Manar Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Fatima Category :  Romance

Chapter   13 / 66

36K to 39K   out of 196.2K words

ko kallo bai isheta ba ta ci gaba da cin dankalinta,ya kalleta ya wuce ba tare da ya yi magana ba,a zaune ya ganta Aunty a kusa da ita tana mata fad'an ta daure ko tea d'in ta sha,ita dai sai kuka take ta k'i sha,ya k'arasa ya ajiye ledan hannunsa kan bedside drawer,ya kallesu fuskarsa a d'aure yace "Aunty ajiye kawai ki rabu da ita,idan taji wahala za ta sha" Aunty ta d'aga kai ta kalleshi then ta ajiye cup d'in ta nufi hanyar fita,Manar tana ganin za ta fita ta fara kuka,Waleed dake had'a allura ya mata tsawa yace "hey! Hey!!" Da sauri ta sauke k'afarta k'asa za ta mik'e,ya ajiye syringe d'in hannunsa ya rik'ota,da k'arfi ta kwala wani uban k'ara tana kiran Aunty da Dadda,Allah ya taimakesa muryarta bata fita da tuni ta tara masa jama'ah,ya fizgota ya matse sosai a jikinsa yana fad'in "shhhiii" turesa ta dunga yi tana son k'wacewa,da yaga ta k'i tsayawa ya d'aure fuska ya mata tsawa,babu shiri ta nutsu,ya saketa ya nad'e hannuwansa a k'irji ya zuba mata idanu cikin tsare gida yace "kin wuce kin d'auka kin shanye ko sai na gaura miki mari" yadda taga fuskarsa babu alamun wasa da sauri ta juya ta d'auki cup d'in ta kafa kai,duk zafin shayin bata ajiye ba sai da ta shanye tas ta ajiye cup d'in tana hawaye,ya maka mata harara yace "Oyah! Turn around" jin ya yi magana ta tsaya kallonsa ba tare da ta gane me yace ba,sai da ya sake mata tsawa yace "juya nace.. Ki bar kallona" da sauri ta juya tana runtse idanunta,ya d'auki syringe d'in ya gama had'a alluran ya matsa inda take,tayi masa k'ik'am tak'i d'aga rigar sai da yace "Uhn! Kina jira na d'aga miki rigan?" Idanunta a kulle ta janye rigarta sama da sauri,siraran k'afafunta farare tas masu yalwar gashi suka bayyana,a hankali ya dunga bin jikinta da kallo sanda ya kai idanunsa dai² buttocks d'inta a hankali ya runtse idanunsa ya kai hannunsa da niyyar janye red colour d'in pant d'inta ta saman hannunsa ya tab'a jikinta,kamar wanda wuta ta ja da sauri ya janye hannunsa a gurin yana fitar da wani wahalallen numfashi,ya ware idanunsa akan bayanta,idanunta a rufe tana jira ya gama ta ji shiru,a hankali cike da tsoro duk da muryarta ba ta fita tace "Yaya!" Kasa amsawa yayi duk da he clearly heared her,ta sake cewa "Yaya" sanda taji ya k'i mata magana muryarta tana rawa tace "Yaya na zauna? K'afafuna sun rik'e" ya ja numfashi ya fesar a hankali yace "stay still" da kyar ya daure ya mata alluran,sanda ya tsira bata ji zafi ba,sai da ya zare ta kuwa fasa masa kuka,da sauri ta juya ta fad'a jikinsa,yace "sake ni ki murza gurin" a shagwab'e duk ta k'ank'amesa tace "ni ka murza mun bazan iya ba" jikinsa duk ya mutu da kyar ya kai hannunsa gurin ya fara mulmula mata,ta kulle idanunta da k'arfi tace "assshhh! Yaya da zafi kake min fa" da wani murya mai nuni da mutum baya cikin hayyacinsa yace "oohh! Sorry" taji yana sake cuddling nata jikinsa kuma was vibrating a little,da sauri ta tureshi tace "Yaya!" Ta koma bakin gadon ta zauna tana zumb'uro masa baki,bai iya ce mata komai ba ya juya da kyar ya kwashe kwalbar alluran ya fita. Hjy Dadda zaune a parlor ita da Abba da Aunty suna magana,ya fito zai wuce Abba ya kirasa,bai iya amsawa ba ya tsaya because ya san dole a ganosa,Abba yace "ka gama ne?" Yace "ehh Abba" Abba yace "ina wayarta daka karb'a?" Idanunsa a k'asa yace "suna can gida" Abba yace "ka d'auko ka kawo min" ya amsa ya fita ransa a b'ace,bai dawo ba sai da yayi wanka ya shirya,ya shigo parlon sanye cikin k'ananun kaya ya tarar da Dadda ita kad'ai tana goge²,ba tare da ya kalli inda take ba ya wuce ya nufi hanyar d'aki,ta d'aga kai ta bisa da kallo tak'i kulasa,da ya shiga yaga tana bacci bai tsaya ba ya fito,ya kalli Dadda dake aikinta tana wak'e irin na mutan da,ya tab'e baki yace "Abba fa?" Kamar tana jira ya yi da ita a fusace tace "yo Allah na tuba shi Yaron asararre ne da zai ta zama yana jiranka kamar wani kai ka haifesa?" Bai tanka ta ba ya nufi k'ofa yana fad'a mata dosage d'in maganin Manar,yana gamawa ya sa kai ya fice. Manar tana jin fitarsa ta bud'e idanunta tana hararan k'ofa,ta zumb'uro baki ta tura hannunta k'asan pillow ta d'auko wayar da Ameerah ta kawo mata kafin ta tafi skul,number Azaan kad'ai ne a call log tayi dialing ta fara kiransa,yana ganin kiran ya katse ya kira back,ta d'auka ta kai wayar kunnenta,a hankali tace "Yaya!" Yayi still jin muryarta kamar mai rad'a yace "Baby! Ya kike?" Tace "lafiya lao" jin ta sake masa magana a haka yace "me ya samu muryanki naji shi haka?" Hawaye suka fara kawowa idanunta ta kai hannu ta share tace "ba ni da lafiya" yace "Subhanallah! Me ya sameki?" Da muryar kuka² tace "zazzab'i da ciwon kai" yace "eyyahh sannu! Allahu k'ara lafiya" tace "ameen!" Yace "kin yi kuka da yawa ko?" Ta gyad'a kai kamar yana kusa da ita a shagwab'e tace "to ba Yaya ne yasa nayi ba" yace "me yasa kika yi?" Tace "kukan" yayi shiru yana tunani kafin yace "me kika masa? Na san maybe kin masa laifi ko?" Ta girgiza kai tace "ni fa ban masa komai ba" yace "no! Tell me the truth" zumb'uro baki tayi tace "nifa banji me kace ba" yayi murmushi yace "fad'amin gaskiya nace" ta kyab'e baki tace "to ba wayana daka sa a k'ara kawomin ya kuma kwace min ba" murmushi yayi yace "shi ne yasa kika yi kuka?" Tace "ehh!" A shagwab'e irin yadda sakarkarun yara keyi,yayi murmushi yace "anya baki masa laifi ba baby?" Tace "nifa ban masa komai ba,shi ne dai yake takura ni" a hankali ya lumshe idanunsa yana tuno lokacin yarintarsu,rashin jituwarsu da fad'an da suke akan Manar tun sanda ya zo Nigeria,haka komai ya dunga dawo masa fresh kamar yanzun yake kan faruwa,taji ya yi shiru bai ce mata komai ba tace "Yaya" a hankali ya bud'e idanunsa yace "Na'am! Guddi (absolute beauty)" zumb'uro baki tayi tace "me kace?" Ya dafe forehead d'insa yace "sorry baby! Ba wani abu nace ba" tace "amma ai ka yi magana" yayi murmushi yace "na manta abunda nace ko za ki tuna min?" Ta tab'e baki tace "me zan tuna maka?" Yace "abunda kika ji na ce" tace "to ni na ji me kace ne?" Yace "okay! Tunda baki ji ba shi kenan" kulle idanunta tayi a hankali tace "Yaya bacci zan yi" yace "ok! Sleep tight,Allah kara sauk'i" ta tab'e baki bata amsa ba ta fara kashewa. Da dare Waleed ya dawo a gajiye ya samu Abba zaune a parlor yayi sallama,Abba ya amsa yana kallonsa bai ce masa komai ba,Waleed yace "barka da hutawa Abba" yace "yawwa! Ka dawo?" Yace "ehh Abba!" Abba ya gyad'a kai yace "ya aikin?" Yace "alhmdllh" Abba yace "ina maganar da muka yi da safe?" Kansa a k'asa yace "na je can ban sameka ba" Abba ya d'ago yana kallonsa yace "ya za'ayi ka sameni dama,ko kuwa zanyi ta zama ina jiranka?" Ya sake yin k'asa da kansa yace "i'm sorry Abba" d'auke kai Abba yayi yace "je ka kawo min kada ka b'atan lokaci" d'agowa yayi kad'an ya kalli Abba then ya tashi ya haura sama,ya bud'e bedroom d'insa ya shiga,a inda ya ajiye nan ya gansu ya d'auko yana fitowa Mama ta fito daga bedroom d'inta ta bisa da kallo tace "yaushe ka dawo?" Bai tsaya ba yace "yanzu na shigo" ta gyad'a kai ta biyosa tana tambayarsa office yace "alhamdulillah" ta k'arasa kusa da Abba tana fad'in "sannu da hutawa Alh" yace "yawwa!" Ba tare da ya kalleta ba,Waleed ya k'arasa ya zauna k'asa kan rug yace "ga shi Abba" kallonsa Abba yayi yace "kaje ka mayar mata abunta,daga yau kuma idan ka san ba kai ka sai mata ba kada ka sake ganinta da abunta ka gwada mata fin k'arfi.. Ka ji me nace?" Ya gyad'a kai yace "in sha Allah" Abba ya d'auke kai ya ci gaba da kallon news d'insa,Mama dai sai kallonsu take bata fahimci komai ba har Waleed ya tashi ya nufi k'ofa zai fita ta bisa da kallo tana kallon hannunsa mamaki duk ya hanata cewa komai. A ciki² yayi sallama ya shiga,Dadda dake zaune ta d'aga kai ta bisa da kallo,ya zauna kan kujera fuskarsa a d'aure yace "ina yini?" D'auke kai tayi itama kamar an mata dole ta amsa tace "lafiya" ya dunga juya wayan da d'ayan dake cikin kwali kafin da kyar ya daure yace "ina yarinyar nan take?" Dadda tayi kamar bata jisa ba,ya kalleta ya tabbatar ta jisa,haushi yasa shi mik'ewa ya nufi hanyar d'akin,a kan gado ya ganta ta juyawa k'ofa baya,ya taka cikin d'akin bai yi magana ba sai da yaje kusa da ita ya kai hannu ya yaye bargon data rufa,still tak'i motsawa ya kai hannunsa ya d'agota ta bud'e idanunta da sauri tana zumb'ura baki tace "Yaya meye haka bacci fa nake ka tashe ni" ya kalleta yace "yaushe kika fara baccin?" Tace "yanzu" sake kallonta yayi sosai fuskarta babu alamar ta fara bacci yace "da kika ji shigowata ko?" Ta b'ata rai ta k'i kallonsa,ya mik'a mata wayoyinta yace "take" d'aga kai tayi ta kallesa,yace "karb'i nace ki bar kallona" ta karb'a tana b'ata rai,har ya juya zai fita ya waigo yaga shi take kallo,ya d'aure fuskarsa yace "kiyi duk yadda kike so kin ji?" Tana kallonsa ya sa kai ya fice gaba d'aya daga apartment d'in" sanda ya koma gida,yana shiga yayi hanyar sama Mama ta tashi za ta bisa Abba ya d'aga kai ya kallesu gane nufinya yasa Abba ya kirasa ya amsa ya dawo,Mama ma ta tsaya gurin taba jin kamar ta dawo,ganin kallon da Abba yake mata yasa tayi sama cikin jin haushi,ya zauna kusa da k'afar Abba yace "here i'm Abba" Abba ya ajiye remote d'in hannunsa yace "wane magana muka yi da kai kwanaki?" Waleed yayi squeezing fuskarsa yana tunani,Abba yace "ka manta?" Ya girgiza kai yana sauke ajiyar zuciya yace "a'a Abba" Abba ya gyad'a kai yace "to ya ake ciki?" Waleed yace "Abba ai kai kace za kamin magana idan ka yi tunani,and i thought ko da naji baka ce komai ba an fasa ne" Abba yace "ba'a fasa ba" Waleed yace "to Abba yanzun ya za'ayi?" Abba yace "na yi magana da Aunty'n ku,ta ce min suna hanya k'arshen shekara,and she said shawararka mai kyau ce" yayi murmushin gefen baki duk da ba ya cikin mode d'in yin hakan,Abba yace "ina ga gobe idan Allah ya kaimu ka d'auketa kuje makarantar su Ameerah,duk abunda ya dace kayi" ya amsa da "toh Abba" sun d'anyi maganganu sosai kafin Abba ya sallameshi ya tashi ya haura sama zuciyarsa fari tas,yana bud'e bedroom d'insa ya shiga Mama ta fito ta biyo bayansa,ya juya da sauri jin an shigo idanunsa suka sauka kan Mama dake masa wani kallo,ya juya ya zauna ta k'araso tace "Waleed wayar waye na gani a hannunka?" Kai tsaye tace "na Manar ne" wani kallo ta dunga masa tace "Manar?" Ya d'auke kai bai ce komai ba,tace "me ya had'a ka da kayanta? Ban hanaka shiga shirginta ba?" Ya d'ago da sauri zai yi magana..


#Babu voting sosai,idan ba kwa jin dad'in labarin ya kamata na sani.


#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
©®2021.




                    *♡MANAR¸.•💥*
               



*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://t.me/joinchat/VHlmxxheyxG6m9VoUJZbZA  

_Devoted to My Mamma Hjy Maryam Alhassan (Jikar Kulu)._

_Bestowed to Fateema Abdulmajid._



                                12.

#Rede..

     Tsawa ta masa,idanunta gaba d'aya sun kad'a sunyi jaa tace "ka rufe min bakinka a nan gurin.. Kada ka kuskura ka furta ko wane irin kalma" kamar yadda ta buk'ata yayi shiru ya sunkuyar da kansa k'asa,cikin masifa tace "waye ya ba-ta wayar?" Bai d'ago kansa ba yace "Azaan" ta dunga kallonsa tace "wane Azaan d'in? Mutumin da ba ya k'asar" ya d'ago da sauri ya kalleta zai yi magana a fusace tace "ka san ba zan tab'a yarda ba ko?" Yace "why not Mom?" Cikin masifa tace "ni za ka rainawa hankali Waleed? Munafurcinka kuma wanne ne ban sani ba?" Girgiza mata kai yake yace "Mama!" Ta sake masa tsawa here ta dunga sirfa masa ruwan bala'i sanda tayi iya yinta ta gaji tace "billahillaziiy idan baka mayar da hankalinka jikinka ba za mu samu sab'ani da kai" shi dai ya mata shiru,tsabar mamakinta gaba d'aya ya kasa ko bata hak'uri dan kanta da ta gaji tace "tunda ka iya siya mata kace ba kai bane su kuma k'annenka fa?" Ya d'ago yace "Mama na fad'a miki fa ni ban siya mata waya ba" tace "dallah rufe min baki ni za kawa k'arya?" Ya d'auke kansa ransa a b'ace,tace "ni dai na fad'a maka ka fita harkar yarinyar nan,idan ba haka ba kuma duk abunda ya faru kayi kuka da kanka" ta juya ta nufi k'ofa tana ci gaba da bambamin fad'a,ajiyar zuciya ya dunga saukewa bayan fitarta,ya rik'e kansa da yake jin yana sarawa da hannuwansa biyu,ya jima a zaune yana tunani kafin ya tashi ya rage kayan jikinsa ya shiga bathroom,yana fitowa ya shirya ya d'auki keys d'insa yayi waje fuskarsa babu annuri,kafin ya k'arasa parking space Manar ta fito daga gidan tana tafiya kamar tana counting steps sanye cikin wani red colour d'in riga,hancinta ta mak'ala masa ring shaped d'inta,kallonta ya tsaya yi musamman lips d'inta da suka sha red colour chapstick,ya lumshe idanunsa a hankali yana jin wani irin yanayi yana mamaye jikinsa,yana bud'ewa suka had'a ido ta zumb'uro masa baki ba tare da ta kulasa ba,harara ya maka mata ya d'auke kansa ya k'arasa gurin motar ya bud'e zai shiga,gigitaccen ihun da tayi yasa shi fasawa da sauri ya saki murfin motar ya nufi inda take,ganinta a durk'ushe ya kai hannu zai tab'ata tayi sauri ta d'ago,mamakin abunda ya gani yasa shi zuba mata idanu ya kasa mata magana,ta tashi tsaye tana karkad'e rigarta ya d'aga kai ya kalleta,a hankali ta fara tafiya tana barin kusa da shi ta masa gwalo ta fashe da wani dariya,sakin baki yayi yana kallonta ya kasa mata magana,haushin raina masa hankalin da tayi yasa shi mik'ewa a fusace zai rik'ota,tana gama karantar abunda yake niyyar yi ta fella a guje,da yaga haka kawai sai ya tsaya kallonta yadda take gudun k'afafunta kamar za su tsinke ya fi komai basa dariya,ya dunga kallonta daga inda yake yana darawa,sanda ta kai balcony kafin ta tsaya tana maida numfashi,kamar ance ta waiga ta hangoshi a inda ta barshi,ya nad'e hannuwansa a k'irji yana kallonta,ta bud'e idanunta sosai tana kallonsa,dariya yayi mata wanda ya bayyana hak'oransa,ta dunga kallonsa daga inda take cike da mamaki duk a tunaninta ya biyota ne,yayi mata wink kafin ya juya ya shige motarsa ya bar gidan yana sakin murmushi. Har ya fita bata matsa daga gurin ba,Ameerah ta k'araso gurin ganinta tsaye ta zubawa get idanu ta dafa shoulder ta kafin tayi mata magana Manar da hankalinta baya tare da ita jin an tab'ata ta daddage ta kwalla k'ara,Ameerah ta koma baya da sauri a tsorace tace "dallah meye na ihun,ni ce fa kika wani b'are baki" harararta Manar ta juya tayi tace "kuma sai ki tsorata ni?" Ameerah ta kyalkyale da dariya tace "ke dai kin cika tsoro wallahi daga d'an tab'akin nan har kin tsorata" ta harareta tace "ban sani ba" ta wuce ta shige gidan. Tuk'i yake bayan fitarsa amma da ya tuna gudunta sai ya kad'a kai yayi murmushi,cike da nishad'i ya tsaya wani eatry ya siya abunda yake buk'ata ya fito,a hanya ya sake tsayawa wani bakery ya siya ice creams then ya juya kan motarsa ya nufi gida,yayi parking yana kallon apartment d'in yayi murmushi ya fito ya d'auko ledojin ya wuce part d'in Dadda,a parlor ya jiyo maganarsu ya k'arasa ya bud'e k'ofar yayi sallama,Manar tana jinsa ta waiga suka had'a ido,da sauri tayi zumbur ta mik'e za ta kwasa a guje,ya d'aure fuska ya d'auke kansa,ta dunga kallonsa sanda ya k'arasa shigowa ya zauna yana kallon Dadda da tak'i kallonsa,yayi wani murmushi cike da tsokana yace "wai fushi kike yi har yanzu?" Kamar mai jira tace "a'a dariya nake" ya gyad'a kai yace "ohooo! Thought fushi kika yi na rarrasheki" wani kallo ta masa tak'i tankasa,ya tashi ya nufi kitchen ya d'auko plates biyu ya dawo,ta d'aga kai ta bisa da kallo tana jira taga me zai yi,ya koma inda ya taso ya d'auki d'aya a cikin ledojin da ya shigo da su ya ciro coil paper da akayi wrapping ya warware,Manar dake tsaye ta zuba masa ido tana jira taga me zai fito da shi,kamar ya san me take ya d'ago ya had'e rai,ta b'ata rai itama ta wani d'auke kai kamar ba kallonsa take ba,yayi murmushi a ciki ya bud'e,zazzafan k'amshi ya cika gurin,ya juye ya ciro ice creams manya biyu daga d'ayan ledar da wani fura dake cikin roba shima,plate d'aya ya d'auka ya kai gaban Dadda da robar furan ya zauna yayi flexing legs d'insa ya d'auko yankan hanta d'aya yace "bud'e bakinki na baki" ta kalleshi ta kalli plate d'in hantar tayi murmushi tace "Allahu akbar.. Allah jik'an Malam ya masa rahama" Waleed yayi murmushi yace "ameen Hjy ta.." Tace "lokacin yana raye sai abunda nace ina son ci.. Dan wannan hantar kuwa ai sai na ture faranti" murmushi ya sake yi ya gyad'a kai yace "muci to sai ki ba-ni labari" tasa hannu ta fara ci,Manar dake tsaye ta tab'e baki ta juya za ta bar gurin Waleed ya kalleta ta gefen ido bai mata magana ba,sai da ta shige ya tab'e baki ya d'ago yace ma Dadda "ita wancan ba ta ci ne ta shige d'aki?" Dadda ta girgiza kai saboda dad'in dake hauramata cikin ka,sai

13 / 66