would like to thank Almighty Allah again for the gift he has bestowed on me,and i extend my heartfelt congratulations to my followers as well,hakur'in saurarona da kuka yi babu dare babu rana,prayers da kullum kuke min sending ina godiya sosai da sosai,and i ask Allah (S.W.T) to forgive me and u for the mistake i made in writing of this story,wad'anda na b'atawa rai kuyi hak'uri ku yafe min this is nothing but human nature,wanda yayi min na sani ko ban sani ba Allah ya zama shaida akai na yafe muku³,yan paid group d'ina,thank u very much for ur patronizing my book,fatan Allah ya sake had'a fuskokinmu da alkhairinsa.. Allah yasa watan ramadhan da za mu shiga,mu yi ibada lafiya,kuma ya zama karb'ab'b'e,Allah yasa ibadar da za muyi ya zama silan shigarmu aljannah,ameen.🤲
Zan yi kewarku sosai mutane na..😪😥
For any other problem/complain/enquiry chat via 08165726609.
*#BISSALAM...👋*
#Ur's Hawwa Muh'd Usman.
#Twitter-Jeeddahmu898.
#Wattpad Real-smasher.
#I.G realsmasher898.
#Asli Smasher.
#Oum Janan.
#Manar.
#End's Wednesday 07/April,2021. @6:10pm GMT.