Manar Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Fatima Category :  Romance

Chapter   24 / 66

69K to 72K   out of 196.2K words

yasa baki zo da naki motar ba?" Matar za tayi magana Mama tayi saurin tarar numfashinta "kuyi hak'uri dan Allah Hjy Saratu,muje ciki please" wacce aka kira Hjy Saratu ta kalli Mama tace "wallahi Hjy Asama'u ba don ke ba da ko kallon mu akace tsohuwar nan tayi ba ta iyawa,amma saboda ta samu mun mata shiru har wani magana take yab'a mana,ita a wa? Za ta kallemu ta fad'a mana magana bamu yagata ba?" Hangame baki tsofaffin suka yi wata tace "ikon Allah! Anya y'ar nan kin san darajan furfura kuwa?" Hjy Saratu cikin fusata tace "kinga Baba ban sa dake ba,ki rabu dani kafin na gaya maki magana" Dadda tace "k'awar tawa kike cema haka?" Hjy Saratu tace "an gaya mata,ko ke ba kyaleki zan ba idan kika fad'a min,dan kunga ana muku shiru sai ku nemi rainama mutane hankali.. Da Allah kuma mu wuce mu tafi inda muka fito,ko dole ne zuwa d'aukan amaryar?" Dadda ta fara sharar kwalla tana runtuma ihu,tace "yau na ga abunda ya ishi kakata laraba.. Iyayenmu suna ce mana y'ay'an k'arshen zamani,ashe basu ga komai ba yanzu ne zamanin yazo k'arshe.. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Manar dai dariya kawai take har da rik'e ciki,mother da ta shigo d'akin ta ganta jikin window tana dariya tace "ke lafiyarki kuwa?" Ta juya da sauri tana goge k'wallar data zubo mata tace "mother zo kiga Hjy!" Saurin k'arasawa mother tayi tace "me ya faru da Hjyr?" Dai² lokacin Dadda tana kurma wani uban ihu,mother ta zaro ido ta juya da sauri ta fita,Manar ta bi bayanta tana dariya,Momella dake zaune parlor ita da Aunty tunda suka ji mother ta ce baza ta d'aukan amaryar ba suka zauna nan suna hira,wucewar mother cikin sauri Aunty tace "mother lafiya kuwa?" Mother da har ta je k'ofa tace "ina fa lafiya" tayi waje da sauri Aunty da Mommella suka biyota a baya,cincirindon mutanen da suka gano tun daga nesa ga muryan Dadda sai tashi yake tana fad'a Mommella tayi saurin ratsawa tsakiyar gurin ta rik'ota tace "Hjy lafiya?" Dadda tana matso wasu hawaye tace "ina fa lafiya Hafsatu,da raina da lafiyata,ina matsayin kakar Waleed wata shegiya za ta kirani mai wanke²,idan ban hana zuwa d'aukan amaryar ba Allah tsine min,in yaso iyayenta suka gaji sai su warware auren daga kan jika na" Mommella cikin masifa tace "wace shegiyar ce tace maki y'ar wanke²?" Dadda ta nuna matan da suke tsaye gurin tace "cikinsu nan duk da kike gani babu wadda bata fad'a min magana ba iyakar iyawarta.. Fisabilillahi zanyi gayyar k'awayena ace baza suje ganin gidan Mamman ba? Shi kenan kuma daga na yi magana sai aga bak'i na,nifa bance dukanmu sai munje ba,amma ina laifi idan su k'awayen nawa sunje,ni ko Manar bata raka ni ba idan aka kwana biyu naga inda yake zaune" ran Mommella ya mugun b'aci ta dunga masifa mother dai sai hak'uri take bawa Dadda da tsofaffin,wata cikin k'awayen Mama tayi tsaki tace "kai wannan tsohuwa ba dai tijara ba" wata dake kusa da ita tace "ai ke da ganinta kin san dama masifaffa ce" mother ta kallesu da sauri tace "Hjy ku iya bakinku,kada kuga an maku shiru kuce za ku fad'awa mutane magana,bazai yuwu ku shigo har gida kuce za ku cima mahaifiyarmu mutunci ba" matar ta d'auke kai tace "toh ikon Allah" mother tace "gaya maki dai nayi,gara ki kiyaye harshenki kada yaja maki masifar da zaifi k'arfin ki.." K'arshen dai da kyar aka samu Dadda tayi shiru bayan su Mother da Aunty sun gama saka k'awayen nata a mota,Mama ta cika tayi fam ganin an bar mata mutanenta a tsaitsaye cikin fushi ta kira Abba tana kuka tace "to Alh ni dai ga-ni gida da tarin k'awayena Hjy ta tada rigima ta hanasu tafiya d'aukan amaryar,na yi magana Hafsah da su Fatima sai zagina suke,ban san me na musu ba ni dai suka tsaneni har haka.." Da sauri Abba yace "asshsha amma abu bai yi dad'i ba! Gamu nan a hanyar gidan bari mu k'araso" tace "to" tana share k'wallar kissa,ko mintuna biyar ba'a yi ba motar Abba da Daddy suka shigo gidan,ganin taron mata Daddy ya fito da sauri suka k'arasa gurin,ya kalli mother yace "me yake faruwa?" Momella tace "wallahi matar nan da ba ta son zaman lafiya za ta tada mana rikici" Daddy yace "wace mata?" Ta nuna masa Mama dake gefe tana kuka,Abba dai kasa cewa komai yayi yace "please general muje ciki" suka nufi b'angaren Dadda tare,har sunyi gaba Abba yace ma Mommella "Hafsah ku same mu b'angaren Hjy" tace "to Yaya" Dadda dai ko kallonsa bata yi ba tace "ai dai kwa bari na gama sallamar k'awayena ko?" Daddy ya girgiza kai bai ce komai ba suka k'arasa part d'inta,sanda motocin suka fara fita daga gidan Dadda da Tasallah sai d'agawa k'awayen su hannu suke suna masu Allah kiyaye hanya,suna gama barin gidan su Aunty suka wuce b'angaren Dadda,Mama kam kasa binsu tayi sai da Abba ya sake kiranta yace "Hjy ke kad'ai muke jira kin sani kuma kink'i zuwa,kin san dai duk nan babu yaronki ko bare kisa mu jiranki?" Tace "na sani Alh ga ni nan" yayi tsaki ya kashe wayarsa,Daddy ya kalleshi yace "calm down brother" kamar jira Abba yake ya fara fad'a "haba da Allah,matar nan ta gama kaini k'arshe ne,ko wane lokaci ita kenan kai k'ara,da ka fara k'ok'arin bibiyar al'amarin kuma sai kaga ita ce ba ta da gaskiya" Daddy yace "kayi hak'uri please,sha'anin ne sai ana hak'uri" shigowar Mama kanta a k'asa yasa Abba dakatawa ya dunga binta da wani kallo yace "me ya faru ne wai?" Mama ta kasa d'aga ido ta kallesu,sai da ya mata tsawa ta fara magana cikin sanyi,ya kalli Mommella yace "wai me ya had'a ku ne?" Tiryan² Mommella ta fad'i abunda ta sani,wani haushi ya ciyo Abba yana kallon Mama cikin takaici yace "baza ki canja hali ba ke dai ko?" Ta sunkuyar da kanta k'asa tana matsar ido tace "kayi hak'uri Alh" a fusace Abba yace "wane maganar banza kenan? Kullum sai dai kice ayi hak'uri,amma baza ki daina ba.. Billahillaziiy duk ranan da na gaji ki sani hukuncin da zan yanke bazai maki dad'i ba" saurin kallon Daddy Mama tayi tana share kwalla tace "dan Allah Abban Manar ka tayani bashi hak'uri in sha Allah ma haka bazai kuma faruwa ba" Daddy da yaga ta yi kalar tausayi ya gyad'a kai ya bawa Abba hak'uri,da kyar Abba yace ta bawa Dadda hak'uri,idan ita ta hak'ura to shima ya hak'ura if not kuma zai yanke hukunci mafi tsauri,Mama cikin kuka ta matsa gaban Dadda ta rik'e k'afarta tana ba-ta hak'uri,Dadda data d'auke kai gefe ta tab'e baki ta kalli Abba tace "ni dai Yaro ba don halin wannan matar ba na hak'ura,yo Allan da ya haliccemu ma muke masa laifi ya yafe bare mu,Allah dai ya yafe mu baki d'aya.." Suka amsa duka parlon,Daddy ya fara tashi zai fita,Manar dake lab'e jikin k'ofa tana ganin Daddy'nta tayi sauri ta bar gurin tana dariya. Da dare sama ko k'asa Mama ta nemi Waleed ta rasa,duka kuma layukan wayarsa a rufe babu wanda bata kira ba amma basa tafiya,lokacin Manar ta shigo gidan cikin sand'a dan tun ranar Friday bata k'ara kwana gidan ba sai yau ta shigo ta wuce d'akinsu tana zumb'uro baki,ganin babu wanda ya ganta da sauri ta datse k'ofar ta ciki ta fara tub'e kayanta za ta shiga wanka,sanda ta gama kwab'ewa pant kad'ai ne bata cire ba,kamar wanda aka ce ta d'aga kanta suka yi ido hud'u da Waleed dake kishingid'e jikin gadon ya kafeta da wani mugun kallo ko k'iftawa baya yi,k'ara ta fasa da sauri ta juya masa baya tana kare k'irjinta,ya lumshe idanunsa da k'arfi saboda har cikin kansa yaji ihunta,then ya taso a hankali yana tafiya yana layi kamar wanda yasha wani abu ya d'auko mata towel,ya k'arasa kusa da ita ya warware towel d'in ya rufa mata,hannunsa da yake nan zafi zau yana tab'a jikinta tayi sauri d'agowa a rikice ta rik'o hannun nasa tana matsawa da tambayarsa "Yaya me yake damunka jikinka ya yi zafi?" Da sauri ya dafa bango,ta sake matsawa kusa da shi ta rik'e hannunsa tace "Yaya me yake damunka wai?" A hankali yace "i'm feeling cold" zaro ido tayi tace "Yaya fever ke damunka?" Ya d'aga mata kai,ta d'ora hannunsa kan shoulder d'inta tace "sannu.. Rik'e ni to muje na rakaka ka zauna" da kyar ya dafata suka je bakin gadon,ya zauna yana mayar da numfashi da kyar,ta juya za ta fita ya kirata "Manar!" Da sauri ta dawo kusa dashi tace "gani Yaya" yana rik'e da kansa da yake jin ya yi masa nauyi yace "help me please kije d'akina ki kawo min kaya" tace "Yaya to ka bari na kawo maka magani kasha ka ji?" Yace "no fara kawo min kayan nasa" kallonsa ta dunga yi cike da tausayi tace "Yaya ka ci abinci?" Ya girgiza mata kai yace "no! Ki samo min black tea" wani kallon tausayi ta dunga masa kamar za tayi kuka tace "to" ta juya da sauri bayan ta d'auki hijab cikin kayanta ta sa ta fita daga gidan..


#Thanks for the prayers,Allah k'ara zumunci... Mama ta ce a maku godiya y'an gayyar sod'i..😷😁


#Share pls.
#Asli Smasher.
22...





*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*


*Subscribe and read happily without feeling any guilt.. It's ₦200 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman,Access Bank or MTN recharge card/VTU and then show ur evidence of payment through my whatsapp account 08165726609 to be added in the paid group.*





Part d'insu ta shiga,cikin sand'a ta wuce kitchen ta had'o masa abinci da tea d'in da yace mata,ta had'a komai cikin basket ta d'auka ta fita,tana tsintar kanta balcony da ta tabbatar babu wanda ya ganta tayi ajiyar zuciya ta kulle k'ofar a hankali,ta juya za ta tafi kenan taga Azaan tsaye yana kallonta,tsabar tsoron da taji sai da zuciyarta ya bada wani rass ta daure tana masa murmushi tace "Yaya! Barka da dare" ya amsa yana kallon hannunta da take b'oyewa cikin hijab yace "Guddi what are u hidden?" Ta sake yin baya da hannunta tace "ni ban b'oye komai ba" yace "really?" Ta gyad'a masa kai,yace "mmm! Fito dashi muga" girgiza masa kai tayi da sauri bata tsaya ba tayi gaba tana zumb'uro baki tace "i said babu komai fa" tsabar mamakinta yasa shi kasa tafiya sai da yaga shigarta gidan Dadda then ya juya yana tafiya a hankali cikin compound d'in,ta tura k'ofar parlon a hankali ta rufe tana satar kallon k'ofar Dadda ta shige,a zaunen da ta barsa a haka ta tarar da shi k'afafunsa a k'asa ya rik'e kansa da hannu biyu,ta k'arasa ta ajiye basket d'in tace "Yaya.." Bai iya amsawa ba sai da ta zuba masa black tea d'in a cup tace "ga shi Yaya" a hankali yace "ajiye zan d'auka" ta dunga kallonsa kafin tace "zai yi sanyi ai" yace "ina kayan da nace ki kawo min?" Tace "yanzu zanje na d'auko" ya bud'a idanunsa kad'an ya d'ago ya kalleta,yadda tayi da fuskarta kamar kana mata magana za ta kece da kuka,ya d'auke kansa ya zuba idanunsa akan cup d'in tea data ajiye masa,sympathetically take kallonsa tace "sannu.." Ya d'an gyad'a mata kai kad'an yace "thank u" then ya d'auki cup d'in ya rik'e a hannunsa,Manar dai sai kallonsa take tana jera masa sannu,yace "je ki kawo min kayan please" tashi tayi za ta fita,har ta je k'ofa ta waiga tace "wanne zan kawo maka?" Yace "anyone ki kawo min" ta juya ta fita da sauri,har ta shiga gidan babu wanda suka had'u da shi,ta bud'e d'akinsa ta shiga,though ba yau ne karo na farko da ta fara shiga d'akin ba haka nan ta tsaya k'arema d'akin kallo kafin ta d'aga k'afarta ta nufi press d'insa ta bud'e ta ciro masa wani milk d'in yadi sai hula da takalmi,ta tsaya kad'an tana tunani kafin ta juya ta bud'e k'ofar ta fita,dai² lokacin Azaan yana bud'e k'ofar d'akin Amaar zai shiga,suka had'u a corridor d'in ya kalleta ta kallesa,bai dai ce mata komai ba ta wucesa ta sauka k'asa tana zumb'uro baki ya bita da kallo,sanda ta kai masa ya d'ago ya kalleta yace "ina singlet da gajeren wando?" Ta kalleshi da sauri tace "Yaya ba akwai wasu a jikinka ba?" Ya girgiza mata kai yace "ki kawo min wasu" haka ta koma duk a sad'ad'e saboda tsoron gamonta da Mama ta d'auko masa ta had'o masa da magani,bayan ta kawo ta fita parlor ya gama shiryawa yana fitowa ta d'aga kanta ta kallesa duk yayi wani iri,bai kalleta ba yace "good night Baby!" Da wani sanyayyan murya kamar wanda dai yake jira ta bashi umarnin kada yaje ko ina,kanta a k'asa tana wasa da fingers d'inta tace "baza ka ci komai bane?" Yace "no i'm ok" da kyar ta iya gyad'a masa kai tace "Allah tsare hanya.." Ya kalleta kad'an kafin ya amsa ya nufi hanyar fita zuciyarsa duk a cunkushe yana jin babu dad'i,bai iya jira ya yiwa kowa sallama ba ya bar gidan,da kyar bayan tafiyarsa ta iya tashi daga gurin ta shiga d'akin,ta tarar da kayansa da ya cire a kan gadon,ta k'arasa ta d'auke ta nad'e su taje ta saka cikin kayanta,tunda ta koma d'akin ta kasa zaune ta kasa tsaye,ta kalli k'ofa ya fi a k'irga,ta tsaya jikin window ta fara kukan da ita ma bata san dalilinsa ba,wani tuk'uk'i taji zuciyarta na mata,tana ta tsaye har bayan kusan minti goma then ta dawo ta haye gadon ta kwanta tayi shiru tana ajiyar zuciya,gaba d'aya ta rasa tunanin da za tayi. Tun daga ranar gaba d'aya gidan suka dena ganin dariyarsa,duk mutum idan yayi aure ana ganinsa cikin farin ciki shi kam sab'anin haka ya kasance,kullum fuskarsa a d'aure babu alamun dariya,ko gidan ya zo ma ba ya wani jimawa yake tafiya,ko daga gurin aikinsa ma idan ya tashi wucewa kawai yake saboda Mama ta kafa masa sharud'anta na babu gaira bare dalili,idan ka ga ya shigo gidan ya jima sai dai idan b'angaren Dadda yaje ta rik'esa da surutu. Cikin haka lokacin JSCE d'in su Manar ya gabato,ranar da suka fara exam sosai yazo musu da sauk'i saboda lesson teacher d'insu kusan duk ya koya musu abubuwan da za su fito exam din,so shi yasa duka lokacin suka mayar da hankalinsu kan karatu ita da Ameerah dan ko wayoyinsu ma Dadda suka bawa ajiya suka ce sai sun gama exam ta basu,a hakan suka gama,bayan fitowar exam suka wuce S.S 1,inda aka kai su science class ita da Ameerah,su Deejah kuma commerce,wata ranar Friday sun taso skul lokacin da yake ana kwad'a rana suna shigowa gidan around 12am sai ga motar Waleed ta shigo a bayansu,driver ya yi parking suka fito ita da Ameerah za su wuce gidan Dadda,Waleed ya fito motar,Manar ta kalleshi idanunsa a kanta ta sunkuyar da kanta a hankali tace "ina wuni?" Ya amsa fuskarsa a d'an sake unlike before,daga d'aya gefen Afiyah ta fito cikin tsadadden lace d'inta sea green ta yafa red d'in mayafi da takalminta mai tsini da jakarta duk kalar mayafinta,kallo d'aya Manar ta mata suna had'a ido ta d'auke kanta tak'i gaisheta,Ameerah ta gaida ta kafin suka wuce abunsu tana k'ara kallon Manar,su Deejah suka tsaya suna ihun murna suna fad'in "ga in-law²" shi kam Waleed tuni yayi cikin gidansu ya barsu tsaye a compound,Afiyah da tsaf ta gane su Manar da suka wuce,ta kalli Deejah tace "wai wancan ma k'annen D ne?" Diyanah tace "wa kike nufi Aunty'n mu?" Afiyah tace "su duka'' Diyanah tace "Ameerah dai step sister mu ce,ita kuma wancan d'ayar cousin d'inmu ce,Daddy'nta ne k'anin Abbanmu" wani damm k'irjin Afiyah ya bada saboda bata manta kallon da Manar ta mata ba kafin ta wuce,tace "dama ba Mamar ku d'aya ba duka?" Deejah ta girgiza kai tace "haba dai su uku fa duka sa'anni ne da Diyanah,ni ce na girme su da 2 yrs" Afiyah tace "really?" Deejah tace "yeah! Da yake ni lokacin da Mama ta haife ni ba ni da lafiya sosai,shisa sai ba'a kaini makaranta ba da wuri sai da za'a sa su,kuma ko lokacin ma Abba cewa yayi a barni har na k'ara samun sauk'i Mama tace a'a,shi ne aka had'a mu duka aka kaimu class d'aya,so bayan mun gama primary kuma shi ne ita sai bata ci gaba ba,grandma d'inmu tasa rigimar sai su Abba sun biya mata kujeran Saudiyya,tana so taje neman kud'i kamar yadda k'awarta ta tafi,shi ne da za ta tafi sai ta tafi da ita,da Mama tana ba mu labari lokacin ta ce ba k'aramin rigima aka yi ba,Dadda ta dage sai ta tafi da ita,k'arshen da kyar su Abba suka hak'ura suka barta ta tafi da ita.." Gyad'a kai Afiyah tayi tace "okay!" Suka wuce tare cikin gidan,a parlor suka tarar da Mama ta sakko tana ganin Afiyah ta tafi hannuwanta a bud'e tana fad'in "oyoyo daughter-in-law" Afiyah ta k'arasa suka rungume juna da Mama,Waleed dake sakkowa lokacin tare da Aunty ya d'auke kansa yace "Mama na je gurin Dadda daga can zan wuce masjeed" Mama tace "alright! Za ka dawo da wuri ne?" Ya girgiza kansa yana kallon agogon wrist d'insa yace "a'a zan lek'a hospital daga can" ta amsa tace "to a dawo lafiya.." Ya amsa yayi hanyar fita without ya kalli direction d'in da Afiyah take yace mata "sai na dawo" a k'arshen throat,saurin tashi Afiyah tayi tana kallon Mama tace "Mama bari na bisa mu gaisa da kaka" Mama ta wani washe baki tace "to sai kun dawo" Waleed da har ya saka k'afarsa waje ya juya ya mata wani kallo yace "da baki yi niyyar zuwa ba sai da zan fita?" Bata kulasa ba ta wucesa ta fita,yayi k'wafa ya juya ya fita,yana kallonta tayi gaba yak'i ce mata komai sai da ya kai apartment d'in mother ya k'arasa balcony ya tsaya,Afiyah da tayi gaba ta waigo ta hangosa balcony d'aya gidan,da mamaki sosai a fuskarta tace

24 / 66